Join Our WhatsApp Group

ABDULMALIK BOBO Complete Hausa Novel Document by ABDULMALIK BOBO


ABDULMALIK BOBO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 99108



ABDULMALIK BOBO

Reading Time: 8 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Bilyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 638.81 kb

File Type: txt

Views: 1967+

Download: 2133+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: [11/12, 2:10 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻.


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_



_story & editin_
*_aunty Bilyn Abdul_*


_Written_
*_Marak'isiyya_*


_hak'in mallaka_
*_Aunty bilyn Abdul_*


*_Bismillahirrah manirrahim._*


*_gareku Readers._*
_assalamu alaikum, da farkodai nasan zakuyi mamaki, auntyna, bilyn Abdul itace tayi tallan buk d'in nan ABDUL-MALEEK, daga baya kuma sai tafasa rubutawa saboda wani aiki data zomata._
_to nikam nakaranta buk d'in danta rubutashi tuni a littafi yana ajiyene, littafin yayimin dad'i Dan haka nanemi izini tabarni na rubutamuku._
_nidai Marak'isiyya ba writer bace, wlhy koza'a kasheni bana iya rubuta page d'aya na novel, to amma yanzu zanyi muku copy insha ALLAH, ina fata zaku kasance dani kamar aunty bilyn Abdul, Dan labarin natane. Ngd._

*_sanda tayi tallansa ta rubuta sadaukarwa ga Abba Gana, batul mamman, bily giro, tonima zan cikamata niyyarta, Dan haka sadaukarwane ga wad'annan mutane uku._*



*_page 1⃣&2⃣_*

Kowa ka kalla yana harkokinsa acikin makarantar, wasu karatu sukeyi wasu kuwa hira da samarinsu ko k'awaye.
Shigowar wata bak'ar mota wulik cikin makarantar shine yaja hankalin mafi yawan d'aliban.
Safna tasaki Baki da hanci da ido itama tana kalo.
Motar tatsaya daidai wata bishiyar dalbejiya, ayanzu kallo yakomane akan Wanda zai fito daga cikin wannan mota mai k'yau da d'aukar hankali.

K'afarsa yafara zirowa k'asa maisanye da sauciki na farin takalmi, yakuma zuro d'ayar itama, saikuma yafito gaba d'ayansa.
Ajiyar zuciya safna ta sauke tareda fad'in ya salam!.
Zeenat tad'ago tana kallonta Dan ita kokad'an batasan bikin da akeyiba, tasaka iyafis akunne tana wayane.
Safna wai lfy mikike kallone haka kamar wata sakara?.
Safna da bakinta yaymata nauyi takasa cewa uffan, tad'aga hannu dak'yar tanuna mata matashin saurayin dake tsaye, Wanda ak'alla zaikai shekara 33 aduniya.
Masha ALLAHU zeenat tafad'a itama tana mik'ewa tsaye.
Farine sosai dogo kuma dankuwa yanada tsayi sosai, kallo d'aya zaka masa kagane k'ak'k'arfane saidai bashida k'iba, masha ALLAHU akwai k'yawun fuska, gashi kuma ya k'awata fuskar tasa da saje bak'i sid'ik, yakwanta sai wlk'iya yakeyi, sanyake da farar shadda wando da Riga d'inkin zamani, kayan sun masa k'yau....
Tunaninsu yatsaya lokacin dasukaga ya sunkuya yafiddo wata yarinya mai tsananin kama dashi, "bazata wuce shekara 6 ba aduniya.
Sanye take da doguwar riga ja iya kwaurinta Dan batakai k'asaba, ank'awata adon rigar da fararen filawoyi, kanta kam kalbace irin mai nannad'ewarnan kamar igiya (twisting), yasha ribom ja da fari, sai lilo sukeyi.
Ta rik'e d'an k'ugunta da hannu biyu tana kallon saurayin, baby inanenan mukazo?, tafad'a tana bin ko ina da kallo.
Murmushi yay mata Wanda yazauta dayawan 'yammatan gurin, musammamma safna, shima yarik'e k'ugunsa baby nan makarantace, munzo wajen uncle Hamza ne.
Lah baby dama uncle Hamza baigama makarantaba har yanzu?, yafayi babba sosai?.
🤦🏻‍♂kansa yadafe ya ce, "o,o me baby, kefa magana bata k'are miki, kinga muje ciki saiki tambayesa.
'Yar dariya tayi tareda kama hannunsa suka nufi office d'in uncle Hamza, Wanda yakasance lecturer a makarantar.

Cikin farinciki uncle Hamza yamik'e cike da murmushi yana fad'i oyoyo Nawal d'ina.
Itama sakin hannunsa tayi taje da gudu tashige jikin uncle Hamza, yarungumeta yana juyi da ita suna dariya.
Shikam yajingina da k'ofa yana musu murmushi, uncle Hamza ya ajiye Nawal suna sauke numfashi da dariya.
Sai sannan ya kalli saurayin, cikin zolaya ya ce, "oyoyo my Bobo!.
Shima hararsa yayi cikin wasa, kace hakafa yanzu, bayan baka kulaniba tun d'azu sai baby.
Hhhhhh afuwa kasan nida Nawal ba'a shiga tsakani, daga ina haka?.
Bobo yayi murmushi yana sauke numfashi, wlhy daga gidansu Ni'ima muke kasan mama babu lfy shine nace bari mubiyo mugaisheka.
Kai amma naji dad'i wlhy sosai, amma yajikin mama?, da sauk'ika gsky.
To ALLAH yak'ara sauk'i, nima anjima nashiga nak'ara dubata.
Okey ALLAH yakaimu.

Surutu Nawal takema uncle Hamza babu ko k'ak'k'autawa, shikam sai dariya yakeyi.
Bobo kam yamaida hankalinsa akan latsa wayarsa.
Aka kwankwasa k'ofar.

Uncle hamza ya ce, " ashigo."
Safna ce da zeenat k'awarta, risinawa sukai suna gaishesu, idon safna nakan bobo.
Uncle Hamzane kawai ya amsa, amma Bobo ko d'agowa baiyibama.
Safna incedai lfy?, uncle Hamza yatambaya yana kallonsu.
Zeenat ta zunguri safna dake kallon Bobo babuko k'yafta ido.
Uncle Hamza yana kallonsu, Dan haka ya girgiza kai.
Ina saurarenku yak'ara fad'a idonsa akansu.
Um....um sir dama..... Saikuma tayi shiru tana satar kallon bobo.
Bobo yad'ago yad'an kallesu fisha saikuma yamik'e, Ya Hamza bari muwuce mubarka da d'alibanka.
Baby oya tashi muje.
"Kai bobo da wuri haka?, cewar uncle Hamza yana kallonsa.
Karka damu gobe idan ALLAH yakaimu zanshigo na gaida aunty Ruky, baby taso mana.
Nawal ta mak'ale kafad'a zatayi kuka, a'a nidai zan zauna wajen uncle Hamza.
Harararta yayi baby banason rigimar banza fa kinsani, idan nabarki da aikinsa zaiji kokuwa da shegen surutunki magananniya.
Dariya uncle Hamza yayi, yashafa kumatun Nawal, kinga my durling kibisa kuje, idan natashi aiki, zanzo gidan Ammi na d'aukeki nakaiki wajen ya Ahmad ko?.
Da sauri ta d'aga kai tana 'Yar dariya, by by uncle.
By my Nawal.
Hannu bobo yabashi sukayi musabaha yafita rik'e da hannun Nawal.
Duk abinnan yana faruwane agaban su Safna.
Safna tabisu da kallo kamar ta had'iyeshi.
Murmushi uncle Hamza yayi, Dan yasan K'anin nasa yayi sata batareda yasaniba.
Ina jinku yafad'a yana maids hankalinsa kansu...........





_Ku kasance da Marak'isiyya_
*_(auntyna bilyn Abdul, abar alfaharina.)_*
Tana nan tana shiryo muku had'ad'd'en buk, saikungansa😉😘
[11/12, 2:10 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻



❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_



_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*


_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*



3⃣&4⃣
........cikin in ina safna ta ce, "sir dama akan test d'in dakayi jiyane, wlhy banida lfy shiyyasa banshigo school ba.
d'an murmushi yayi kawai, yasan bayau yafara lecture safna bata nanba, amma bata ta6a neman afuwaba sai yau.
Ita kullum kanta Asama yake, tana gani tafi kowa, yasan yauma akwai abinda yakawota, bai wuce ganin bobo ba datayiba, Dan kallon datake masa kawai ya fallasa asirin zuciyarta.
Ajiyar zuciya yasauke tareda fad'in babu damuwa safna zan duba.
Godiya suka masa suka fice.

Binsu yayi da kallo yana girgiza kai, afili ya ce, " lallai safna kinada aiki, bakisan waye Abdulmalik bobo ba.

*_Wacece safna?._*
Alh Bilal mai Gold, shine sunan mahaifinta, cikakken bakano d'an asali, d'an kasuwane babba Wanda yake juya Gold yazama Naira.
Matarsa d'aya Haj Sa'adatu, suna kiranta (Ummi).
Yaransu hud'u mata biyu maza biyu.
Shaheed shine babba, yayi aure harda yara biyu, sai Muneer shima yayi aure, matarsa tanada tsohon ciki yanzu, sai Safna tana karatu yanzu, saikuma auta Rahma, bana ta kammala Secondary.
Yaran 'yan gatane sosai, saidai wannan baihanasu samun tarbiyyaba, iyayensu suna kula dasu sosai.
Saidai Safna batajin magana ko kad'an.
Wannan kenan.


++++++++++++
Suna fitowa daga office d'in zeenat taja tsaki, kai Safna ALLAH yau kinbani haushi, wai ina ajin nakine?, haba Dan ALLAH, jibafa kigani sabida wulak'anci kod'agowa yakallemu baiyiba yanata latsa waya, daga k'arshema saiyayi tafiyarsa.......
Kinga zeenat ya isheni haka, idanfa bazaki taimakamin nakai ga nasaraba tofa sauraramin, ninagani na ce, "inaso, angaya miki shi sakaran namijine da 1 time zai dubemu, ashema babu aji taredashi.
Mtsooow zeenat taja tsaki, aii idanshi ya iya rik'e NASA ajin, kekam naki yana hanyar zubewa.
Tana gama fad'a tayi gaba abinta.

Itama Safna abin yabata haushi, danhaka tashige motarta tayi gida


+++++++++
Bobo kam gida yanufa abinsa, yana tsaida motar Nawal tafita da gudu zuwa cikin gida, kansa yagirgiza yana fad'in ALLAH ya shiryeki baby.
(nace amin).

Bayan yakashe motar yakwashi wayoyinsa shima yay ciki.
Ammi dake zaune Nawal nakusada ita ta kwa6e fuska zatayi kuka, ta amsama bobo sallamarsa.
Yak'araso cikin falon yana kallon Nawal, kekuma lfy daga dawowarmu?.
Ammi tasauke ajiyar zuciya ta ce, " maganar kullumce dai takawo rigimar.
Shiru yayi baice komaiba.
Ammi takalli Nawal dahar tafara hawaye ta ce, "haba tagidan Appa kiyi hak'uri insha ALLAHU kinkusa ganin momynki kinji.
Da sauri bobo yad'ago yana kallon ammi, k'irjinsa sai harbawa yake da k'arfi, yakasa cewa komai.
Ammi takauda kai, ranta a6ace ta ce, " nagaji da ganin kukan yarinyarnan wlhy, amma babu komai bari Appanku yadawo, zand'auki mataki.
Hannun Nawal takama suka haura sama.
Bobo tamkar zai fasa ihu haka yakeji, yarintse idanu zuciyarsa na zafi, afili ya ce, "baby miyasa kikeson sakani a matsalane?.
Ganin babu maibashi amsa yamik'e yanufi d'akinsa.

*_Wanene Bobo_*
Abdulmalik d'ane ga Alh Aliyu Abdulmalik Hamshak'i.
d'an siyasa sananne wad'anda suke gwagwar Maya da ilimi dakuma nemawa talakawa 'yancinsu, matarsa d'aya Haj. Zahura (Ammi).
Yaransu shidda maza hud'u mata biyu.
Is'haq shine babba, yanada mata d'aya da yara hud'u, sai Sulaiman, shima yaransa uku da mata d'aya, sai Hamza matarsa d'aya shima da yara biyu, sai Abdulmalik (matarsa ta rasu) yarinyarsa d'aya, sai 'yan biyu duk mata basuyi aureba.
ALLAH ya azurta Alh Aliyu Hamshak'i da yara maza masu kwazo da himma, yaa is'haq ma'aikacine na banki, yaa Sulaiman kuwa likitane, sai yaa hamza lecture, sai Abdulmalik (bobo) cikakken lauya mai zaman kansa.
Kansu ahad'e yake, idan kagansu saika d'auka abokaine musamman ma yaa hamza da Abdulmalik, komai zasuyi saida shawarar junansu.

*_Abdulmalik_*
Mutumne mai zafi da sauk'i, gaba d'aya 'yan uwansa yafisu fad'a, saidai zasuzo daidai da ya is'haq (Dan shima mafad'acine).
Abdulmalik mutumne dabayason raini ko kad'an, baya wasa da mutane, baizama dolema kuzauna har kurabu kaga dariyarsaba, kullum cikin d'aurewa yake, amma yanada son jama'a sosai.
Abdulmalik bobo, yasamo sunan bobone tun yana k'arami, kasancewarsa mayen shan Bobo sai 'yan uwansa suke kiransa da bobo, ahankali sunan yay tasiri kowa Yakoma cemasa bobo, bayan ya girma saiya zama bobo na gsky saboda gayunsa ga k'yau ga kud'i ga ilimi, komaidai zam zam.
Bayan ya kammala karatunsa yafara aiki iyayesu sukace saura aure.
Yay tsalle yadire bashida budurwa, wannan yasa Appa yanema masa auren d'iyar k'anwar Ammi mai suna Ni'ima.
Da farko baya sonta ko kad'an, amma k'yawawan hali irin na Ni'ima yajanye hankalinsa harya tsunduma a k'aunarta.
Shekararsu biyu da aure ta haihu mace, wadda taci sunan Ammi, suna kiranta Nawal, shekarar Nawal d'aya Ni'ima takuma samun ciki, amma wajen haihuwa ALLAH yay mata rasuwa itada abinda ke cikinta.
Bobo yashiga rud'ani Dan saida aka had'a da addu'a sannan yadawo daidai.
Tundaga nan baisake kallon wata mace da sunan so ba, damashi matan bawani damunsa sukaiba.
Bobo yanada k'yau daidai gwargwado, gashi d'an gayu, akwai tsafta da iya d'aukar wanka, dolene mace mai lfy taga bobo ta k'yasa, kullum cikin k'amshi yake.
Shiyyasa Madeena ta k'yasa.
(To aunty bily dai ta ce, "ki kama kanki Dan bama kulaki zaiyiba, danshi aharkar mata ba gwani bane😜).

Shekarar Ni'ima 5 kenan da rasuwa amma bobo yak'i k'ara aure, iyayen sunata fama dashi amma yak'i sunata fama saidai yace zaiyi amma yak'iyi.
Kullum zancen Nawal akaita gurin momynta, haka take damunsu Ammi da Appa hardashi dadyn Nata, itadai tanaso taga momynta, kullum zancen kenan.
Abin yana damun yayyensa da iyayensa, shikam ko'a kwalar rigarsa, harkar gabansa kawai yakeyi.
Wannan kenan.


*_Mundawo labari_*.........







*_{Aunty bilyn Abdul na gaisheku masoya😘😍.}_*
[11/12, 2:10 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻



❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_



_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*


_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*


_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*



5⃣&6⃣
........Safna tadanna hon afusace, da sauri maigadinsu yazo yabud'e mata get, ta danna hancin motarta cikin gidan, tana kashe motar tasuri jakarta da wayoyinta zuwa cikin gida.
Wani wawan tsaki tasaki Dan ganin Rahma k'anwarsu kwance akan cinyar ummi.
Daga Ummi har Rahma baki suka saki suna kallonta.
Ummi ta ce, "kekuma lfy daga shigiwa zakiyi mana tsaki?, wai Safna ban hanaki halinnanba ne?.
Baki ta turo gaba tana Harar Rahma, haba Ummi ALLAH wannan abun kunyane, wannan k'atuwar yarinyar shrkara 17 haryanzu bataida halin yaraba, aiiko jafar d'in ya Shaheed baya wannan ta6arar.
Rahma ta girgiza kai danjin akanta yayar tata take tada jijiyar wuya, tarasa miyasa basa shan inuwa d'aya da 'Yar uwarta, (ita aganinta abin yafara wuce fad'an sako da sako), afili kuma sai ta ce, " aunty Safna miyayi zafi shiba wutaba, zauna ki huta Dan ALLAH.......
Duka takaima Rahma ummi ta kare, Safna kishiga hankalinki danifa, uwarmi tamiki daga shigowa?.
Cikin huci ta ce, "ummi kinajinfa maganar datake fad'amin, ALLAH yarinyarnan ta rainani, zan koya miki hankali kwanannan wlhy.
Ummi ta tamke fuska tana nunama safna hanya, kinga tashimin anan.
Ran safna a6ace tabar wajen tanufi d'akinsu tana mita.
Rahma kam ta sauke ajiyar zuciya tana k'ara gyara kwanciyarta.
Ummi ma kai ta girgiza ALLAH ya shiryaki Safna tafad'a tana shafa kan Rahma.

Safna tacire kayanta tanata masifa harta shiga wanka, (nikam mamaki take bani, Dan banga abin fad'aba anan).

Rahma tanason shiga d'akinsu tayi wanka tana tsoron masifar Safna, Dan tasan wlhy bata bartaba, k'ilama yau kwana zatayi bala inta da mitar tsiyarta.
d'akin umminsu tanufa dantayi wankanta kawai, yafi sauk'i.


+++++++++++++++
Bobo yana kwance ad'akinsa sai juye2 yakeyi, barci yakesonyi amma yak'i d'aukarsa, maganar Ammi ce kemasa yawo akwakwalwa.
Yasan Ammi sairai babu sauk'ice, indai Abu ya6ata mata rai saita d'auki mataki, shikam yana tsoron zancennan yaje kunnen Appansu, yad'an cije le6e yana sauke numfashi, tund'azu soyake yafita amma yana shakkar had'uwa da Appa.
Yasan fita tazame masa tilas Dan dole...


Read / Download ABDULMALIK BOBO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album