Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO 1 Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO 1


HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 20588



HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 26, Sep 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 105.59 kb

File Type: txt

Views: 713+

Download: 163+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 1. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
.
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
.
Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Haruna, Bukar Mada.
.
An yi wani mutum a cikin Birnin Bagadada, lokacin mulkin Halifa Haruna Rashid, mai suna Sindibad. Wannan mutum ya kasance talaka ne, ba shi da wata sana'a sai dako - watau ya rika daukar wa mutane kaya bisa kansa daga wani wuri zuwa wani wuri ana biyansa. Wata rana Sindibad ya yi dakon wasu kaya masu nauyi, lokacin kuwa ana koda rana, kafin ya isa wurin da zai kai kayan nan ya yi gumi sharkaf, ga shi kuma ya gaji likis, sai ya biyo ta gaban wani babban gida. Da ganin wannan gida na wani babban attajiri ne, mai ji kudi. An share gaban gidan tas, an zuba wa shuke-shuken da ke wurin ruwa. Kodayake ana tsananin zafin rana amma gaban wannan gida sai wata iska mai sanyi ke kadawa kamar lokacin hunturu. Sindibad ya hangi wani dandamali a gaban gidan cikin shuke- shuken nan, ya ce a ransa, "Bari in dan zauna wurin nan in sarara kadan." Ya ajiye kayan dakonsa ya zauna bisa dandamali yana kwasar sassanyar iskar da ke tashi, sai ya ji wani irin kamshin abinci mai dadi na jifarsa daga cikin gidan nan. Can kuma sai ya rika jin kidan molo da busar sarewa na tashi. Ya jiyo muryoyin 'yan mata na rera wakoki, sai dai bai jin abin da suke fada saboda nisa. Daga cikin lambun gidan kuma tsuntsaye ne iri-iri bisa furannin suna ta rera nasu wakoki. Da ya duba kasa kuma sai ya ga wadansu 'yan kananan kwari masu ban sha'awa suna ta kai da komowa a cikin ciyawar da ta fito kasan furannin.
.
Sindibad ya yi mamaki matuka da yadda Allah mai girma da daukaka ya tsara wadannan abubuwa daki-daki, kowane gwanin ban sha'awa. Zuciyarsa ta yi fari bisa ga wadannan abubuwa da ke debe masa kewa. Amma kuma da ya tuna da halin da yake ciki na talauci sai ransa ya baci. Ya tashi ya leka cikin lambu sai ya hango bayi suna ta aiki sai ka ce gidan wani Sarki, wasu na ban ruwa, wasu na nome ciyayi, wasu na tsinkar 'ya'yan itace. Hancinsa kuwa ya ce me zai shaka in ba kamshin soyayyen nama ba. Da Sindibad ya ga irin wannan daula da mai gidan nan ya ke ciki sai ya daga hannayensa sama yana cewa, "Godiya ta tabbata gare ka ya Ubangijin talikai, mai arzuta wanda ya so a lokacin da ya so. Ya Ubangiji ina rokonka, ka yafe mini dukkanin zunubaina, gare ka kadai nake neman gafara. Ya Ubangiji kai ne mai yin yadda ka so ba tare da shawarar kowa ba, kuma babu wanda ya isa ya tambaye ka don me. Kai ne Ubangijin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu. Kai ne mai arzuta wanda ka so, ka kuma talauta wanda ka so. Kai ne mai daukaka wanda ka so, ka kuma kaskanta wanda ka so. Na tabbata babu wani abin bauta wa da gaskiya sai kai. Hakika kana daukaka wanda ka so kamar yadda ka daukaka ma'abucin wannan gida. Kana talauta wanda ka so kamar yadda na tsinci kaina a ciki." Sai ya wake wadannan baitoci: Mutum nawa ke wahala tamkata, Ga wasu sai hutu da sakewa. Kowace rana ga ni wahalce, Dauke da kaya babu dagawa. Dubi wadansu suna nan kwance, Kullum shan gara da dadawa.
.
Ba su tunanin daukar kaya, Mai nauyi ko mai sabawa. Asalinmu da kai duka daya ne, Ruwa na maniyi mai turawa. Banbancinmu akwai shi da dama, Tamkar na madaci ko zumuwa. Ya Allahu gare ka na roka, Ba ka zalunci cutarwa. Lokacin da Sindibad dan dako ya gama rera wannan waka sai ya dauki kayan dakonsa ya dora a kai zai tafi. Sai ga wani bawa ya fito daga cikin gidan, mai kyakkyawar fuska da madaidaicin jiki, da tufafi na alfarma. Ya kama hannun dan dako ya ce, "Shigo ciki shugabana na kira." Dan dako ya yi tsaye ya ki shiga cikin gida, ya ce wa bawa shi sauri yake yi ya kai kayan da ke bisa kansa. Bawa ya ce babu makawa sai ya shiga cikin gida. Da dai ya ga bawan nan ba zai bar shi ya tafi ba sai ya ajiye kayansa a bakin kofa, inda wani bawa ke gadi, ya bi bawan da aka aiko suka shiga cikin gida tare. Dan dako ya yi ta ware ido yana kallon kayan kawar da aka sanya a cikin gidan. Suka shiga cikin wani babban dakin shakatawa, suka tarar da mutane zazzaune bisa ababen zama, kowane daga cikinsu yana sanye da tufafi na alfarma masu tsadar gaske. Kallo daya za a yi musu a gane cewa babu daya daga cikinsu da ya san wani abu wai shi talauci. A gaban kowane mutum an ajiye akushin nama, da goran abin sha, da 'ya'yan itace, da furanni masu kamshin gaske. Ga kuma kuyangi kyawawa suna kada molo suna waka da rawa a gaban wadannan mutane.
.
Mutanen nan na zaune ne sahu-sahu, gwargwadon yawan dukiyar kowa. Manyan attajirai su ne a sahun farko, masu bi musu a sahu na bayansu, su ma masu bi musu a sahun bayansu. A gaban sahun farko akwai wani mutum dattijo mai tsawon gemu, wanda hurhura ta fara fitowa jefi-jefi a cikin gemun. Tufafinsa sun fi duka na sauran mutanen da ke wurin kyau. Yana da fuska mai annuri da yawan fara'a. Ga shi da kwarjini da farin jini. Wannan mutum dai shi ne mai wannan gida.
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
.
Sindibad dan dako ya dubi dakin shakatawar nan ya yi ajiyar zuciya, ya ce a cikin ransa, "Wallahi da a ce mutuwa na yi, na tashi na gan ni a wannan wuri, da na ce Aljanna ce. Babu shakka wannan wuri fadar wani babban Sarki ce, inda yakan zo domin shakatawa." Ya matsa gaban dattijon nan da ke gaban mutane ya durkusa ya gaishe shi, ya kuma gayar da sauran attajiran da ke cikin dakin. Ya mike tsaye a gabansu kansa a sunkuye yana duban kasa. Shugaban attajiran, dattijon da yake zaune a gaban sauran attajirai, ya umurci dan dako ya matso kusa gare shi. Ya yi masa barka da zuwa sa'annan ya sa aka kawo masa abin zama, ya umurce shi da ya zauna. Bayan ya zauna sai aka kawo masa abinci da abin sha. Dan dako ya wanke hannunsa, ya yi bismillah ya gini abinci har sai da ya kai masaba gatari. Ya wanke hannunsa ya yi hamdala, ya kuma yi wa attajirai godiya. Mai gida ya ce masa, "Mun yi murna da zuwanka. Amma menene sunanka?" Dan dako ya ce, "Ya shugabana, sunana Sindibad dan dako.
.
Amma Sindibad din har ya kusa bacewa sai dai a kira ni da dan dako, domin ita ce sana'ata." Mai gida ya wangame baki, alamun mamaki, ya ce, "Ka kuwa ga sunanmu daya da kai. Ni ma sunana Sindibad bahariyi ko kuma mai teku. Ana kirana da mai teku ne saboda yawan tafiye- tafiyen da na yi a cikin teku. Ko za ka rera mana wakar nan da muka jiyo kana rerawa a waje?" Dan dako ya sunkuyar da kansa cikin jin kunya, ya ce, "Ya shugabana, ka sani cewa idan talauci ya dabaibaye mutum bai san lokacin da yake furta wasu kalamai ba." Mai gida ya ce, "Kada ka ji kunya, ai yanzu ka zama dan uwana. Na ji dadin wakar ne lokacin da kake rera ta, shi ya sa nake so ka kara rera mini ita yanzu." Dan dako ya karkace kai ya kara rera waka. Yayin da sauran tajirai suka ji wannan waka sai suka cika da mamaki. Mai gida ya ce, "Ka sani ya kai dan dako, labarina abin mamaki ne. Zan gaya maka irin wahalhalun rayuwar da na shiga har Allah ya ba ni wannan tarin dukiya da kake gani. Kamar yadda ka ji ana cewa, zomo ba ya kamuwa daga zaune, to, wannan gaskiya ne.
.
Domin na sha wahalar rayuwa iri daban-daban, kafin in zama yadda nake yanzu. Ba don Allah ya kaddara ina da tsawon kwana ba ai da tuni an manta da ni saboda hadurran da na shiga Allah ya kubutar da ni. Na yi tafiye-tafiye har guda bakwai a cikin teku, kowace tafiya daya tana kunshe da labari mai ban tu'ajjibi. Kamar yadda na ce ma ba don Allah ya kaddare ni da tsawon kwana ba da tuni na halaka a cikin wadannan tafiye-tafiye."Daga nan sai Maigida ya daga murya da karfi, yadda duk wanda ke cikin dakin ke iya jin sa, ya ce, "Ya ku abokaina attajirai, yau zan gaya muku labarin tafiye-tafiyen da na yi guda bakwai masu hatsarin gaske da ban mamaki a cikin teku." Sai ya ci gaba da labari:
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
.
TAFIYAR SINDIBAD TA FARKO A CIKIN TEKU
.
Mahaifina attajiri ne na gaske mai ji da sulalla. Dukkan mutanen gari na son shi saboda yawan kyautarsa da kyawun dabi'unsa. Babban abin da ke ba mutane mamaki game da mahaifina shi ne duk da tarin dukiyar nan tasa ba ya da girman kai ko kadan. Ban girma na yi wayo tare da mahaifina ba, ya rasu lokacin da nake yaro, ya bar mini gadon tarin kudinsa da gidaje da gonaki, kasancewar ni kadai ne dan da ya haifa. Da na girma na yi wayo, sai idona ya bude da kudi. Na shiga cikin dukiyar nan ina bundum- bundum.
.
Ba na cin abinci sai lafiyayye mai kyau mai tsada, haka ma abin sha. Sutura kuwa sai irin ta 'ya'yan Sarakuna nake sanyawa. Wurin da nake kwanciya kuwa ko sarauniyar duniya duka sai haka. Na yi abokai da yawa, kullum sai in ta kashe musu gara suna kwasa a fayu. Su kuwa sai su yi ta zuga ni suna tara mini kasa ina hayewa, ina jin dadi. Ni kuwa na ci gaba da facaka da dukiya, a tsammanina ba za ta taba karewa ba. Haka na dawwama tsawon wani lokaci, har aka wayi gari ran nan ko dirhami bai rage mini ba. To, wanda ma ya tattali dukiya ya ya kare da ita, balle ni da na shiga barnatar da ita? Ko da na farga lokaci ya kure mini, domin ban da gidan da nake ciki babu wani abu da ya rage mini na dukiya. Hankalina fa ya tashi, ga abokaina duk sun guje mini saboda yanzu ba ni da sule.
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
.
Da ma an ce kuda ba ku biyar mai kayan gawai. Ban ga laifinsu ba, domin hannu mai miya ake lasa. Wata rana na yi zaune zugum ina tunanin inda zan sami dan dirhamin da zan sayi abinci, sai maganar Shugaba Sulaimanu Dan Dawuda (Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su) wadda nakan ji mahaifina yana yawan karantawa ta fado mini, "Gwamma abu uku da abu uku: gwamma ranar mutuwa da ranar haihuwa; gwamma kare mai rai da mataccen zaki; gwamma shiga kabari da bakin talauci." Da na tuna da wannan magana sai na tashi na tattara 'yan sauran komatsan da na mallaka har da suturata duka, na kai kasuwa na sayar a kan kudi dirhami dubu uku. Niyata in bi fatake in shiga duniya wurin fatauci, domin an ce babu maraya sai raggo, kuma sai an nema akan samu.
ete
Littattafan Hausa
2. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD
DAN DAKO
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
... Da na tuna da wannan magana sai na tashi na
tattara 'yan sauran komatsan da na mallaka har
da suturata duka, na kai kasuwa na sayar a kan
kudi dirhami dubu uku. Niyata in bi fatake in
shiga duniya wurin fatauci, domin an ce babu
maraya sai raggo, kuma sai an nema akan samu.
Kamar dai yadda mai waka ke fada a cikin
wadannan baitoci:
Sai an sha wuya akan sha dadi ku ji,
Mai neman kudi duka sai ya sha wuya.
Mai son jauhari a teku yakan zan nitso,
Mai son dukiya yakan shiga can duniya.
Kowacce a kan gado zai sami dukiya,
Wannan ya zama abin yi wa dariya.
Na tafi wurin madugun fatake na gaya masa
niyata ta bin su, na nemi shawara gare shi a kan
hajjar da ya kamata in saya in tafi da ita. Bayan
ya gaya mini hajjar da zan saye, na tafi kasuwa
na sayi dukkan abin da ya fada mini na kai gida
na ajiye ina jiran ranar da ayarin fatake zai tashi.
Da ranar ta zo na kwashi kayana muka shiga
wani babban jirgi tare da fatake, muka fada teku
muka tasar wa Birnin Basara. Muka isa lafiya,
muka dan taba ciniki a nan. Daga nan kuma
muka shiga jirgi muka tsunduma cikin teku. Gaba
da baya, dama da hauni, ba abin da mutum ke
gani sai ruwa. Muka yi ta keta ruwa kwana da
kwanaki, idan muka tarar da gari a bisa tsibiri sai
mu yada zango nan, mu dan taba ciniki sa'annan
mu yi gaba. Haka muka kasance muna tafiya
cikin teku, har wata rana muka iso ga wani dan
karamin tsibiri mai yawan tsire-tsire da furanni
masu ban sha'awa. Ga koramu na gudana da
tsuntsaye na shawagi. Kai! wannan tsibiri da
kyawo yake, ka ce shi wani yanki ne na Aljanna.
Madugunmu ya ce a sauka a wannan wuri a
daure jirgi.
Aka tsayar da jirgi bakin gaba, kowa ya sauka.
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
Da yake lokacin hunturu ne, sai wasu suka kunna
wuta domin su ji dumi, wasu kuma su dafa
abinci. Wasu kuma, har da ni, muka shiga zagaya
wannan tsibiri domin kashe kwarkwatar ido.
Muka shagala, muka sakankance a cikin wannan
yanayi. Can ba zato ba tsammani sai muka ji
Madugu na kwala mana kira da karfi, "Ya ku
jama'ar fatake! Ku yi gaggawar ceton rayukanku,
ku komo cikin jirgi da sauri! Ku sani wannan wuri
ba tsibiri ba ne face doron bayan wani katon kifi
da ya yunkuro domin shan iska. Ya dade a haka,
shekara da shekaru har rairayi ya taru a bayansa,
tsire-tsire suka fito. Wutar da kuka kunna ta
kona
shi, zai nutse cikin ruwa tare da ku. Ku yi sauri
ku tsira da rayukanku kafin ya nutse da ku cikin
ruwa."
Wadanda suke kusa da jirgi suka watsar da abin
da suke yi, na dahuwa da wankin tufafi da
wanka, suka fada cikin jirgi babu shiri. Amma mu
da muke nesa da jirgi kafin mu kawo wurinsa sai
muka ji tsibirin nan ya yi girgiza ya yi kasa da
mu cikin ruwa. Tozayen ruwa suka hadiye mu,
muka nutse cikin teku. Dukkan mutanen da muka
nutse tare suka halaka, amma ni da yake Allah
ya nufe ni ina da sauran shan ruwa a gaba,
wajen buge-bugena sai na ji na bugi wani
gungumen ice, na yi karfin hali na kama shi na
haye. Allah kuwa ya sa icen nan ya taso sama
da ni. Na yi kwance bisansa, ina iyo da kafafuna
iska na ingiza ni. Na hangi jirginmu...


Read / Download HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album