Join Our WhatsApp Group

MIJIN AMMINA NE SILA Complete Hausa Novel Document by MIJIN AMMINA NE SILA


MIJIN AMMINA NE SILA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 68845



MIJIN AMMINA NE SILA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 13, Dec 2023

Author: NoorEman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07082281566

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 375.63 kb

File Type: txt

Views: 570+

Download: 428+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: Written by noor Eemaan鉁?
Wattpad username:NoorEemaan

All characters in this story are all drawn from my imagination, any resemblance of story or life style should be consider as a coincidence.

Ban yarda ajuyamin labarina ta ko wacce siga ba, sannan duk wanda yayi daidai da yanayin rayuwarsa yayi min afuwa馃檹


The experience writer of RAYUWAR FAHEEMAH and now👇
MIJIN AMMINA NE SILA

In the name of Allah most glorious, most merciful.

Page1-2
*ASALINSU*

Rahilat yar asalin cameroon ce, su biyu kadai iyayensu suka haifa, ita da yayyarta raheenat, tun tasowarsu basu san wani dangin nasu ba domin suma haka iyayyensu suka taso yan siraru, yau da gobe wasu sun mutu basu kuma sun bar garin domin neman na kai domin sosai suke fama da talauci akauyen nasu.

kwance tashi har Allah yakawo wa raheenat miji aka yi biki wanda mijin mai suna nadeem kauyensu ke gaba dana su rahilat, akwai ranar da su rahilat baza su taba mantawa da ita ba, ranar da aka yi ruwan sama mai karfin gaske wanna yayi sanadiyan rayuwarsu domin ko gawarsu ba'a gani ba rahilat kuwa tana gidan yayarta raheenat, ta yi dare sai tayi zamanta dasafe sai tayi sammakon tafiya domin daman maa( mahaifiyarsu) tace mata matukar ta kai sakon yamma tayi mata ta zauna zuwa safiya domin hanyarsu bata da kyau, ai kuwa a washegari labari ya je musu, hankali tashe sukayi kauyensu, sosai sukayi kuka ganin gidan nasu tamkar mutum mai rai be taba rayuwa a ciki ba, har bukkar dasuke kwana ba alamarsa domin ruwan ya tafi da komai da kyar nadeem mijin raheenat ya rarrashe su suka koma kauyen da raheenat ke aure...

Su raheenat sun cigaba da kula da rahilat iya iyawarsu, bayan shekaru hudu rahilat ta hadu da wani buzun saurayi dan nijer me suna sajeed wanda kasuwanci ya kowashi nijer, ya rasa ubanshi tun yana karami yana tare da mahaiiyarsa tare da yan'uwanshi a babban gidan shi dake nijer domin yana da wadata, silan ahaduwarsu kuwa aranar raheenat ta aike rahilat kasuwa yayinda sajeed yazo kasuwar kauyen domin kasuwanci sa babu abunda ya dau hankalinsa kamar nutsuwarta da kuma brown skin dinta domin kyakyawa ce ajin farko amma ba fara bace, sabanin shi dayake fari sosai, be bar kauyen ba sai da ya datsa soyaayar sa azujiyar rahilat...

Bayan makonnin hudu yadawo tareda iyayensa domin a nema masa auren rahilat, duk da an kai ruwa rana kafin mahaifiyarsa ta amince domin acewarta tafi son ya auri yar nijer din, babu bata lokaci aka saka sati biyu masu zuwa da labarin talaucin su rahilat ya riski ummi mahaifiyar sajeed take takara jin tsanar rahilat domin ita kam bata son hada jini da talaka haka akayi auren suka kaita nijer wanda su raheenat jikinsu ita da nadeem asanyaye suka dawo asanadiyyar irin tarban wukalanci da aka musu

Haka ta cigaba da zaman hakuri a gidanta wanda tare da mahaifiyar sajeed har ma yan`uwansa na jiki ke zaune a babban family house din nasu, sosai rahilat ke zaman hakuri dasu, wurin mutane biyu kadai take jin dadi a gidan daga sajeed sai kanwar sajeed zulaihat wacce ke so rahilat sosai, sannan idan sajeed na gida basa takura mata domin duk wani nauyin gidan shi ke dauke musu shiyasa idan yana gari basa taruka mata bare sata aiki.



Bayan shekaru biyu rahilat ta haifi kyakyawar yarta wacce ta dauko brown skin din rahilat, duk wahalar nakudan da rahilat take ummi na ji amma bata ko leko ba, sai da zulaihat ta dawo daga makaranta hankali tashe ta kira wata unguwarzoma ta karbi haihuwar sai dai rahilat ta galabaita da kuma zub da jini sosai, domin ta kyar ta haihu saboda karfinta ya kare...

Kwanan ta biyar da haihu sajeed ya dawo daga tafiyan harkan kasuwancinsa, yayi murna sosai yama ki ajiye baby, su zulaihat sai dariya suke masa rada mata suna yayi kana ya kallesu fuskarsa dauke da murmushi yace Allah ya raya mana ABRAR SAJEED.
Dan'uwa menene ma'anar sunan yayi dadi, abrar ya nufin (mai tsoron Allah) masha Allah suka fada a tare domin sunan yayi musu. Zuhailat ummi bata shigo bane? ban ga kowa ba tun shigowata sajeed yatambaya inda- inda tafara yi domin batasan mezata ce masa ba duk da abunda ummi keyi bata jin dadi sam. bata jima da fita ba ka shigo rahilat tayi saurin fadi, cikin gamsuwa da jindadi ya jinjina Kansa, ajiyar zuciya zulaihat ta sauke ahankali tana yaba kyakyawan haleyan rahilat azuciyarta...

Kwance tashi ba wuya a wurin Allah abrar tana da shekaru goma 13 a duniya yanzu tun bata gane cewa yan'uwa babban ta basu sonta har ta gane domin abayyane suka nuna mata tsana banda zulaihat wacce aure ya rabasu a yanzu, abin burgewa kuwa abrar ta sauke qur'ani a wanna kananun shekarun na ta, haka zalika tana ss2 abangaren boko. A yau sajeed ze dawo daga china domin yanzu harka ta kara buda masa, abrar sai zumudi take abbi ze dawo, duk inda tayi rahilat na bin ta da kallo cikin kaunarta domin komai na ta ta dauko tamkar photocopy har ma ta zartata a kyau da kyawun fata abu daya ta dauko na mahaifinta gashinsu mai uban yawa na buzaye.

bayan wata biyu sajeed ya fara rashin lfy wanda be dau lokaci ba, Allah ya karbi ransa, ranar sun shiga tashin hankali domin sun rasa babban jigo mai kula da dukkanin al'amuransu.

Bayan wata biyar da kasuwar sajeed wanda rahilat ta gama takaban ta, sauran kwana uku araba musu gado, ummi ta kori rahilat cikin dare, babu irin rokon da bata yi ba, har ma da abrar rokon ummi take, amma haka ta kore su babu tausayi, suna kuka haka suka dau yan kayansu tare da kudadden da sajeed ke bar mata bata kashewa wanda ummi batasan da su ba. Gaba daya rahilat ta rasa ina suka nufa ga dare yayi, a tasha suka kwana washegari da asuba tunanin komawa cameroon ya zo mata, da zuwansu can suka ga gidan raheenat arufe wani gefen ma ya rushe alamun anjima ba mutum a ciki, gashi ba wasu gidaje kusa da gida balle ta tambaya ko suna ina, haka suka bar kauyen tana kuka domin bata sani ba ko yayarta da mijinta na raye ko a mace???

da fitowarsu cikin gari ta rasa ina suka nufa domin dare yayi, gaba daya tsoron komawa nijer take domin bata san sharrin da ummi ke dashi akan su ba, tunanin mai zurfi ta shiga can ta yanke shawaran barin kasar zuwa NIGERIA domin sanda sajeed ke raya yana yawan bata labarin kasar tana kuma sha'awar zuwa din, take taji mutuwar mijinta ya dawo mata sabo hawaye masu zafi suka saukar mata kwanansu uku a hanya suka iso domin da rabi da rabi ta dinga hawa abun hawa saboda kudin ya kai mata domin bataso su shiga halin matsi idan sun je kasar da basu san kowa ba. Tarihinsu a taikace kenan

*ABUJA*
A unguwar maraba dake abuja suka sauka domin nan sai sun fi samun saukin rayuwa domin a unguwar akwai masu karamin karfi ba laifi, da taimakon wata mata dasuka hadu a tashar abuja tasamu hayar daki daya a dubu arba'in da biyar.


washegari suka je kasuwa ta siyi leda dakin, labule, babban roban zuba ruwa, kwanunka, tukunya, cokula da dan abinda ba'a rasa ba a daki. Ragowar kudin ahannunta idan aka canza su zuwa kudin nigeria ze kai dubu dari, tunanin wani sana'a ya kamata su fara take domin kada kudin su kare a siyan abubuwa sun shiga halin kunci maganar abrar ya katse mata tunani

"Ammi ki siyamin nama in ci tun da abbi ya barmu na daina ci" abrar ta fada da hausarta wacce bata kama bakinta ba sosai kasancewar ba'a fi yi mata hausa ba, daga yaren cameroon sai buzanci, amma duk da haka hausar tayi dadi a muryanta mai gardi.

hawaye ne suka ciko idanun ammi domin kalaman diyarta ya sa ta tuno gwarzon mijinta, tabass shi ya saba mata da cin nama domin shima ma'abocin son nama ne sosai.

"abrar idan muka cigaba da siye-siye a haka kina tunanin kudin ze kai wani lokaci ba tare da ya kare ba?"
turo baki tayi batare da tace komai ba, murmushi ammi(rahilat) tayi cikin kaunar yar tata tace "wato ni kike turo wa karamin bakin ki nan zaki ga wanda ze siyo miki naman"
cikin sauri ta fada jikin ammi tace; kiyi hakuri ammina murmushi ammi tayi cikin canjin daya rage na siyeyyan ta bata dari biyar . "Maza je ki siyo awaje gidan nan kidawo domin nasan shi kika gani tsahon kwadayinki ya tashi" dariya abrar tayi ta fice cikin sauri domin har wani hadiyan yawu take tun kafin ma ta siyo😅

Washegari ammi ta siyo musu kayan abinci daze dade musu, kana ta yanke shawaran yin sana'ar kosai da kudin daya rage mata cikin ikon Allah ta fara kuma ba laifi tana ciniki sosai .

*BAYAN WATA UKU*
zuwa yanzu babu wanda be san ammi mai kosai da kunu ba domin har kunu take hadawa yanzu, har runfa gareta kuma tana samun riba har tana tunanin da an fara biyan kudin waec da neco zata biya wa abrar domin so take tayi karatu mai zurfi domin kula da rayuwarta koda bata raye...


Ahankali ya daidaita parking din motarsa kana ya fito yana bubbudewa kasancewar shi mai jiki, kayan jikinsa kadai ze tabattar maka da cewa shi din ya tara masu gidan rana(kudi) be cika fara'a ba, haka kuma shi din ba mai daure fuska bane baki ne sosai saidai halin jindadi dayake ciki yasa bakin nasa ke shining ashekaru be zae wuce49yrs ba.

Abrar dake taya ammi dauraye kwanunka kosai domin sun tashi kasanewar yau garin da sanyi yasa suka siyar da wuri, tun daga nesa take kallon wanna mutumin hakan nan ta ji sam be kwanta mata ba duk kananun shekarun ta.

Sallama yayi cikin kakkauran muryansa, ammi dake wanke kwanuka ta dago hadi da amsawa "sannu hajiya ya kasuwa?"
"Lafiya Alhamdulillah" ammi ta amsa
"Am idan bazaki damu ba inason magana dake na yan mintuna"

Mikewa ammi tayi tare da cewa "lafiya alhaji? eh toh lafiya lau ya amsa "
zan fara da cewa duk da baki nemi ki sani ba

" Sunana shettima turai a nan garin abuja na taso na rasa iyayyena tun ina karami
ban san kowa nawa ba, hakan yasa ban san ainihin garinmu ba domin iyayyena basu taba kaini ba ni dan kasuwa ne, shiru yayi kana ya cigaba yau kusan hudu ina hucewa ta nan ina ganinki, kuma na sha aikowa yarona yazo siyamin kosai awurin ki ina kuma jin dadin kosai domin kin iya sarrafa sosai, murmushi kawai ammi tayi domin babu wanda bayason ayaba masa shima alhajin murushi yayi ya cigaba da cewa maganar gaskiya inasonki da aure, nasa anyi min bincike akanki an kuma tabattar min da baki da aure a yanzu shine nace ko zaki taimaka ki auri wanna tsohon tuzurun ya karasa azolaye"

shiru ammi tayi tama rasa abun cewa domin ita kam ba aure a tsarinta, tun da ta rasa gwarzon mijinta auren ya fita kanta domin yanzu burinta shine ta inganta rayuwar tilon diyarta abrar.

" hmmm alhaji a gaskiya bazan... ammi kizo mu cigaba da aikinmu ni banason wanna mutumin ki rabudashi kizo muyi wanke-wankenmu" abrar ta fada cikin daga murya da yaren cameroon boyayyen ajiyar zuciya ammi ta sauke jin bada hausa tayi maganan ba.

"Ko zan iya sanin tarihin ki?"

Atakaice ta bashi labarinta, hakan nan taji bata yi musa masa
" a gaskiya na tausaya miki Allah ya jikan iyayenki tare da mijinki, idan kuma yar'uwarki da mijinta na raye Allah ya bayyanasu"

"Ameen" ta amsa cikin jin dadi.

Nan ya fara jan ta da hira da soyaaaya irin nasu na manya, sai da ya tabattar da cewa ya siye zuciyar ammi batare da ta sani ba lolz sannan ya barta da nufin tayi tunani ze dawo jibi, sallama yayi mata ya ja motarsa ya harba titi...

Runfar ta koma domin karasa aikinta saidai halin data ga abrar aciki yasa gabanta faduwa, hawaye ta gani a fuskar diyar ta mafi soyuwa arayuwarta
abrar!
abrar!!
abrar!!! ta sake kiranta a karo na uku kuma atsawace, fadawa jikin ammi tayi tana kuka har wani shidewa take, cikin shesheka tace
" ammi banason wanna mutumin kada ki kara yi masa magana kinji?" Tsoro ne ya kama ammi, domin abrar mai matukar son jama'a ce, tayaya daga ganin mutum yau daya ta tsaneshi? cikin son kwantar mata da hankali tace; abrar meyasa bakya son shi? mutumin kirki ne fa. ammina ni banason shi, haka kawai banason shi"

shiru ammi tayi cikin nazarin yaya zatayi? ga abrar na rigima, ga alhaji shettima na jiran amsar ta, ita kam har ga Allah ji take bazata iya bijirewa bukatarsa ba, domin hakan nan taji ya kwanta mata, duk da ada babu kara yin aure a lissafin ta, amma banda yanzu...

*BAYAN KWANA BIYU*
Alhaji shettima ya dawo domin yaji amsar sa babu dogon magana ammi ta amince masa, sosai yayi murna, kana ya bude motarsa ya mika mata shopping din da yayi wa abrar
" ayi haka alhaji kada dawainiyyan tayi yawa.
haba hajiyata ni ma ubanta ne ai, don haka komai zan iya mata in sha Allahu" cikin jindadi tayi masa addu'a domin duk mai son naka ya gama maka komai, haka ya kuma kara masa matsayi aranta...

bayan tafiyar alhaji ta koma cikin gida abrar ta samu zaune shiru har da taguminta.
"abrar?"
"na'am ammi"
"lafiya meke damunki?"
"babu komai ammi ta amsa asanyaye.

"toh gashi sabon daddyn ki ya siyo miki" ammin ta fada tana fitowa da kayayyakin, su chocolate, ice-cream, biscuits, tareda katuwar gashashiyyar kaza acikin ledan me dauke da tambarin shoprite.

abrar! ammi takira ta ganin ko motsi bata yi ba bare nuna jindadinta ga kayan musamman mutuminta nama.
"bakiji me nace ba? ko wani sabon hali kika tsiro dashi"ammin ta fada cikin yaren buzanci kasancewar sajeed mai rasuwa yana koya mata.

" ammi banaso indai wanna mutumin ne yakawo banaso
cikin mamaki ammi tace" har da kazar" ta fada tana nuna kazar dake ta daukan ido
har shi ammi banaso ta fada tana fashewa da kuka"

galala ammi tayi tana kallon ta cikin madaukakin mamaki domin duk wani hali da abrar take ciki bata wasa da nama, amma yau da bakinta tace bataso ran ammine ya baci domin bata ga dalilin daze sa abrar ta canza lokaci daya haka ba. Nan ta shiga yin fada sosai, tare da gaya mata cewa idan zata kwantar da hankalinta ta kwantar domin shine wanda zata aura...

kuka abrar ta fashe dashi kana tace "ammi kin daina sona ko? kin daina...


Read / Download MIJIN AMMINA NE SILA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album