Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAUL HAYAT Complete Hausa Novel Document by MATAUL HAYAT


MATAUL HAYAT

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 84541



MATAUL HAYAT

Reading Time: 7 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Sakinat Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 430.73 kb

File Type: txt

Views: 912+

Download: 1173+

Last download: 2 days ago

Description/Story:
(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤02¤¤
.
¤Wannan Sadaukar wa ce zuwa ga..... Boss dina, Yaya na, Dan uwa na, Bappa na, wanda adomin sa na ke nan, Allah ya ba shi sa'a da nasara a komai nasa da sauran en uwa musulmai gabaki daya...
(MARABAS DAN ANTY) jinjina gare ka.¤
.
Ci gaban labari...
.
Yace; Me zan taho miki dashi? Tana murmushi tace; ''Goba'' Yayi dariya yace; Kedai kam ina ga sai kin haifi da mai kalar goba...Shikenan sai na iso.
Ya kashe wayar ya dauki makullin motarsa. Yana shirin fita ke nan Basiru masinja ya shigo ofishin rike da zungureren fayil(file) a hannunsa suka yi kici6us ya rusuna yace:
Yalla6ai ga takardun injinan nan da akayi bonanza daga ofishin peter yace akawo maka kasa hannu.
Ya kar6i fayil din ya dora akan tebur ya dauki biro yasa hannu(signing) sannan ya mikawa Basiru. Yana fita yaci karo da Alh. Sammani Sabo. Don haka dole suka koma cikin ofishin, suka gaisa Alh. Sagir yana dan fara'a yace;
Alh. Sammani jiya nake tunanin na kira ka ban samu sarari ba. Alh. Sammani yayi murmushi yace; kada ka damu ni gani nazo da kaina. Alh. Sagir ya dan yi shiru na wani lokaci sannan yace;
Gaskiya nayi tunani mai zurfi naga hakan bazata samu ba, musamman idan nace zan 6ullo da hakan a kungiya baza a aminta ba, don haka kawai nake ganin mu hakura......
Alh. Sammani ya bugi teburin da hannunsa yana dan murmushi yace; Kada ka damu Abokina,Aminina ni na san kai masoyi nane ko bayan ba raina zaka iya taimakon iyalina. Nagode da bayaninka yanzu yaushe ne za a dauka?
Alh. Sagir yace; Eh, to kamar yadda aka soma fada tun can baya. Alh. Sammani ya yunkura yace; shikenan aminina ba matsala, amma ni zan yi tafiya zuwa Dubai har sai bayan komai ya kammala zan dawo. Don haka ina neman afuwa ga kowa-da kowa, a kuma kula da ci gaba da abubuwan da ake yi yadda ya kamata.
Alh. Sagir yace; Yauwa aminina nagode kwarai da yadda ka hakura ka sadaukar. Babu komai.
Ya rako shi har bakin kofa, sannan shi kuma ya koma cikin ofis din ya dauko makullunshi daya ajiye cike da farin ciki ya fito ya tunkari inda suke ajiye motoci.
Ya kusa karasawa kenan yayi tuntu6e da wani 'Kashi ya kife kasa, bisa tsautsayi ya kama aman jini.
Mutanen dake shawagi a gurin suka ankara da abinda ya faru don haka da sauri suka tunkaro shi, don kawo masa dauki.
Aman jinin yake kashir6an saboda haka sai ba a tsaya 6ata lokaci ba aka kwashe shi aka nufi Asibiti dashi. Ko kafin a isa Asibitin ya gala baita sosai, da gaggawa aka shiga dashi Emergency room.
Alh. Saminu wanda ya jagoranci zuwa Asubitin yayi amfani da wayar Alh. Sagir ya lalubo lambar Alh. Ahmad ya kira shi. Bugu daya wayar ta shiga. Yana dauka yace; Yane Baban gobe? Ko an sauka ne? Alh. Saminu yace; Bashi bane Daya daga cikin ma aikatan gidan gonarsa ne, don Allah ka same mu a NAJNOOR HOSPITAL, Saboda oga yazo hawa mota yayi tuntu6e ya kama aman jini. Shine muka kawo shi Asibiti.
Cikin tashin hankali Alh. Ahmad yace; To gani nan zuwa. Mintin sha biyar a tsakani Alh. Ahmad ya iso Asibitin. A lokacin suna da damar shiga inda yake saboda an samu aman jinin ya tsagaita.
Suna shiga suka tarar dashi dik ya yamutse kamanninsa dik sun sauya,tamkar wanda yayi ciwon shekara. Alh. Ahmad ya matsa kusa dashi yaga idanunsa sunyi jajur kamar jan gauta. Wani irin siririn haske ne acikin idonshi,sai kace yana saitin hasken kwan lantarki.
Cikin tausayawa Alh. Ahmad yace; sannu Alh. Sagir. Bai iya amsawa ba, sai dai idanu kawai da ya zuba masa,kai kace wannan shine karo na farko da yayi tozali da shi.....
ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤03¤¤
Dama baka lafiya ne ko kuwa sanadin tuntu6en ne? Har yanzu bai iya tankawa ba sai Alh. Saminu ya amshi zancen da cewa; Gaskiya nima ina tunanin bashi da lafiya, domin yaui sukuku yake a gidan gona,tunda ya shiga ofis dinsa bai fito ba sai da wannan sanadin ya faru.
Alh. Ahmad yace; To Allah ya bashi lafiya? Gaba daya suka amsa Ameen. Sun shafe mintuna goma babu wanda ya sake magana daga cikinsu. Sai zuwa can Alh. Sagir ya lumshe ido Alh. Saminu yace; Ina ga ma ya samu bacci.
Alh. Ahmad ya dago kai ya dubi Alh. Sagir, sai ya ga ya bude ido, amma kwayar idon ta sauya launi ta koma KORE shar, sannan ta koma DORAWA, sai ta koma BAKI. Shikenan ya maida idon ya rufe.
Gaban Alh. Ahmad ya fadi, bai fahimci abin da ya gani ba, ya dubi Alh. Saminu da sauri yace; Ku duba ku gani yadda kwayar idonsa ke sauya launi.
Da sauri suka dubi Alh. Sagir amma sai suka ga kwayar idonsa a rufe Alh. Saminu yace ai bacci yake. Alh. Ahmad ya dunga tunanin anya kuwa bai ga wani al'amari ya faru da dan'uwansa ba? Amma jin amsar da suka bashi yasa ya share maganar.
Alh. Saminu yace ya kamata a sanar da maidakinsa. Alh. Ahmad yace; Eh ba ma ita kadai ba harda mahaifanmu. Ya ciro waya yana niyyar doka kira kenan, Alh. Sagir ya mike a firgice ya dafe kansa da hannunsa guda da ba a dora masa ruwa ba? Alh. Ahmad ya maida wayar a aljihu ya matso da sauri kusa da dan'uwan shi yana tambayar; Ya jikin? Amma shiru bai tanka ba daga karshe sai ya koma yaraf! Akan gado. Gaba dayansu suka saka sallallami, daya daga cikinsu yayi saurin kirawo likita. Ya duba shi ya tabbatar musu da RAI YAYI HALINSA.
Kwalla suka sirnanowa Alh. Ahmad cikin karfin hali ya kirawo mahaifinsu ya shaida masa halin da ake ciki. Sannan ya kira Alh. Sada shima ya bayyana masa abinda yake faruwa.
Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankalinsu a tashe.
Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankali a tashe, aka gama dik abinda ya dace sannan aka basu mota (Ambulance) da zata kai musu gawar a gida.
Suka taho,kowannensu cike da wannan jimamin wannan BABBAN RASHIN da sukayi, Saboda rashin irinsu Alh. Sagir yana da matukar ta6a zuciya.
Jan gwarzo jarumi wanda ya tsayu da kyautatawa na kasa dashi, zai yi wuya talaka ya kawo kukansa ga Alh. Sagir ba tare da an share masa hawaye ba. Amma duk wannan yakana tasa bata hana ya amsa kiran mahaliccinmu ba.
Laillai Allah baya barin wani don wani yaji dadi!!! Kuma dik jarumtar rai da nuna hazikanci, dole ne ta dandani mutuwa.
(Dacin mutuwa mai ta6a zuciyar wadanda aka yi wa komai, ma'ana juriya da jarumta basu isa su hana rai dandanar mutuwa ba, yayin da suka rasa wani nasu)
mu samman ma Alh. Sagir da ya zamto tamkar shugaba a wannan tsatso, saboda yapi kowa kudi a cikinsu.
.
(ALLAH YA JIKAN MARUBUCIYAR WANNAN LITTAPIN YA GAFARTA MATA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA AMEEN)
.
Ci gaban labari...
KADDARA TA RIGA FATA Haj. Karimatu tana zaune a falo Haj Asmo ta shigo dauke da faranti a hannunta, fuskarta kunshe da fara'a tace; Yau dai ina sauke hakkin da ya rataya a wuyana. Haj karima tayi murmushe tace; uhm kaji manyan masu gida, don anyi min sanwa shine ake koda kai? To dama kin bari domin ba gwaninta kikayi ba tunda ba ci zanyi ba shi dai na karfen ya dawo yaci. Haj Asmo ta zauna a gefenta tace ke kin isa? Ai bazan wahala a banza ba. Haj Karima tace ; Ko yanzu ba kiyi wahalar banza ba,tunda dan'uwanki zai dawo,kinga kin hutashshe dani. Tace wlh kuwa ke nifa yau tinda na tashi nake jin gabana na faduwa komai ba yayi min dadi,hatta yawun bakina daci yake min. Ga shi dan da yake cikina yana ta yamutsamin 'ya'yan hanji. Haj Asmo ta danyi murmushi tace; To ko dai haihuwar ta zone? Don dama naga cikin naki yayi kasa sosai. Haj Karima tayi murmushi ita ma tace; Wai ita mai tsohon ciki babu wani ciwo ko damuwa da zata shiga sai dole nakuda? Ni fa wallahi tsoro ma nake kada na zo haihuwar nan na wuce. Haj Asmo tace; Ai haihuwa ba mutuwa bace ke dai Allah ya sauke ki lapiya, amma ki daure kici abincin nan zama da yunwa yana azabtar da mai ciki. Haj Karima tace; Bazaki gane me nake nufi ba, sam ba na jin yunwa kuma bana iya kai komai a bakina. Ke dai kici kawai ba ra na shiga daga ciki. Haj Asmo ta dan harare ta, ta wutsiyar ido tace; Ke dai ko wayo kike so ki yi min ki shiga daki ki haihu sai dai na jiyo kukan jariri? Dariya Haj Karima tayi tace; A'a wallahi kinga ma na fasa shiga dakin shike nan? Za tayi magana suka ji karar tsayuwar mota Haj karima tace; Ina ga ma gashi nan ya iso. Haj Asmo tace mai
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAUL HAYAT

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album