Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SAIFUL ISLAM Complete Hausa Novel Document by SAIFUL ISLAM


SAIFUL ISLAM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 84730



SAIFUL ISLAM

Reading Time: 7 Hours

Added On: 20, Aug 2023

Author: Miss Xoxo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 08030811300

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 477.99 kb

File Type: txt

Views: 1895+

Download: 1961+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: [1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL💕*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*😻
*BILLYN ABDUL*🌹



*SHAFI NA D’AYA (1)*


*Daga shafi na d’aya xuwa na biyar na ki ne uwar d’aki na,ni kadai banda Hafsat Rano😆.Sis UMMI AISHA👌🏾*💕


بسم الله الرحمن الرحيم


*ABUJA*

*A* jiye yaron da ke hannunta tayi akan gadon sa tare da d'ora kansa akan pillow irin na jarirai dinnan, wanda lokaci d’aya ya keta sharar baccin sa, ta shafe shi da addu'a,sannan ta dauki macen dake ta faman wangale wawulon bakin ta da babu hakori a ciki.

Kallo d’aya zakai wa yaran kasan cewar 'yan biyu ne.Tashi tayi ta dinga zagaye parlorn da yarinyar a hannunta, tana d'an jijjiga ta har sai da tayi bacci, sannan ta kwantar da ita a kusa da tagwai d'in ta.

Komawa tayi gefen su ta rage volume d'in tv da ketayi a tashar Africa magic yoruba. ‘jenifa’s diary’ ake yi lokaci zuwa lokaci take d'an murmusawa, da alama sosai take jin dad'in drama series d'in.

Wayar tace ta fara rurin kara ‘Miftahul qalb’ shine sunan dake ta yawo a samab screen d'in wayarta ta, da azama ta d'auka tare da karawa a kunne had'e da mikewa a hankali tabar wajen gudun kada ta tashi yaran nata dake ta baccin su.

“Assalamu Alaikum Qalb..”

“Wa’alykm Salam sugar, yanzu na sauka fa” Cewar *SAIFULLAHI* dake janye da akwatin sa madaidaici a harabar airport d'in Lagos .

“Wayyo! Sannu qalb.. ka sauka lapia?!
Ubangiji Allah yasa albarka a abinda akaje nema, rabbi ya dawo daku lapia, yanzy dai ka samu abinci kaci banda shan abu mai sanyi dan Allah...kaji?”

Ajiyar zucia ya sauke, Allah ya sani yana matukar son matar sa da yaran sa, dole ce tasa yake nisa da su saboda yanayin aikin nasu, muryar tace ta sake dawo dashi daga tunanin su daya tafi ida take cewa.

“Kaji Zawj?”

“Na..Naji Love! Insha Allah bazan sha ba”

“Toh! Bari na kyale ka, ka huta tukunna anjima sai na kiraka muyi video call kaga 'yan biyun ka dan tuni sunyi bacci babu dadewa”

Shafa kwantaccen sajen sa dake kwance luf-luf a saman fuskarsa yayi, dan ba kad'an ba yana jin wani shaukin sonta na kuma ratsa shi yana lalata duk wani jini dake shiga jikinsa..

Cikin kasalalliyar murya ya furta,

“Okay love..! Yanzu zamu wuce ikoyi da Abbas anjima kuma zamuje ikeja filling station d'innan saboda traffic d'in lagos da safe..will call you when I’m done idan dare be yi nisa ba..”

“Okay zawj.. I love and miss you sai anjima..”

Sallama suka yiwa juna, bayan kowannen su ya sakarwa d'an uwansa zazzafan kiss ta wayar, cike da kadaicin junan su kowannen su ya katse kiran had'e da nannauyar ajiyar zuciya.

Komawa tai parlor wajen 'yan biyun ta dake ta bacci cikin nutsuwa. Tuni har angama shirin jenifas diary an shiga yin wani kuma, kallon agogo tayi 11 saura.

“Wai..haka dare yayi?..”

A gaggauce ta dau yaran nata ta takai d'aki, bayan ta canza musu kaya izuwa kayan bacci, band'aki ta fad'a wandake cikin d'akin tayo wanka hade da dauro alwala ta fito. Sai da tai nafilfilinta sannan ta koma kan gado tai azkhar na bacci hade da addu’oi na kariya ta tofe su sannan ta dauki wayar ta tana dannawa, ganin har sha biyu tayi bai kira ba, tasan lalle aiki ne ya rike sa. Gajeren message ta tura masa kamar haka,

_“Every day, I fall in love with you more. I don’t know how that’s even possible when I’m sure that I couldn’t love you more than I love you now. I guess you just have this thing about you that makes loving you so easy and natural. I miss you already. Sleep now,honey. Sweet dreams. Allah ya yi jagora a abinda akaje nema”_

Ajiye wayar tayi a gefen bedside drawer dake gefen ta, ta bud'e ta zaro photo album d'insu na secondary school, wato BRITISH NIGERIAN ACADEMY(ABUJA)tana kalla..

Memories ne suketa dawo mata kallon 'yan ajin nasu take yi, d’ai-d’ai har tazo kan 'yan gidan da suke uba d’aya dasu wato Hafsat Khaleel Mai Mota sai ta biyu wadda sunan ta ke rubuce da Hidaya Khaleel Mai Mota, sai babbar kawarta Haleema Sameer Ameer sai kuma hotan ta dake k’arshen Page d'in rubuce da Bilkisu Khaleel Mai Mota *(ISLAM)*

Murmushi fadad'e a fuskarta take bin kowan ne hoton 'yan ajin nasu da kallo, tun daga kan matan har zuwa mazan ajin nasu take kallo abubuwan da suka faru na dad'i dama akasin haka take ta tunanowa harta gama ta rufe photo album d'in wanda suka kammala makaranta a shekarar dubu biyu da goma sha hud'u (2014).

“Such is life” (haka rayuwar take) Shine abinda Islam take ta maimaitawa kafin ta kwanta bayan ta kara yin wata addu’ar.

Kwanciya tai zuciyarta fal da abubuwan da suka faru a baya, idan na kunya ne ta rufe ido, Idan na dariya ne ta murmusa ita kad’ai.

Haka bacci barawo ya sace ta, zuciyarta cike take da tuna bayan rayuwar ta, tana ta shek'a baccin ta saifullahi yayo mata reply,

_"Sugar pie.It does not matter how my day was, I always long for the night, to cuddle you all night as you quench my heart.It was a stressful night,aiki muke tayi yanxu ma muna construction site na ikeja... A shafa min kan Arya da Aryan...I love you more than life itself. Goodnight my love.."_

Asubah ta gari masoyan juna.. *SAIFUL_ISLAM*💕

Da wannan Ni Nana hafsatu nace shin wacece ISLAM?wacce irin rayuwa tayi da har take tunanin ta haka?!..Ya kamata mu koma shekarun baya don ganewa idanuwan mu abubuwan da suka shud’e🏃🏽‍♀

***** *ASALIN LABARIN*


*BRITISH NIGERIAN ACADEMY...SS1b*

Zaune kowannen su yake a kujerarsa da yake monday ce duk yawanci ransu a b’ace yake musamman da yake first period maths ne.

Back sitters babu abunda suke sai ciye-ciye sai kuma 'yan lovey dovey squad dake hirarrakin soyayya da yake mix school ce (makarantar mata da maxa a hade).. Sai 'yan seat d'in gaba wato su ISLAM madam serious ita da kawayenta, kowannen su kansa a kasa suna ta karatu kafin malamar maths din ta shigo..

Shigowa Miss Abigail tayi daga ita sai mini skirt da top d'in riga tasha attachment a kanta, mikewa class d'in suka yi masu hararta nayi mazan nata faman sakin fito a hankali, da yake rabin su sun tsani maths, kuma a jin sune sahun gaba a rashin ji, Da karfi 'yan gaba suka fara;

“Good morning ma..! we are happy to see you ma’am, God bless you ma..” Banda 'yan baya dake cewa,

“We are not happy to see you ma.. God punish you ma” A hankali yadda bazata jisu ba.. Ita kuma sai washe baki Miss Abigail d'in take yi tana cewa.

“God bless you too..Thank you.. have your seats please”

Juyawa tayi tana rubutu a board, ‘Matrix and Matrices’ shine abunda ta rubuta kafin ta juyo ta dube su..

“Okay class..Today we are going to discuss and solve Matrix and Matrices’ I’m going to solve Number one question and one of you will come and solve the other.. I’m I clear?!”

“Yes Ma..” Suka fad’a da karfi.

“Good..”

Ta fad'a tare da juyawa tana solving banda su Islam, babu wanda yake sauraronta sai ma cigaba da hirar su da suka yi har ta gama tayi musu bayani sannan ta kalli class d'in tana cewa.

''Okay who’s going to solve the next?”

“Maa..” Islam da ta d'aga hannunta alamun zata iya, had'e da gyara zaman medicated glass d'inta.

“Good..” Cewar Miss Abigail tana mikawa Islam d'in marker..

“Mtcew” Hafsaat da suke uba d’aya sannan tana d'aya daga cikin 'yan back seat taja tsaki a hankali tana furta,

“Sai dai nacin karatu kawai da san iyawa, banxa mai bakin jini..”





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*



*NA*



*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*



*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_



*SHAFI NA BIYU (2)*


Sam Islam bata bi takan ba’ka’ken maganganun da Hafsat da kawayen ta ke gasa mata ba,Tana jin su suna aiba tata suna mata mugayen fata,haka tai ficewar ta gaban board,babban burin ta bai wuce tai solving equation dinnan dai-dai ba..

Kaman yadda Miss Abigail da kawayen Islam suka tsamma ta akan Islam, hakan ce kasance, domin dalla-dallah Islam ta kalkuke maths din, Tafi (round of applause)Miss Abigail tasa yan class din suyi nan suka fara ji kake.

“Raf raf raf..”

Ajin ya dauka da tafin masoya da kawayen Islam amman banda bangaren su Hafsat wato ‘yan back sitters da suke jifan Islam din da harara.

10marks sukutum Miss Abigail ta bawa Islam,kan idan exams tazo tanada additional ten marks,godia Islam tayiwa Miss Abigail tare da ‘yan class sannan takoma seat dinta ta xauna.

“Lam Lam all the way..Go gurl..”

cewar Haleema Sameer Ameer wadda suke
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SAIFUL ISLAM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album