Join Our WhatsApp Group

YAR RAWA Complete Hausa Novel Document by YAR RAWA


YAR RAWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 52832



YAR RAWA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 13, Sep 2023

Author: Haermeebrah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 264.4 kb

File Type: txt

Views: 622+

Download: 336+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [1/9, 2:46 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼






BY HAERMEEBRAERH




*Assalamu alaikum warahmatullah, 'yan uwana makaranta, ga sabon novel mai suna 'YAR RAWA, zan fara, ina fatan zaku karbe shi, ku bini kamar yanda ko fiye da ku kaima novels dina na baya, ina roqon Allah daya sanya albarka a ciki, ya bani ikon rubuta daidai, duk abinda zan fada in ba zai zama alkairi garemu duka ba Allah ya karkatar dani da barin shi, Allah ya yafen kurakuren da zan yi har i zuwa qarshen kammalawa. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON DUKKAB MASOYAN TA DA MASOYAN NOVELS DIN TA DUK INDA KUKE, ME LOVE U XX❤*






" Sannu Tabawa, Allah zai baki lfy, da kan ki za ki reni abinda kk haifa, shi ciwo ai ba mutuwa bane" Yana fada yana share kwallar dake maqale a manyan idanun shi, shigowar yar budurwar yarinyar su da bazata wuce shekaru sha 12 ba, ne yasa Tabawa ta daga kai da kyar ta kalle ta, miqa mata hannu tai akan ta isa gareta, da kyar cikin azabar ciwo da kanta yake mata, tare da zafin da take ji a qirjin ta, wanda ji take kamar hucin garwashin wuta take fiddawa, ta fara magana, bayan yarinyar ta bata ruwan da ta debo mata," Ameenee,..... ki ji tsoron Allah a duk inda kk,.... ki ma mahaifin ki biyayya, shida abokiyar zamana,....ki kasance yarinyar kirki da kowa zai sha'awar zaman ki tashi...... ki kiyaye dokokin Allah Ameenee.... Allah zai kiyaye ki da zuri'ar ki har qarshen rayuwar ki,.... Malam ka riqe amanar yarinyar nan,...... kar ka bari a cutar mana ita...... ka saka ta tai ilimi.... domin kai mai ilimi ne....." tari ne mai qarfi ya sarqe ta, yi take ba qaqqautawa, cikin tashin hankali, Malam Muhammad ya miqe ya dakko ruwan zai bata, sai yaji diyar su Ameenee, tana kalmar shahada,mahaifiyar ta na mainaitawa, idon Ameenee na zubar da hawaye, kamar an bude famfo, Malam kasa motsi yar, ganin dagawar da girjin matar shi yai, tare da jan wani nunfashi, ta kwanta, hannun ta Ameenee ta daga, ta ga alamar ya sake, kuka ta fara can qasan maqoshin ta, mara sauti, ta farama mahaifiyar ta addu'a" Ya Rab Ya ilahy, Allah ina roqon ka ka gafarta ma mahaifiyata, ka kai rahama qabarin ta, Allah ka tada ta cikin bayin ka muminai salihai, Allah ka bata ikon amsa tambayoyin qabari," Malam Muhammad da yai mutuwar durqushe ne , kama kanshi yana juya shi, hawaye masu mugun zafi, suke fama kwarara a idon shi, amsa addu'ar diyarshi yai wadda gaba daya bai san me take cewa ba sai daga qarshe ya fahimta, qanqame matar tashi yai kamar zai maida ta cikin shi, hawaye ke zuba, cikin ranshi yana nema mata rahamar Allah, daga baya ya sake ta ya kwantar da ita, ya rufe mata ido, sannan ya lullube ta da abin rufar da ta rufa da shi, tashi yai ya fita tsakar gidan nasu, wata gambasheshiyar mata na gani tana ma yaran ta wanda suke dika maza magana,akan suyi su gama cin abinci su debo mata ruwa, turo baki suke suna su ba inda za su, ganin malam ya fito cikin tashin hankali fuskar shi duk hawaye yasa ta qarasawa wajen shi da gudu2 sauri2, daurin qirjin ta na rai da rai na neman faduwa, ta damqe shi, " Delu, Allah daya ban tabawa ya fini son ta, a yau ya amshi abar shi,ta tafi ta barnu cikin kewar ta, da quncin zuci, wannan qunci daja shiga ban san ranar fita ba Delu" wani tuquqin baqin ciki ne ya tokare mata wuya, jin kalaman shi, amma dake makira ce,sai ta fake da kukan mutuwar da taji ta saka hannu a ka ta kurma ihu ta fadi qasa dabar, tana turje2n kafa da hannaye, tare da cire dankwalin ta kanta da ya cure dan datti ya bayyana," wayyo ni Delu na shiga ukuna, na rasa 'yar uwata, mai sona da qaunata, Tabawa kar ki tafi ki bar mu, muna tsananin son ki, ki yafe mana laifin da mukai maki" Malam ne ya sunkuya ya daga ta, yana qara jin wanu tausayin kansu dika, dan rasa mace kamar Tabawa babban asara sukai,mace ce mai kunya, kawaici, tsafta, rufin asiri, da kuma juriya da hakuri, ga rufa asirin mijin ta, in basu da shi zatai duk qoqarin ta tai providing masi kamar itace mijin, daga mijin har kishiyar tata suna morar ta ba ladan ba, ya fifita ta da kowa a zuciyar shi fiye da kowa, ya bata mazauni mara misalin fada a cikin zuciyar shi da ruhin shi, ta zama wanu bangare na jikin shi, lokacin da sukai aure suka dare basu haihu ba, ita ta matsa mai ya auro Delu, tana zuwa ta fara da haihuwar maza, taso ta fito da iskancin ta fili Malam yai mata barazanar saki, ko nace ya sake ta ma, amma dake Tabawa mutuniyar kirki ce ta bashi hakuri, ta fada mai duk randa ya saki Delu itama ta bar zama da shi kenan, hakuri ya bata suka je ita da shi suka dawo da Delu,kowa na mamakin hali irin nata na kyautayi da kyautatawa, dan haaka sai ita Delu ta fara yi mata kisan mummuqe, a haka har sai da ta haifi yara biyu maza, masu suna Habeebu da Hamza, sannan Allah ya azurta, Tabawa da cikin Ameena, wadda ta sha gata wajen malam, kamar mai sabuwar haihuwa, hakan ne ya qara dasa qiyayyar Tabawa da duk abinda zata haifa a ran Delu,tayi iya qoqarin ta na ganin ta zubda cikin amma Allah bai bata dama ba, ran da kuwa taga mace aka haifa tai rawa tai juyi a daka tana waqoqin samun nasarar kasamcewar yaranta maza kuma sune manya, a haka rayuwa ta ci gaba sai ta dauki Ameenee da niyyae raino da ta kauce tai ta mata azaba, tana kuka, sai tace daga dan matsawa yara suka dake ta, ta hau sababi ma yaran, in Tabawa ta karbe ta tai ta mata fadan dan me zata ma yara fada, suma ai qanana ne,haka dai har Ameenee ta girma ta gane halayen Delu tsaf, mahaifiyar ta bata gano ba, Malam ma haka, ran da ko ta sanar ma da mahaifiyar ta ta sha duka sosai, a haka ta ja bakin ta tai shiru, dan yarinya ce mai biyayya sosai.
Daga ta Malam yai ya gyara mata zanin ya miqa mata dankwalin ta yana mai lallashin ta, daki ya kaita, ya miqo mata rigar kayan akan ta saka da hijab, ta saka tana wanai kuka kamar na gaske, can qasan ran ta kalaman da ya fada suna qara yunquro mata kamar kumallo. A haka aka gyara Tabawa akai mata wanka da sallah aka kaita gidan ta na gaskiya, Ameenee ta sha kuka tin tana iyawa har taji ba zata iya ba, daki ta koma ta kwanta inda Innar ta ke kwanciya,ya rungume filo tana hawaye, addu'a take ta mata a ranta ta samun rahamar Allah.






Bayan an yi sadakar arba'in ne na rasuwar Tabawa, komai jin shi suke ba dadi, tsakanin Malam kenan da Ameenee, wadda Delu ta mayar baiwa,a bayan idon mahaifin ta, amma in yana nan, har rungumar ta take a jikin nan nata mai dankaren tsami, tana nuna mata kulawa,dan haka suke qara bama Malam tausayi, in ya fita tun safe sai dare, baya jure ganin su cikin quncin da shima ya addabe shi, hakan ne ya ba Delu da yaran ta damar musgunawa marainiyar Allah, ga horon yunwa, da ya dawo sai kuji tana" zaki qara abincin ne Ameeneenaa, na kula ba ki son cin abinci, ki taimake ni kina ci, dubi yanda kk rame? Mutuwar nan duk muma a cikin dacin ta muke...." sai ta kasa qarasawa ta hau kuka, Malam ne zai rarrashe ta, ya karbi dan abincin ya ba yar tashi, ta wuni da yunwa amma gudun kar ya gane komai, dam an mata warning mai girma akan kae ta bari ya gane daidai da rana daya kashin ta ya bushe, daki take komawa ta hau ci kamar mahaukaciyar data shekara ba abincin, tana ci tana hawaye.


Mai gari ne yace a kira Malam Muhammad, sabida ya ga tunda akai rasuwar ya daina hada2r shi na Islamiyyun da ya taimaka aka bude a qarin nasu na Rimin Gata, hakuri ya ba mai garin, ya kuma tabbatar mai zai koma normal, daga wannan satin.



El- mustapha Sadauki, wani shahararren mutumi ne wanda yake da arziqi da taimakon gidan marayu,da islamiyyoyi, yau qungiyar su ta baro qasar su dake Niger, ta taho Nigeria, domin taimakawa, islamiyyar da malam Muhammad ke jagoranci, ya samu labarin qoqarin shi ne, ta bakin wani mai masa hidima, a nan Nigeria, dan yana da masu nemo masa rahotanni a qasashe don ya samu damar taimakawa.

El-mustapha yana da nasaba da kuma jinin larabawan Dake da mazauni a Dubai, garin tainakon shi ne yasa ya baro qasar shi ya kafa gidauniya anan Niger, wanda da dawowar shi da komai bai fi shekara biyar ba kenan, ya samu tsananin qiyayya daga 'yan uwan shi na can, wadan da ba su qaunar shi ko kadan sakamakon son talakawa da yake da, rayuwar shi daban da tasu, ta dalilin haka ne ya tattaro ya dawo, iyayen sun rasu. Dawowar shi nan bai sa ya yanke alaqar shi da su ba, yana zuwa a kai akai, dan sada zumunci, gaba daya hakan da yake yi ji suke kamar su kashe shi su gaje dukiyar shi, tinda yaqi auren 'yayan kowa a qasar yace bai ga wadda ta mai ba, yana son yarinyar da zai aura ta kasance daga gidan tarbiyya, da mutunci, amma fa talaka, wannan kalmar qarshen ta baqanta ma yan uwan shi ba kadan ba, a haka suke har yau da yashirya zasu so Nigeria, sannan Unguwar Rimin Gata, kuna gidan Malam Muhammad mai Islamiyya......





*Hello guys, can u pls do me a favor? Ku dan aje wannan page a wani wajen, yanda koda nai nisa kunji sha'awar bi na sai ku lalubo ku karanta,ba sai nai nisa kuna tambaya ba, wayata yar qwaya ce,lols😉 ta yi nauyi da yawa, saboda abubuwan da take dauke da shi, ba zai yu na dinga sendin abu mai yawa ba ba tare da tana riqewa ba, so pls ku na adanawa, Thank u*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼




BY HAERMEEBRAERH






page 2:







Sun iso a gajiye, inda suka fara isa gidan mai garin, suka gabatar da kansu da dikkan bayanan abinda ya kawo su, nan take mai gari ya aika a kira Malam Muhammad, domin bangaren shi ne, isowar shi keda wuya, suka gaisa sannan aka qara kora mai jawabin komai, godiya ya musi mai tarin yawa, sannan ya nemi izinin tafiya da su masauqin da yakan aje baqi in sun zo, tashi sukai suka isa gidan Malam din, daidai lokacin Ameenee ta fito wanka tana shiryawa, kiran ta Malam yai ta je tare da durqusawa, " Abba gani" " Ameenee je ki dauko mazubin ruwa mai kyau da tsafta ki debo ruwan sha mai sanyi na randar gefen madafi ki kai wa baqi a dakin baqi, sai ki dawo a kai masu abinci kinji?" Amsawa tai da " To Abba" sannan ta miqe ta tafi ta qarasa saka riga da skirt din ta na atampa, ta dora hijab din ta akai, saboda Allah ya mata halitta mai kyau da diri, wannan dalilin ne yasa bata ta'ammili da mayafi. Sallama tai cikin muryar ta mai sanyi, kanshi a duqe yake a hankali ya dago dan ganin mamallakiyar wannan daddadar muryar, kallon ta ya tsaya yana yi kawai yana mamakin samun yarinya mai kyau a cikin Africa kuma a Nigeria, Nigerian ma a kano, lumshe idanun shi yai da suke madaidaita da cikar kyau ya amsa sallamar ta, ruwan ta miqa mai ya karba ta gaida su, cikin hausar shi da ba wani ji yake ba sosai, ya amsa, miqewa tai ta tafi ciki ta qara dawowa dauke da abincin da ita ta dafa, taliya ce mai mai da yaji, sai maggi da aka bada mata? Irin taliyar murjinnan ce, amma tai wara2 kamar ba ta murji ba, sannan Malam ya siyo kifi manya aka dora musu akai, a da da aka kai El-mustapha sadauki ya fara ganin anya zai iya ci? Kawai a dakko mai abincin shi a mota ya ci, sai kuma zuciyar shi ta raya mai ya tambaye ta. " Yaya sunan ki?" Murmushi tai dan jin hausar shi, ta amsa mai da" Suna na Ameenaa" " Malama Ameena ana zuwa makaranta kuwa?" " Eh ina zuwa, dan na sauke alqu'ani da shekara goma, da sauran littafan addini, yanzu ma ina taya Abbana koyar wa a wasu daga cikin ajujuwan da suka rage ba malamai" " Masha Allah" shine abinda ya fada cike da jin dadin tabbas abinda yake ayyanawa zai tabbata da yardar Allah, " Malama Ameenaa kin iya girki ne?" Ya tambaye ta da alamar zolaya, amma ti be honest yana son jin wa yai girkin ne, cikin jin kunya da. Sadda kanta qasa ta amsa mai da" Eh, ni nake girki dama" godiya ya mata yace ta je, miqewa tai ta fita, ya hango yanda jikin ya ke ta cikin hijab, ya tabbatar an yi halitta a wajen, dakko kwanon yau ya fara ci ba sai ga El-mustapha ya tashi da taliya da manja ba😂fadi yake lallai, Bahaushe akwai hikima......
( Ana kiran shi da Sadauki ne saboda jajrcewar shi wajen taimakon al'umma duk rintsi duk wuya, sannan duk nisan gari da surquqin qauye zai shige shi, amma asalin sunan shi shine El-mustapha Ahmad Nabeel.)


Sun kammala dukkan abinda ya kawo su, a cikin kwanakin nan ba qaramin shaquwa da sabo ne ya shiga tsakanin shi da Ameenee ba, duk da cewar, bqi taba furta mata kalmar so ba, amma soyayyar ta ta gama da dukkan jiki da ruhin shi, ita kuma a nata bangaren bata san me ne ne take ji game da shi ba, all she know is that in ya tafi she will miss him alot, and she don't even want him to go. Samun kan ta tai da shiga damuwa a duk sanda ta tina sallamar da sukai daran jiya, Delu kuwa hankalin ta ya fara kwanciya dan jin za su tafi, dan ta kula da take2n El-mustapha, wanda taci alwashin ko zata mutu bazata bari ya aure ta ba. Shi da malam ne suke ban kwana a dakin da aka sauke su, anan yake shaida ma...


Read / Download YAR RAWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album