Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AMANA TABARMIN Complete Hausa Novel Document by AMANA TABARMIN


AMANA TABARMIN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21508



AMANA TABARMIN

Reading Time: 1 Hours

Added On: 20, Aug 2023

Author: Zahra Muhammad Mahmud Surbajo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 128.87 kb

File Type: txt

Views: 995+

Download: 505+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)


WHATSAPP NO:
+2349030159301
[07:39, 07/09/2017] ‪+234 806 958 0725‬: ⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩
*AMANA TA BARMIN*
⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩


Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

BISSMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.

*BAN YARDA WANI KO WATA YAJUYA MIN LABARINBA,IN AKAYI NABAR MUTUM DA ALLAH*


*1-2*


Sauri yake zashi gurin,ayki,sabida yayi latti,dan haka hankalinshi nakan hanya.

Yazo danja,besaniba,saura kaɗan ya bigeta,dan har motar tafara,taɓa jikinta,da sauri yataka burki,ya fito yana kare mata kallo.

Ɗago da kanta tayi itama,ta haskeshi da fararen idanunta,tsintar kanshi yayi da sakin murmushi.

"yanmata kiyi hakuri don Allah wlh ban kula dake bane shiyasa"ya faɗi yana murmushi.

Itama murmushin tayi,sannan tace tana juya ido.

"lah karka damu,ay abun ma yazo da sauki tunda baka bugeni ba"

"ina kika nufa,inji ko hanyar mu daya na rage miki hanya?"

"kaida kace kana sauri,kaine kuma dason ragemin hanya,baka tsoron asaka a gurd room?"

Dariya yayi me bayyana kyanshi,sannan yagyara tsyuwar hularshi ta sojoji,yace.

"muda guardroom sede mukai wani,amman bamuba,kina cinye lokaci,ina kika nufane"

Murmushi,tayi,sannan tace.

"zani,yusuf dantsoho memorial hosital,ne"

"good hanyarmu daya,sede ni 44 zani,danhaka muje nasaukeki"

Ba musu tashiga motar,yaja suka tafi,ahanya yana janta da hira kamar haka.

"me zakije yi a asibitin?"

"ni nurse ce acan,shiyasa zanje"

"daga wacce anguwa kenanfa?"

"unguwar sarki"

"sunanki fa?"

"maryam"

daga haka sekuma sukayi shuru,zuwacan de yace mata.

"duk dade cewa shishshigi zanyi,amman hakan baze hanani faɗamiki sunanaba,am,captain farouk Ahmad,nigerian army,from unguwan dosa,kozan iya samun numberki?"

Dariya maryam tayi sannan tabashi numberta,yayi saving.

seda yakaita har cikin asibitin sannan,yajuya yakoma gurin nashi aykin,wato Asibitin 44.

yana,isa gurin ayki,ma'aikata,sojojin se sara masa sukeyi.
har ya isa office dinshi.

Jakar laptop dinshi ya ajiye yafice duba marasa lafiya.

Be baro asibitinba,se,karfe shida na yamma.

Tafe yake yana tunanin maryam wacce suka haɗu da safe,yarinyar ta burgeshi,game da saukin kanta,ba wulakanci ba komai,(abinda yanmatan zamani suke kira jan aji,hmmm yarinya ja aji ki tsufa gidanku).

Har ya isa gida yana tunaninta.

Yana shiga falon gidan yafara,cilli da kayan jikinshi,kamar ƙaramin yaro,ya wurga hula can,riga can,wando can,takalmi can,safa can,sannan ya zauna dagashi se singlet da gajeren wando.

Hajiya mahaifiyarshi ce tashigo falon,kamar kullum,da takalminshi tafara cin karo,tsayawa tayi riƙe da baki tace.

"Farouku wai se yaushene zaka girma,kayarda kuma ka girman?"

Tasowa yayi yana murmushi yace.

"Hajiyata Allah yajamin nisan kwananki da lafiya,matuƙar kina raye hajiyata,kullum ni yarone,ɗa duk girmansa baya girma agaban iyayensa"yaƙarasa maganar yana rungumeta.

Tureshi tayi sannan tafara tsince kayan nashi tace.

"ka kiyayeni,farouku,da daɗin bakinnan naka,wlh aure zanmaka,kajecan matarka taci gaba da kulawa dakai"

Dariya ya kwashe da ita,daga baya kuma ya haɗe fuska,irin shagwabarnan.yace.

"hajiya wacce,macece zata ɗauki ɗawainiyata,bayan ke dakike uwata kullum,cikin ƙorafi kike dani?".

"oho maka,kaika sani,duk inda ma zaka nemota kanemo,nide nagaji wlh,ace ƙato kamarka,baze iya adana,kayanshi ba,kullum nice zan adana maka,ruwan wanka bazaka haɗawa kanka ba kuma bazaka yarda me ayki ta haɗa maka ba dole seni,tsurfa kalakala ka iyata,gurin zaɓar abincin dazakaci,shine zanci gaba da zama dakai haka,mutumin dako takalmin ka na ayki baka iya sawaba,baka,iya sa belt ɗinka ba dukafa ninake maka farouku katausayamin kayi aure don Allah,kaji me sunan manya"

Dariya ya kwashe daita sannan,yafice da gudu yabarta tsaye tana bin bayanshi da kallo.

Ɗakinshi yanufa,kamar kullum,mahaifiyarshi,ta gyara mishi shi,sosai yayi kyau se kamshi ke tashi.

Wanka yashiga,yajima kamin yafito,ɗaure da alwala,ya zura doguwar riga,yafice zuwa masallaci,domin gabatar da sallar magrib.


Muje zuwa.


surbajo for life.
[07:39, 07/09/2017] ‪+234 806 958 0725‬: ⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩
*AMANA TA BARMIN*
⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩



Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION



*3-4*


Be dawo ba se bayan sallar isha,kai tsaye ɗakin mahaifiyarshi,yanufa.

Akan abun sallah yasameta zaune tana lazimi.

Guri yasamu yazauna,harta kammala,sannan ya matso ya kwantar da kanshi akan cinyarta,yace a shagwaɓe.

"Hajiya me kika dafamin yunwa nakeji"

"tuwon dawa akayi da miyar kuɓewa ɗanya da busasshen kifi"tabashi amsa.

Miƙewa yayi yanufi dinning,yacika tumbinsa,ya leƙa ɗakin hajiya yamata seda safe sannan ya haura sama ɗakinshi.

Koda yaje bacci tunanin maryam yahanashi sukuni,hakanne yasa ya ɗauko wayarshi yakirata,bugu biyu ana ukun ta ɗaga cikin zazzaƙar muryarta tace.

"salamu alaikum"

Shuru yayi muryar tagama ratsashi tukuna sannan yace.

"waalaikumussalam yanmata ykk"

Tund yafara magana tagano muryarshi,dan itama wuni tayi tunaninshi,cike da faraa tace.

"au captain ne ashe,lafiya lau nake,kaifa?"


Dogon fasali yaja sannan yace.

"kinji daɗinki niko gani kwance banida lafiya"

aruɗe maryam ta furta.

"hasbunallahu waniimal wakeel me ya sameka,captain?"

Murmushi yayi sannan yace.

"ciwon sonki maryam,tunda naganki,kin hanani sukuni,pls karkice bakya sona,kisa na hana hajiya bacci yau"yaƙarasa maganar cikin shagwaɓa,nida nake gefe nace su farouk anyiwa hajiyama mara dalili,bare wannan me dalili ce.

Jikin maryam gaba ɗaya yamutu da salon na farouk,rasa abunyi tayi,murna zatayi kome.

shi yakatseta da cewa.

"pls kibani amsa don Allah,karkice zakimin wulaƙancin da yanmatan zamaninnan sukewa samari da sunan jan,aji,inkinasona kawai ki faɗamin base kin wahal daniba"

murmushi maryam tayi danta lura farouk rigimammene na ajin farko,intace zata ja lokaci bata bashi amsa ba,ze iya samata kuka.dan haka cikin salon siye zuciya,ta furta.

"nima ina sonka farouk,Allah yasanya akhairi atarayyarmu dakai"

wata ajiyar zuciya yasaki sannan yace.

"Ameen my wish"

daga haka hira yaɗan jata daita,se da dare yafarayi sukayi sallama kowa yakwanta cike da farincikin sabuwar soyayya.

Washegari dawuri yatashi yatafi masallaci yana dawowa yatarar hajiya ta haɗa mishi ruwan wanka,dan haka wanka yashiga,yana fitowa ya zura kakin shi,ya ɗauki takalmin da belt a hannu yasauka kasa gurin hajiya yakaimata tasa mishi.

Ayko tana sawa tana mushi mitar yayi aure ita tagaji,shiko se dariya yake mata,har tagama shiryashi,yaje yaci abinci,yafice yanufi gurin ayki.

*********

Farouk Ahmad sunan shi,haifaffen garin kaduna ne,saurayine ɗan kimanin shekaru talatin da haihuwa.

Mahaifin farouk,Alhaji Ahmd babban soja ne,inda yake da tarin dukiya me yawa,tunda suka haifi farouk basu sake haihuwa ba abunka da ƴan boko daga uwa har uba se basu damuba suka ci gaba da kulawa da ɗansu.

Farouk nada shekaru goma shabiyar mahaifinshi yarasu,kamin rasuwar mahaifinshi,yadamƙawa mahaifitarshi amanar farouk,tare da roƙonta tariƙe masa amana,karta bar farouk yayi kukan maraicinshi.

Wannan shine maƙasudin da hajiya saude mahaifiyar farouk ta ɗauki so da ƙaunar duniya ta ɗora masa,duk da kulawar datake bashi batayi wasa da ɓangaren tarbiyyarshiba,tana bashi tarbiyya dede gwargwado.

Tun tasowar farouk yake da shaawar zama likita,dan haka yana gama secondry school yatafi ƙasar egypt ɗomin karantar likitanci.

shekarunshi bakwai acan yadawo da shaidar kammala karatunshi,bayan daeowarshine kuma yaji yana shaawar,yazama soja kamar mahaifinshi,hajiya bata hanashiba fatan alkhairi taimasa.

Ayko yashiga gidan soja da ƙafar dama,yana shiga yayta samun ƙarin girma har zuwa yanzu dayake riƙe da muƙamin captain,yana kuma ayki a Asibitin 44 a matsayin babban likita.


farouk mutumne me tarbiyya,ko kaɗan baya aykata abun Allah wadai,ƴanmata da yawa nasonshi,amman shi ba abinda yadameshi dasu.

Farouk kyakkyawane ajin farko,namijine shi me cikar zati,shiyasa yake da kwarjini da haiba,a idon duk wani me kallonshi.

wannan kenan.

yana isa asibitin be jimaba,yafice zuwa nasu maryam.

Akunyace,tazo suka fan taba hira sannan yakoma bakin aykinshi.

koda maryam ta tashi agurin nata aykin,shi yazo ya ɗauketa yakaita har gida sannan yadawo bakin nashi aykin.

*******

Kimanin watanni biyar kenan farouk da maryam suna soyayya,hatta iyayenta sunsan dashi,hakanne yasa mahaifita faɗawa farouk yaturo magabatanshi,inda yamusu alƙawarin zuwansu cikin satin.

duk abinda akeyi ko kaɗan be bari hajiya tasaniba dan so yake yabata mamaki.

Gurin ƙannen mahaifinshi yaje yashaida musu,kuma ya roƙesu karsu bari hajiya taji,ba musu suka amince dan suma sun ƙosa farouk ɗin yayi aure.

cikin satin sukaje nemawa farouk auren maryam,inda basu baro gidanba seda aka tsaida ranar aure,watanni biyu masu zuwa.

murna gurin farouk da maryam kamarme,duk sun ƙosa ranar tayi.

Yau saura wata guda bikin,su farouk tuni har ankai lefe gidan su maryam batare da hajiya tasaniba,itade kullum cikin yimasa gorin yayi aure,take,sede yayi dariya yace,

"hajiyata kenan insha Allahu,sena baki mamaki,wato zanyi aure batare dakin saniba se ranar da aka kawo miki amarya kisa mata albarka"

Wata guɗa hajiya tasaki tace.

"da ko inkamin haka har in mutu bazan dena samaka albarka ba zanyi farinciki fiye da tunaninka,rawar dazan taka kuwa,seka riƙeni"

Kullum haka yake shaida mata,ita kuma tabashi amsa da haka.

Duk wata hanya da hajiya zata samu labari farouk yatosheta,dan gaba ɗaya hidimar bikin gidan kawunshi dake hayin banki aka koma yi,kuma kowa ya gargaɗi iyalinshi akan kar abari hajiya taji.


Da yake farouk yana da gida acikin malali GRA,gyarashi yayi yamasa sabon fenti,acan akaje akayi jeren kayan amarya,nandanan gida yafito yayi kyau,se fatan Allah yakawo amarya da angon cikinsa lafiya.


***********

Rana bata ƙarya,yau aka ɗaura auran farouk da maryam,bisa jagorancin kawunnanshi.

Murna da farincikin da farouk da maryam suke ciki baya misaltuwa.


ƙarfe biyar na yamma,motocin ɗaukar amarya,sukaje suka ɗauko amarya,haka aka ɗaukota cikin rakiyar danginta se kuka takeyi.

baa zame ko ina da ita ba se gidan hajiya domin tasa mata albarka.

muje zuwa

surbajo for life.
[07:39, 07/09/2017] ‪+234 806 958 0725‬: ⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩
*AMANA TA BARMIN*
⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩⛩


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*5-6*


Hajiya na zaune a falo tanashan fruitsalad taji ƙarar buɗe get,a zatonta farouk ne amman guɗa da hayaniyar data dunga jiyowane yasa tamiƙe ta leƙa ta window.

Jamaa birjik a tsakar gidan sun nufo falonta,da sauri ta koma ta zauna tana zaman jiran tsammani har mutane suka shigo falon da sallamarsu.

Ganin matan kawunnan farouk riƙe da wata wacce ta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AMANA TABARMIN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album