Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MUMMUNAN ZATO Book 2 Complete Hausa Novel Document by MUMMUNAN ZATO Book 2


MUMMUNAN ZATO Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38697



MUMMUNAN ZATO Book 2

Reading Time: 3 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Halima K Mashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 186.85 kb

File Type: txt

Views: 644+

Download: 637+

Last download: 4 days ago

Description/Story: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO Book 2📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*page 1*



A hankali ta maida ƙofar ta rufe, sannan ta juyo da nufin ta ƙaraso cikin ɗakin. Idanu ta zare tare da dafa ƙirji, sannan ta ce "innalillahi" lokaci guda ta juya baya ta runtse idanu,duk ta yi haka ne sakamakon ganin Uncle ya fito daga wanka daga shi sai gajeren wando,yana goge jikinshi da tawul. Ta kama ƙofar zata buɗe, ya ce "Beby" ta ce "Umm." Ta ce "bari....em....bari na dawo in ka gama ban san kana ciki ba ne,don Allah ka yi haƙuri." Ya ce "Me ki kayi min? Ki zo kiyi aikinki,kin ji ko" ta juyo amma ƙasa take kallo tana tafiya ta ci karo da gado, da sauri ta ɗago idanunta ta sauke su akan gadon, cikin mamaki ta tsaya kallon gadon sam bai kai nata girma ba, kuma shinfiɗe yake da zanin gado an lailaye shi,ta ɗago kai ta kalli Uncle tayi sauri ta kuma sunkuyar da kai don ganin har yanzun bai saka riga ba, kuma bai damu ba sai shafa manshi yake yi. Cikin in ina ta ce "An....an ma riga an gyara ashe?" Ya dube ta,duk ta daburce. Ya ɗauki riga shirt fara mai gajeren hannu ya saka,ya tako zuwa gurinta.

Ya kamo hannunta ya zaunar da ita yana riƙe da yatsunta cikin nashi kanta yana kallon ƙasa har yanzu bazata iya kallonshi ba saboda gajeren wandon bai rufe cinyoyinshi ba sannan duk cibiyoyinshi gashi ne, ya ɗan murza mata yatsun "Beby bai haramta ki ga tsiraici na ba,ko ni in ga naki ba" ta dube shi da sauri ya ce "Yes saboda ni da ke halalin juna muke" Ta sauke kanta ƙasa amma zuciyarta tana son ya fayyace mata komai don ita bata gane nufin shi ba,ya ce "yanzu dai Beby ni wanene a gurinki? Ma'ana menene matsayi na?" Ta dube shi sannan ta kuma sunkuyar da kai,a hankali ta ce "Miji" ya ce "me ake nufi da Miji? Ta yi shiru zuwa can ta ce "Wanda ya yi aure shi ne Miji" Uncle ya yi ɗan murmushi don jin shirmenta, ya ce to menene aure?" Ta ce "Aure?" Ya ce "Umh" ta ce kamar dai yanda ake yi mutane su taru a ɗaura shi kenan sai kuma a kai matar" ya ce "to daga nan fa?" Ta ɗan dube shi sannan ta rufe fuska, ya ce "Gaya min idan an kaita sai tayi me a gidan? Ta ce "zata rinka yin shara da wanke-wanke tanayin girki,ta rinƙa kula da yara.

Ya shafa hannunshi yana cewa, "Good, ashe kin sani? Ta yaya akeyi ta samu yaran?" Ta ce "Iye!' Ya ce "Ya ya za'ayi ta samu yaran?" Ta ce, "Ita ce zata haife su." Ya ce, "Haka nan zata haife su?" Ta ce "Eh,in cikinta ya yi girma." Ya gyara zama don jin sun gangaro inda yake son ji, ya ce "To ya ya akeyi ciki ya fito mata?" Ta ɗan yi jim,can ta ce, "Nima ban sani ba,ƙila wani abinci ake ci." Dariya ta kufce mishi, duk cikin matan da ya aura babu wadda ba ta san kan zaman aure ba kamar A'isha, duk da cewa akwai sa'arta cikin su, ya dube ta.

"Kina son ki san yadda ake a yi ciki?"

Kanta yana ƙasa ta ce, "Eh" ya yi ɗan murmushi ya ce, "In na tambaye ki abu ɗaya yanzun ba ki san shi ba, idan baki san shi ba,zan haɗa su in miki bayani. Amma in kin san shi to zan bar ki har ki sani da kanki,wato zai zama assignment,amma fa ba zaki tambayi kowa ba,kin yarda?" Ta ce"To ya ya za'ayi na sani in ban tambayi kowa ba?" Ya ce "Zaki sani,yau da gobe." Ta ce "To yi tambayar in ji". Ya ce "Kin san Haila? Da sauri ta saka kanta cikin cinyoyinta,don ya taɓo mata abinda ta fi jin kunya a rayuwarta,don in tana Haila ko Ummanta tana jin kunyar ta sanar da ita, sai dai ta yi ta nuƙu-nuƙu har Umman ta gano da kanta, ballantana Uncle wanda bata daɗe da saninshi ba,ba su yi sabon da zata yi mishi wannan maganar ba. Cikin dariya ya ce, gaya min mana Beby,kin taɓa yi ne? Miƙewa ta yi har tana cin karo ta fita da gudu.

Ɗaki ta koma ta faɗa kan gado zuciyarta tana ta bugawa, ita dai tana matuƙar jin kunyar Uncle,shi bai sani ba ne zai mata wannan tambayar?.

Shiko dariya ya dinga yi,lallai dole ya haƙura da A'isha yanzu don ba ya son takura mata. Ya fi son a yi komai cikin sauƙi kuma cikin ilimi.

Jummai kuwa tana ɗaki cikin murna haka nan wani gefe sai ta ji ranta ya ɓaci, da tana da iko ko macen ƙuda ba zata yarda ta saukar mata a kan miji ba, balle mutum, shi yasa ta sha alwashin ko zata tafi tsirara ne sai ta halaka duk macen da ta ce zata zauna zaman aure da mijinta. Ta sani goben nan yarinyar nan ta zama gawa,don haka ita ranta kar yake, insha Allahu. Ƙwana ta yi tana kai-kawo cikin ɗakinta,don ba zata iya runtsawa ba.

A'isha tana zaune tana tasbihi , sai kurum taga an turo mata ƙofa da ƙarfi. Cikin tsananin firgita ta miƙe tsaye, ganin Hajiya Jummai tuni ta soma karato addu'a cikin zuciyarta. Hajiya Jummai ta yi sororo ganin A'isha tsaye. Ta ce, A'a, ihun wa nike ji? Sai na ji kamar kakari a nan ɗakin." A'isha ta ce, "Kai,anya nan ne?" Ta ɗan yi tsaki tare da cewa, "Gaskiya ba nan ba ne." Hajiya Jummai ta shiga waige-waige, zuciyarta tana mai tabbatar mata ihun A'isha ta ji, amma abin al'ajabi A'ishar ce gabanta tana mai tabbatar mata cewa ba a ɗakin ba ne. A'isha ta ce "Allah ba nan bane Hajiya." Sannan ta ɗan rusuna ta ce, "ina ƙwana Hajiya?" Tsaki mai ƙarfi taja sannan ta fita a fusace, tare da sakin ƙofar da ƙarfi. Aisha ta yi shiru,a ranta tana son sanin me hakan ya ke nufi? Daga baya sai kurum ta taɓe bakinta gami da ɗaga kafaɗarta alamar su dai suka sani,ta koma ta zauna tana nazarin hirarsu da Uncle ta jiya. Daga bisani ta miƙe ta nufi kitchen ba don Uncle ba ne ya yi mata wannan tambayar game da Haila da zata ce ɗan iska ne,Don dai ta san halin Uncle shi ba ya iskanci. Uche ta samu yana aikinshi, suka gaisa sannan itama ta shiga haɗawa Uncle abin karyawa. Uche yana ɗan taya ta,ɗakinta ta nufa da tiren, tana shiga ta same shi zaune bakin gado cikin shirin fita. Ta dubi agogo,taƙwas saura ƙwata, ta ce Uncle har ka fito?" Ta dire tiren a gabanshi ta shiga haɗa mishi tea. Ta miƙa mishi sannan ta soma zuba mishi dankali da kwai tana saka mishi bota jikin bread,ya ce har fa na manta ina karyawa a gida,bari na sakko ƙasa Beby" ta miƙe ta ɗauko dardumar sallah ta shimfiɗa mishi, ya zauna ya shiga karyawa, sannan ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa cike da jin daɗi, sannan ya ce "Ya gajiyar gudu jiya daga tambaya Beby sai ki ka gudu ko?"

Cikin cinyarta ta saka kanta,ta ƙi ɗagowa me zai sa Uncle ya dinga irin wannan maganar? Ai wannan kamar na ƴan iska ne. Ita fa ko a school ba ta wannan hirar da ƙawayanta,nata ganin bai dace ba.

Ya ce "shin wai Beby menene abin jin kunya? Ta ce "Uncle don Allah ni dai ka daina wannan zancan." Ya ce "na daina Beby, shikenan?" Ta ɗaga kai alamun "Eh" ya ce "To oya ci abincin ki." Ta ce, Uncle nifa sai anjima zan karya, wannan duk naka ne" Ya ce,ya ya zanyi da wannan Beby? Ai babu tsari ga kowane musulmi ya zauna ya yi mugun ci, Manzon Allah (S.A.W) yana kasa cikinsa kashi uku ne, ɗaya abinci, ɗaya ruwa, da kuma ya shaƙi numfashi dashi,don haka kin ga tunda da shi muke koyi, sai mu ma mu ƙwatanta. Zaka ci ka ƙoshi amma ta yanda ba zaka kasa tashi ba.

Aisha ta ce, "Haka ne." Sai kusan tara ya fito daga ɗakin,yana son yarinyar ta shiga ranshi,ba ya gajiya da zama da ita yana son shirmenta,wani sa'in ta yi magana tamkar babba, wani sa'in kuma ta yi masa aikin ƙuruciya,waton shirme.

Kai tsaye ɗakin Jummai ya nufa,don yi mata sallama kamar yanda ya saba,in ba ya ɗakin ki zai zo ya yi miki sallama da safe in zai fita. Tana zaune abin duniya duk ya taru ya yi mata
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MUMMUNAN ZATO Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album