Join Our WhatsApp Group

YAR TALAKAWA Complete Hausa Novel Document by YAR TALAKAWA


YAR TALAKAWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 41840



YAR TALAKAWA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 05, Apr 2024

Author: Afrah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 233.7 kb

File Type: txt

Views: 217+

Download: 285+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: ο»Ώ[8/8, 3:50 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳

Episode 1⃣



By ~ afrah


Bismillahil rahmanil rahim


"Tafe nake a cikin wata kasuwar fruits(kayan marmari),nazo wuce wata rumfa,mai dauke da kayan marmari kala kala, wata kyakkyawar yarinya na hango a ciki, sanye take da wasu kodaddun atamfa riga da skirt,yarinyar ba zata wuce shekaru sha shidda ba, sai tsalle take tana fadin, kuzo ku siya, namu sunfi zaki, tana maganar fuskar ta dauke da murmushi,kumatun ta sun lotsa, mutane dayawa suka tsaya a wurin suna kallon ta,kwanin sha'awa, gata kyakkyawa, ta dauko lemu,ta dauko alaba da sauran fruits din, tana fadi musu anfanin su,dan kawai su siya.

Ni afrah nace bari na bi wannan yarinya mai siyar da kayan marmari, dan kwaso wa masoyana labari.



Wani mutuni na gani ya kira ta ciki, yarinyar na murmushin mai kara mata kyau, tace ya habu har zamu tashi ne, naga akwai sauran jama'a a kasuwar, mu dan kara jira kaji, ya habu ya kalle ta yace NI'IMATU, ke bakya gajiya ne , tun safe kike tsalle tsallen nan, niimatu ta dara, ta kai wa ya habu naushi a hannu, ni ban gaji ba Allah, mudan kara jimawa kaji, ya habu yayi dariya, ke kam da namiji ce , da anyi jarumi.

Niimatu ta daure fuska, ohh ni yanzu ba jaruma bace ashe ko? Ta turo masa dan karamin bakin ta, ya habu yadan dungurar mata da kai, yace a tsalle tsallen kike jaruma, ya wuce waje abunsa, niimatu taja tsaki, sannan ta murmusa itama ta bishi wajen.


Umma !umma! Ina kike gamu mu dawo, umma ta fito cike da fara'a, niimatu tayi saurin ajiye ledar hannunta,tayi wurin umman ta rungume ta, umma tayi murmushi, niimatu bakya girma ko?, niimatu tayi murmushin ta, tana kallon umman tace, umma idan dai a gaban kine ni har yanzu yarinya ce karama, koda na haifi yara dari ne, umma tayi dariya , ya habu ya karaso ciki, yace umma sannu da gida?, umma tace ko keda sannu habu.

Sunyi wanka sun ci abinci, suna zaune dan tsakar gidan su, wanda ko siminti babu,ga ginin gidan duk ya lalace duk da na bulo ne, amma da yake ya tsofa, duk ya zaizaye.

Ya habu yasa hannu cikin aljihun sa, ya fiddo wasu yan kudi, ya mikawa umman, ga wannan nasan malam sahabi yazo, umma tace yazo kuwa dazun da rana, dama yace gobe idan munsan bamu da kudin hayan , toh kada mu sake ya iske mu anan, ya habu ya girgiza kai, Allah yana sane damu, kuma mun gode masa, daya barmu da ranmu da kuma lafiyar mu ,umma tace aini har yanzu ina nan ina wa bawan Allah nan daya baka rumfa , kuma ya baka kudin jarin nan addu'a, dan ba karamin taimakon mu yayi ba ,Ya habu yace nima ina masa addu'a har yanzu, umma.

Niimatu dake kwance kanta bisan cinyan umma, tana barci,sai munshari take, tana juye juye ,ya habu ya tafka mata bugu a baya, kee uwar munshari tashi ki koma daki. Niimatu ta mike ta kura masa ido tana smiling, ya habu yaja tsaki, ke wai bakya gajiya da murmushi ne, kumatun ki baya gajiya?, umma tace kyele ta habu ta huta, ba karamin kokari take ba, niimatu tace nifa ba barci nake ba yaya, kuma yaushe nayi munshari?, ya habu ya mike yace umma sai da safe, ke kuma , ya nuna niimatu, saura kiyi ta barci, kada ki tashi ki shirya da wuri, niimatu ta washe baki, ta nuna kanta nifa jaruma ce yaya.... ya habu yayi dan tsaki ya fice abunsa, dan idan zai biye wa niimatu bazai samu barcin kirki ba....






β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:50 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah



Episode2⃣




Washe gari da safe,niimatu ta kumo safko,tayi wankan ta,ta shirya cikin wata rigar ta gown ce ta shadda,shaddar kalar ja ce amma se ka rantse da Allah ba jar bace saboda kodewa, lekawa tayi cikin kicin dinsu na galan galan duk ya huhhuje ,hayaki ya turnuke shi,ummana ina kwana?,umma da idon ta yadan canza kala don hayaki tace, niimatu har kin tashi,ai da kin dan kara jimawa tunda yayan naki ma bai tashi ba, niimatu tayi murmushin ta tace , inna ya habu fa raggo ne, ko a kasuwa sai yayita wani gyangyadi, ni ce ma fa karfin wannan sana'ar tamu,kuma ma..

Ya habu da shigowar shi kenan cikin gidan, dan shi dakin sa a waje yake, jin niimatu na gulmar sa sai ya lallabo, yana zuwa bayanta yasa hannu ya dungurar mata da kai.

Auuuuushshshs..ya ya habu!!! Umma data dauko dan bokitin koko a hannu ta,tace ni ku dan matsa daga kofar nan na wuce...niimatu ta matsa,ya habu ya samu wuri ya zauna, niimatu tazo gaban sa tana dafe da kanta tace, ya habu mai na maka zaka dungure ni??? Ya habu yace gulmata na kama ki kina yi, niimatu ta tsoke baki, sannan tadan matso kusa da ya habu, tasa hannun ta a kansa taja gashin kansa kadan, habu yayi yar kara , keee miye haka?eyee!, niimatu ta kwashe da dariya, tace nima na rama ne ai, umma dake juya koko tace kai kuzo ku sha kokon ku tafi kasuwan kada rana tayi muku,.. su niimatu suka zauna suka sha kokon dawar su, dama shine suke sha duk safiya, sai idan Allah yadan huro sun dan samu ciniki sosai , suke sauyawa da wani abun.


Sun shiga kasuwa, niimatu taci gaba da advertising fruits dinsu, wasu dan kawai suga murmushin nan nata kawai suke zuwa siye a wurin su.


Da yamma ya habu ya kwala mata kira, tana daga dan cikin rumfar ta amsa, tace gani yaya, hijabin ta ya juye gefe guda, ya habu yayi dariya da gani an fara jin yunwa, dan naga anyi lauro, ba kuzarin tsalle tsallen da ake , ga hijabi kuma na kallon gabas itama, niimatu tayi murmushin ta, duk da eh da gasken yunwa take ji sosai, tun kokon safen da suka sha, gashi yanzu, har karfe biyar na yamma, ai dole taji yunwa.

Ya habu yace kici ayaba kuda biyu, yasa hannu cikin aljinhun sa, naira hamsin ya dauko ya mika mata, ga wannan kije wurin laure mai shinkafa da wake ki siwo mana mu dan ba cikin mu hakkin sa, da sauri ta dauki ayaban ta fara ci kamar ba suke siyar wa ba, ya habu yace ci a hankali niina, niimatu ta cika baki da ayaba amma sai data murmusa, ta mika hannu kawo hamsin din, ya habu ya mika mata yana dariya,easy niina, ta amsa da sauri, sannan ta fice da gudu.

Tana tafe tana murmushi, duk inda ta wuce sai an kalle ta, yarinyar ce akwai kyau ga fara'a.

Tazo wuce mai sai da kayan lambo, bata ankara ba taji ta buge mutum, jakar matar ta fadi kasa, a fusace ta juyo cikin masifa da isa.. ta kalli niimatu kasa da sama, kee miye haka ko bakya gani ne, tana maganar tana yatsine fuska.

Niimatu ta dago kanta ta kalli matar, sakin baki tayi, ta shagala da kallon kyakkyawar matar, gashi tasha ado sosai cikin kayan alfarma, ga kayan kyele kyele a jikin ta, matar ta wanka mata mari, keee.. bakya jina ne??!!!,,, niimatu tayi saurin cewa kiyi hakuri, ban lura bane wlh, matar ta watsa mata harara, mai saida kayan lambo yace hajiya kiyi hakuri dan Allah ba halin yarinyar bane rashin kunya,da gasken nasan bata lura dake bane..

Matar taja tsaki, tace wuce daga nan plss, niimatu tayi saurin wucewa tana waiwayen matar tana murmusawa abunta, matar ta sake jan tsaki , YAR TALAKAWA kawai sai iya kallon mutum kamar zata cinye ka.....




β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:50 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah




Episode 3⃣





Niimatu taje ta siyo musu dan shinkafa da waken su,ko mutum daya sai ya cinye bai koshi ba.

Sun tashi daga kasuwa da dan wuri,saboda ba yawan jama'a sosai a kasuwar, sun isa gida kenan aka kira sallar mangariba.

Niimatu na zaune tsakar dakin umma, litattafan makarantar ta ne take sake gyarawa,kusan kullum sai ta gyara su take yin barci.

Umma ta shigo dakin da fitila a hannunta,niimatu kin san dai ba wadda kika ajiye dazai kwashe miki kayan shanyarki ko?! Niimatu ta juyo tana kallon umma tana smiling, zan zo na kwashe yanzu umma, ina dan sake gyara jakar makaranta na ne, kinga damun samu kudin school fees din saina koma kawai , umma ta kura mata ido, yanzu ashe dama har yanzu niimatu bata cire rai da karatu ba?,! Yanzu a kalla an kusa shekara biyu da kuro ta daga makaranta, niimatu ce tadan taba umman nata, umma tunanin me kike, ko kinyi fushi ne dan banje na kwashe kayana ba a shanya??? Umma tayi murmushin dole, ta shafa kan niimatu, ni bana fushi da auta ta, ko nayi ma, wannan murmushin naki, zaisa na huce ai, niimatu ta wangale baki tace Allah umma??? Umma na neman zama a yar katifar su tace, eh mana murmushin ki nasa nI tuna mahaifun ku, niimatu tayi saurin zuwa ta zauna kusa da umma, shima haka babn mu yake? Yana son yin murmushi irin nawa? Umma ta kada mata kai, sannan ta jawo ta jikin ta, niimatu tace umma baki taba fada mana komai akan baban mu ba, sai a ringa cewa mu bamu da baba ne?? Umma tayi saurin share hawayen dake niyyar fitowa daga idonta, tace niimatu kuna da uba kinji, niimatu tayi smiling, na sani umma muna dashi, tunda ba yanda za'ayi ki haife mu ke kadai, umma tace hakane su auta an fara girma ashe, niimatu ta turo baki tana shure shuren shagwaba, ni ban fara girma ba umma , umma tayi dariya ta mike, ke ni tashi ki kwaso kayan ki dan ban manta ba.



****************************

Aysha shine asalin sunan umma, ba wanda zai iya fada maka daga inda take? Daga wane gari take, tazo garin suleja tun abubakar(habu) yana da shekara goma, lokacin niimatu na jaririya, a gidan wata tsohowa take zama, wadda ita ce ta taimake ta lokacin da bata da wurin kwana, a tasha suka hadu, tsohuwar ce ta rika su har na tsawon shekaru bakwai, sai Allah yayi mata rasuwa,yaran ta sukazo dan rabon gado, sahabi shine ya samu kason gidan dasu umma ke ciki, ya bar musu amma da sharadin sai umma ta amince ta aure shi, umman ta ki yarda da sharadin nasa, sahabi yace toh fah sai dai su bar masa gidan sa, umma ta roke shi ya bar musu gidan a haya, duk wata zasu ringa biyansa kudin sa.
Umma ba karamin wahala tasha ba, wurin ciyar da yaranta, har habu ya samu ya shiga collage, ita kuma niimatu aka sanya ta pri, kullum cikin koro niimatu ake daga makaranta, dan bata da kayan karatun irin su textbook, books da sauran su ,habu na ajin karshe a collage dinsa , aka bukatu wasu kudi daga garesu, na final year exams dinsu, umma tayi bakin kokarin ta dan ganin ta samo kudin amma inaa, duk inda take tsanmanin samu bata samo ba, haka habu yaci gaba da zuwa kasuwa yana dan samo musu na Maggie, karatu kuma tun daga lokacin ya fitar da ran yinsa,niimatu na jss2 , aka koro ta dan bata taba biya kudin makaranta ba tunda ta shiga school din.

Itama tunda daga ranar bata sake komawa ba. Har habu ya hadu da bawan Allah nan daya taimake su, habu ya fara saida kayan marmari a kasuwar suleja, niimatu ta matsa wa umma ita tana son ta ringa bin habu kasuwa, umma da farko taki yarda, ganin yadda niimatu ta dage sai ta amince ta sanar wa habu, shine yanzu suke tafiya tare.




β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:50 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah




Episode 3⃣





Niimatu taje ta siyo musu dan shinkafa da waken su,ko mutum daya sai ya cinye bai koshi ba.

Sun tashi daga kasuwa da dan wuri,saboda ba yawan jama'a sosai a kasuwar, sun isa gida kenan aka kira sallar mangariba.

Niimatu na zaune tsakar dakin umma, litattafan makarantar ta ne take sake gyarawa,kusan kullum sai ta gyara su take yin barci.

Umma ta shigo dakin da fitila a hannunta,niimatu kin san dai ba wadda kika ajiye dazai kwashe miki kayan shanyarki ko?! Niimatu ta juyo tana kallon umma tana smiling, zan zo na kwashe yanzu umma, ina dan sake gyara jakar makaranta na ne, kinga damun samu kudin school fees din saina koma kawai , umma ta kura mata ido, yanzu ashe dama har yanzu niimatu bata cire rai da karatu ba?,!...


Read / Download YAR TALAKAWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album