Join Our WhatsApp Group

GENERAL NASEER ZAKI Complete Hausa Novel Document by GENERAL NASEER ZAKI


GENERAL NASEER ZAKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23813



GENERAL NASEER ZAKI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 01, Dec 2023

Author: Azizat Hamza ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137311900

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 124.6 kb

File Type: txt

Views: 1040+

Download: 423+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Page 001


***

*2014*

*SOMEWHERE AROUND MADAGALI, ADAMAWA STATE*


Sati biyu kenan da Sojojin da ke ƙarƙashin ikon Colonel Naseer Muhammad Zaki suka kai hari wa sansanin 'yan bindigan Boko Haram.
An ɓadda wuta sosai a karon battar da aka yi, dan kuwa dukkan ɓangarorin biyu sun jigata sosai, daga ƙarshe dai Sojoji suka samu nasaran koran 'yan bindigan.

Sai dai fa tsugunne bata ƙare ba dan yadda 'yan bindigan suka gudu zuwa cikin duhun daji Sojojin na buƙatar a basu umurnin shiga cikin dajin dan su samu damar gamawa da 'yan bindigan gaba ɗaya.
Sai dai jiran wannan umurni da kuma ƙarin makamai da suke buƙata ya sa har yanzu ba su tsunduma cikin dajin ba. Amma a koda yaushe Colonel Zaki ƙoƙari ya ke wajen ganin ya horas da Sojojin da ke ƙarƙashinsa da shirin kota kwana.

"Colonel" wani Soja mai muƙamin Sergeant ya ɗaga hannu ya sarawa Colonel Zaki da ke tsaye yana duba wasu takardu cikin matsakaicin tantinsa.

"Sergeant Umar, ba ka yi bacci ba?" Colonel ya faɗa dan kuwa ya gane Sojan. Sati biyu da suka wuce da suka yi musayar wuta da 'yan bindiga aka kashe wani abokin Sergeant Umar ɗin wanda ya sa shi yin ƙaramar hauka a sansanin nasu. Da ƙyar aka samu Colonel ya lallaɓa shi har ya dawo dai-dai.
A lokacin ne Colonel Zaki ya ke ce masa idan sun samu fita daga wannan waje lafiya dole ne Sergeant Umar ya je rehabilitation saboda lafiyar ƙwaƙwalwarsa.
Colonel Zaki ba zai taɓa mantawa da abokinsa da ya haukace tuɓuran bayan sun dawo daga wani aiki da aka tura su ba.

"Colonel, ina jin tsoro" Sergeant ɗin ya katse masa tunani. "Ban yi aure ba. Bani da kowa sai Innata da ƙannena, saboda su na shiga aikin Soja"

"Umar" Colonel ya kira sunansa tare da dafa kafaɗansa. Dole ne ya kwantar masa da hankali dan Sojan da ba shi da ƙwarin gwiwa ba zai iya aiwatar da abinda ake buƙata ba.
Ba a san Soja da tsoro ba. Sai dai, Soja shi ma mutum ne da zai iya shiga wani yanayi na rashin ƙwarin gwiwa. Dan haka hakkinsa ne a matsayinsa na Shugaba ya ƙarfafa masa gwiwa.

Zuwa gobe da safe aka ce za a kawo musu makaman da suka buƙata. Dan haka ba za a jima ba za su shiga cikin daji su far ma 'yan bindiga.

Colonel Zaki ya shiga ba wa Sergeant ɗin baki tareda ƙarfafa masa gwiwa da cewa da sun samu nasara a harin da za su kai za su samu damar komawa gida, wannan zai ba shi damar samun kyakykyawar budurwa ya aura. Sergeant Umar ya buge da murmushi duk da kuwa zuciyarsa ta karaya sosai da aikin na su. Idan ya koma gida ɗin kam zai zauna kusa da Innarsa ne yai aure ya tara mata jikoki, zai ajiye aikin Soja gaba ɗaya.

Basu ankara ba sai suka jiyo ihu daga waje haɗe da ƙaran tashin gurneti.

"Colonel, we're ambushed, we're ambushed" Suka fara jiyowa daga waje. Wani Soja ya shigo tantin yana haki ya fara yiwa Colonel magana.
Yana ɗaya daga cikin masu gadin sansanin na su.

Kafin Colonel ya iya magana suka jiyo ƙaran bindigogi. Ashe ma 'yan bindigan har sun ƙaraso kusa da su.

Tuni Sergeant Umar ya saki fitsari saboda tsoro yayin da Colonel ya fita saboda a sansanin nasu shine mai bada umurni.

Wannan hari na bazata da 'yan bindigan suka kawowa sansanin Sojin da ke ƙarƙashin ikon Colonel Zaki a dai dai misalin ƙarfe biyun dare ya hargitsa sansanin na su gaba ɗaya.
Harbi da tashin gurneti kawai kake ji ta ko'ina yayinda Colonel ke ƙoƙarin bada umurni da iyaka ƙarfin muryansa. Sai dai kash! 'Yan bindigan sun riga sun cinmusu.

Musayar wuta aka cigaba da yi duk da kuwa cikin duhun dare ake, babu wani haske illa hasken taurari da ya ƙawata sararin samaniya.

Babu yadda za a yi su iya kare kansu daga harin bazata da aka musu. Idan ba su ceci kansu yanzu ba 'yan bindigan za su iya ƙarar da su gaba ɗaya, dan kuwa na su harsashen sun fara ƙarewa gashi kuma 'yan bindigan muggan makamai suka riƙo.

Wannan tunanin Colonel Zaki ya yi ya yanke hukuncin cetan rayukan Sojojinsa.

"Fall back. Fall back." Ya ke ta faɗa da iya ƙarfin muryansa yayinda ya ke ƙoƙarin gocewa harbin da ake kawo masa. Tuni Sojojin suka fara ja baya suna ƙoƙarin bin umurnin shugaban su.
Dole ne su gudu su samu mafaka saboda ta'adin da ake musu ya yi yawa.

Wutan da ke ci na wani tanti da aka cillawa wuta ne ya haskawa Colonel fiskar Sergeant Umar da ke tsaye jikin wata bishiya ya ɓuya.

"Sergeant Umar, Fall back" Colonel ya bashi Umurni amma tsoro ya hana Umar ɗin ya matsa daga wajen gashi kuma 'yan bindigan sun kusa isowa ta wajen da ya ke.

"Colonel" wani Soja ya dafa shi lokacin da ya sa kai zai je ta wajen da Sergeant Umar ɗin ya ke.

"Bamu da lokaci. Sun iso mu"
Ya gane me ya ke nufi amma ba zai iya barin Sergeant Umar ba. Gaba ɗaya Sojojin da suke nan suna da hakki a kansa.

Da kai ya yiwa Sojan da ya taɓa shi magana ya juya da sauri ya nufi inda Sergeant Umar ya ke da gudu. Yana cikin gudu aka harbe shi a kafaɗa sai dai harsashin wucewa ya yi ta gefen kafaɗansa ya ɗan goge shi. Wannan bai sa ya tsaya ba sai ma ƙara gudu da ya ke yana maimaita kalmar Shahada a bakinsa.

Yana isowa wajen Sergeant ɗin ya juya ya ga babu halin komawa baya saboda 'yan bindiga sun iso wajen. Sojan da ya taɓa shi ɗazu ma an halbe shi ya faɗi ƙasa.
Colonel Zaki ya kama Sergeant Umar suka kutsa cikin daji suna kaucewa harbin da ake musu.

Kafin su shige cikin duhun bishiyoyi aka harbi Colonel a gefen ciki.
Sergeant ya sake tsurewa amma kuma Colonel bai karaya ba ya ce su cigaba da gudu kawai.

Tun tsakar dare suke gudu har kusan Asuba kafin suka samu ɓoyewa cikin wani kogo.

Gaba ɗaya Colonel ya jigata saboda jini da ya ke ta zuba.
Sergeant Umar sai kuka ya ke duk da kuwa shi ba a harbe shi ba.
Da ƙyar Colonel ya samu kan Sergeant har ya iya ɗaure masa cikinsa da rigan Colonel ɗin.

Colonel ya rufe idonsa yana nishi saboda ba ƙaramin jin jiki ya ke ba.
Iya Abu ce ta fara faɗo masa. Yana da mata da 'ya'ya huɗu amma Mahaifiyarsa ce ta fara faɗo ransa. Aikin Sojan nan dai da naci da kuma kasancewar babu yadda ta iya ya sa mahaifiyarsa ta amince masa, amma har yanzu bata sonsa da aikin nasa. Idan ya je gaisheta da Uniform ɗinsa cewa ta ke " Nasiru ni kam ka dena karya min zuciya da kayankan nan" wannan ya sa idan ba uzuri ba in har zai je gabanta to kuwa sai yana cikin kayan gida.
Ya sani aikinsa na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Iya Abu ta ƙi zama da shi.

Da gari yai haske taimama suka yi suka yi Sallah a cikin kogon. Colonel Zaki dai sai a zaune ya yi Sallah.

Lokacin da rana ta fito Colonel ya ce su fita su nemi hanya ko za su iya isa ga samun taimako sai kuwa Sergeant ya birkice wai su cigaba da ɓuya cikin kogon kawai.

"Idan ba mu fita ba Umar yunwa da ishirwa zai kashemu a cikin kogon nan"

"Ba zan iya fita ba. Za su kashemu Colonel" Sergeant ɗin ya faɗa bakinsa na rawa dan gaba ɗaya ya kiɗime.

"Mutuwa ɗaya ce Umar. Idan za mu mutu gara mu mutu wajen ƙoƙarin tseratar da kanmu ba wai mu zauna mutuwa ta same mu muna matsorata ba"

Duk bayanin da Colonel ke yi babu wanda ke shiga kan Sergeant ɗin dan zuciyarsa ta riga ta gama tsorata babu wani sauran jarumta a tare da shi.

A haka dai Colonel ya haƙura suka wuni cikin kogon yunwa da ishirwa na koɗa su.

Da dare Colonel ya kasa haƙuri. Idan ya cigaba da zama a haka ba zai jima ba zai mutu, duk da ya dena zubar da jini zaman harsashin a cikinsa babbar illa ce ga rayuwarsa.
Da ya mutu matsoraci, gara ya mutu a jarumta.
Shi ba matsoraci bane. Naseer Muhammad Zaki ba matsoraci bane.

Da wannan ya ce wa Sergeant Umar su fita daga kogon su nemi koda ruwa ne sannan su sake maɓoya dan kuwa zamansu a nan ma haɗari ne.

Sergeant ya ƙi fir, wai yana tsoro.
Colonel ya daka masa tsawa ya ce masa idan ba zai fita ba zai bar shi a wajen.
Sai a lokacin Sergeant ya bi shi suka fita.
Colonel na ɗingishi suka fara tafiya suna neman gane hanya amma dajin ya juye musu.
Sai da suka yi tafiya mai nisa kafin suka samu wata ƙaramar ƙorama suka tsaya suka sha ruwa. Bayan nan kuma Sergeant Umar ya ce su nemi wajen ɓuya.
Tabbas shima Colonel ɗin ya gaji saboda gaba ɗaya bashi da ƙarfin jiki.
Basu samu abin da za su iya ci ba sai ganyen Kalgo suka tsinka suka ci.

Wannan karan da suka ɓuya Colonel ya sa a ransa gobe da safe za su fita ne su cigaba da tafiya. Ƙila idan suka yi tafiya cikin haske za su iya gane kan jejin sannan za su iya samun abinci ma.

Da safe kuwa da suka tashi gaba ɗaya ƙafafun Colonel sun kumbura. Duk da haka Colonel ya miƙe ya ce su fita su tafi, amma sam Sergeant Umar ya ƙi.

Colonel ya fita ya barshi a maɓoyarsu da niyyar zai je ya dawo.

Da ɗingishi ya ke tafiya yana ɗan tokarawa da bindigarsa da ta rage harsashi biyu a ciki.

Abinda ya fara lura da ya ke tafiya shine dajin da suka shiga shine dajin da 'yan bindigan suke, babu mamaki idan suka ce za su ƙara kwana a nan 'yan bindigan za su iya gano maɓoyarsu.

Yana cikin tafiya ya hango bishiyar Magarya ta yi 'ya'ya sun yi kore shar sai 'yan kaɗan kuma da suka fara nuna.
Ba tareda ya ji tsoron ƙayan ba ya fara cire 'ya'yan magaryan yana kaiwa bakinsa yana ci. Yana cikin tsinkan magarya ya jiwo hayaniyar 'yan bindiga. Cikin zuciyarsa ya yi kalmar shahada ya ɓoye cikin bishiyar ƙayoyin bishiyar suka soke shi har fuska.

Yana tsaye suka zo suka wuce basu ganshi ba. Sai da suka wuce ya fara tunanin Sergeant Umar dan hanyar maɓoyarsu suka yi.
Ba zai iya far musu ba dan kuwa za su kai su shabiyu gashi harsashi biyu ne kawai ya saura masa a cikin bindigarsa.

Ikon Allah ne ya kiyaye shi ya sa basu ganshi ba dan haka ya fara addu'ar Allah ya tsare masa Sergeant Umar.
Bai gama addu'ar ba kuwa ya jiyo ihunsu suna cewa Soja ne, Soja ne. Daga bisani ya jiyo ƙaran harbin bindiga har sau bakwai kafin ya ji shiru.
Hawaye ne suka zubo masa. Da ya sani bai bar Umar a baya ba. Da ya takura masa ya tursasa shi sun fito tare.

Sai da ya jima yana ƙoƙarin saita nitsuwarsa kafin ya tuno cewa tsawuwarsa a nan akwai hatsari.
Ya fito daga maɓoyarsa ya fara gudu.

Yunwa, ƙishi, gajiya, da kuma ciwo su suka saka Colonel Zaki ya gigice ya rasa ma ina ya nufa.
So ya ke koda wani gari ne ya samu ya cimma kafin rai ya yi halinsa. Yana fata koda Allah zai ɗau ransa to ya kasance kusa da mutanen da zasu masa sutura ko kuma su rufe shi. Ba ya so a ce gawarsa ta yi mushe a saman ƙasa.

Da dare ya yi ya samu jikin bishiya ya ɓuya. Sunan Allah kawai ya ke kira dan daga shi sai Allah ne yanzu, babu mai iya kuɓutar da shi daga halin da ya shiga sai Ubangijin da baya bacci.

"Ni kam aikin Sojan nan, Nasiru, Toh! Allah dai ya tsare, amma zuciyata bata so"
Ya tuno kalaman Iya Abu. Ya fara murmushi haɗe da hawaye.

Da sanyin Asuba ya sake miƙewa bayan ya yi sallah. Yanzu kam da izinin Allah sai ya cimma gari kafin dare.
Tafiya ya ke dan ba ya iya gudu yanzu. Ƙarfin jikinsa ya ƙare, dauriya ce kawai irinta Soja, Sojan ma namiji mazan fama.
Bai fara aikin Soja dan ya bari ba. Bai shiga aikin Soja ba sai da ya shirya.

Tafiya ya ke kawai baya ganin gabansa. Sunan Allah kawai ya riƙe a bakinsa.

Ƙarfinsa ya ƙare gaba ɗaya. Jan ƙafa kawai ya ke yana haki. Bai ankara ba kafarsa ta harɗe yai tuntuɓe da wani dutse ya faɗi. Ashe gefen wani rami ya ke. Ɗan yunƙurin da yai zai tashi ya ji ya gangara ƙasa ya faɗi tamau...

Ance kafin mutum ya mutu ya kan iya tuno gaba ɗaya rayuwarsa cikin abinda bai fi ƙiftawar ido ba.
A halin yanzu Iya Abu, matarsa Munira, ya'yansa Muhammad, Zarah, Khalil da Zainab ya ke hangowa.
Ƙila ya yi rayuwa mai kyau, ƙila kuma bai yi ba. Zai san makoman rayuwar da yayi ne kaɗai idan Malakul Mautu ya ƙariso gareshi...






***

To fah! Jama'a yanzu muka fara labarin General Naseer Zaki, da fatan za ku shigo da shirin ku dan a yi tafiyar tare da ku.


Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks. @ Azizat.
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 002





*1995, AZARE*



Iya Abu ke zaune a ƙofar ɗakinta, tana ƙoƙarin saita rediyo dan ta kamo labaran yammaci. Rediyon sai shiiii shiiii shiiii yake alamar dai ba a kamo setin tasha ba.
Ta sa hannu ta fara bubbuga rediyon dan ta ɗan fara jin alamar magana amma ƙaran ya hana maganar fitowa.

Ta buɗe bayan rediyon batiran ciki sun kumbura har sun fara baƙi-baƙi. Ta ciro su ta ɗan bubbugasu ta sa harshe ta ɗanɗani saman batiran, ɗan garɗin sinadatin acid...


Read / Download GENERAL NASEER ZAKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album