Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

AMAL Complete Hausa Novel Document by AMAL


AMAL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 49905



AMAL

Reading Time: 4 Hours

Added On: 28, Apr 2024

Author: Zeenaseer ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 285.26 kb

File Type: txt

Views: 318+

Download: 279+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: [12/29, 10:34 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.

GODIYA TA MUSAMMAN GA ALLAH SUBAHANAHU WATA ALAH,DAYA BANI DAMA DA BASIRA TA RUBUTA NOVEL,TARE DA GODIYA GA HAMAGEE NOVELS GROUP,ALLAH UBANJIGI YA BARMU TARE AMEEN.

🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)

1-5

Amal! Amal!!
Hjy ladi take faman kwala mata kira kamar Wanda makoshinta zai fito waje.hakanne hakan ne yasanya Amal rawar jiki,da murya mai rawa tace,ganinan hajiya.tsoki tana sannan ta koma saman kujera ta zauna,tana faman mita.yarinya sai shegen nawa,saikace wacce zata gasan sarauniyar kyau,karasa ubanme take,acikin daki,wani tsaka taja,sannan takuma bude murya ta a fusace.wai ubanme kikiye cikin dakinnan,wlh kika batamin lokaci jikinkine zai gaya miki,sai shegiyar nawa kika iya,cikin hanxari tafito daga dakin tana daura dankwali.cikin zuciyarta tana fadin,ko minti goma mutun beyiba amma ake faman yimasa fada kamar za'a cinyeshi.
Zuwa tayi ta durkusa agaban ta,kanta akasa,cinkin rawar murya tace hjy gani Dan girman Alla.....,Bata karasaba ta kwasheta da wani wawan mari,daya sata kifawa ba shiri ta dafe kuncinta tana hawaye.
Ubanme zaki gayamin shegiya mekama da aljannu,wallahi saina hanaki yin wankan gaba dayama,kin mai danima sa'ar wasanki,kin barni tun daxu anan ina faman jiranki,kuma kinsan sarai fita zanyi.
Cikin muryar kuka tace kiyi hakuri wallahi bansan fit......,Rufemun baki munafuka,inma kinsani fadamin zakiyi,wallahi kika cikani saina fasa miki baki,cewar hjy tana zaro Ido waje.
Ki bude kunnuwanki dakyau kijini,zanyi bako Dan gidan hajiya bilki zaizo daga London, kuma anan gidan zai zauna,Dan tayi tafiya zuwa Dubai. Girki zakiyi mai,kuma ki hadami drinks, sannan ki huce ki gyaramai wannan dakin nawajan garden. Kina jina ko kuwa.cikin rawar murya tace eh.yauwa saura kuma kimin hauka wallahi saina karyaki.
Cikin muryar kuka tace hjy ammafa yau kusan satina biyu banje islamiyaba kum.....,kuma me,kina nufi bazakiyi abunda nasakiba kenan.lallai Amal huyanki ya isa yanka,wallahi saina hadaki da ubanki,inni ban isa dakeba,shi ya isa dake.cikin kuka ta rike kafafunta tana kuka,wallahi zanyi hjy Dan Allh karki sanar masa,zanyi.mikewa tayi tare da hankade ta tafada sanman kafet,en dakin tana kuka.karma kiyi,gyalenta ta yafa,tareda rataye jakarta,tadau key din matarta ta fice daga falon.
Wani irin kukane mai karfi ya kwace mata,wannan wani irin ukubane ni Amal nake ciki,yaushene zansamu gata irinna kowane da,Allah na rukeka kasamamin mafita ya ubangiji,hawayene me zafi taci gaba da bin kuncinta.
Abun bakin cikinta shine ace itada gidan ubanta amma yn aeki sunfita samun hutu.kukan tacigaba dayi bame lallashinta harna wani Dan lokaci.
Hanne me aikici ta shigo Wanda shekarunta baxe dare na Amal enba.haba Amal kuka kuma,Dan Allh kiyi hakuri,nasan koda baki fadaba hjy ce,amma inda sabo kin saba,so kike kijama kanki wani ciwon ko Amal? Dan Allh kibar kuka kinji,badamin yanxu me zakiyi.
Hanne kinsan yau kusan satina biyu rabuna da islamiyah,kuma hadda zanyi amma shine hjy saboda tsabar mugunta tabani wani uban aeki,Wanda bawani nataba za aemawa,kawai dan gidan kawarta.hmmmm to shikenan naji yanxu de babu abundant zanyi taso muje muyi tare,dn Allh kibar kuka,baranaje na shanya kayan nan,saina dawo kinji tashi.Ahnkali ta taimaka mata ramike tabar falon.
Komai tare sukayi da hanne Har gyaran dakin,sai wajajan 4:00pm sannan suka kammala.
Saman dinning suka jere abincan da drinks en.sanna ko wance tayi dakinta da tsaftace jikinta.
Misalin karfe 5:00pm daidai jirgin so Annur ya sauka a airport en jigawa.bayan en mintina da saukarsa fasinjoji suka fara saukowa.
Ahankali yake takowa daga steps en jigin zuwa kasa,iska mai ddi tana kadawa,fuskarshi dauke da murmushi,fone inshine yayi kara,cikin nutsuwa ya sanya hannun shi cikin aljihunsa,da amsa kiran.murmushi yayi lokacin dayaga sunan me kirannashi.
Hello ummina abunda ya fada tare da kara wayartashi a kunne.daga dayan bangaran ta amsa, Son kun sauka lfy.lfy qlau Ummi.yauwa ga kawatana hjy ladi tun daxu take jiranka,a gidan ta zaka sauka nasan zata kulamun dakai sosai kaji son,cikin sanyi jiki yace ohk.be jira cewartaba ya katse wayar,Dan harga Allah ya tsani wadannan frnds en na umminshi Dan de bayanca zaiyi.
Hajiya ladi dake zaune akujerun gurin,lkc lkc tana kallon agogon hannunta,da tun around 4:30pm take agurin,waya dake rike a hannunta tana kallon pic en Annur da hjy Bilki ta turo mata.
Daga kan da zatayi ta hangoshi yana tahowa fuskarshi ba annurin dariya.baki bude take kallon sa,da ganinshi a zahiri.
Kyakyawan namiji dogo,me bakin suma da tsayi,yr madedeciyar fuska mai dauke da manyan idanu,a lumshe kamar namejin bacci,dagon hanci,da karamin baki,duk enda ake Neman namiji cikakke da yahada komai,kwarjini,ilmi,kudi,hankali,kasaita,Annur ya hada.
Gabanshi tasha tare da washemai baki,umm ..ammm Annur ko?kai kawai ya gyadamata tare da yimata Kallan mamaki,gaba yayi tareda jan trolley ensa,batare da yakuma magana ba,idonta ta kulle hadeda hade hanna yanta a kirji,son Annur na da da,shiga zuciyar ta,ta furta dulema alhaji kabar duniya Dan na samu cikar burina.

Dis page goes to my best grp ❤BEST FRIENDS❤tnkuuu for d Lov nd care.

Written by zeenaseer😘
[12/29, 10:34 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)

5&10

Misalin karfe 5:19mp,
Suka isa kobar gidan Alhaji Aliyu Dutse,horn biyu me gadi yabude gate en gidan,hancin motar ta tura zuwa cikin gidan,a parking space tayi park en motar.a hankali tabude side enta na driver,tafito,A hankali ta nufi side en da yake axaune,kafin ta budemai ya futa a hankali,sannan ya nufi Boot da fito da kayan sa.sanna ya tsaya yana jiran ta nuna masa masaukin sa,cikin kararraya takaraso tana kissa,yauwa muje mana ko,nabarka kanata faman wahala,ko kallanta beyiba yaci gaba da danna wayarsa,saida ta kuma maimaitawa sannan ya nuna mata hanya.tana tafiya tana rangwada,shikuwa kota kantama bayayi,har dakin ta rakashi,sanna ta bude masa,kanshin turaran hutan da sanyin AC ne ya daki hancinsa,ahankali ya lumshe idanunsa Dan turaran yayi masa ddi.da sallama ya shiga dakin bakin gado ya anje trolley ensa,sannan ya juwa ya fuskanceta cikin sanyin murya yace nagodeee!.lumshe Ido tayi sabo da ddin muryarsa tare da rufe idanu.juyawa tayi tana rangwada harta fice,murmushi yayi danshi mamakima take bashi,babba da ita amma take abun yara.hadawa yayi kan gadon tareda rufe idanun sa,ya bude ahankali ya saukeshi akan silin dakin.mikewa yayi ahankali yanufi toilet dan watsa ruwa.ya dade a toilet en Dan ruwan yayi masa ddi,sosai ya jima kafin ya fito ya sanya jallabiyan shi.
Masallaci yanufa danyin sallah magrib.
Bayan hjy ladi tagama tabaro dakin Annur, daki tanufa danyin wanka,bayan ta fito daga toilet zama tayi ta tsara kwalliyan ta,kamar wata budurwa,English wears ta sanya sannan matsatsato,tafbas tayi kyau.hjy dadi farace tas amma akwai Karin mai,tanada jiki,amma ko kadan bata da kyau,farinne kawai ya ceceta.
Bayan ta gama shirinta tamike cikin takunta na kasaita.dakin Annur tanufa tana rangwada.knocking tayi sau biyu sanna yabada iznin shiga,cikin sallama tashiga tana,ta huce bakin gado,tazauna kusa da kansa,a fusace ya miki yana kallan ta,meye hakane baki da hankaline,ko ke ba matar aure bacene,zakina shigewa mutumin daba muharraminkiba,pls kibar dakinnan karki batamin rai pls.cikin sanyin jiki tamike tanufi kofa,sannan ta juyo cike da kissa,dama cewa zanyi dakai abincinka na jiranaka.tana gama fadin haka ta turo masa kofar.tsaki yaja yana jin haushi irinna wannan ballagaxar mata.mikewa yayi badan yana soba,saboda yinwar dayake ji.
A dinning en ya sameta a zaune kujera yaja can nesa da ita ya zauna,yana danna wayarsa.kallonsa taci gaba dayi kamar mayya.
Amal! Amal!!
Amal dake zaune kan abun sallah tamike da hanzari tanufi kofar fita,a dinning ta sameta tare da bakwanta,cike da harara ta kalleta,kin tsayawa mutane,baki iya gaisuwaba,batare da ta kalleshi ta gaidashi,gabanshine ya buga lokacin dayaji murya mai ddi da sanyi,yana san dagowa ya kalli me wannan muryar amma yana ganin kamar ya zubda girmansa.
Dalllacan kizo kiyi serving en mutane suna jin yinwa,batace mata komai ba tafara zuba musu abincin.white rice ce,da stew tasha kaji,ta zuba masa fruit salad,da mango juice, sannan ta turamai gaban sa.tunda aka bude abincin kanshi ya cikamai hancinsa,burinshi kawai yafara ci yaji tests en abakinsa.
Jellof en taliya da tasha vegetable da kifi,ta zubama hajiya.sannan ta juya tanufi dakin ta.
Tafdi Jan!,abunda ya fito kenan daga bakin Amal,wato matarnan neman maxa kuma ta koma kenan,kina da auranki kizauna kina cin abinci da wani katan gardi,cikin irin wannan shiga,Allh ya kyauta.
Saida ya dauki kusan mintina goma kafin ya jawo abincin yafara ci,cikin nutsuwa,hajiya ladi data anje spoon enta,tana kallan Annur cike da so da kauna,komai nashi burgeta yakeyi,Allh ya bani wannan yaro,abunda take ta faman nanantawa cikin zuciyarta.shikuwa da besan tana yibama abincinsa kawai yakeci,cikeda jin ddin shi,yayi mai ddi sosai kamar Karya kare.sosai yadau lokaci kafin ya gama cin abincin,sannan ya shanye fruit salad en nasa,mikewa yyi,sannan ya nufi hanyar dakin sa.
Binshi kawai take da kallo kafin ta cemai saida safe.ko takanta be buba ya hucewar sa.naunauyar ajiyar zuciya ta sauke,sannan itama ta mike ta nufi part enta.

Sunday mrng 4:56am
...


Read / Download AMAL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album