Join Our WhatsApp Group

BONGEL Complete Hausa Novel Document by BONGEL


BONGEL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36693



BONGEL

Reading Time: 3 Hours

Added On: 30, Aug 2023

Author: Zee Yabour ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HASKE WRITERS ASSO

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 200.42 kb

File Type: txt

Views: 1472+

Download: 509+

Last download: 12 hours ago

Description/Story:  Zee Yabour: BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


Bismillaahir rahmanir raheem
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai'

SHAFI NA D'AYA


GGC KABOMO

Yara ne mata manya da k'anana duka sanye da uniform na makaranta, kowa da abunda yake yi, wasu na wasanni, wasu na cin abinci wanda ke nuni da lokaci ne na break, Yanayin yaran zai tabbatar maka iyayen su ba masu hali bane, makaranta ce ta gwamnati wacce ana jeka ka dawo kuma akwai b'angaren yan' kwana.


Budurwa ce yar' kimanin shekaru 17 da haihuwa zaune a aji ita kad'ai, littafi a gabanta tana bitar karatu, "Bongel sarkin boko, wai bakya gajiya da karatu" Cewar Asiya da shigowar ta kenan, itama ba zata gaza shekaru 17 da haihuwa ba, Ta d'ago kai ta kalle ta tace "Hmm Asiya kenan, wannan shine matakin k'arshe na sakandire wanda ya kamata nayi k'ok'arin ganin na fita da sakamako mai kyau, haka karatun nan shine gatana, shi zanyi na taimaki iyayena, basu da buri da ya wuce ganin na samu ilimi mai zurfi, saboda shi na baro ahalina" Asiya ta jinjina kai da cewa "Allah ya bada nasara", "Amin" Ta amsa, ta juya ta cigaba da karatun, Asiya ta zauna kusa da ita, itama tana d'auko nata littafin.



"Sannu Baffa, Allah ya tashi kafad'un ka" Dattijuwar mata wacce ba zata gaza shekaru arba'in ba ta fad'a da k'arasawa da hawaye, Wanda aka kira da Bappa kansa ya girgiza yace "Ko bayan raina kada a cire Bongel makaranta ita kad'ai Allah ya bani ikon sawa makaranta, Dan Allah ku cika mun burin nan nawa na ganin tayi ilimi mai zurfi", "Baffa In Shaa Allahu kana tare damu, zaka tashi ka cigaba da rayuwarka", Kansa ya girgiza ba tare da ya sake cewa komai ba,



Bongel komai yau sukuku take yin sa, duty d'inta na ranar kawai tayi sa ne, ta fito hostel, Tun shigarta aji bata cewa kowa komai ba, dama ita ba gwanar surutu ba ce, sai dai shirun yau yasha bambam dana kallo, Ta rasa dalilin da yasa bata jin dad'in ranta, ga gabanta dake yawan fad'uwa.


"Hafsat Aliyu" Taji muryar Vice principal d'insu na kiranta, Ta amsa da mik'ewa, "Zo" Ya fad'a yana yin gaba, ta biyo bayansa har zuwa admin, Hamma Bala ta tarar a zaune ofishin vice principal, "Hamma ina wuni?" Ta gaishe sa cikin sanyin murya, "Lafiya lau" Ya amsa murya a raunane wanda daga yanayin sa ya tabbatar mata zuwan nasa ba na lafiya bane, Rubutu VC d'in yayi a takardar ya mik'awa Hamma Bala, Ya juya kan Bongel "Idan akwai abunda zaki buk'ata a gida, kije ki d'auko zaku je gida", "Gida" Ta nanata a ranta, yayin da k'irjinta ya doka, ko shakka babu ba lafiya ba, tsawon shekarun da tayi a makaranta tun js1 ba'a tab'a zuwa d'aukarta ba, biki ko suna Bappa baya bari saboda yadda ya d'auki karatun ta da muhimmanci, "Bana buk'atar komai" Ta fad'a dan a halin yanzu burinta ta ganta a gida dan sanin meke faruwa,

   Babur na Hamma Bala ta hau, yaja su zuwa malumfashi kasancewar babu nisa, Taron mutanen data gani a k'ofar gidansu, yasa jikinta tsinkewa, ko shakka babu mutuwa ce, wani daga cikin yan' gidansu ya rasu, Tana dosar k'ofar shiga ta fara jiyo koke koke, jikinta ya soma rawa da k'yar ta rab'a mutane ta shiga ciki, idonta ne ya sauka kan mahaifiyarta wacce ke faman zubar da hawaye, da gudu ta k'arasa kusa da ita ta fad'a jikinta,

  "Mun rasa Bappa Bongel Allah ya k..." Bata k'arasa ba sakamakon sumar Bongel, mutane sukayo kanta ana yayyafa mata ruwa, A hankali ta bud'e idonta tace "Nene Dan Allah kice mun mafarki nake bamu rasa Bappa ba", Hawayen data gani shimfid'e kan fuskar Nene ya k'ara tabbatar mata gaskiya ne,

  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Take nanatawa idonta a runtse, hawaye na ambaliya saman fuskarta, mutanen da ke wurin ta basu tausayi matuk'a sanin irin shak'uwar dake tsakanin ta da Bappa.

  Ta jima zaune a wurin tana zubar hawaye, kiran sallar la'asar yasa kowa mik'ewa zuwa gaida ubangiji, Bongel ta d'ago rinannun idonta da suka koma jajir saboda kuka suka sauka kan Dije da Fatsuma wanda suke cin tuwo hankali kwance babu d'igon hawaye a kan fuskar su, Kanta ta kawar gefe cike da takaicin su, bata d'auka rashin imanin su ya kai haka ba, Alwala tayi a famfon dake tsakar gida ta shiga d'akin Nene, ta dad'e tana addu'o'i,

  "Adda! Adda!" Ta d'ago tana kallon k'anwarta Ramla yarinya yar' kimanin shekara 14, hannun ta rik'e da k'aramin k'anensu dan' shekara hud'u, "Adda Bappa ya tafi ya barmu" Ramla ta fad'a tana fashewa da kuka, ta fad'a jikin Bongel, K'aramin k'aninsu Abu shima ya fad'a jikin Bongel, ta k'ank'anme su jikinta, suna kuka mai tsuma zuciya.


  Goggo Hajjo wacce k'anwar Nene ce ta dad'e tsaye a d'akin tana kallonsu cike da tsantsar tausayi, Kafin ta nisa tace "Haba Bongel kece babba cikin su, ke da ya kamata ki lallashe su kin sasu gaba kuna kuka, Bappa addu'ar ku yake buk'ata ba kuka ba, nasan da ciwo amma haka zaku jure, mutuwa na kan kowa",


  Muryarta da k'yar take fita ta dishe tsabar kuka tace "Ashe haka mutuwa take da d'aci da rad'ad'i, mun rasa Bappa Goggo dole muyi kuka", Kusa dasu ta duk'a ta kamo hannun Bongel da Ramla ta soma lallashin su tare da musu nasiha, a hankali sukaji natsuwa na saukar musu sun tsagaita da kukan.


   Da zazzab'i Bongel ta kwanta, ana cewa bacci b'arawo sam bai sace ta ba a daren ranar, Ramla da Abu sun samu yin bacci, Nene itama haka ta kwana lazimi tana rok'arwa Bappa rahamar ubangiji.


   Kwana uku ana zaman makoki, kowacce rana da irin halayyar dasu Dije ke nunawa, har mutane sun fuskanci basu damu da mutuwar ba, haka kowa ke tafiya dasu a baki.


  "Na sha jin labarin facaloli amma ban tab'a ganin kishin matan sauri irin naku ba" Cewar Hajjo, Nene ta numfasa tace "Nasu dai, ni kaina abun yana matuk'ar bani mamaki da d'aure kai, ban k'ara tsinkewa da lamarin su ba sai rasuwar nan", "Ni kaina na k'ara shaida Dije da Fatsuma basa sonki kuma bana jin zasu tab'a sonki", Nene tayi murmushin takaici tana girgiza kai, Bongel shiru tayi tana k'ara nazarin rayuwa irin ta ahalin su, yadda ake gudanar da masifaffan kishi tsakanin matan gidan, su ba kishiyoyi amma har sun fi kishiyoyi kishi.



   Bongel da Ramla suna zaune kan tabarma dake shimfid'e a d'akin, Nene na zaune kan katifa ta jingina da bango, Abu yayi matashi da cinyoyin ta, kowannensu yayi shiru yana sak'ar zuciya, yayin da d'imbin kewar Bappa ta zagaye zukatan su, a irin wannan lokacin sukan zauna suna hira, cike da nishad'i.


   Nene ta dubi Bongel tace "Gobe ya kamata ki koma makaranta", "Gobe Nene ko sadakar bakwai fah ba'a yi ba", "Jiran me zaki tsaya Bongel, kina matakin k'arshe na kammalawa, kada kiyi wasa da karatun ki, Bappa bai bar wasiyyar komai ba sai na karatun ki, yana da burin kiyi ilimi mai zurfi, Dan Allah ki cika masa burin sa", A raunane ta d'aga kai tare da cewa "In Shaa Allah zanyi k'ok'arin cikawa Bappa burin sa, haka zaku yi alfahari dani", "Allah ya yarda" Cewar Nene, Dukkansu suka amsa da "Amin"



   Washegari Hamma Bala ya mayar da ita makaranta, ta koma da k'udurin k'ara zage dantse wurin ganin ta cika burin Bappa, da son ganin ta taimaki mahaifiyarta da k'annen ta, Asiya tayi murna sosai ganin Bongel ta dawo, itace aminiyarta rashin ta kwana biyu yasa tayi kewarta sosai, Ta mata gaisuwar Bappa, kuma tace ana yin hutu ita da yan' gidansu zasu je yi ma Nene gaisuwa.


  "Mahaifin yarinya ya rasu ko bakwai ba'a yi an tura ta bokon iskanci" Fatsuma ke yada habaici a tsakar gida, Dije ta kama mata da fad'in "Taya ni gani, dama wanda ya mutu ai shi ya mutu, tun kan ayi sati iyalinsa ma sun soma manta shi", Nene bata tanka su ba, idan da sabo ta saba da halayyar su, sam bata biye musu, ba'a tab'a jin ta da kowa ba, sai dai suyi tsakanin su, a zahiri zaka ce soyayya da zaman amana ne a tsakanin Dije da Fatsuma, amma a bad'ini kishi, kyashi da hassadar juna suke.

Ku biyoni cikin littafin BONGEL, wanda zai k'ayatar daku, ya nishad'antar daku IN SHAA ALLAH

LABARI MAI D'AUKE DA
K'IYAYYA
SOYAYYA
RUD'ANI
TAUSAYI
NADAMA


*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


   *HASKE WRITERS ASSO..*

SHAFI NA BIYU

  ASALINSU

Aliyu Ard'o shine mahaifinsu Bongel, asalinsa d'an garin katsina ne k'aramar hukumar malumfashi, bafullatani ne gaba da bayansa, Mahaifiyarsa Hafsa shi kad'ai ta haifa, Allah ya mata rasuwa, bayan ta rasu ya sake aure, ya auri Hanne ta haifa masa yara biyu maza Bala da Siddiku, Hanne bata k'aunar Aliyu duba da yadda mahaifinsu ke son shi, yake tausayin sa saboda rashin uwa, haka suma su siddiku suka tashi da k'iyayyar sa, duk da Bala na dan’ b'oye tasa k’iyayyar, Mahaifinsu ba mai k'arfi bane, manomi ne, da suka isa aure, ya musu k'aramin gini na k'asa, kowannen su yace ya fitar da mata, Aliyu ya fara samun mata,Nene  zuwa tallar nono daga rigarsu, suka k'ulla soyayya,  bayan shekara d'aya Bala da Sidddiku sukayi aure suma, Bala ya auri fatsuma, Siddiku ya auri Dije, matansu haka suma suka d'arsawa ransu tsananin kishin Nene, duk da irin mugun hali da suke nuna mata, bata bi ta kansu, Bongel ce yar'su ta farko wacce taci sunan kakarta Hafsa, Bappa ya saka mata Bongel saboda kyawunta, kaf yaran gidan babu wanda ya kaita kyau, fari da gashi, Bala nada yara hud’u Hamza, Lawal, Sa’ade, Habiba, Hamma Siddiku nada uku Hassan da Husaini, Saudat, Duka yaran gidan babu wanda ya samu ilimin boko sai Bongel, Bappa nada burin ganin yaran sa sun samu ilimi, sai dai rashi da talauci yasa Bongel kad’ai ya samu sakawa, Siddiku da Bala basu damu a saka yaransu ba a cewar su a boko yaro ke lalacewa, ba irin k’ananun maganganun da basuyi ba kan saka ta makaranta, Bappa ya toshe kunnen sa.

***************

  Bongel sun soma zana jarabawar WAEC wacce sam bata wasa da karatu, duk jarabawar data shiga bata jimawa take fitowa saboda sauk'in da take mata, yau ma maths sukayi kusan kowa ka kalla cizon biro yake saboda wahalar da jarabawar tayi, wasu na raba ido ko zasu samu satar amsa, sab'anin Bongel da kanta ke duk'e kan takardarta tana faman calculation, lokaci kad'an ya d'auketa ta kammala ta fito,


  Zama tayi bakin hall d'in tana jiran fitowar Asiya, istigafari ta soma kar tayi zaman banza, kusan awa d'aya da zamanta kafin Asiya ta fito, "Bongel nikam wacce irin baiwa ce Allah ya baki, yadda jarabawar nan tayi wahala amma kika kammala da wuri", Murmushi tayi tace "Allah dai ya bamu sa'a", Asiya ta amsa "Amin", Bongel ta mik'e suka tafi hostel.


  A kullum safiya da tunanin Bappa, Bongel take tashi haka dashi take bacci, bakinta baya gajiya da rok'ar masa rahamar ubangiji.


   Sati shida suka d'auka suka kammala jarabawa, a cikin sati shidan suka zana jamb, wanda Bongel tafi kowa samun sakamako mai kyau a cikin d'aliban makarantar, d'ari uku da sha biyar ta samu, Tayi murna sosai haka duk wani masoyinta ya taya ta murna,


   Ranar da suka kammala jarabawa aka sallami kowa gidan iyayen sa, sai sakamako ya fito su dawo su karb'a, kowa ka gani fuska d'auke da farin ciki, ana ta faman rubuce rubuce a rigunan juna, da karb'ar numbobi, sab'anin Bongel data koma gefe tana zaune kan akwatin ta, wannan shine karon farko da bata zumud'in zuwa gida, lokutan baya tun ana saura sati d'aya hutu take soma had'a kayanta tsabar zumud'i, ba wanda tafi muradin gani kamar Bappa dan tarba ta musamman take samu daga gare sa, a ranar raba dare suke suna hira gaba d'ayan su, tana basu labarin makaranta da abubuwan da suka faru,


   Ta jima zaune tana jiran zuwan Hamma Bala shiru, har kowa ya fara watsewa, tun fara makarantar bata tab'a kai lokaci kamar haka ba'a zo d'aukarta ba, addu'a ta soma Allah yasa lafiya,

  Har kowa ya watse ya barta ita kad'ai, Jikinta ya k'ara yin sanyi tana ji a ranta ba lafiya ba, ta yanke shawarar samun machine ya kaita gida, ba tare da b'ata lokaci ba ta samu machine, ya fad'i kud'in da zata basa, Tace "Idan mun isa gida zan shiga ciki na karb'o maka", Harara ya watsa mata yace "Kinga idan baki da kud'in na tafi abuna", "Wallahi muna zuwa zan shiga na d'auko na baka", "Na sha d'aukar irinku kuna guduwa, dan haka ki nemi wani" Yaja babur d'insa ba tare da ya jira cewar ta ba, Tabi bayansa da kallo cike da takaici,

  Kusan machine uku tana tara suna k'in yarda, da k'yar ta samu wani tsoho ya d'auketa, Yana ajiyeta bakin gidansu, bai tsaya karb'ar kud'in ba, yace ta tafi kyauta ya kawota, ta masa godiya sosai,  Daidai k'ofar shiga taci karo da Ramlat na fitowa, "Adda kin dawo, yanzu Nene tace naje gidan Goggo Hajjo nace Dan Allah taje ta d'auko ki", "Ina Hamma Bala ne?" Bongel ta tambaya da mamaki, Ramla tace "Yace ba zai je ba", Bongel ta jinjina kai cike da mamaki, ba tace komai ba, suka k'arasa cikin gidan,


   Kallo d'aya tayiwa mahaifiyarta tasan ba lafiya ba, Jiki a sanyaye ta zauna kusa da Nene ta gaisheta, Bata amsa gaisuwar ba tace "Bongel ya akayi kika dawo gida, ko wani ya dawo dake?", "Ni na dawo da kaina", "Dama zaki gane hanya", "Haba Nene shekaru shida ina bin hanyar", Nene ta jinjina kai tace "Ga abincinki can a kwano sai dai kiyi hak'uri da tarbar da kika samu wannan karon", Bongel tayi murmushi tace "Kowacce irin tarba ce indai daga wurinki ne Nene haka nake ji tamkar daga Bappa ne", Nene tayi murmushin farin cikin ganin Bongel ta karb'i komai da sauk'i.


   Wanka ta fara yi, ta canza kaya zuwa atamfa doguwar riga, ta d'auki kwanon abinci ta soma ci, Tace. "Nene nikam meya hana Hamma Bala zuwa d'aukata makaranta yau", Nene ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya tace "Dan' adam mai wuyar gane hali, haka gane masoyin gaske sai Allah, Bala ya bani mamakin da ban tab'a zata ba", "Me yayi Nene?" Bongel ta tambaya cike da k'aguwa, "Yau tun safe
yazo ya sameni kan cewa ba zai iya zuwa d'aukar ki ba, ya gaji ni naje, Nace masa ina takaba, kuma idan yayi hak'uri wannan shine k'arshe tunda kin kammala, bud'ar bakinsa yace ba wata takaba da nake, ai ban damu da mutuwar tasa ba, tunda na tura ki makaranta tun kan ayi bakwai, idan zanje da kaina naje, idan ba zanje ba nasan tayi,...


Read / Download BONGEL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album