Join Our WhatsApp Group

ZULFA Complete Hausa Novel Document by ZULFA


ZULFA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 78144



ZULFA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 21, May 2023

Author: Aysha Ya'u Kurah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 420.66 kb

File Type: txt

Views: 3326+

Download: 2228+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: : ●● ZULFAH ●● 1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Dare ne mai cike da dumbin rahama, kowa na cikin gidanshi sakamakon Ruwan da ake tsugawa, masu abin hawa suna ciki, masu tafiya a kafa da mashin sun fake saboda ruwan yinshi akeyi kamar da bakin kwarya, ma'aikatan dare suna wajen aikinsu,
A wannan lokacin zulfa'u na cikin ruwan tana wanke kwanukan da aka ci abincin dare a gidan, yawan ruwan da akeyi baisa goggo marka ta tausaya mata ba, yayin da ita kuma take dakinta na kasa, kan rubabiyyar katifarta, rushi ne a gefenta suna shan dumi ita da yarta Salaha, can gefe kuma mahaifin zulfa ne zaune yayi tagumi yana leken yarshi dake faman aiki cikin ruwa, zuciyarshi na zafi amma bashi da yadda zaiyi saboda marka ta fi karfinshi, Allah Allah takeyi ta gama ta shiga dan karamin dakinta da bai wuce taku shida ba, tana gamawa ta gyara gurin da sauri saboda ruwan kamar dada ingizoshi akeyi, tayi maza ta tsaya bakin kofar dakinta ta cire kayan jikinta saboda kar ya jika mata daki dama ga dakin ba kofa ruwa duk ya jika kofarshi, matse kayan tayi ta shanya a saman kwanonta, tasa wasu yagaggun kaya da suka zaizaye saboda tsufa, da sauri ta hau kan katifarta wacce bata da maraba da tabarma, yunwa sosai take ji dan ragowar da take samu ma yau basu rage ba, gara ma na kabiru yayan salaha ya dan rage kadan saboda ta samu, amma saboda tsabar ta kosa taji muryar dake debe mata kewa tasata bacci cikin farin ciki, muryar dake sata manta ko wani irin bacin rai yasa ta share yunwar da takeji, ta dakko redionta da gurin kunnanawan a cire yake, in ka ga radion bazaka taba cewa in an kunna zaiyi aiki ba, kibiyarta tasa ta kunna shi, cikin zakuwa ta kamo tashar liberty ta kure muryar radion dan battery ya kusa mutuwa, ta tura kanta cikin zaninta ta kara radion a kunnenta, saura 5mints takwas tayi, ta dinga sauraren wakokin da akeyi, takwas dai2 taji ansa sassanyar waka mai tsuma zuciyar masoya, lumshe idonta tayi saboda tasan taken isowar gwaninta kenan, kara gyara kwanciya tayi ko kadan sanyin da takeji ya gushe, muryar "Abubakar sadiq marafa" ita ta daki dodon kunnenta cikin salonshi na isa da kasaita, salon dake burge dubban mata masu aji dake cikin garin kaduna da kewayenta, sallama ya fara yi cikin harshen hausa da larabci, ya mika gaisuwa gurin masoyanshi da turanci, sannan ya fara programme dinshi cikin harshen hindu (indianci) cikin kwarewa yake gabatar da program dinshi, duk wata mace da ta isa a duk ranar friday to tana manne da radionta tun takwas har tara na dare, wasu ma da radion suke fita tadi saboda gudun kar a barsu a baya, ko wata shida sadeeq marafa baiyi da fara program dinshi ba amma saboda kwarewarshi da yadda mutane ke sonshi zaka rantse tunda aka bude gidan radion yake aiki a gurin"""!,

kasancewarshi mutum mai girmama soyayya da son yanayi na damuna yasa aka kayata mishi wannan daren da wakoki masu sanyaya zuciya, karfe 8:40 bayan ya kammala da gabatarwa, ya rage amsa tambayoyin masoya, tambaya uku kadai yace zai iya amsawa a ranar saboda yana son yin bankwana da masoyanshi, gaban zulfa ya fadi hankalinta ya tashi, ta yaye xanin da ta lulluba dashi saboda wani gumi da taji ya keto mata"", cikin taushin murya zee gayu ta fara wurgo mishi tambayar farko, tace tambaya ta farko ta fito daga gurin "Salma Ibrahim, " tambayar da akullum sai MARAFA ya amsata babu mamaki malama salma bakuwace a cikin wannan shirin namu, tambayar itace shin sadeeq yana da aure,,, dariya sadeeq yayi saboda yadda zee ta karasa maganar yace zeee kenan, malama salma bani da aure, sai dai kuyi min fatan samun mace ta gari kuma kamila, zee tace bakayi niyya ba dai ga mata nan kamar zasu ci kansu, murya can kasa saboda kar masu sauraro suji yace zee ban hadu da muradin raina ba har yanzu, ya lumshe idonshi yana siffanto irin macen da yakeso tun yana yaro, zee ta bude murya da karfi tace to masu sauraren mu marafa dai yace bai hadu da muradin ranshi ba har yanzu, sai ku tayashi addu'ar samu nan kusa, in kuma wacce zata kasance muradin ran nashi tana sauraronshi to sai tayi fatan Allah ya hada ta dashi komin daren dadewa, zo kuga mata a gidajensu yadda suke amsa ameen, zulfa ta share kwallar dake idonta, dama ita tasan bazata taba haduwa da sadeeq ba, saboda yayi mata nisa sosai yafi karfin ajin mace marar galiho da gata irinta, amma muryar dake sata manta bacin ran da ake mata a gida yau zata ma kunnenta bankwana, , to saboda me zaiyi bankwana?? Ta tambayi zuciyarta, kafin ta samo amsar tambayar har ya gama amsa tambayoyin, cikin taushin murya yace zanyi bankwana daku masoyana, zan ajiye wannan progrm din saboda bukatar hakan ta taso, ina rokonku da duk wanda na taba batawa a rayuwa ya yafe min, na yafe ma duk wanda ya bata min, wadanda basu sanni a fuska ba ina adduar Allah ya hada mu daku a aljanna firdausi, nagode da kaunarku Allah ya kawo wanda zai maye muku gurbina, a karshe ina bukatar addu'ar ku akan Allah ya taimakeni ya bani nasara akan abin da nake nema, nagode, nagode Allah ya barmu tare,,, wakace ta cigaba da tashi a kunnuwan masoyanshi dake kuka, zulfah ta wurga radion bayan yagalgalalliyar jakar kayanta ta shiga kuka baji ba gani, daren da ya kasance mai cike da sanyi da dadi ga ma'abota soyayya, ya kasance dare mafi zafi da kuncin a gurin baiwar Allah zulfah....

Mrs tijjani shattima ...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari tun biyar na asuba ta farka duk da ba wani isashshen bacci ta samu ba, tsakar gida ta fito taga tulin kayan wanki a kofar dakinta kayan goggo marka ne da na salaha, ta kalli kayan cikin faduwar gaba saboda yawansu ga danshin damina, ga kanta na masifar sara mata saboda rashin bacci da bata samu ba, ta zauna ta buga tagumi da buta a gabanta tana tunanin irin rayuwar da take ciki tun bayan rasuwar mahaifiyarta tana yar shekara goma take aikin bauta bata da wani lokacin farin ciki kullum tana cikin wahala, bata ko samun isashen abinci, wannan dalilin ne yasa ko da yaushe in kaga zulfa bata cikin walwala, bata kula kowa koda a makaranta ne, magana mai yawa tana yi mata wuya, in tayi magana ko kai wanda take ma maganar ba lallai bane kajita saboda tsabar sanyin maganar, tasha dukan asara gurin goggo saboda yanayin maganarta amma duk da haka bata sauya zani ba, saboda babu wanda zai iya canza nature, rankwashi mai karfin gaske shi ya katse mata tunanin da ta keyi, tayi maza ta sauka daga kan dakalin da take rike da kanta, goggo tace uban me kika zauna kikeyi agurin nan, duk ga ayyukan gidan nan babu ko daya da kika fara saboda tsabar iskanci da lalaci, to bari kiji kinga wannan wankin wallhy kika kuskura gari ya waye baki gamashi ba sai nayi mugun saba miki shegiya mai suffar mayu, ta wuce gurin kullun wainarta ta na masifa kamar zata ari baki, makota sun riga sun saba dajin muryar marka me waina a ko wace safiya, bare mahaifin zulfa malam ado da abin ya zame mishi jiki kuma bashi da yadda zaiyi ya fitar da yarshi daga cikin bautar marka, shiyasa a ko da yaushe yake fata da yi mata adduar samun miji tayi aurenta ta bar gidan, ya kudura a ranshi ko dan garuwa ne yazo neman aurenta in dai zai dauke mata ci da sha wallhy zai bashi, zulfa ta idar da sallah tayi yan adduointa, ta fito da sauri ta dauki katon bokitin penti ta shiga jido ruwa a mono din dake masallacin layinsu Allah ya taimaketa babu layi saboda gari bai waye ba,,,
saleem dan limamin unguwarsu kuma malamin islamiyyarsu shi ya ganta tana diban ruwa bayan ya fito daga sallah, cikin tausayawa ya karasa gurin mono din, tanata bugawa tana haki taji sallamarshi tayi murmushi a hankali tace ina kwana malam, lafiya lau yace mata yana kokarin fara tayata buga panpon, tace ka bari malam nama gama wannan shine na karshe, bai saurareta ba saida ya gama cika bokitin, ya sa hannu zai dauka ta rike gefen bokitun tace dan Allah malam ka barshi kar in baka wahala, kallonta yayi yace saki bokitin ki wuce muje, batayi musu ba ta saka suna tafe har suka kai kofar gidan, ya ajiye dai2 dakalin shiga gidan, shi kanshi da yake namiji saida kirjinshi ya dan amsa saboda nauyin bokitin,,,, ,
ya kira sunanta a hankali yace kiyi hakuri zulfa wuya bata dorewa, komai na duniya mai wucewa ne,,
kullum ki dinga addu'a Allah ya kawo sanadin da zai fitar dake cikin wannan bakar rayuwar, idonta ya ciko da kwalla tace nagode malam Allah ya saka da alkhairi,
yace ameen,, kinsan yau zaku fara jarabawa kiyi sauri ki gama ki taho makaranta, tace to nagode malam, ta dauki bokitin ta shiga ciki da sauri ta fara wanki sai gurin shida da rabi ta gama duk sanyin da akeyi zulfa bata ji saboda tsabar wahala, tana gama dauraya ta shanya wasu a gidansu ta shiga gidansu inna delu inda suke shanya ta shanya sauran,,,
hanne ce ta fito daga daki tana mika alamar yanzu ta tashi daga bacci, hararar zulfa tayi taja tsaki tace wahalalliya, a wahala zaki kare har karshen rayuwar ki sai shegen girman kan tsiya sai kace wata yar sarki, zulfa ko kallonta batayi ba saboda ta riga ta saba da duk wata masifar da inna delu da diyarta hanne suke mata, goggo ameena ce ta fito daga daki tace haba hanne ku sakar ma yarinyar nan mara tayi fitsari mana, da wanne zataji da na marka da salaha ko da naki ke da delu, ko dai wani ta kashe muku ya isa ace kun barta haka bare ba daya bare kanwar biyu,,,! haba ay nan goggo ameena ta kara harzuka hanne ta rufe ido tana surfa mata bala'i cikin raini har inna delu ta jita ta fito ta tayata suka dinga yi harda zungurin zulfa,,, faiza yar goggo amina ita ta taya zulfa shanya har suka gama ko kallon su hanne basuyi ba,
goggo Ameena tace faiza kice zulfa kar ta tafi ta tsaya taci tuwo, fa'ee tace to mama, taja zulfa suka zauna suna dan hirar jarabawa goggo ta kawo musu dumamen tuwon dawa miyar tafasa, nan suka wanke hannunsu da ruwa suka fara ci saida sukayi katt saboda yawan tuwon,
da sauri zulfa ta tashi ta deka dakin tace goggo nagode sosai bari in shiga gida, goggo ameena tace to zulfa ayita hakuri dai,, mai hakuri shi keda riba wata rana sai labari, tace to goggo nagode sosai, ta fito
tace fa'ee sai kin biyo ta fita da gudu da bokiti a hannunta, tana shiga ta tarar maza da yawa zagaye da goggo marka masu siyan waina sai hayaniya sukeyi, ruwan sanyi ta diba a ruwan da ta debo ta wuce bayi tayi wanka saboda yawan mazan dake gurin yasa ta dauko kodaddan uniform dinta ta shirya a bayin, dakinta ta shiga ta dakko robar vaseline ta dinga kwakuloshi saboda ya kare da kyar ta samu kadan ta shafa a fuskarta, gurin kitchen taje ta tsuguna tace ina kwana goggo, ta kalleta a wulakance ta amsa tace rikakkiya ina kuma zaki, tace goggo islamiyya yau zamu fara jarabawa, salaha dake zaune kusa da wani me napep sun hada kansu guri daya wai suna kallon waya tayi tsakii sosai tace uban waye zai gyara miki dakin,, haka zaki barshi da datti saboda ba a ciki kike kwana ba, zulfa ta marairaice ko kallon salaha batayi ba tace goggo yau zamu fara jarabawa kuma ance muzo da wuri walhy daga na dawo zanyi, murfin tukunyar dake gefenta shi ta wurgo ma zulfa ya sameta a jikinta duk manja da bakin tukunya suka b'ata hijab dinta, cikin tsawa goggo tace dan ubanki wuce kije ki gyaro ko ina kuma ki fita ki k'aro ruwa ki cika ko'ina na gidan nan, kiyi zaman jiran a gama waina ki wanke komai ki daura girki,,
idon zulfa ya ciko da kwalla ta mike ta shiga daki tanajin mazan gurin yan tasha suna shewa suna taya goggo aibata ta wasu ma har tafawa sukeyi da salaha da ke zaune a tsakiyarsu, ta gyara dakin goggo ,, ta fito ta dauki bokiti ta fita a kofar gida sukaci karo da fa'ee, fa'ee tace a'ah ina kuma zaki da bokiti, tace ruwa zan debo ki tafi kawai kar in bata miki lokaci, fa'ee ta fisge bokitin da karfi cikin tsiwa ta wurga shi cikin gidan taja hannun zulfa da karfi suka fita tana janta zulfa na tirjewa, hakan bai sa faiza ta saki hannunta ba har saida suka karya kwana, zulfah cikin muryar kuka tace fa'ee kinsan irin bala'in da kika jamin ne, meyasa zakiyi haka, kinsan bani da mafita dan wallhy goggo bazata yarda bani na wurgo bokitin ba, yau Allah ne kadai zai iya kwatata a hannunta dan yau kasheni ne kadai ba zatayi ba,
Kuka sosai ta tsuguna a kasa takeyi, fa'ee tace tsoronki shi ke ja miki matsala, kalleki zulfa wallahi kin wuce duka, amma kullum ayita kirbarki kamar jaka ke bazaki iya kwatar ma kanki yanci ba saidai ki zauna ki dinga kuka shiyasa duk suka raina ki, wani yanci fa'ee ni har inada wani yanci a rayuwata, mahaifina bai nemar min yanci ba sai ni zan nemawa kaina, fa'ee rayuwar nan da nake cikinta bana neman taimakon kowa sai Allah, shi kadai yasan dalilin barina cikin wannan halin, kuma ina gode mishi a ko da yaushe tunda ya barni da rai da---- da lafiya suka ji an karashe daga bayansu, fa'ee ta tsuguna tana murmushi tace ina kwana malam, ya amsa yana kallon zulfa dake ta faman kuka, itama ta gaisheshi, ya amsa a gajarce yace ku wuce maza makaranta dan lokaci na kurewa, fa'ee ta kamo hannunta suka wuce tana share hawaye, binsu yayi da ido cikin tsananin tausayi a ranshi yace Allah ka kawo sauyi cikin rayuwar baiwarka zulfa'u....

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 3⃣
By Aysha Ya'u kurah

Tafiya nakeyi da sauri duk kafata ta gaji saboda rashin abin hawa ga unguwar da zanje da nisa, a wani katafaren kayataccen gida kafata ta tsaya, gidan da zan iya cewa duk cika da batsewar GRA...


Read / Download ZULFA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album