Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

SALON SO Complete Hausa Novel Document by SALON SO


SALON SO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 52726



SALON SO

Reading Time: 4 Hours

Added On: 06, Jun 2024

Author: Hadiza Salisu Sherif ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 259.06 kb

File Type: txt

Views: 502+

Download: 599+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: SALON SO!
NA:
_*HADEEZA SALISU SHAREEF*_
POSTED BY:
SULAIMAN BOMBOY.
.
PART 1 TO 6
.
Kyakkyawar yarinya ce 'yar kimanin shekara goma sha bakwai, direbanta ya yi parking da mota ya zagayo ya bude mata ta fito ta shiga cikin wani hadadden gida kerarre, ke da kallon tsarin ginin kin san hoto ne daga kasar waje aka yi irin sa. A kofar falon ta yi sallama ta shiga. Matar da take hakimce akan kujera cikin tsantsararriyar kwalliya ta kece raini, tana ta girgiza kafa da wayar sadarwa a hannunta da take hira. Tana ganin shigowar yarinyar ta dire wayar cikin fara'a ta tare ta, tare da cewa, "A'a Jawahir 'yar Dady yau a gari? Ko dai batan kai kika yi ne?" Jawahir ta yi murmushi yayin da ta durkusa gabanta ta ce, "Aunty ina yini?" "Lafiya lau Jawahir, amma dai a nan za ki kwanar min ko.? Tun da gobe ba ku da makaranta." Jawahir ta yi dariya tare da cewa, Tafiya zan yi Aunty yau Dady zai dawo daga saudiya, da kuma ya dira a kasar nan ni zai fara tambaya, kuma ni ma ba zan so ya dawo ba mu hadu ba. Aunty ta yi murmushi ta ce Jawahir gidan Daddy ke dai kullum kina like a gida kamar daddawar daka ba kya son zuwa ko ina ko?" Amma zan je na samu mommy dinki na ji ko ita take hana ki zuwa." Jawahir ta yi murmushi, "Wallahi Aunty babu rawan mommy Daddy na ne baya son na rinka fita. Sallamar da ta ji ce ta sa ta yin shiru, sai da aka amsa masa sannan ya shigo. Ya zauna a kan kafet tare da rissinawa ya gaisar da Aunty. Aunty ta amsa cikin kulawa ta musamman ta kalle shi ta ce, Ba dai har ka dawo daga office din ba?" "Wallahi Aunty vacci nake ji shi ya sa na taho gida don na kwanta na huta." Aunty ta girgiza kai tare da cewar, "Ba ka kula da bakuwa ba ne?" Sai sannan ya kalle ta ya ce, "Wallahi ai kamar jawahir ko.?" Au ka mance ma? To ita ce, Jawahir ta dan rissina ta ce, "Yaya Haidar ina wuni?" Ya amsa cikin kulawa sannan ya ce, "Ya su Dady?" "Daddy ba ya kasar, yau dai muke sa ran dawowarsa." "To Allah ya dawo da shi lafiya, Abin da Haidar ya ce kenan ya mike ya nufi sashensa. Jawahir ta mike Aunty zan tafi" "Haba jawahir har tafiya zaki yi.?" "Wallahi Aunty tafiya zan yi doki nake yi ne na je na fara shirin tafiya taryar Daddy. "To 'yar Daddy ki gaishe min da shi, kafin na zo gobe yi masa sannu da zuwa. "Ta fito da sauri, direbanta ya karbi kayan da yake hannunta ya zuba a but ya bude motar ya shiga ya tayar suka miki hanyar gida +++++++++++++++++++++ Alhaji Ibrahim shine mahaifin Jawahir, mutumin kirki ne, akwai shi da son jama'a ga yawan kyautatawa na kasa da shi, sam ba shi da kyamar talaka. Yana da dadin zama idan ka kiyaye abubuwan da ba ya so, na farko ba ya son raini, kuma shi kaifi daya ne, in dai ya ce, "I, ko "A'a" to ba wanda ya isa ya tankwara shi sai uwarsa. Su uku ne a wajen iyayensu, shi ne babba sai Aisha wato Aunty babar Haidar sai Aminu, wanda shi ne autansu. Ubansu da suke kira da Baffa ya dade da rasuwa sai mahaifiyarsu Rahmatu da suke kiranta da Inna. Inna mace ce mai kirki da hakuri ga ta da son zumunci, duk inda aka ce ga dan uwa ko ta yaya suka hadu ta jawo shi a jiki ita bare ma jawo shi take yi don ya zo ya ci arzikinta. Tana zaune a unguwar sabon tatin mandawari. Tana matukar son jawahir don a cikin jikokinta babu wanda ya kama kafar son da Inna take yi wa jawahir. Alhaji ibrahim matarsa daya Hajiya Hafsatu, ita ce mahaifiyarsu Jawahir, suna ce mata Mommy. Mommy tana da 'ya'ya shida biyar maza daya mace. Akwai Abba me sunan kakansu sai Abdullahi, sai Nasir, sai Jawahir da Auwal da Sani. Jawahir ita ka dai ce mace a gidan, kowa ji yake da ita ba ma kamar Alhaji ibrahim da yayyanta. Suna son ta suna shagwabata amma duk da haka ba ta sangarce ba don tana tsoronsu tana kuma jin maganarsu. Jawahir yarinya ce kyakkyawa tana da hankali da nutsuwa akwai ta da biyayya ba ta da rowa. Sai dai miskila ce ba kowa take iya sakewa da shi ba, ba ta fiya son magana sosao ba, in kinji hirarta ce ne da Daddynta ne ko yayyanta sai mommynta, to shi ne za ki ji har da dariya. Amma shagwababbiya ce ta kin karawa don ita har kannanta Auwal da Sani shagwaba take yi musu bare kuma su Yaya Abba da uwa uba Daddynta. Bayan Auwal ne ya dauke min babban turarena da ya fi kowanne tsada. Shi ne kike kuka? Rabu da shi zai gamu da ni ne je ki cikin dakina kan mudubi ki zabi wanda kike so share hawayenki ki yi dariya. Ta fada dakin Dady da gudu tana murmushi yaya Abba ya ce, Su jawahir sarkin rigima. Shi kuwa Haidar a zuciyarsa cewa ya yi, Kai wannan yarinyar tafi ya shagaba shi ya sa take ba ni haushi sai na ga kamar na doke ta in ana lallabata. Yarinya sai shagwabar tsiya sai ka ce ita ce Auta." Tunaninsa ya katse ne a dai dai lokacin da jawahir ta fito daga dakin, hannunta rike da sunkumemen turare. Ta nunawa Dady ta ce, Dady ga shi na dauka. Yace, "To 'yar Dady ya yi miki wannan din?" Ta daga kai, "To maza ki je ki boye abunki ki ta fesawa. Ta durkusa fuskarta cike da murmushi ta ce,Na gode Dad Allah ya kara girma, Ya shafa kanta yana murmushi ta yi waje a guje. Takaici ya cika Haidar a zuciyarsa ya ce, Ya za a yi ma wannan 'yar yarinyar a ba ta wannan turaren? Ya za ta yi da shi? don kudinsa wajen dubu goma sha biyar ne,to ita ta san darajar kamshin ne ma. Yanzu haka wasanta za ta yi da shi kawai. Yaya Abba ya girgiza shi tare da fadin, Haidar me kake tunani ne? ko ka tuno America ne? da yake tare suka yi karatu a can shi da Haidar din. Dariya suka yi suka tafa. Kiran sallar da aka yi ne ya sa su tashi don zuwa su ba da farali. To irin wannan halayyar ta Haidar ita ce take bawa jawahir haushi don haka ko gidansu ya zo ba ta kula shi karkari ta ce masa ina wuni ta wuce shi ba tare da ta jira amsarsa ba. Dan mulki kenan. Ita jawahir duk da miskilancinta ba ta da daukan kai kuma akwai ta da yi wa mutum murmushi tana da halin kyauta duk inda ta ga talaka ko kaskantacce in dai ta san mai bukata ne, to za ta gayawa Daddy ya taimaka musu. wannan halayya tata ita take kara sa kaunarta a zuciyar Daddynta. Kamar yau da safe jawahir ta gama baccinta ta fada toilet a yi wanka ta fito ta tsaya gaban mudubi aka shiga kalailayar jiki, a shafe nan a goge can, ta tsara kwalliyarta cikin boyal shudi rigar fitet da zane ta sa hadadden fashion dinta yari da sarka da abin hannu me shudin dutse, Daddynta ne ya siyo mata daga london. Ta hadu iyakar haduwa fuskar tata sai sheki take yi ta feshe jikinta da turaruka ta fito ta nufi sashen Dady. Ta kwankwasa ya yi mata izini ta bude ta shiga. "A'a 'yar Dady kwalliyar ta yi miki kyau, Ta yi murmushi ta durkusa ta gaishe shi, "Don Allah Dady ina so yau zan je gidan Inna. "Kin sani jawahir ba na so ki rinka yawan fita amma tun da gidan Innata za ki je ba komai sai ki je. To me za kaiwa Innan? Jawahir ta dube shi tana murmushi ta ce, Dady duk abin da ka ba ni. To shi ke nan 'yar gidan Dady, daman ke ake jira tashi mu je a yi brek. Mominta ta fito daga cikin dakin Dadyn cikin rantsatsiyar kwalliya kamar me shirin zuwa fati. Jawahir ta yi saurin zubewa ta gaishe ta, mommy Daddy ya bar ni zan je gidan Inna Ta ce, "Yauwa koke fa, ai gwanda ki je kusan kullum Inna sai ta yo miki waya ta ce ba ta jin dadi idan ta dau lokaci ba ta ganki ba. Suka fito babban falo suka hau tabir inda 'yan samarin suke jiransu. Jawahir ta gaida Yayyanta inda ita kuma kannenta suka gaishe ta, al'adar gidan ke nan kowa sai ya gaisar...


Read / Download SALON SO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album