Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RUMBUN QAYA Complete Hausa Novel Document by RUMBUN QAYA


RUMBUN QAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23711



RUMBUN QAYA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 20, Jan 2025

Author: Hafsat Rano ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 127.34 kb

File Type: txt

Views: 382+

Download: 234+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: DANDANO DAGA LITTAFIN

💥RUMBUN QAYA💥

ZAFAFA BIYAR 2023

©®HAFSAT Rano



***Tana tsaye gaban coat din sa dake rataye a jikin hanger da yake makaleta kullum yazo office din, waige-wage take tana son yin sauri ta dauki key din, sai da ta tabbatar da babu motsin kowa tayi saurin saka hannu a aljihun rigar ta jawo key din ta damke a hannun ta.

"What are you doing..." Ya fada yana tsaye daga bayan ta

Saura kiris glasses din idon ta ya fadi kasa, tayi saurin tare shi da dayan hannun ta juyo tana kallon sa. Takowa ya shiga yi har zuwa gabanta yana kare mata kallo tun daga sama har k'asa, kafin ya maida kallon sa zuwa wajen coat din tashi dake sakale.

"Me kike yi anan?"

Yace muryar sa a d'an shake yana kallon fuskarta, kanta ta sunkuyar kasa sosai ya cigaba da kallon ta a nutse kafin yace

"Are you trying to steal something?"

Zaro idanun ta, tayi da sauri ta hau girgiza kai

"Then tell me, me kike min a wajen rigana?"

"Am..am... Dama nazo na kawo maka wanchan report din da na hada ne, so sai na tarar kana restroom shine na ajiye a saman table shine sai naga kamar wani abu a saman rigar shine nazo zan duba na cire maka."

Dan jim yayi yana kallon ta, kafin ya ja siririn tsaki ya nufi wajen zaman sa ya zauna.

"Show it to me."

Yace yana jan mouse ya dora hannun sa akai. Fakar idon sa tayi ta tura key din a cikin aljihun jacket din dake jikin ta sannan ta karaso ta dauki report din ta bud'e ta fara masa bayani. Danne dannen sa yake har ta gama sai da yaji tayi shiru sannan ya dago ya dan kalle ta

"Ina jinki."

"That's all." Tace

"Shikenan abinda kika iya samu?"

Gid'a kanta tayi kad'an

"Come here."

Yace yana maida kansa ya cigaba da abinda yake, gefen sa ta matsa ta tsaya daga dan baya

"Result din nake son gani, show it to me."

"Ok!" Tace ta dan runkwafo kad'an ta shiga nuna masa. Kamshin turaren ta ne ya shige masa chan cikin hancin sa ya haifar masa da mixed feeling, dan muskuta jikin sa yayi yadda ba zata gane ba amma still yana jin kamar sake matso shi yayi.

"It's ok!" Yace da dan karfi

"Just go, ki tura min ta email zan duba anjima."

"Ok...Thank you"

Tace dauki report din zata fita

"Wait..." Yace ta juyo ta tsaya

"Ki bawa Kamal shayi na ya kawo min."

"Ok sir."

"Sannan...karki kara saka turare me karfi idan zaki zo aiki."

"Na'am?"

"You heard me right! You may leave."

"Ok." Tace da saurin ta, ta fice hadda dan gudun ta

Tana fita ya saka hannu ya hau janye necktie din wuyan sa yana mikewa tsaye, ya isa gaban dan madaidacin fridge din sa ya dauki ruwa me sanyi ya hau sha

"May I come in?"

Ya turo kansa ya rike kofar ba tare da ya shigo ba

"Kana da matsala, kayi ta tsaiwa a wajen."

Yace yana dire robar ruwan ya shiga takawa zuwa seat din sa ya zauna. Shigowa yayi ya rufe kofar ya samu waje ya zauna shima yana murmushi


"Ya akayi?" Yace yana duban sa

"Akwai babban labari..."

"Kamar na me fa?"

"Barrister Nasir Matawalle is out!"

"What!!!? Ya fada yana mikewa

"Da gaske ko da wasa?"

"Allah kuwa, naji labari daga majiya me karfi ya fito earlier last week, but zancen dai be fito sosai ba dan kamar yaran sa ne basa so a sani saboda suna so ya samu kulawa ta musamman ne."

"Alhamdulillah!"

Ya fada a hankali yana maida kansa baya ya jingina da jikin kujerar yana lumshe idon sa.

"Me ya kamata ayi yanzu?" Kamal yace ganin yayi shiru, bud'e idanun sa yayi ya zauna sosai yace

"Time zamu samu muje mu ganshi, inaso na ganshi dan shi kadai yasan abinda ya samu Mom, shi ne kawai zai taimaka min na cika buri na."

"Kana ganin bud'e case din ba zai zama matsala ba? Kasan fa Daddy baya so, sannan sau nawa kana zuwa prison dan ganin sa amma yaki, kana ganin zai saurare ka yanzu bayan da be saurare ka ba?."

"I don't know... "

Yace yana tuna jelar zuwa prison din da ya dinga yi dan duk ya samu ganin shi amma fafur yaki yarda su yi wata doguwar magana.

"Toh yanzu dai menene abun yi?"

"Zuwa zamuyi mu ganshi din, ba kuma zamu hakura ba har sai ya hakura ya ganmu munyi magana, he's my only hope."

Shiru ya danyi sai ya dora

"Gaba daya rayuwata na yi ta ne akan jiran wannan ranar, that's what keeps me going, ba zan taba hutawa ba har sai na san abinda ya samu Mommy, wannan alkawari na ne, sai na bi kadin mahaifiyata, ko da hakan na nufin..."

"Shikenan, shikenan. You have my support, Allah ya bayyana Mama gaskiya."

"Amin thank you."

Yace yana hasaso abinda zai faru kuma, ajiyar zuciya ya sauke ya sake tashi da nufin dauko key din nan ya bawa Kamal.

***Tana fita daga office din nasa ta dauki handbag dinta akan table ta zare rigar saman ta ajiye ta fita da saurin ta, a titi ta tsaya ta kira wayar tana kokarin tsaida me napep

"Hello..." Tace tana fadawa cikin napep din bayan ya tsaya

"Eh na dauko, ina hanya ma."

Magana akayi daga dayan bangaren tace;

"Ok tam.."

ta kashe wayar tana sake duba key din ta tabbatar yana ciki. Tafiya kad'an suka isa unguwar, ta bashi kudin sa ta sauko ta karasa gidan a kafa.
Ciki ta shiga bayan an bud'e mata kofar tangamemen gidan da kaf unguwar babu me girman sa, yau ne karo na biyu da ta zo gidan amma sai take ganin kamar yau ne karon farko. A hankali take tafiya tana karewa gidan kallo har ta isa main part din. Tana zuwa daidai kofar ta bud'e da kanta, ta saka kanta ciki bakin ta dauke da sallama.
Tana hakimce a saman daya daga cikin kujerun falon rike da door remote din dan ita ta bud'e mata kofar dan ta hango ta tun sanda ta shigo gidan.

"Rayhana..."

Ta kira sunan ta tana sakar mata murmushi, murmushin ta maida mata itama ta gaishe ta a nutse sannan ta sa hannu ta ciro key din ta mika mata

"Good! Kin taimaka min sosai kamar yadda nima na taimake ki, kin saka alkhairi da alkhairi nagode sosai."

"Ba komai Aunty!" Tace tana murmushin jin dadi

"Me zaki sha a kawo miki?"

"Ba komai, komawa zan kar ya gane na fita."

"Ok! Zan kiraki kinji?"

"Ok." Ta mike tana rataya jakarta tayi hanyar fita

"Kin ga jirani mu fita dake dan nima wajen hanyar taku zanyi."

"Ok nagode."

Tace ta koma ta zauna ita kuma ta tashi ta shiga ciki bayan ta dora wayarta a saman hannun kujerar da Batul din ke zaune. Tana zaune wayar tayi yar kara alamun shigowar sako, kallon wayar tayi sai ta dauke kanta kawai tana cigaba da more kallon dankararren falon. Wani sakon ne ya sake shigowa a wannan karon sai ta kasa dauke idon ta akai ta shiga karanta sakon da yake yawo a saman wayar

_"An gama hajjaju, an zuba poison din, wuyarta Aryan yasha tea din nan, sai dai wani ba dai shi ba, tunda mun samu key din sai kiyi kokarin kwashe duk wani abu da ya tanada as evidence, ita kuma yarinyar ita za'a kama da case din poison din, kinga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya!!"_

Wani irin sarawa kanta yayi cikin yanayin tashin hankali ta mike tsaye

"_Na shiga uku!"_

Ta furta tana dafe kirjin ta.

_" Amfani dani tayi kenan? Karya tayi min tasa na dauko mata key din? Duk abinda ta fada min akan sa kenan karya take?."_

"Shayi? Wayyo innalillahi." Ta fada gabanta na faduwa

_"Ya Allah!!!"_

Da sauri ta juya har da dan gudu-gudu ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Zeenat ta fito, mamakin rashin ganin ta ya kamata ta shiga kiran sunan ta, waya ta dauka ta kira gate ta tambaya aka ce mata yanzu ta fito ta fita

"Ok... Ta huta" Ta dauki wayoyin nata ta watsa su a handbag dinta ta shiga kwalawa mai aikinta Harira kira

****Yadda take gudu zaka dauka mahaukaciya ce sabuwar kamu, kamar zata fada duk napep din da tazo haka ta dinga bin su idan ta tsaida su basu tsaya ba, a karshe ta samu wani ta fada tana haki. Suna isa ta ciro kudi bata duba ko nawa bane ta cilla masa ta shiga building din a guje. Bata san in da take jefa kafarta ba har ta isa reception din, baki daya ma'aikatan wajen duk suna tsaitsaye sun yi cirko-cirko, kallon ta suka shiga yi irin kallon tuhumar nan, jikinta ne ya hau rawa tayi saurin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RUMBUN QAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album