Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

TUMFAFIYA UWAR KWANKWAMAI Complete Hausa Novel Document by TUMFAFIYA UWAR KWANKWAMAI


TUMFAFIYA UWAR KWANKWAMAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33653



TUMFAFIYA UWAR KWANKWAMAI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Zainab Idris Makawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08036959257

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 177.88 kb

File Type: txt

Views: 542+

Download: 492+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: [16/12/2022 11:21 AM] Zee Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWAN MAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA

1️⃣

YA ALLAHU,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA A KANKI BA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN ,,,,,,,,

YAR UWA DA BAZANKU MUKE RAWA IDAN BA MAKARANTA BABU RUBUTU GODIYA GAREKU HAR KULLUN DA IRIN GOYON BAYAN DA KUKE BAMU MUKE CI GABA KULLUN,,,,,,,,

Matashine ke tafene da sauri a cikin tashin hankali kamar yadda kowama a unguwar yake cikin sauri dan yanayin da gari ya nuna idan da rabo ruwane zai iya gwaucewa a ko wani lokaci a garin.
Saidai shi kana ganin shi kasan yanayin shi baya cikin walwala a lokcin don yadda yake tafiyan zaka iya fahintar hakan gareshi .
Sauri yakeyi a cikin tafiyan shi irin na mazan dake da karfin kira da zatin karfi inda yake dan hadawa da sarsarfa don kada hadarin daya game gari yana shirin saukoda ruwa ya sameshi a hanya lokacin.
Yayafi akafara dan sakewa haka yasa ya kara saurinshi a lokacin ba komai yakewa sauri haka ba sai don abu biyu zuwa ukku na farko don kada yan tufafin dake jikinshi su jike dan ko a gobe su yake da niyar mayarwa a jikinshi da kuma yar jakkar shi da yake adana takardun karatunshi a ciki wanda ke rataye a kafadan shi.
Sai abuna biyu tunawa da kakan shi Dije dake gida ita kadai a wanan lokacin yasan ba kafane gareta ba a yanzu saboda tsufa daya fara kamata kafan na dan rike mata lokaci lokaci don ko da zai fita da safe ya barta dashi dan ya taso mata haikan yana mata ciwo a cikin yan kwanakin nan sosai.
Da sallama ya fada gidan idonshi ya fara tozali da Dije dake tsakar dan gidan nasu tsaye tana tafiya da kyar tana kokarin kama dabbobin dake ta kuka saboda yanayin hadarin da suka gani suma a lokacin.
Da sauri ya karasa inda take ya karbi dabbobin daga hannunta ya nufi dan rumfar da ake dauresu ya fara turkesu ita kuma tana kokarin juya zuwa daki take mashi sannu .
Yana ciki yana dauresu yaji saukan ruwan da karfi wanda kafin ya fito ruwa ya fado sosai ta yadda sai ya jika jikinshi dole don karfin ruwan.
Dakin kwanan dijen ya nufa da sauri ya fara walwale ledan da suke tare ruwan sama dake diga a dakin idan ana ruwan sama sai sukanyi wanan dabaran a daura leda koda ruwan zai zobo ba zai taba yan kayan dake dakin ba sai ya tsaya iya leda kawai.
Bayan ya gama daura ledan ya dan fara samun natsu a lokacin kafin ya kai hannu saman rigan jikin shi da ruwan ya riga ya taba ya fara balle bottom din rigan a hankali yana kallon yadda ruwan saman ke zuba.
Kallon rigan yayi ruwan saman ya riga ya taba duk da baiso hakan ba a lokacin saboda ita din yake da niyar mayarwa idan Allah yakaimu washegari zai fita.
Duban ruwan yayi daga inda yake tsaye a cikin dakin yaga yadda ruwa da iska ke zuba da karfi lokaci guda irin na tsakiyan damana din nan mai barna ga mutane da kaddarorinsu.
Ajiyan zuciya ya sauke don yasan yau akwai barna idan ba Allah ya gyara ba ke nan dole haka ya ratsa ruwan ya fito a guje zuwa dan karamin dakin shi da yake kwana a cikin gidan tsohuwan kakan nasa da ita ke nan masa tillo dake kula da komai nasa .
Kayan ya sauya tare da baza wanda ya cire a jikin shi zuwa wani tsohon gajeren wandon shi da wata riga nasa daya tsufa har ya dan fara cacakewa don tsufa amma haka yake amfani dashi idan yana cikin gida.
Komawa yayi ya rakube a wuri daya kafin ya fara bin dakin da duba na dan lokacin yana sauke ajiyan zuciya a hankali tare da kara kai kallonshi gun kofa yana kallon yadda ruwan ke zuba da karfin Allah.
Wani ajiyan zuciya ya kara saukewa a hankali tare da lumshe idanuwan shi yana ci gaba da tunanen kuncin rayuwan da sukeyi a gidan dashi da kakanshi Dije.
Baida kamar Dije din yanzu a duniya don da Dije ya bude idanun shi da Dije ya taso a rayuwanshi yau duk abinda ya zama Dijene silla itace gatanshi a duniyan nan.
Don itace uwa uba kaka a gareshi tun tasowan shi bai san kowa na kusa nasa ba idan ka debe Dije dake bashi kulawa irin na mahaifa don a tare da ita ya taso ya bude idon shi.
Wani irin tsawa aka sake lokaci daya tare da walkiyan da yai sanadiyar budewan idonshi da sauri yana karanto addua a bakin shi subbuhul kudus wal,mala,ikatu walruhu,,,,,,
Ihun da yaji kamar a makwabtansu yasashi bude idon da sauri tare da kara dan firgitashi lokaci guda don yana ji yasan ihun bana lafiya bace.
Don kusan haka suke fama duk shekara sai sun samu wanan matsalan ruwan saman kasancewa gidanjen unguwar duk tsofin ginene ne irin nada can baya.
Wanan yasa duk shekara idan ruwan sama ya fado hannunsu a gaba yake don fargaban ruwan sama yadda zai kasance masu yawancin gidajen basu da sukuni idan ba sunga an dauke ruwa ba.
Gashi talauci irin na yan arewa yayi masu katutu ba zarahin gina wani a garesu sai wanda Allah ya tallafawa ya samu wani budi zai dan yiwa nasa kwaskwarima ko a fita ciki.
Wanan yasa ake kiran unguwan da tsohon gari don mafi yawan gidajen dake unguwar duk gidajen tallakwane a wurin matasa da masu kudi sunfi komawa daga bayan gari
suna ginan su irinna zamani.
Kakan wanan matashin gidanta na daga cikin jerin gidajen dake cikin wanan unguwar ta tallakawan dake fama da barazanan ruwan saman a duk shekara.
Duk da karfin ruwan saman da iska da akeyi a lokacin bai hana yan unguwan jin kururuwan wasu mazauna unguwan da iska da ruwan saman yayiwa barna a ranan .
Haka ya jawo hankalin sauran yan unguwan suka fara fitowa daga gidajen su don zuwa bada agaji kamar yadda suka saba bawa junan su lokaci lokaci.
Dakin kakanshi ya fara nufa inda ya samu duk da ledan daya daura mata don tare feshin ruwa dake diga a dakin yau karfin wanan ruwan bai tsaya a iya ledan ba kwarai ga tsohuwar tsugune tana faman tara yan tsummakara tana tare ruwan dake dan dinga daga saman dan rufin kwanon dakin wanda duk kwanon ya riga daya tsufa sosai a lokacin saboda dadewan da yayi.
Ihu nake ji a waje ya fada yana karban abinda take kwasan ruwan dashi dake hannunta bata kai ga mika mashi ba, take fadin jeka kakai masu agaji saboda Allah.
Tun ganin yadda aka hada hsdarin nan nasan yau unguwar nan sai yadda Allah yayi damu don wanan ruwan da karfi ga iska yake sauka ji dakin na duk da wanan dabaran saka mai ledan da kayi amma sai zuban ruwa yakeyi yau din nan.
Juyawa yayi da sauri ya fice ya barta a duke tana magana ita kadai yana fita abinda ya gani ya kara daga mai hankali don ruwane ko ina a kwance zakace a tsakiyan rafi gidajensu yake a unguwar.
Da sauri ya kara kai kallon shi gefen hagu gidan malam Tanimu mai faskarene yayi flat kamar ba a taba gina a wurin ba.
Gasu tsatsaye sai ihu iyalinshi keyi suna neman taimako ga jama,a da suka fito don kawo masu agaji ga kururuwan neman agajin da sukeyi.
Hankali tashe ya nufi wurin a gigice da alama akwai wani da ginan ya rufta dashi don yadda suke kururuwan taimako daga jama,a.
Gashi sai su biyu yake ganin sun fito don basu agaji don kowa na cikin gidansa a lokacin ya kasa ya tsare ana duban hukuncin ubangiji.
Malam suke fadi kawai don matar gidan daga ita sai zani daura gaba kawai a...


Read / Download TUMFAFIYA UWAR KWANKWAMAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album