Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[1/9, 2:46 PM] Haermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ 'YAR RAWA ๐Ÿ’…๐Ÿผ






BY HAERMEEBRAERH




*Assalamu alaikum warahmatullah, 'yan uwana makaranta, ga sabon novel mai suna 'YAR RAWA, zan fara, ina fatan zaku karbe shi, ku bini kamar yanda ko fiye da ku kaima novels dina na baya, ina roqon Allah daya sanya albarka a ciki, ya bani ikon rubuta daidai, duk abinda zan fada in ba zai zama alkairi garemu duka ba Allah ya karkatar dani da barin shi, Allah ya yafen kurakuren da zan yi har i zuwa qarshen kammalawa. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON DUKKAB MASOYAN TA DA MASOYAN NOVELS DIN TA DUK INDA KUKE, ME LOVE U XXโค*






" Sannu Tabawa, Allah zai baki lfy, da kan ki za ki reni abinda kk haifa, shi ciwo ai ba mutuwa bane" Yana fada yana share kwallar dake maqale a manyan idanun shi, shigowar yar budurwar yarinyar su da bazata wuce shekaru sha 12 ba, ne yasa Tabawa ta daga kai da kyar ta kalle ta, miqa mata hannu tai akan ta isa gareta, da kyar cikin azabar ciwo da kanta yake mata, tare da zafin da take ji a qirjin ta, wanda ji take kamar hucin garwashin wuta take fiddawa, ta fara magana, bayan yarinyar ta bata ruwan da ta debo mata," Ameenee,..... ki ji tsoron Allah a duk inda kk,.... ki ma mahaifin ki biyayya, shida abokiyar zamana,....ki kasance yarinyar kirki da kowa zai sha'awar zaman ki tashi...... ki kiyaye dokokin Allah Ameenee.... Allah zai kiyaye ki da zuri'ar ki har qarshen rayuwar ki,.... Malam ka riqe amanar yarinyar nan,...... kar ka bari a cutar mana ita...... ka saka ta tai ilimi.... domin kai mai ilimi ne....." tari ne mai qarfi ya sarqe ta, yi take ba qaqqautawa, cikin tashin hankali, Malam Muhammad ya miqe ya dakko ruwan zai bata, sai yaji diyar su Ameenee, tana kalmar shahada,mahaifiyar ta na mainaitawa, idon Ameenee na zubar da hawaye, kamar an bude famfo, Malam kasa motsi yar, ganin dagawar da girjin matar shi yai, tare da jan wani nunfashi, ta kwanta, hannun ta Ameenee ta daga, ta ga alamar ya sake, kuka ta fara can qasan maqoshin ta, mara sauti, ta farama mahaifiyar ta addu'a" Ya Rab Ya ilahy, Allah ina roqon ka ka gafarta ma mahaifiyata, ka kai rahama qabarin ta, Allah ka tada ta cikin bayin ka muminai salihai, Allah ka bata ikon amsa tambayoyin qabari," Malam Muhammad da yai mutuwar durqushe ne , kama kanshi yana juya shi, hawaye masu mugun zafi, suke fama kwarara a idon shi, amsa addu'ar diyarshi yai wadda gaba daya bai san me take cewa ba sai daga qarshe ya fahimta, qanqame matar tashi yai kamar zai maida ta cikin shi, hawaye ke zuba, cikin ranshi yana nema mata rahamar Allah, daga baya ya sake ta ya kwantar da ita, ya rufe mata ido, sannan ya lullube ta da abin rufar da ta rufa da shi, tashi yai ya fita tsakar gidan nasu, wata gambasheshiyar mata na gani tana ma yaran ta wanda suke dika maza magana,akan suyi su gama cin abinci su debo mata ruwa, turo baki suke suna su ba inda za su, ganin malam ya fito cikin tashin hankali fuskar shi duk hawaye yasa ta qarasawa wajen shi da gudu2 sauri2, daurin qirjin ta na rai da rai na neman faduwa, ta damqe shi, " Delu, Allah daya ban tabawa ya fini son ta, a yau ya amshi abar shi,ta tafi ta barnu cikin kewar ta, da quncin zuci, wannan qunci daja shiga ban san ranar fita ba Delu" wani tuquqin baqin ciki ne ya tokare mata wuya, jin kalaman shi, amma dake makira ce,sai ta fake da kukan mutuwar da taji ta saka hannu a ka ta kurma ihu ta fadi qasa dabar, tana turje2n kafa da hannaye, tare da cire dankwalin ta kanta da ya cure dan datti ya bayyana," wayyo ni Delu na shiga ukuna, na rasa 'yar uwata, mai sona da qaunata, Tabawa kar ki tafi ki bar mu, muna tsananin son ki, ki yafe mana laifin da mukai maki" Malam ne ya sunkuya ya daga ta, yana qara jin wanu tausayin kansu dika, dan rasa mace kamar Tabawa babban asara sukai,mace ce mai kunya, kawaici, tsafta, rufin asiri, da kuma juriya da hakuri, ga rufa asirin mijin ta, in basu da shi zatai duk qoqarin ta tai providing masi kamar itace mijin, daga mijin har kishiyar tata suna morar ta ba ladan ba, ya fifita ta da kowa a zuciyar shi fiye da kowa, ya bata mazauni mara misalin fada a cikin zuciyar shi da ruhin shi, ta zama wanu bangare na jikin shi, lokacin da sukai aure suka dare basu haihu ba, ita ta matsa mai ya auro Delu, tana zuwa ta fara da haihuwar maza, taso ta fito da iskancin ta fili Malam yai mata barazanar saki, ko nace ya sake ta ma, amma dake Tabawa mutuniyar kirki ce ta bashi hakuri, ta fada mai duk randa ya saki Delu itama ta bar zama da shi kenan, hakuri ya bata suka je ita da shi suka dawo da Delu,kowa na mamakin hali irin nata na kyautayi da kyautatawa, dan haaka sai ita Delu ta fara yi mata kisan mummuqe, a haka har sai da ta haifi yara biyu maza, masu suna Habeebu da Hamza, sannan Allah ya azurta, Tabawa da cikin Ameena, wadda ta sha gata wajen malam, kamar mai sabuwar haihuwa, hakan ne ya qara dasa qiyayyar Tabawa da duk abinda zata haifa a ran Delu,tayi iya qoqarin ta na ganin ta zubda cikin amma Allah bai bata dama ba, ran da kuwa taga mace aka haifa tai rawa tai juyi a daka tana waqoqin samun nasarar kasamcewar yaranta maza kuma sune manya, a haka rayuwa ta ci gaba sai ta dauki Ameenee da niyyae raino da ta kauce tai ta mata azaba, tana kuka, sai tace daga dan matsawa yara suka dake ta, ta hau sababi ma yaran, in Tabawa ta karbe ta tai ta mata fadan dan me zata ma yara fada, suma ai qanana ne,haka dai har Ameenee ta girma ta gane halayen Delu tsaf, mahaifiyar ta bata gano ba, Malam ma haka, ran da ko ta sanar ma da mahaifiyar ta ta sha duka sosai, a haka ta ja bakin ta tai shiru, dan yarinya ce mai biyayya sosai.
Daga ta Malam yai ya gyara mata zanin ya miqa mata dankwalin ta yana mai lallashin ta, daki ya kaita, ya miqo mata rigar kayan akan ta saka da hijab, ta saka tana wanai kuka kamar na gaske, can qasan ran ta kalaman da ya fada suna qara yunquro mata kamar kumallo. A haka aka gyara Tabawa akai mata wanka da sallah aka kaita gidan ta na gaskiya, Ameenee ta sha kuka tin tana iyawa har taji ba zata iya ba, daki ta koma ta kwanta inda Innar ta ke kwanciya,ya rungume filo tana hawaye, addu'a take ta mata a ranta ta samun rahamar Allah.






Bayan an yi sadakar arba'in ne na rasuwar Tabawa, komai jin shi suke ba dadi, tsakanin Malam kenan da Ameenee, wadda Delu ta mayar baiwa,a bayan idon mahaifin ta, amma in yana nan, har rungumar ta take a jikin nan nata mai dankaren tsami, tana nuna mata kulawa,dan haka suke qara bama Malam tausayi, in ya fita tun safe sai dare, baya jure ganin su cikin quncin da shima ya addabe shi, hakan ne ya ba Delu da yaran ta damar musgunawa marainiyar Allah, ga horon yunwa, da ya dawo sai kuji tana" zaki qara abincin ne Ameeneenaa, na kula ba ki son cin abinci, ki taimake ni kina ci, dubi yanda kk rame? Mutuwar nan duk muma a cikin dacin ta muke...." sai ta kasa qarasawa ta hau kuka, Malam ne zai rarrashe ta, ya karbi dan abincin ya ba yar tashi, ta wuni da yunwa amma gudun kar ya gane komai, dam an mata warning mai girma akan kae ta bari ya gane daidai da rana daya kashin ta ya bushe, daki take komawa ta hau ci kamar mahaukaciyar data shekara ba abincin, tana ci tana hawaye.


Mai gari ne yace a kira Malam Muhammad, sabida ya ga tunda akai rasuwar ya daina hada2r shi na Islamiyyun da ya taimaka aka bude a qarin nasu na Rimin Gata, hakuri ya ba mai garin, ya kuma tabbatar mai zai koma normal, daga wannan satin.



El- mustapha Sadauki, wani shahararren mutumi ne wanda yake da arziqi da taimakon gidan marayu,da islamiyyoyi, yau qungiyar su ta baro qasar su dake Niger, ta taho Nigeria, domin taimakawa, islamiyyar da malam Muhammad ke jagoranci, ya samu labarin qoqarin shi ne, ta bakin wani mai masa hidima, a nan Nigeria, dan yana da masu nemo masa rahotanni a qasashe don ya samu damar taimakawa.

El-mustapha yana da nasaba da kuma jinin larabawan Dake da mazauni a Dubai, garin tainakon shi ne yasa ya baro qasar shi ya kafa gidauniya anan Niger, wanda da dawowar shi da komai bai fi shekara biyar ba kenan, ya samu tsananin qiyayya daga 'yan uwan shi na can, wadan da ba su qaunar shi ko kadan sakamakon son talakawa da yake da, rayuwar shi daban da tasu, ta dalilin haka ne ya tattaro ya dawo, iyayen sun rasu. Dawowar shi nan bai sa ya yanke alaqar shi da su ba, yana zuwa a kai akai, dan sada zumunci, gaba daya hakan da yake yi ji suke kamar su kashe shi su gaje dukiyar shi, tinda yaqi auren 'yayan kowa a qasar yace bai ga wadda ta mai ba, yana son yarinyar da zai aura ta kasance daga gidan tarbiyya, da mutunci, amma fa talaka, wannan kalmar qarshen ta baqanta ma yan uwan shi ba kadan ba, a haka suke har yau da yashirya zasu so Nigeria, sannan Unguwar Rimin Gata, kuna gidan Malam Muhammad mai Islamiyya......





*Hello guys, can u pls do me a favor? Ku dan aje wannan page a wani wajen, yanda koda nai nisa kunji sha'awar bi na sai ku lalubo ku karanta,ba sai nai nisa kuna tambaya ba, wayata yar qwaya ce,lols๐Ÿ˜‰ ta yi nauyi da yawa, saboda abubuwan da take dauke da shi, ba zai yu na dinga sendin abu mai yawa ba ba tare da tana riqewa ba, so pls ku na adanawa, Thank u*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ ' YAR RAWA ๐Ÿ’…๐Ÿผ




BY HAERMEEBRAERH






page 2:







Sun iso a gajiye, inda suka fara isa gidan mai garin, suka gabatar da kansu da dikkan bayanan abinda ya kawo su, nan take mai gari ya aika a kira Malam Muhammad, domin bangaren shi ne, isowar shi keda wuya, suka gaisa sannan aka qara kora mai jawabin komai, godiya ya musi mai tarin yawa, sannan ya nemi izinin tafiya da su masauqin da yakan aje baqi in sun zo, tashi sukai suka isa gidan Malam din, daidai lokacin Ameenee ta fito wanka tana shiryawa, kiran ta Malam yai ta je tare da durqusawa, " Abba gani" " Ameenee je ki dauko mazubin ruwa mai kyau da tsafta ki debo ruwan sha mai sanyi na randar gefen madafi ki kai wa baqi a dakin baqi, sai ki dawo a kai masu abinci kinji?" Amsawa tai da " To Abba" sannan ta miqe ta tafi ta qarasa saka riga da skirt din ta na atampa, ta dora hijab din ta akai, saboda Allah ya mata halitta mai kyau da diri, wannan dalilin ne yasa bata ta'ammili da mayafi. Sallama tai cikin muryar ta mai sanyi, kanshi a duqe yake a hankali ya dago dan ganin mamallakiyar wannan daddadar muryar, kallon ta ya tsaya yana yi kawai yana mamakin samun yarinya mai kyau a cikin Africa kuma a Nigeria, Nigerian ma a kano, lumshe idanun shi yai da suke madaidaita da cikar kyau ya amsa sallamar ta, ruwan ta miqa mai ya karba ta gaida su, cikin hausar shi da ba wani ji yake ba sosai, ya amsa, miqewa tai ta tafi ciki ta qara dawowa dauke da abincin da ita ta dafa, taliya ce mai mai da yaji, sai maggi da aka bada mata? Irin taliyar murjinnan ce, amma tai wara2 kamar ba ta murji ba, sannan Malam ya siyo kifi manya aka dora musu akai, a da da aka kai El-mustapha sadauki ya fara ganin anya zai iya ci? Kawai a dakko mai abincin shi a mota ya ci, sai kuma zuciyar shi ta raya mai ya tambaye ta. " Yaya sunan ki?" Murmushi tai dan jin hausar shi, ta amsa mai da" Suna na Ameenaa" " Malama Ameena ana zuwa makaranta kuwa?" " Eh ina zuwa, dan na sauke alqu'ani da shekara goma, da sauran littafan addini, yanzu ma ina taya Abbana koyar wa a wasu daga cikin ajujuwan da suka rage ba malamai" " Masha Allah" shine abinda ya fada cike da jin dadin tabbas abinda yake ayyanawa zai tabbata da yardar Allah, " Malama Ameenaa kin iya girki ne?" Ya tambaye ta da alamar zolaya, amma ti be honest yana son jin wa yai girkin ne, cikin jin kunya da. Sadda kanta qasa ta amsa mai da" Eh, ni nake girki dama" godiya ya mata yace ta je, miqewa tai ta fita, ya hango yanda jikin ya ke ta cikin hijab, ya tabbatar an yi halitta a wajen, dakko kwanon yau ya fara ci ba sai ga El-mustapha ya tashi da taliya da manja ba๐Ÿ˜‚fadi yake lallai, Bahaushe akwai hikima......
( Ana kiran shi da Sadauki ne saboda jajrcewar shi wajen taimakon al'umma duk rintsi duk wuya, sannan duk nisan gari da surquqin qauye zai shige shi, amma asalin sunan shi shine El-mustapha Ahmad Nabeel.)


Sun kammala dukkan abinda ya kawo su, a cikin kwanakin nan ba qaramin shaquwa da sabo ne ya shiga tsakanin shi da Ameenee ba, duk da cewar, bqi taba furta mata kalmar so ba, amma soyayyar ta ta gama da dukkan jiki da ruhin shi, ita kuma a nata bangaren bata san me ne ne take ji game da shi ba, all she know is that in ya tafi she will miss him alot, and she don't even want him to go. Samun kan ta tai da shiga damuwa a duk sanda ta tina sallamar da sukai daran jiya, Delu kuwa hankalin ta ya fara kwanciya dan jin za su tafi, dan ta kula da take2n El-mustapha, wanda taci alwashin ko zata mutu bazata bari ya aure ta ba. Shi da malam ne suke ban kwana a dakin da aka sauke su, anan yake shaida ma Malam manufar shi, Malam yayi farin ciki sosai, inda yace ai wannan magana ya kamata mai gari ya jita, dunguma sukai can wajen mai garin, a gaban su ya rabbatar ko bayan ran shi suka dawo batun auren Ameenee a aura mai ita, godiya yai mai yawa suka wuce Nijer.



Tafiyar shi da kwanaki ne malam ya hau rashin lafiya a tsattsaye, wata rana ya tashi ya tafi fadar mai gari ya same shi daga shi sai mai garin yace mai " ranka ya dade ina neman wata alfarma, ina son ko bayan raina in yaron nan ya dawo ku taimaka, ku bashi auren Ameenee, dan na yi alqawari bana son na mutu ban cika ba kuma ba a cika min ba, na sanar da Abubakar amini na shima hakan," " Hab Malam Muhammadu, ai ciwo ba mutuwa bne, in Allah ya so da kan ka zaka aurar da Ameenatou" kada kai malam yai yace " Kayya ranka shi dade ni na san me nake ji kawai a zuciyar nan tawa, na kasa cire tinanin margayiya a raina, da zan iya da nayi na huta, amma zuciyata kamar ta rabe gida biyu nake ji" ya qatasa yayin da wata qwalla ke bin fuskar shi, gogewa yai, a lokacin da mai gari ke ta kwantar mai da hankali tare da mata addua, godiya yai ya tafi gida, ba ai sati ba Allab yai ma Malam Muhammad cikawa, sakamakon ciwon zuciyar da ke damun shi, Ameenee tai kuka sosai kamar ranta zai fita, in da Delu kam da yaran ta sun yi kuka na ranar daga baya suka shiga harkokin su, jira kawai take ai arba'in a raba gado.


Bayan an dan kwan biyu ne ya tattara ya tafi Dubai don sanar da 'yan uwan shi batun auren shi, sannan da gayyatar su zuwa auren nashi,fafir suka mai rashin mutunci,suka nuna su fa ba zasu tako qafafun su garin takakawa ba, masu qaramin qarfi, ya buga ya raya, amma fir suka qi aminta, yai kuka yai kuka har yaji ba dadi, take kewar mahaifan shi ta addabe shi, tabbas da suna da rai da hakan bata kasance ba, ya sani ko mahaukaciya ya nuna zai aura ba zasu qi ba,balle mahaddciyar qur'anul kareem, share hawayen shi yai ya aje masi doguwar takadda da wasu daga dukiyar da Allah ya bashi, yai umarnin su raba a tsakanin si, sannan ya tafi ya koma Niger, bayan ya iso ne ya samu wani daga abokin shi, da suka zama kamar yan uwa, wani hamshaqin mai kudi ne shima a nan qasar, ya roqi arziqin zuwa ya zama waliyyin shi, a haka suka iso Nigeria. Tana gaban murhu tai budu2 da hayaqi ne taji Sallamar shi, tabbas ba zata taba rasa gane muryar shi ba, hijab din ta ta dauka ta fita da sauri, tana ganin shine, ta durqusa a wajen tana kuka, ita kanta bazata ce kukan meye ba ne, kukan maraicin daya mamaye ta ne da shekaru qananan da ba zata wuce sha uku sha hudu ba a yanzu? Aa ko kukan murnar ganin shi ne? Itama ba zata tantance ba, durqusawa yai gaban ta shima, ya qurawa zara2n gashin idon ta da suke a lumshe idoj na zubar da hawaye ido, " Meenaa, me ya faru, ko baki son ganina ne na koma" da sauri ta daga kai ta girgiza kanta, " Abbana ya rasu bayan tafiyat ka" cike da tashin hankali ya miqe yana baya, idon shi nan da nan suka kada sukai jawur, " Ameenee saboda tsabat iskanci da tsagwaron tijara na saki aiki ki aje ki tafi yawon iskanci, dan najiyo muryar maza, wane ne yazo?" Tana tozali da shi tashin hankali qarara a fuskar ta, to in ma ta bar wannan ya zo ya dauke mata Ameenee gadon ta da ta lissafa za ta sake kayan daki da sho uban wa zai bata? Sannan wa zai ci gaba da mata ayyukan gidan? " ke dawo baya wannan dan rainin ne yazo, ba sallama da manya kawai sai kazo ka tasa yarinya qarama a gaba da zance? Kai kuma na gefe waye kai, ka tsaya ka tsare ni da ido?" Duqawa El-mustapha yai har qasa idon shi na hawaye, dan tunawa da nagartar Malam Muhammad da yai, ya gaida ta ya mata ta'aziyya, shima haka abokin shi mus'ab yai, a kaikaice ta amsa tana kada qafa, " ke ! Wuce ciki ki qarasan abinda kk yi tin fari" miqewa tai tana waiwayen shi, kada mata kai yai alamar karta damu yana nan ba inda zai je, wani dadi ne ya lullube ta tai ciki da gudu, ta je nan da nan ta hau girkin ta gama, tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar atampa, bunjimemiya, ta dora hijab, ta zauna tana bitar katatun ta, ita kuma iya masifa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sawa tai yaran ta suka kira bappanin su, tace tana son magana da su, nan da nan ko suka taru.
Shi ko yana tashi wajen mai gari ya nufa,ya sanar da shi ya dawo kuma a yau da yamman yake son a daura masu aure gobe ya wuce da matat shi, dan yanda ya tadda ita ya tabbatar tana cikn wahalar matar uban ta, mai gari bayan ya amsa gaisuwar da ya masa ya tabbatar masa da cewar za ai yanda yake so din da zarar an dawo daga sallar la'asar dan sauran mintina kadan a yi ta, aikawa yai yace a gaya ma bappanin ta in an yi sallah su hallara auren Ameenee.......




*To pah makaranta, anya kuwa auren nan zai yu kuwa,tinda Delu ta murza kanbun mugunta tace ayi mu gani๐Ÿค”*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ ' YAR RAWA ๐Ÿ’…๐Ÿผ





BY HAERMEEBRAERH






Page 3:




Dakin Delu suka shiga suka zazzauna, ta je ta debo masu abincin da Ameenee ta dafa, da ruwa mai sanyi, rabon su da cin abincin gidan dan uwan nasu tun zamanin Tabawa, shekaru biyu kenan, amma yau har da ruwan randar sanyi, tasa daga yaranta suka siyo mata balangu ta watsa masu akai, aiko kamar mayu haka suka hau abincin da ci, ga shi dama Ameenee a yan shekarun ta ba dai iya girki ba, tunda kullum ita takeyi, na safe , na rana, na dare, duk itace dole ta kware. Bayan sun kammala ne ta daya daga cikin su mai suna Bappa Lado wanda yafi kowa baqar zuciya yace, "Delu kin aika a kira mu ina fatan kiran mai amfani ne, dan

Please Login or Register in order to submit comment