Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KANWAR MINISTA Complete Hausa Novel Document by KANWAR MINISTA


KANWAR MINISTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21904



KANWAR MINISTA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Walidation S Mapi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : +234 903 129 9157

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 134.75 kb

File Type: txt

Views: 479+

Download: 402+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: [10/10, 13:37] +234 903 129 9157: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🎀🎀🎀🎀🎀
*KANWAR MINISTA*
🎀🎀🎀🎀🎀

0️⃣1️⃣

_Banyi wannan littafin don cin zarafin kowa ba sai don in faranta muku rai masoyana ina matukar kaunarku sosai_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*_WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE, AND ENTERTAIN OUR READERS_*

_Labari/Rubutawa_

_Walidation s mapi_

*please follow me on wattpad @walidatu232*

_farkon shafin sadaukarwa a gareki ne Eesha🌹ina matukar kaunarki_

_maraba da saduwa dani a sabuwar littafi_

_______University of Maiduguri (Unimaid) misalin karfe tara da rabi na safe 9:00Am yanayin garin kamar za'ayi ruwa amma ba damuna ake ciki ba kenan ba ruwan za'ayi ba saidai sama cike take taf da hadari

Makarantar cike take da ɗalibai fam kowa na jiran a shiga lecture

Wata mota ce kirar land rover pink colour tashigo cikin makarantar

Da kaga motar kasan taji kuɗi wajen siyanta

Saida ta tsaya a motar ta amsa kira kafin ta fito da kafarta guda ɗaya a waje

Ta ɗauki lokaci kafin ta fito gabaɗayanta wata shegiyar doguwar riga ce a jikinta ta atamfa amma kuma tamkar ba atamfa ba saboda wata irin Ado da akayi mata daga sama light pink ne kayan dakuma fari-fari a jikinta sai kuma wata kyalle da aka ɗaura a kwankwasonta kamar zata gaɗa

Saikuma glass ɗin da ta sanya manya-manya brown color kanta kuma yaji wata zazzafan kitso idan kaga kitson zaka zata gashin doki ne amma inaa tsantsar gashine da ita saikuma ɗankwalinda ta ɗaura na kayan me bala'in kyau

Sai kuma wata karamar jaka hannunta pink color cover wayarta ma pink color ce

Yarinyar fara ce doguwa siririya ga hanci ga kuma idanu masu kyau

Takalman kafarta ma cover shoe ce pink color saman tana wani kyalli

Waigowa inda ta hango ƴan department nasu tsaye da takaddu sai kallonta sukeyi

Bayannan bata sake kallon kowa ba tawuce inda tasaba tsayawa ita kaɗai tafara danna wayarta maimakon tayi karatun littafi tunda yau text suke dashi

Tunda tafito daga mota kowa yamayarda kallonshi kanta amma ina kota kansu bata bi ba saboda idan tashigo makarantar bata kallon kan kowa da gashi

Karfe tara da rabi tayi kowa da kowa yakoma department nashi saboda gaba ɗaya makarantar general ake dashi wato English Language

Saida kowa yagama shiga har anfara yin test ɗin kafin Meera ta ɗago kai daga danna wayar da take

Taku tafara ɗas-ɗas kamar bazata taka kasa ba kuma kamar zatayi kuka saboda wai ta gaji

Dai-dai bakin ajin ta tsaya taɗan duba lokaci ba laifi yau takara mintuna shida ne

Shiga cikin ajin tayi taje tasamu waje a baya wadda yake nata ne ita kaɗai babu wanda ya isa ya zauna mata a sit koda batazo ba

Wani lecturer ne ya fusata saboda wannan rashin kunya da tayi musu

Yunkura yayi zaije yafitarda ita sai wani abokin aikinshi ya rikeshi ta baya yace

"Bakada hankali ne Abdul bakasan wacece ita bako?"

"Nasir ko wacece ita sai ta fitamin daga aji yau yarinya tunda nazo na hangota daga waje amma sai yanzu zata shigomin aji" yafaɗa yana menuna alamar ɓacin rai

"Abdul nayi mamaki ace duk zamanka a wannan makarantar bakasan wacece Meera ba" inji Naseer

"Abdul yau fa ko ubanta ne me makarantar saita barmin aji idan yaso daga baya sai a koreni donni bazan ɗauki raini ba" inji Abdul kana ya wufce rigarshi yabar wajen

Dai-dai inda take ya tsaya kem yakasa taɓuka komai saboda mamakin yadda ya ganta

Cikin dauriya yace "kee bakida hankali ne ana test zaki shigo latti kuma kinzo da wuri bayan haka kinshigo kiyi test mana amma chatting naki kikeyi a ruwanki" Abdul ne yake ta maganarshi shi kaɗai

Ko juyowa ta ganshi batayi ba saboda bataji ma meyake faɗa ba

Cikin ɓacin rai ya wafce wayar dake hannunta jikake cas alamar wayar ta suɓuce a hannunshi

Bada sonshi ba shima wayar tafashe amma saiya dake kamar da gan-gan yayi

Mikewa tayi cikin sauri tana so taga wanda yayi mata wannan aikin domin bata taɓa tsumayin haka ba

Cikin masifa tace "kai har waye dazaka fasamin waya? Waye ubanka? Waye uwarka? Suwaye danginka a garinna? kasan wacece ni? kasan daga wani gida nafito?" tareda wanke shi da mari takuma cewa "amsamin!!"

Cikin bakin ciki Abdul yaɗago kanshi wai yau macece ta mare shi abun da mamaki sai kuma yayi wata murmushi alamar bai damu ba ya ɗago kai

Yace "kema waye ubanki? Wacece uwarki? Kinsan ni waye?"

Tace "To bara kaji ni kanwar minista ce kuma zan iya sawa a ɗaure dukkanin ƴan gidanku dama danginku gaba ɗaya wato tsabar bakinciki wayata zaka fasa saboda bakada irinta ko to yau dani da kai acikin school ɗinnan saika biyata kokuma nasa a ɗaure danginka baki ɗaya a yau"

Daga yatsarshi yayi zaiyi magana Abokinshi Nasir ya janye shi daga wajen

Itako Meera bata hakura ba ta ɗauki fasasshiyar wayarta tabi bayansu cikin sauri tace dolene yabiyata wayanta

Ya mika hannu ya karɓi wayara kamar dagaske yaji tsoro kawai sai yasake doka wayar da kasa

Yace "ba dangina ba idan kuɗin ministarda kike ikirari zai iya kulleni ni kaɗai to ki gwada a yau kiga abin mamaki"

Saura kaɗan ta zabga ihu ganin yadda yakarasa fasa mata waya tayi kaca-kaca baka gane komai a cikinta sai dai kawai tayi shirune saboda kada ta zubda class nata acikin school don ga kowa ya taru yana kallonsu

Hannu ta ɗaga tasake kai mishi mari a karo na biyu

Abinda baiyi zato ba kenan yakuma ji yadda yarinya karama ke zubar mishi class acikin makaranta

Shima yaɗaga hannu zai zabga matamari kenan sai Nasir yarike hannunshi yace "Haba Abdul ita macece fa"

Kokarim kwatar hannunshi yake amma ina yakasa saboda Nasir ya danne sosai sai kawai yafashe da kukan bakin ciki

Ita kuma Meera ta ɗaga wayarta daga kasa tace "matsiyaci kawai daka mareni yau da wannan kazamar hannun naka sai nasa an yanketa wallahi banza jinin matsiyata sannan kasani duk sanda kaganni ka canja hanya domin bazaka fasamin waya a bulus ba ɗan iska shege"

Ɗalibanda suke tsaye ne suka kwashe da dariyar asara

Kasa ɗagowa Abdul yayi saboda tsananin kunya daya shiga saida ɗaloban suka fara raguwa sannan Nasir yarike hannunshi suka bar wajen amma har yanzu bai ɗaga kai ba saboda a mugun kunyace yake

Suna zuwa office Nasir yace "kaga abinda nake faɗa maka nace maka kada kayiwa wannan fitsararriyar yarinyar magana amma sam kaki jina yanzu ga abin kunyarda ta jawo mana"

Sai a lokacin Abdul ya ɗago kai yace "Nasir idan har ni namiji ne sai na rama abinda wannan yarinyar tayimin bazan taɓa kyaleta ba"

Nasir yace "kajika ai da shegen wauta yanzu wanda ta ɗan maka bai isheka ba kenan ko?to wallahi gwamma ka daina tun wuri"

Abdul yace "Nasir wallahi na ɗauki Alkawari idan dai ina raye wannan yarinyar tana raye saina rama wannan abinda tayi min kota halin kaka"

Haka dai sukayita yi Nasir yahakura yabarshi akan bakarshi na sai ya rama

Ita kuwa Meera tana barin wajen ba inda ta nufa sai wajen motarta shiga tayi ta kifa kanta kan sitiyarin motar tafara kuka sosai domin kaf cikin wayoyinta babu wanda takeso kamar wannan gashi da tsada yaune tayi amfani dashi na biyu kuma yayanta ne yasiya mata motar tayiwa key tabar cikin makarantar tareda aniyar ɗaukar fansa domin bazata taɓa bari haka a banza yafasa mata waya ba saita rama




Seee meee nex page

More c
omment more typing
[10/10, 13:37] +234 903 129 9157: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANWAR MINISTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

_Labari/Rubutawa_
_Walidation s Mapi_

0️⃣2️⃣

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
'''We are here to educate motivate and entertain our readers'''

_This nice nd cute page is dedicated to you my lovely sister Jiddah s mapi writer of A Gidanmu take really luv uuhh dear_

_________📲Motar tayiwa key tabar makarantar tareda aniyar ɗaukar fansa domin bazata taɓa ɗaukar asararda wannan banza malamin yayi mata ba

Tana fita ba inda tayi sai unimaid garden inda ta zauna ta shakata a wajen an kuma yi sa'a ba kowa a wurin bare suyi faɗa saboda yau general test ake dashi a makarantar

Abdul ne a office yaketa kukan bakin ciki yakasa taɓuka komai yau wai shine mace ta mara abin takaici

Sai wajen sha biyu na rana kowa yafito daga test ɗin inda dai-dai lokacin Meerah itama ta mike tayi hanyar gida ko kula kowa batayi ba

Tana isowa bakin gate tayi horn me gadi bai buɗe ba tasake yi a karo na biyu amma ina yaki buɗewa

Saida wani bodyguard yaji horn ɗin kafin yafito yabuɗe mata

Shigewa tayi da motar tayi saurin fita ta hango me gadi a bakin famfo yana wanke fuskarsa

Karasawa wajen tayi taga yaɗan durkusa bayansa na sama

Dunduu tasakewa wannan tsohon a baya jikake duum

Durkusawa yayi gamida rike bayanshi kobai juyo ba yasan wanda zai aikata mishi wannan abin bazai wuce Meerah ba

"Bakada hankali ne malam? So nawa kakeso in faɗa maka kadaina ɓatamin lokaci idan kaji nayi horn? to wallahi daga yau dai yau nayi maka last warning ko bakasan matsayina bane? to ni kanwar minista ce sau nawa kakeson in nanata maka ne wai iye?" Meerah ce take ta zabga bala'i kamar bata gajiya

Koda baba...


Read / Download KANWAR MINISTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album