Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AMEENATOU 'YAR KAKA Complete Hausa Novel Document by AMEENATOU 'YAR KAKA


AMEENATOU 'YAR KAKA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23253



AMEENATOU 'YAR KAKA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 04, Mar 2025

Author: Aisha Mohammad Sani (Xayyishatul Humaira) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08103080717

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 134.37 kb

File Type: txt

Views: 54+

Download: 73+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: [12/1, 3:22 PM] +2348037420816: https://chat.whatsapp.com/IpsParMb6dOBXLpns86N2u

°°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-1/2*


Wata tsohuwa ce zaune akan kujera 'yar tsugunno tana tankad'e garin masara, a cikin wata 'katuwar 'kwarya.
"Oh! Ni Indo, ko ina Ameenatu ta tsaya ne? A ce tun almuru mutum ya fita har yanzu shiru."
Shiru ta yi kamar wacce ake fad'awa amsa, wani gutun tsaki ta ja ta ce,
"Ni ma na cika mantuwa halin Ameenatu sai dai wanda ba da shi Ibro da Hansai suka haifeta ba, yarinya sai ka ce rainon kaka."

Tankad'enta ta ci gaba hankali kwance, ba tare da damuwar komai ba har ta gama, ta mi'ke ta shiga madafa. Kamar wacce aka jefo ta shigo a guje ta bi ta kan 'kwaryan ta yi d'aki, baki bud'e tsohuwar ke kallon garin da ke zube a 'kasa, sannan ta bi sahun 'kafafunta da kallo, tana shirin magana ta ji sallama daga zaure, tana tsaye a inda take ta bada umarnin a shigo, ta hau 'ko'karin tattara garinta da ke 'kasa.


Ganin mutanen da suka shigo yasa ta d'agowa tare da mai da fuskarta alamun ba wasa, mutune biyar ne sai 'kananan yara 'yan ganin 'kwaf, Tumba mai awara da 'yarta, sai Halliru Mai Kaji, sai wata yarinya da namiji, jikin yarinyar sai zuba yake da manja, sama-sama suka gaisa, d'ayan namijin ne ya ce,

"Mun zo ne domin Ameenatu."

"Uhm ina sauraronku."

"Uwar yarinyar ta aiketa ta kai man ja gidan Sahura doguwa, ta had'u da Ameenatu a hanya, ba laifin zaune tsaye ko kwance ta juye mata shi a jiki bayan ta d'ura mata shi a baki."

Kallon yarinyar ta yi wacce a jiki da tsayi ta linka Ameenatu, nuna ta yi daga sama zuwa 'kasa ta ce,

"Ke kina shirgegeyiya haka kamar buhun siminti ta ya jikata zata yi miki wannan aika-aikar? Kin kwaso wasu 'kafufuwanki kamar fatanya da wannan jemamman tsohon naki kun zo sharrin dai da kuka saba yi ko? Toh ahir d'inku kurwar jikata ko harararta maye bazai yi ba ballantana ci, kai kuma Halliru fad'i naka."



"Zuwa ta yi kamar mutuniyar kirki tana taya Ni aiki da fira, ashe ta sa 'kawayenta su d'ebarmin 'kwayaye, sai da ja'irar yarinyar ta tafi na ga 'barnar da ta yimin."

Halliru Mai Kaji ya kai 'karshen zancen yana haki kamar ya zai sha'ko wuyar Tsohuwar, kallon Tumba da ke cika tana batsewa ta yi ta ce,

" ke ma fad'i kar ta kasheki."

"Ni ai sai na ga fitinanniyar jikar taki ta fito tukunnan."


Ta fad'a tana kallon yarinyarta, wacce goshinta ya kumbura ya yi lemon tsami, ba ta iya bud'e idonta saboda yashin da aka watsawa idon, ga bakinta na jini, fuskar kanta ta canza kammani, kakka'be hannnuwa Tsohuwar ta yi ta ce,

"Ameenatu dai bata nan, sai ki fad'i abin da ke ranki ko ki had'eye abarki."

Dukansu kallon shatin 'kafafuwan da ke zane a 'kasa da gari suka yi, ba sa tantamar Ameenatu tana ciki tana jinsu. Baki bud'e suka maida dubansu ga Tsohuwar, wacce ta 'kara tamke fuskarta.

"Uhm ke fa nake jira, ina da abin yi fa, in ke baki da aikin yi to Ni ina da shi."

Ta fad'a tana kallon Tumba, sannan ta waiwaya ga Halliru ta nunasa da yatsa ta ce,

" Ban ta'ba ganin mutumin banza ba irinka, tsabar rashin mutuncin ka kalli tsabar idanuna ka kira jikata da ja'ira, to babu ja'ira a zuri'ata sai dai ka gani a kanka, da kake maganar sun daukar maka 'kwai, dad'ina da bad'i saurin zuwa, zakkar da baka fitarwa ita suka fitar, ka godewa Allah da ba kazar suka d'auka ba, da kuka kwaso jiki kuka zo so kuke na biyaku, ko kuma na kama marainiyar Allah na jiba kamar jaka, to ba da Indo ba, na daina zubin adashin da babu d'auka ballantana riba, da a ce iya gaskiya kuka fad'a da na biya, amma sai kuka yi rashin sa'a harda sharri a maganarku, dan haka ko gaban Hashimu Mai Gari zaku je ba Baballe Mai Unguwa ba ku je, ku ce Ni Indo Saleh 'kawar wasan 'kasar uwarsa Lantana Sabi'u nace ba zan ba ku ko sisi ba, ku wuce ko fitarmin a gida gayyar tsiya tun kafin nayi muku rashin mutunci, kun ci sa'a yau bana jin rashin mutunci da surutu da kun ga tsiye da ta uwayenku ja'irai."


"Wallahi Inna ki ji tsoron Allah, wannan ba gata kike yiwa Ameenatu ba, a ce yarinya ta yi laifi ba za ki hukuntata ba sai dai ki goyi bayanta, wannan ba gata bane."

"Na daketa saboda gani tsinanniya ko? Na ce na daketa saboda gani tsinanniya ko?"

Gaba d'aya zaro idano waje suka yi ciki mamaki, bud'e baki Halliru ya yi da nufin kare kansu ya ce,

"Inna ba haka muke nufi ba fa, tunatarwa ne dai muke miki."

Wani kuka Tsohuwar ta saki,sai kace wacce aka ce wani nata ya mutu, cikin kukan ta ce,

"Bayan kun kirani da tsinanniya sannan kuma kuka ce min ma'karyaciya, ko iyayenku ba su isa su kira Ni da wad'annan sunayen ba ballantana ku 'kananan 'kwari, bari na nuna muku cewa ku din kananan kwari ne."

Ta'baryar da ke aje a gefen turmi ta d'auko, sanin halin Inna ya sa kafin ta jiyo sai dai ta ga takalma.

"Ai da kun tsaya kun ga 'karshen rashin mutunci marasa mutunci kawai, ke kuma ja'irar sai ki fito ai."




Lekowa tayi a hankali sai da ta tabbatar sun tafi kan ta fito tana kyalkyala dariya.


Taɓe baki Kaka tayi kan ta ce, "Kin ganki nan da wuya kamar mariƙin lema da ma na bari sun jajjaga mun ke ai na huta."


"Yoo su jajjagan mana wa aka ma asara? Kece za ki yi kuka wallahi bani ba,na ga ranar ma ban da lafiya kuka kike ehee sai in mutu ma kowa ya huta tunda kin gaji da ganina kuma ma."



Zaro ido kaka tai kan ta tallafo kan Ameenatou , "Kin ga rufamun asiri bar maganar mutuwar nan, yanzu je kiyi wanka kin ga rabonki da wanka tun shekaran jiya."


"Aradun Allah ba zan ba sai kace wata 'Yar ruwa,ni kifi ma na ke sha'awar ci bara in kira Furera da Lantana muje gun tumbiɗa mai kifi."


Daura hannu akai Kaka tayi.

"Oh ni Indo Allah Na Gode ma da ka bani Ameenatou yanzu duk abun da ki kai yau bai isheki ba sai kin karo wani?"


Ameenatou ta fara tafiya tana tsalle-tsallenta , "ki aje mun ruwan wankan inna dawo zan yi,bara muje gun Alhaji tumbiɗa mu dawo aheee kifi dadi wallahi zan rago miki kar ki damu Babar Maman Ameenatou Indo."


Har ta fita ta dawo aguje.

Sai da Kaka ta firgita.


"Ke lafiya? Me yafaru kuma?"


Buta ta dauka tana nishi, "Wallahi kashi nake ji, kashi zanyi wayyo kashina kar ka fito."



Tsaki Kaka ta yi, "yo ni na zata ma karshen duniyarce tazo ai irin wannan gudu." Ta ci gaba da shararta tana yan wake-wakensu na da.


Ameenatou kuwa kamar an shuka dawa a bandaki tunda ta shiga kusan minti talatin ba ta fito ba.


"Ke Ameenatou
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AMEENATOU 'YAR KAKA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album