Join Our WhatsApp Group

FADEELAH Complete Hausa Novel Document by FADEELAH


FADEELAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 35562



FADEELAH

Reading Time: 2 Hours

Added On: 03, Aug 2023

Author: Fadila Sani Bakori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 08063830828

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 191.5 kb

File Type: txt

Views: 1521+

Download: 443+

Last download: 9 days ago

Description/Story: ο»ΏπŸ“š FADEELAH πŸ“š

πŸ””πŸ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

πŸ’ͺ🏻J.A.W πŸ’ͺ🏻


Daga
Fadila Sani Bakori

Marubuciyar πŸ‘‡πŸ»

1) Oga Habib
2) Abdurrahim matukin jirgin ruwa ne
3) Meenalyn daddy
4) In da rai
5) Rayuwar Haidar
6) So ne sila
7) Daga Allah ko d'orawa kai And now Fadeelah


GARGAD'I: Ban laminta ayi min amfani ko a juyamin littafi ba tare da izinina ba, dan haka a kiyaye.
08063
830828



SANARWA" Masu tambayata akan gyaran jiki ,akwai hanyoyi daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna Fadeela.



GODIYA: Ina godiya da Allah Ubangijin talikai da ya ba ni lafiyar rubuta wannan littafi.Yadda na fara lafiya Allah ka sa in gama lafiya cike da nasarori.



SADAUKARWA" Wannan shafin sadaukarwa ne ga jaruman marubuta masu aiki da jarumta wajan fadakarwa, ilimantarwa ,tare da nishad'antar da jama'a abisa harshen Hausa,wato Jarumai writers association πŸ‘πŸ»


Littafin Fadeela na kud'i ne Auntyna, za ki same shi akan farashi mai sauki #300 kacal .


Page 1


Bismillahir rahmanir rahim.


KADUNA GARIN GWAMNA
Tafiya take yi ahankali da alama dai kamar agajiye take.Sanye take da jalbab Hijab brown har kasa sai madai-daiciyar hand bag da ta rataya a kafad'arta. Yanayin tafiyarta kawai zaka kalla kasan ma'abociyar hankali da tunani ce,dan duk da tafiyar da sauri take yinta,hakan be hana fitowar natsuwarta ba, akwai isassar natsuwa a tare da ita.Wani madai-daicin gida ta shiga wanda daga ganin gidan kasan mutanan cikinsa suna rayuwa a takura ne acikinsa,dan gidan k'arami ne kwarai, kuma gaba d'aya d'akuna biyu ne acikinsa,sai bayi da d'an k'aramin dak'in girkinsu (kitchen).


Da sallama ciki-ciki ta shiga gidan.
Wata dattijuwar matace ta fito daga kicin d'in , wadda ba zata haura shekaru arba'in ba, da gani girki take dan idonta sun cika da hayak'i ,jin sallamar Fadeelah ne ta fito.Kallan mai sallamar ta yi ta ce"Fadeela,yauma sai yanzu kika samu damar dawowa? " Wadda aka Kira da Fadeela cikin sanyi alamun dakyar ma take maganar ta ce"Yi hakuri Mama ,da fatan dai Baba bai dawo ba ?" Matar banza ta yi da Fadeelah ta koma kicin d'in ta ci ga da girkinta.


Fadila ko guri ta samu ta zauna tana mai yaye Hijab din jikinta,tana nan zaune wata yarinya daga gani dai k'anwarta ce ta zo ta ce"Aunty kin dawo?"Fadila kai ta d'aga ma yarinyar,yarinyar kuma ta ci gaba da cewa"Aunty ,Baba d'azu da ya dawo gida sai fad'a ya ke wai har yanzu biki dawo ba,kuma ya ce daga yau kin gama zuwa aiki"Fadeelah cikin furgici da jin abin da k'anwar tata ta ce ta d'ago manya-manyan idanunta tana kallan k'anwar tata da su ,tama kasa cewa komai,sannan dai zuwa can ta ce"Husna, an
b'ata ma Baba rai ne ? Inda ko da zan fita aiki mun gaisa da shi" Husna da yake irin yaran nan ne masu gulma da shaigen surutu, ta ce"Wallahi Aunty, ji na yi yana cewa wai daga y...."Bige bakin Husna da mahaifiyarsu ta yi ne ya sa ta yi shiru.


Fadeelah cikin damuwa ta kalli mahaifiyarta ta ce"Mama,abin da Husna ta ce da gaske ne ko?"Ban sani ba,idan Baban naku ya zo kin ji daga bakin shi,"



Fadila da a Duniya in dai kana so ka ga furgicinta tom ayi mata maganar dakatar da ita daga aikin da take yi a Rahama TV.



Ji tayi gaba daya ma yunwar da take ji ta koma,hakan ya sa ta shiga d'akinsu ta kwanta ,tana tunanin me za ta yi ko tace ma mahaifinta idan ya tunkareta da maganar,dan shekararta d'aya kenan da fara aikin amma kusan koda yaushe haka suke da mahaifinta,kusan kullum dai maganar kenan,har ta fara tunanin aje musu aikin su ta huta.



Fadila na nan kwance ta ji shigowar mahaifinta.Ya shigo ba jimawa aka kira sallar magriba,ana Kira ya tashi ya fita,hakan ya ba Fadeela damar fitowa tsakar gidan ta yi alwallah da sauri ta koma d'aki dan tana gudin had'uwarta da mahaifin nata.


Fadeelah bacin ta idar da sallar magriba ne ta aiki k'anwarta Husna ta zubo mata tuwo ta ci
Tana nan zaune tana jiran Kiran mahaifin nata amma shiru har barci ya kwasheta.


Washegari dama kullum k'arfe bakwai ( 7:00 AM) Fadeelah ke fita aiki, bayan ta idar da Sallah ta yi azakar kamar yadda ta saba duk safiya, ta yi wanka ta shirya ta d'akko Jakarta ta lallab'a tana tafiya,so take ta fita a hankali gudin kar mahaifinta ya ji motsinta,ta kama k'ofar gidan zata bude kenan sai jin muryar mahaifin nata ta yi yana cewa"Fadeelah, zo nan"gabanta na faduwa alamun tsorata da ganinta da mahaifin nata ya yi ta k'arasa inda yake.

Tana zuwa ta zuk'unna kanta k'asa,cikin rawar baki ta ce"Ina kwana Baba"Maimakon ya amsa gaisuwarta sai cewa ya yi"Ina za ki kike sand'o haka?"Cikin rawar baki Fadeelah ta ce"Aiki"Lafiya kike sand'o?" To nan fa ba amsa,shiru ne ya biyo baya.
Mahaifin Fadila cikin d'aga murya alamun ya fusata ya ce"Na ce lafiya kike sand'o? Hakan ya tabbatar min da kin ji sak'ona kenan ?"Fadila dai kanta kasa ta kasa cewa komai.Mahaifin Fadila ko ya ci gaba da cewa"Fadila,daga yau na hanaki wannan aiki dan bashi da amfanin komai gareki illah zagi da kike jawo min wajan jama'a, sannan zan baki zabi guda biyu zaki iya daukar duk wanda ya yi miki ko dai ki kawo min wanda kike so ko kuma ni in zab'a miki ,dan in Allah ya yarda ba zaki k'ara min wata uku agida ba,dan naga abin naki bana k'are ba ne!"Mahaifin Fadila na gama fadin abin da yake fada ya bar Fadila nan zuk'unne ya shige dak'in shi.

Fadila dakyar ta samu ta lallab'a ta tashi ,sannan ta Kira abokin aikinta. Bacin sun gaisa ne ta ce"Jamilu,Baba fa ya yi yadda ya saba,yau ma ya hanani zuwa aiki,ko kuma in ce maka ma yau ya fi na koyaushe, dan bana jin zai kuma barina k'ara zuwa aiki ,ina ganin Jamilu zan hak'ura in aje aiki kawai "
Wanda Fadila ta Kira da Jamila ya ce"A'a,Fadila kar ki yi haka, ni shawarar da zan baki ki yi auran mana, idan kina son aikin Wanda za ki aura in ya amince sai ki ci gaba da aikinki"Jamilu,kasan dai bana maka boye-boye ko? ko kuma ince kasan komai dan gane dani,wa zan aura in kace haka?" Daga can b'angaran Jamilu ya ce"Ina, M'd fa?, Allah Fadila da gaske yake son ki,ko aiki kina ganin sai ki kwana nawa biki zo ba amma ba zai ce miki komai ba,hakan kad'ai ya isa ya sa ki yarda yana sonki so na aur.."Fadila dakatar da Jamilu ta yi ta hanyar cewa"Dan Allah mu yi magana mai amfani kabar wannan maganar ina zan kai tunbin mutumin nan Allah bana son shi"Dariya Jamilu ya yi ya ce"Tom ,shi kenan zan tayaki addu'a, zan zo gidan in na tashi aiki in yi magana da Mama"

Sallama su ka yi ta kashe wayarta ta tashi ta koma d'akin su.Cire hijb din dake jikinta ta yi ta share dan madaidaicin gidan nasu,ta yi wanke-wanke, bacin ta gama ne ta samu mahaifiyarta ad'akin mahaifinta shi kuma lokacin ya fita.
Bacin sun gaisa ne Fadila ta kalli mahaifiyar tasu ta ce"Mama,dama nace inda yanzu Baba kasuwar sai a hankaki ,dan Allah kisa baki ya barni na ci gaba da aikina, albashin zai taimakamana"Mahaifiyar Fadila ta dade tana kallan Fadila bata tanka mata ba ,sannan zuwa can cikin sanyi ta ce"Fadila,mahaifinki fa shi ya biya miki kud'in da kika yi karatu har kika kai haka,kuma da amincewar shi da taimakonshi kika fara aikin nan,sai dai Fadila, tunda kika fara aikin nan k'ananun maganganu suka yi yawa akanki wa mutane,kowa da abin da yake cewa ,tom mahaifinki ya kasa jure maganar mutane dan acewarshi duk abin da aka ciki yawan magana akan shi baya albarka, saboda wasu bakinsu ba mai kyau bane, ni da mahaifinki munsan wacece ke ,tom amma futane sun sa ma aikin nan naki ido ana ganin kamar mun dogara da aikinne kina yawace-yawacanki kina cida mu in da yanzu kowa yasan mahaifinki ba kamar da ba ,dan haka ni yanzu shawarar da zan baki ki yi hakuri da aikin nan idan akwai wanda kuka yi wata magana ki fito da shi ki yi auranki, alabashi idan mijinki ya amince sai ki ci gaba da aikinki a d'akinki"Shiru Fadila ta yi,sannan zuwa can bacin ta ja doguwar ajiyar zuciya ta ce"Tom, Mama na ji na yarda, amma abin da nake so ki fahimta koda da fa na aje aiki a yanzu bani da wanda mu ka yi maganar aure"


Atakaice dai Fadila babu yadda ba ta yi ba ganin ta shawo kan mahaifiyarta akan mahaifinta ya janye kudirinsa akanta ,amma taki fahimta,dole ta hakura ta tashi.

Abu kamar wasa yau satin Fadila biyu kenan da daina zuwa aiki har ma ta hakura.

ADAMAWA STATE

Koda na shiga garin Adamawa ban tsaya ko ina ba sai gidan wani mai da na tsaya shan mai dan in kara gudu.Saidai sosai na mamaki ya isheni ganin an zuba min man ance in tafi ba tare da an amshi kud'ina ba.Mamaki ya sa na ja na tsaya na kasa tafiya.Abin mamaki motar da ke bayana ma hakan take itama ba'a anshi kud'in ta ba,haka akai ta zuba ma duk motar da ta shigo shan mai mai kyauta ba tare da an amshi kud'i ba.Ni ko kasa tafiya na yi dan ina son in ji dalin hakan,hakan ya sa na samu d'aya daga cikin ma'aikatan na tambayeshi dalilin da ya sa suke bada mai kyuta.Cikin washe baki ya nuna min wani bangare daga jikin gidan man ya ce min"Me aka rubuta a can?" Ni ko na bashi amsa da "Alhaji Sagir mai shadda" ya ce min "Tom yau ne ake auran yaronshi d'aya tilo,wato Muhammad Sagir,ai shi ne dalilin da ya sa kaga ana bada mai kyauta, murnar auran ne kasan yana ji da yaron sosai"Kai na jinjina sannan na kama hanya zan tafi,wanda na tambaya tareni ya yi da cewa"Amma dai Malam ba anan garin kake ba?"Eh,ni ba d'an garin nan ba ne,amma me ya sa ka tambayan?"Yau ai duk wanda yake Adamawa ya san alhaji Sagir mai shadda ,kai kuma naga bisa alama baka san shi ba shi ne dalilin tambayar" Kad'a kai na yi na tafi ba tare da na amsa mai ba.Ina fita ban tsaya ko ina ba sai Gidan Alhaji Sagir mai shadda,dan in je in inga wainar da za'a toya agidan ,dan nasan za ayi kallo,hakan ya sa na lalibi gidan.

Tun kafin in isa layin gidan nake jiyo ganguna maroka kala-kala natashi,tafiya nake ina kalle-kalle ganin tsaruwa layin gidan kawai,sai dai mai ina zuwa get d'in farko na shiga gidan akatareni alamun ina get past dina,hakan ya sa dole na ja na tsaya ,ina nan tsaye sai ga wasu maroka sun zo in bude musu get din za su shiga na yi b'adda kama na shige cikinsu muka shege tare.

Koda ganin yawan zama'ar taron bikin kadai ya isa ya shaidamaka bikin d'angata ake yi. Shagullula ake kala-kala na wasannin gargajiya da na zamani, nama rasa ina zan kallah,ga masu gidan gwarya nan da mabiyansu ,da masu kid'an shantu abin dai gunin burgewa.Barin wajan na yi dan naga jama'a sun fi ra'ja'a awani Shashi can da nake hangowa wanda adon wajan yafi na ko ina,sai dai tun kafin in isa wajan daddad'ar sanyayyar muyar Auta MG boy ce ke tashi a wajan,da sauri na isa wajan dan tabbas taron na manya ne.Cikin daddar muryar nan tasa yake rero ma amarya da ango wak'a ,Baitoci ne masu tsada ke tashi awajan Wanda sukasa na kasa matsawa ko ina.Ana cikin haka ne Amarya da ango suka iso wajan,sosai na shakala da kallan Muhammad Sagir,kyakkawan matashi ne dan kwalisa ,kallo daya za ka yi mai kasan bashi da wata damuwa , fuskar nan tashi cike take da annuri ,ga jajan lip's din shi da suka k'ara ma fuskarshi kyau.
Muhammad Sagir mai shadda kyakkyawa ne na bugawa a Jarida.Amayartashi ma ma sha Allah.Komai da komai ya ji dan itama zan iya kiranta kyakkyawa ta bugawa a Jarida.
A haka dai Auta MG Boy ya wakesu da wakar da ya yi ta dominsu.

Haka aka gama shagalgula aka d'auki Amarya aka nufi da ita gidanta da ke Nasarawa road.

Muhammad zaune agaban mahaifinshi da wadda take mazaunin uwa agaresa wato Hajiya baturiya.Mahaifin Sagir kallan hajiya baturiya ya yi ya ce"Ga shi nan ki yi mai nasiha kafin abokanshi su karaso"Murmushi hajiya baturiya ta yi ta ce"Abokanshi ai tuni na yi musu magana nace gobe sun je suga amarya, amma ni da kai za mu raka Muhammad gidan shi, dama kuma ba shi da abokan da suka wuce mu, dan haka ni da kai za mu raka shi"Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce"To fa,wannan kuma wana irin sabon salo ne? ace mu zamu raka shi d'akin shi ga abokanshi ga komai dan Allah ki bari su tafi da abokanshi"
Muhammad da sauri ya kalli mahaifinsa ya ce"Daddy,ka yi yadda mommy ta ce plz"Tom shi kenan Muhammad,amma fa sai dai ka Kira abokanka su je su sallami friends din amarya sannan ,idan ba haka ba, ba za ni ba"Muhammad waya ya ciro ya Kira Usman ya sanar da shi su je su sallami k'awayan amarya, daddynshi da mommynshi za su raka shi d'aki.

Usman da sauran abokan Muhammad suka je suka sallami kawayan amarya.

Can b'angaran Muhammad kuma mahaifinshi ya kallai ya ce"Muhammad,Hafsat dai k'anwarkace kaida ita duk kallo daya nake muku,kuma nasan Hafsat tana da hankali sosai dan Allah Muhammad ku zauna lafiya"Muhammad jinjin kai ya yi ya ce"In sha Allah Daddy"
Hajiya baturiya ma haka ta yi mai nasiha sosai,sannan ta kalli Alhaji Sagir ta ce"Alhaji,mu je anbar amarya ita kadai"

Amotar Alhaji Sagir suka tafi,shi ya ja motar, babu yadda Muhammad baiyi ba amma yaki yace shi angone ya huta.

Suna zuwa mai gadin ya bud'e musu get suka shiga.

Muhammad daidai kukannan hajiya baturiya ya ce"Mommy, ban fa so tafiyar nan da daddy ba, idan fa amarya ta rigo za ta yi min oyoyo ya zan yi da Daddy da muka tawo da shi?"Hajiya baturiya cikin tonan Muhammad ta kalli Alhaji Sagir ta ce"Alhaji,yanzu idan amaryata zo zata yi hugg..."Muhammad cikin zaro ido alamun tsoro da sauri ya rufe bakin hajiya baturi yana raurau da fuska alamun karta fad'a.Alhaji Sagir ko da ya gane inda maganar tasu ta dosa sharewa kawai ya yi yana murmushi.

Bakunansu d'auke da sallama suka shiga tankameman falon amaryar.
Saidai amaryar ba ta falon.
Hajiya Baturiya kallan Muhammad ta yi ta ce"Tom, ka shiga ciki ka fito mana da ita"

Muhammad kallan mahaifinshi ya yi ya ce "Daddy,Wallahi gabana fad'uwa ya ke yi tun...


Read / Download FADEELAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album