Join Our WhatsApp Group

EZNAH Complete Hausa Novel Document by EZNAH


EZNAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 59129



EZNAH

Reading Time: 4 Hours

Added On: 23, Mar 2024

Author: Mamuh Gee ,

Ebook Compiler : Umar Dalha Funtua

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 906 044 6461‬

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 352.83 kb

File Type: txt

Views: 232+

Download: 417+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: Compiled By Umar Dalha Funtua.

[9/7, 9:46 AM] ‪+234 906 044 6461‬: *_EZNAH_*🌹
  _wattpad@mamuhgee_



*1~5*
Bismillahir-rahmanir Raheem.


Dattijo ne 'dan kimanin shekaru hamsin zuwa sama fari sol dashi Wanda kallo 'daya zakayi Masa ka tabbatarda cikakken bafulatani ne,

Zaune yake kan tabarma a tsakar gidansa Yana kallon Mai 'dakinsa cikin farin cikin yanda take gyaran shinkafar daya siyo Dan kawai a girkawa  'yar gaban goshinsa abincin tarbanta na dawowa daga makaranta data share watanni acan.

Da sallama wani 'dan madaidaicin saurayi yashigo hannunsa riqeda baqar Leda ya miqawa innarsu Yana cewa,

Baffa wlh yau kifi yayi wuya daqyarma nasamo wannan 'din sauran abari gobe da sassafe kafin su iso nakoma nagani ko za'a samo.

Fuska cikeda annuri baffan yace,

Ba komai jafar wannan 'dinma zai Isa tunda goben nace aliyu ya Kama kaza biyu ya yanka Mata taci iya cinta.

Girgixa Kai inna tayi cikeda mamakin baffan akoda yaushe da baya iya danne fificin soyayyar  _*ANANO*_ acikin ransa duk garin ansan soyayyarta daban take aransa akan sauran 'yayansa.

Baffa salisu shine cikakken sunansa Kuma haifaffe Dan asalin qauyen 'danja qarqashin wata qaramar dake cikin jahar yola.

Baffa nada Mata 'daya da 'yaya biyar ha'du maza Sai 'daya mace Wadda 'yan biyune aka haifesu Amma husainar takoma tun kafin suna Sai aka barta da sunanta na _HASSANA_ Amma suna kiranta da _ANANO_ ma'ana hassana da fillanci.

Anano itace auta Kuma itace qaramarsu kasancewar ba'a haifetaba Saida duka yannenta suka girma Sai yazamto kowa gidan ji yake da ita musamman baffan daya 'dauki tsananin so da qauna ya 'dora Mata kasancewar ita ka'daice yarinya qarama a gidan Dan tuni yannenta suka Zama samari.

Baffa nada arzikin dabbobi daidai gwargwado hakama yanada gonarsa dayake noma duk shekara shida 'yayansa.

Kaf qauyen Babu Wanda yayi karatun Boko Banda noma da kiwo Sai kuwa karatun addini,

Yusuf shine babba Kuma mai 'dan hakr saidai idan yafara fa'da to yanada wuyar saki,

Aliyu shine Mai bin Yusuf Wanda shikuma akwai fa'da da zafin Rai musamman idan aka ta6asa shiyasa kowa bai cika shiga sha'aninsaba,

Sai Usman wanda Shima akwai rashin ji da fa'da musamman akan anano dayake ganin tafara iya rashin kunya sbd sakarcin shagwa6a.

Jafar shine Mai sanyi da hkr acikinsu musamman akan anano dayake tsananin jida ita shima duk da dai kaf 'dinsu suna tsananin sonta Amma tafi shiri dashi matuqa danshi har dandali yake kaita tayo kallo sudawo gida.

Tunda ta taso take Jin son karatu aranta Wanda kullum firarta kenan da baffanta Wanda yayi niyya tareda alwashin kaita makaranta saigashi cikin ikon Allah aka turo masu fa'dakarwa akan karatun Boko qauyen shine mutum na farko daya yarda 'yarsa taje kafin aka samu wasu qalilan Suma suka amince Nan take aka fara Shirin makaranta suka fara zuwa.

Suna gama primary acikin qauyen suka wuce bording secondary School dake can cikin babban garin adamawa.

Tunda tafara zuwa makarantar idanuwanta suka qara bu'dewa musamman sbd dama can anano akwai tsiwa da ilimin iya fa'dar baqar magana Wadda ba'a fa'da Bata mayarba Koda kuwa mutum waye.

Wannan hutun dasuka koma sun Dade Dan kuwa Saida suka share kusan wata biyar acan kafin suka fara shirye shiryen dawowa Wanda sun gama karatun kenan.

Tunda jafar yaje yadawo yasanarda dawowarta ta gamo makaranta baffa da'di ya ishesa yafara shelar Ananonsa ta gamo karatu zata Zama babbar likita Mai Duba mutane.

Nan take gari ya 'dauka musamman ma da'akaji Wai tazamo likita.

Shiri na musamman yasa ayi na tarbon Anano tareda murnar dawowarta Dan tuni aka fara zuwa tayasa murna tun kafin ta qarason.

Anano farace tas tamkar 'yan gidansu saidai kaf tafisu kyau kasancewarta mace,
Ayanxu data kammala secondary 'dinta tanada shekaru goma Sha bakwai.

Koda dare yayi duk wani toye toye da gashe gashen kifi angama sbd ba abinda tafiso kamar gashashen kifi da albasa tun tana qarama shiyasa harshi Saida baffa yasiyo aka gasa Mata.

Washe gari tunda safe yasa inna ta share ko Ina tareda 'dora girkin shinkafa harda miyar tumatir Wanda takanas sbd ita yabada kudi aliyu yaje birni yasiyo shinkafar Dan adafa Mata.

Koda inna tagama aikin komai 'daki takoma ta kwanta sbd ciwon kan daya saukar Mata lokaci 'daya gashi Rana hartayi yamma na nemanyi Amma shiru 'yan makarantar Basu isoba.


I will only continue ne idan Naga votes naku...


Mamuh💋
[9/7, 9:46 AM] ‪+234 906 044 6461‬: _*EZNAH*_ 🌹
_wattpad@mamuh gee_




6~10
_blk 24 Fancris street LA,,,_

Kwance yake bakin swimming pool sanye da 3quater kawai cikin Yar qaramar rumfar shaqatawa dake gurin idanuwansa a lumshe kamar Mai bacci Amma ba baccin yakeba farar fatarsa Sai wani kyallin hutu da kyau take musamman dayake ba Riga ajikinsa.

Bu'de fararen oily eyes 'dinsa yayi ahankali tareda Kai hannu kan table ya'dau wayarsa akaro na ba adadi ya sake Danna kiranta.

Switch off yakumaji ya tashi zaune zuciyarsa ba da'di sbd wannan karon shine karo na farko daya ta6a Kiran nafeesat tun bayan aurensu Amma wayarta akashe.,

Miqewa tsaye yayi tareda sake Danna kiranta still akashe.

Kasa daina Kiran yayi Saida yajera Kiran kusan so ashirin Amma baya samu,,,

Hannuwansa ya zura a aljihun wandonsa tareda tsayawa bakin swimming pool'din ya qurawa ruwan Ido cikin tunani.

Tunda ya auri nafeesat tsawon shekara biyu kenan Amma bai ta6a 'daga waya yakirataba sbd kullum itace Mai kiransa safe Rana dare harsai ya gaji ya kashe wayoyinsa sbd yanda yake damuwa da kiranta.

Sam Bata fushi da yanda baya kiranta itadai burinta takirasa taji ya yake,
Idan kuwa Yaje Yana tareda ita to batada Zama ta dingi hidimarsa Dan taga ta kyautata Masa ko Kuma taga murmushinsa ko sau 'daya ne Amma bai ta6a ba.,

Nafeesat nada haquri da juriyarda ba kowace mace ce keda itaba,
Wani irin so Mai qarfi na haqiqa take Masa Wanda tun farko yasa ya amince ya aureta sbd ta sadaukarda duk wani farin cikinta akan soyayyarsa,

Bayan aurensu Bata tsinci komai ba Sai baqin ciki da rashin kula tareda halin ko inkula dayake nuna Mata Wanda tsill ta danne sbd Bata ganin laifinsa ko ka'dan,

Tun kafin ta auresa harta auresa Bata ta6a ganin dariyarsaba kosau 'daya duk iya qoqarinta na ganin hakan bata samuba sbd Babu so ko farin ciki dayakeji a rayuwarsa ko ka'dan,

Iya qunci zuciyarta na quntatuwa da yanda ta fahimci ba soyayyarta ko 'digo a zuciyarsa,

Tayi kuka a 6oye tayi a bayyane Amma takasa samun matsuguni a zuciyarsa duk da Yana soja Sam bayada zafin Rai kamar na sauran soldiers shiyasa take qara tsananin sonsa sbd he's calm.

Hakanan ta haqura ta fawwalawa Allah komai tacigaba da kyautata Masa Wanda sannu ahankali tsananin tausayinta ya shigesa sbd hkr da tsananin qaunar datake Masa har Bata ganin laifi ko kuskuren duk abubuwan dayake Mata musamman yanda ko Zama bai cikayi a qasarba.

Dawo da ita LA yayi gurinsa tareda tursasa zuciyarsa Bata kulawa,

Gwargwado yanayin iya qowarinsa gurin Bata kulawa da soyayya Wadda ita azahirin gskia tasan yanayi ne Dan ya faranta ranta,

Cikin ikon Allah ahaka har ciki ya bayyana ajikinta,
Bata ta6a tunanin arayuwarta zatagansa cikin farin cikiba Saida yaji maganar cikin Wanda tun daga time 'din ya qara ninka kulawarsa akanta sbd ayanxu Babu abinda yakeso sama da abinda ke cikinta sbd yanda rayuwarsa ke cikin quncin rashin uwa,uba ko wani 'dan uwa dazai kalla yaji farin ciki Sai yanxu dazai samu 'dan kansa jininsa shiyasa ahankali sonta da tausayinta suka fara samun kyakkyawan guri a zuciyarsa.

Tunda ta auresa ta gano qunci da ka'daicin da zuciyarsa take ciki ta maida dukkanin adduarta akan Allah yakawo farin ciki Mai 'dorewa cikin rayuwarsa musamman data gano mum asee da qaninsa ba qaunarsa sukeba dukiyarsa suke Hari.

Koda cikinta yafara tsufa ya maidata gida Nigeria sbd ta haihu acan bayan ya saka an 'dauko dattijuwar dazata kula da ita duk da su mum na gidan.

Kullum itake kiransa tun asuba har dare Bata gajiya da Kira Koda bai 'daukaba saitabar Masa voice note Amma yau akaro na farko da gari ya waye har Rana ta fa'di Bata kirasaba Wanda yasan tabbas Dole akwai mummnan dalilin daya Hana Dan Bata yarda takasa kiransa komai rintsi.

Sake lumshe fararen idanuwansa yayi tareda qara 'daga wayar ya sake danna kiranta.

Same thing yakuma ji switch off,.

Agogon hannunsa ya kalla yaga time yasan yanzu Nigeria suna gaf da Kiran magrib.

Wayar mum ya latsa Kira tayita ringing ba'a 'daga ba
Ya sake Kira kusan four Misscalls ba answer.

Ji yayi hankalinsa ya fara mummunan tashi Dan hakanan yakejin nafeesan batada lapiya,

Rintse idanuwansa dasuka fara canxa launi yayi yanajin son ganinta dason ganin lafiyarta data babynsa na shigarsa ya bu'de idanuwa ya Danna Kiran wata number.

Ringing biyu tayi aka 'daga daqyar ya bu'de baki cikin wata irin lallausan classy voice yace,

Koma me kakeyi kayishi cikin Daren Nan kaje kayi Mana booking we're going home to tomorrow.

Wat? Are you kidding me?......

Datse wayar yayi Yana yamutsa fuska sbd bazai iya tsayawa sauraron sauran zancen zayyan 'dinba sbd zai iya sakar Masa wani headache 'din bayan Wanda yake fama dashi yanxu.



#vote

Mamuh💋
[9/7, 9:46 AM] ‪+234 906 044 6461‬: *_EZNAH_*🌹
  _wattpad@mamuhgee_



*11*
3:00 pm girls college.....

Zaune take bakin bishiyar da bus 'dinsu ke Lodi tana rero waqarta cikin farin ciki qarshe tashi tayi tana jujjuyawa tareda qara sautin waqarta,

Hannu tasa ta jawo hannun ubaidah tana cigaba da jujjuyawa.

Nusaiba data nufo gurin da ruwan pure water guda uku a hannunta data siyo musu tayi saurin qarasowa cikin rawa tana bin waqarda dataji Anano tanayi cikin farin ciki.

Kallonsu ubaidah tayi bayan ta Sha Rabin ledar ruwa 'daya tasaki qaramin tsaki tana girgixa Kai kafin tace,

Wai Dan Allah Anano ku yaushe zaku San kun fara girma,
Ko kunya bakwaji dai yanxu gaban mutane da dama kuke rawa Kuna waqa.

Wani juyi tayi tareda kar6ar ruwa 'daya ta bu'de ta 'dansha kafin tazauna kusada ubaidah 'din fuskarta ta canxa zuwa yanayi sanyi ahankali tace,

Inason ne nayi duk wani farin ciki a yau kafin nakoma gida sbd hakanan zuciyata ke Jin kamar yau itace ranar farin cikina wata qila na qarshe ko Kuma mabudin wani sabon farin cikin.,,

Kallon nusaiba tayi jikinta na tsananta sanyi tace,
Nusy kece kusan komai na halayyarmu yake 'daya kinajin yanda nakeji ayau kuwa?

Kallonta nusaiban tayi tareda kamo hannunta tace,

Anano banajin komai a zuciyata Sai tsantsan farin ciki dason ganin na Isa gida da wurwuri.

Kafin suyi wata maganar direba yace kowa ya shiga mota angama shirya Kaya.

Miqewa suka tareda sake bankwana da sauran abokanansu cikin kewar juna dazasuyi suka shirshiga motar.

Acan baya suka zauna Anano ce bakin window Sai nusaiba a gefenta kafin ubaidah da wata 'yar qauyensu Nana.

Cike bus 'din take taf da 'dalibai 'yan qauyensu da wa'inda qauyensu yake gaban nasu maza da Mata.

Tunda suka 'dau hanya taji gabanta na tsananta fa'duwa Nan take mararta ta fara mur'dawa ta lumshe ido tanajin lokacinda period yazo Mata gashi idan tana period sosai take rushing.

Kallon nusaiba tayi cikin sanyin murya tace,

Wlh jinake kamar na rufe Ido naganni cikin gida musamman yanxu Da jini yazo Mata tasan kafin akai koyayane saitayi staining.

Qaramin tsaki taja lokacinda taga har magriba tayi musu ahanya sbd yanda drivern ke tuqi sbd tsufa da rashin isashiyar lafiyar motar Dan sun tsaya gyara yafi so uku a hanya gashi still da akwai sauran tafiya.

Qarfe tara da minti arba'in motar ta qara tsaya musu a hanya wannan karon suna kusa da shiga qauyen nasu ne,

Duk Wanda ke motar ba Wanda yake cikin walwala sbd tuni suka gaji da Zama da Kuma tafiyar kowa a matse yake daya Isa gida sbd ga yunwa ga qishirwa ga dare dayayi musu Dan tuni sawu suka fara 'daukewa.

Firfitowa sukayi kowa na sakin tsaki dattijon direban kuwa bu'de gaban motar yayi ya fara 'dan duddubawa gwanin tausayi sbd shima yau 'din motar tafi basa wahala.

Ita ka'daice Bata fitoba sbd sanin datayi kayanta sun Jima da lalacewa.

Wani tunani yashigeta lokacinta wata tsohuwar a Kori kura ta wuce ta haska hanyar dasuke...

Murmushi tasaki cikin farin ciki tareda tasowa ta fito motar tana sake kallon hanya.

Juyawa tayi cikin murna zata kirasu ubaidah saitaga duk sun tsallaka titi gurin yin fitsari Sai kawai ta juyawa tareda cewa,

Kusameni a gida Dan nasan saina rigaku idan nabi ta gonar Nan.

Gangarawa tayi batareda tsoron komaiba sbd idanuwanta sun rufe dason ganin ta Isa gida Dan murna da farin ciki.

Saidata kutsa sosai cikin dajin taja cak ta tsaya sbd motsin mutane da kunnuwanta suka jiyo mata.

Fa'duwa gabanta yayi Amma saita cigaba da tafiyarta
Sake Jin wani babban motsin tayi sai tasake saurarawa taji ba tantama motsine Kuma kamar kusanto gurin datake motsin yake.

Jujjuyawa tayi gabanta nadan faduwa cikin tsananin tsoro da fargaba bataganin komai sbd duhun dare hasken farin watama datayi tunanin zai hanatajin tsoro harta Isa gida tsawon shukar masara da gero duk ya hanata ganin hasken.

Sake juyawa tayi da qarfi Jin sawun gudu na kusanto inda take nan take hankalinta yafara tashi tafara qoqarin juyawa tana kutsawa cikin shukar batareda tasan inda take saka qafartaba.

Ji tayi wata qatuwar muryar data qarasa hargitsa kayan cikinta tana cewa,

Karku Bari ta tsare ku kamo ta kota halin qaqa araye ko amace.

Qara qaimin gudunta tayi tana waiwayen bayanta duk da Bata ganin komai gashi tuni tayi Nisa ma da hanyar garinsu tabi wani 6angaren dayayi nesa sosai da garinsu batareda tasaniba.

Tsayawa tayi jikinta na tsananin rawa tafara waige waige sbd Jin sun kusa isowa daf da ita.

Kukane ya qwace Mata ta nufi wata qatuwar bishiya ta lafe cikin hakukuwan qarqashinta jikinta na tsananta rawa ta rintse idanuwanta.

Ahhhh...taji wata tattausar muryar mace ta fa'da cikin azaba da yanayi na wahala.

Bu'de idanuwanta tayi da sauri jikinta na same karbar rawa,,

Mace tagani da tsohon ciki ta fa'di kife kan cikin tafara qoqarin tashi cikin aza6a sbd tacigaba da gudu.

Qoqarin tashi take suka iso tareda zagayeta su biyar kowannensu fuska ba 'digo ko alamar imani sbd daka gansu kaga makasa mutane ta kowace irin hanya.

Dafe cikinta tayi da hannu 'daya cikin tsananin azaba da hawaye tafara qoqarin tashi babban cikinsu ya 'daga hannu ya kwasheta da wani irin gigitaccen mari saidata sake kifewa kan cikinta tasaki wata azababbiyar qara Mara sauti sosai sbd qarfinta daya fara qarewa.

Qafa yasa ya mirgina ta tareda taka cikin da qarfi yace,

Ko kafa'da Mana inda kika 6oye takardun Nan ko na harbe cikin jikinki ayanzu.

'dago fuskarta tayi cikin tsananin azaba tana hawaye tace,

Har abada bazan fa'di inda takardun sukeba,
Na gwammace na mutu akan na fa'di inda takardun suke Dan kawai a tarwatsa rayuwar SAHEEB.

wani mugun duka yakaiwa bakinta tareda sake take cikinta cikin 6acin Rai dai zuciyarsa takai maqura gurin qonuwa Dan shi baya tsayawa dogon zance yake aika mutum lahira Amma wannan tun safe dasuka satota take wahalardasu .

Waya ya fitar Rai a6ace ya Danna Kiran mum.

Rai a 6ace itama ta 'daga  sbd Sam takasa samun nutsuwa Sai nafeesat tafadi inda takardun kadarorin saheeb inda suke.

A hasale cikin muryar cikakken 'dan ta'adda yace,

Hajiya wannan fa taqi fa'da gashi tana neman 6ata Mana aiki Dan yanzu hakama so biyu tana guduwa mun kamata yanxu hakama muna dajin wani qauye da ita acan nesa.

Miqewa tsaye tayi daga kan kujerar datake cikin rashin imani da takaici tace,

Bullet ku sake tambayarta for the last time idan taqi fa'da ka saita bindiga a cikinta ka harbeta idan Bata...


Read / Download EZNAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album