Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hana shi ba.......











*to makaranta ga dai lamyah an gama secondary, kun san dai yanzu kyau ba a magana, ko yaushe zata fara rawar? Ni na matsu ta fara๐Ÿ™„*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ ' YAR RAWA ๐Ÿ’…๐Ÿผ




BY HAERMEEBRAERH




Me koko kawas, this page is for u dear, ai sana'a lfy, sana'a goma maganin mai zaman banza๐Ÿ˜‚ ME LOVE U XXโค






Page 10:








Lamyah ce zaune tana ta danna waya , tayi sabbin qawaye, ta whatsapp, ta sanadin Farha, wadan da da damar su masoya rawa ne, hirar wata waqa suke da tanda ake stapes din rawar waqar, yanda Lamyah take bayani ba qaramin burge su tai ba, dan ta nuna masu ita fa gwana ce wajen rawa, ji tai an zauna a gefen.ta, " kaiii kaiii waye wannan dan Allah ni duk zaki soke ni da qashi๐Ÿ™„" ai ko Farha ta ji haushi dan ba ta so ana zancen ramar ta, qara zaune Lamyah tau tana dada sossoke ta da guiwar hannun ta, ita kuma Lamyah tana ta dariya dan abun kamar cakulkuli yake mata, Tani ce ta shigo, riqe da hannun Mubarak, yana ganin su haka da gudu shima ya taho ya haye" Mama Tani kina gani sun min taron dangi ko?" Dariya Tani tai tace" Hmmm yanzu na topa nawa ku juya ni kumin taron gari ba, ba ruwana haka na ganku, in kun gama ku taso ku ci abinci," miqewa sukai suna murna, dan dama yunwa suke ji, abinci suka.ci suka zauna suna hira," Lamyah yaushe zamu je wajen Faisal ne, kema a saka ki a wannan harka, ki fara, shiga taro kina bada mamaki? Dan na kula burin ki kenan, ki rawa a kalla a yaba maki, dan na san za sui matuqar son ganin taki salon rawar," kaiiii Farha wannan dogon sharhi haka, ni ko yau da yamma muje Bala ya kaimu," "yippyyyy, ba ri naje na dau wankan sikari, yau sai mun ba ma yara mamaki, dan kaf stapes din ki ba wanda ban dauke ba, yai sai....." " My goodness Farha, do u really need to talk much all the time?" ๐Ÿ™„ " yeh right, ya kamata na nutsu kar a raina mu, dan kin san akwai ni da maqiya a wajen nan basu son a ce yau ni zan rawa , dan ba qaramin kudi nake samu ba, sun san bana bin ko wanne qato daki, so kudin dana ke samu na daban ne" " mu ai ba ruwan mu da kowacce qatuwa kawai burina bai wuce nai rawa a min tafi ba na burge kowa sai naji nishadi a zuciya ta," haka sukai ta tattaunawa, har biyar na yamma, Lamyah ce ta fara tashi ta shige dakin su, dan tare suke kwana, yanzu mubarak ya zama yana kwana shi daya, wannan dalilin ne yasa suka ware mai daya dakin shi daya, Tani da sassafe take zuwa sai takwas na dare take tafiya.


Bayan sunyi saallar isha'i ne suka yi ma Bala magana, ya fiddi mota, kowaccen su ta sha baqar abaya, tai rolling kanta, cikin ko kayane qanana, inda Lamyah ta saka skirt tsukakke ta qugu, qasan shi kuma mai fadi sosai, ga wasu yan stones masu gyalli da shegi daga qadan, haka akai wa ta saman ma ado, sai rigar ra dingilalliya, data kama jikin ta, tsam, ta gyara gashin ta , ta daure ta sake shi bayan ta tsaga gefen shi.ta kwantar da shi, avun dai ba a cewa komai sai wanda ya gani, Lamyah ba qaramin kyau tai ba, Farha sake baki tai.tana kallon ta kawai, " Farha kallon yao yawa tun muna shiri kk kallo na har yanzu, sai munje kin ja an raina mu," Farha ce ta gyara zama ta juyo gaba dayan ta ta fuskanci Lamyah zata fara zuba danneman surutun nata, Lamyah ta katse ta da" Farha na roqe ki da Allah ki hakuri, kar ki zuqen energy kan rawar," murguda baki tai ta juya ta ce " Fine"๐Ÿ™„ dariya Lamyah tai qasa2, dan tai imanin ta bar Farha ta bude baki, har su isa ba zatai shiru ba.

Sun isa suka tadda Faisal a gofar shiga wajen rawar yana ta jiran su " Haba dan Allah sai kace wadan da ba zaku zo ba, kun shanya ni malamai," hakuri Farha ta fara bashi tana fari tana son zuba mai zancen nata yace" dakata kanya, dan in kk fara zuba sai an rasa mai kwashe ki yanzu, muje ciki a rubuta sunan ta ai komai a gama ta fara gudanar wa yau mu gani," ran farha ya baci sosai " Eh ai ko yau ko kun qi Allah sai nai surutu, dan kuwa ina cikin farin ciki, ba wanda ya isa ya hana ni magana ehe tin da ba d leben kowa nake zancen ba," ta qarashe cikin hawayen shagwaba, ita a dole yau an qi sauraren ta, Lamyah ce ta kamo ta tana lallashi, sannan ta hakura ta gyara tsaiwa zatai qala'in maganar da. Batai ba dazun aiko suna kula da hakan basui.magana.ba bare tace anqi ji suka sa kai ciki, bata gane ba, bin.su tai tana ta zuba , ko A ba mai gane wa, Bala dake gefe sai dariya yake, kama hannun Mubarak.yai suka tafi shan ice cream, dan da shi suka.taho, Lamyah ta ce suna tahowa da shi.tinda.ba kowa gida, Tani ta tafi. Wani waje suka je aka gama komai na tabbatar da Lamyah a cikin masu rawa, zuwa sukai wani daki dan yin kwalliya, sai Faisal ya dakko wasu kaya ya bata akan ta saka, qanana ne sosai, tace " A'a wannan ma sun yi qanqanta in gaskiya ne, balle ka ban wannan, barni da wadannan, tinda ni.ba wai wani abu ya kawoni ba bayan rawa, and wannan sune perfect kayan da zan yi rawar da nake son yi d su, cire doguwar rigar tai, ta baza gashin ta, sai da faisak ya kusa suma dan ganin kyau tsabar shi, ga wani gashi da tin da take sai dai a TV yake ganin irin shi,magana take mai ta shirya bai ji ba, sai d ta bugi kafadar shi sannan cikin in ina ya amsa ta da su je, yana tafe yana juyowa baya, sai tuntube yake, dariya kawai suke ta mashi, har suka isa, wani irin kishi ne mai tsanani ya kama yammatan wajen da ganin fitowar Lamyah.............
















*nima dai kishi ya kama ni na ganin Lamyah zata danse ba ni a ciki*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ ' YAR RAWA ๐Ÿ’…๐Ÿผ





BY HAERMEEBRAERH





*Alhamdu lilLAAH for another blessed and healthy year, Ya Allah increase me in Eeman, health, wealth, and taqawa, ya Allah make me among the Salihun. HAPPY BIRTH DAY TO ME๐ŸŽ‰๐ŸŽ‰๐ŸŽ‰๐ŸŽ‰๐ŸŽ‰๐ŸŽ‰*
โค








Page 11:






Tana hawa wajen da zata gudanar da rawar kuwa gaba daya hankulan mazajen wajen ya dawo kanta, wasu daga cikin matan dake wajen kansu sai da suka razana da ganin ta," wannan daga ina?" Waqa ce ta Arabs aka kunna mai matuqar dadi , a hankali ta fara takawa, dan sai taji gaba daya idon mutane ya mata yawa, amma da ta ci gaba da yanayin yanda aka fara tafa mata sai ta ware, daga nesa Farha ta kwada mata kira " Go Lamyah, show them what u got" kaii rawa fa tai rawa, kudi ne kawai on air, sai watsa mata su ake, qugun nan kamar zai karye saboda juya shi da take, amma ko a jikin ta, Farha ce ta zabura ta haye itama, rigar ta ta wurgowa Faisal, dan ko ankarewa bai ba, kan ya miqa hannu ya cafo ta har ta zille, tana " inaaaa wannan casu ba zan taba bari ya wuce ni ba, in na bari ya wuce ni sai kunyi jinya ta" gaba daya stapes din Lamyah kusan ba wanda bata dauke b a zman su, nan fa suka ci gaba da bada mamaki, haba mana, wasu maza ne daga gefe suka taso su biyu, suka iso gaban su suka balle farare bugun ABUJA, zuba su suke kamar ba sa so, tun faisal na kwasa shi daya sai da wasu ma'aikatan cikin wajen suka fara taya su, as promised, suna cikin rawae 10 na dare tayi, Faisal ne ya matsa kusa da Lamyah ya rada mata, ai ko tai wani irin juyi da qugun ta, tai baya da kanta sannan a hankali, cikin kwarewa ta dago, wani ihu.aka saka a cikin wajen, cikin nishadi da jin dadi ta jawo hannun Farha da ba ta san me ke faruwa ba kawai tiqar rawa take, masifa ta juyo tayi sai taga Lamyah," My goodness ni fa ban dade da fara wa ba , haba ki bari nima.na maida kwadayin rawata mana," Lamyah bata kula ta ba, Faisal ya wurga mata rigar ta, Lamyah ta nuna mata agogon jikin wayar ta da ta karba hannun Faisal, kame baki Farha tai, ta bi bayan Lamyah, suka shiga wajen kwalliya, ta dau kayan ta, bayan sun kimtsa ne, Faisal ya shigo, riqe da kudi masu yawa a hannun shi, wanda a qalla zasui dubu 70k hankalin farha ba qaramin tashi yai ba data ga yawan su, ita da sai dai a bata irin 30k 20k dinnan, tana ganin ta sha kwana da yawa, yau ga kudi masu yawa a gabanta, gyara tsaiwa tai tana son magana, sai ta bude baki ta yarfa hannu.sai kuma.tai shiru ta hadiyi yawu, data kasa magana kawai sai ta doka tsalle ta dane Lamyah, Lamyah dariya tai ta karbi kudin sukai godiya suka tafi, a mota suka tarda Bala daga shi har Mubarak sun fara bacci, shiga sukai, suka zauna inda Lamyah ta mannawa Mubarak kiss a goshi, tana shafa kanshi, nan take ta sa hannu a jaka ta zaro kudin rawar da suka samo, dubu goma ta miqawa Bala, sannan sauran gaba daya ta miqawa Lamyah, sannan ta dora mata gannu akan lips din ta alamar bata son godiya ko wani surutu, Farha kasa magana tai, ta qame qam, toshe bakin ta tai tana hawayen farin ciki, Lamyah zamewa tai kadan ta jingina da bayan kujerar ta lumshe ido, tunani kala2 ne cikin zuciyar ta, tinanin Abii, Ammiii, Yah Amee din ta, da kuma rayuwar kadaici ta rashin 'Yan uwa da iyaye da take ciki, kiss taji an mata a kumatu, ta bude ido tace " WTF Farha, do u have to do that? Ni nace maki na yafe komai kin tsorata ni gaba daya hankali na baya nan," rungume ta Farha ta qara yi, tana kukan murna," you have no idea how this mean to me, ba wan da ya taba ban dubu biyar ba tare da ya nemi wani abu daga wajena ba, na shiga qunci da matsin rayuwa, ba mai taimakona, a kullum inna tashi kk ga na samu kudi to naje nai rawa ne, dan ita kadai ce abinda na iya nake mora a rayuwata, mutanen duniya basu da kirki Lamyah, ki gode Allah baki san babu ba, baki san halayyar mutane ba, wanda sai sun ga kina cikin matsi zasu so kassara rayuwar ki" ta qarashe cikin kuka sosai, sakamakon tina baya da tai lokacin tana ita daya, ba mataimaki sai Allah, Lamyah qara rungume ta tai," its k dear, everything s ganna be just fine inshaa Allah, nothing will ever disturbe u i promise,"Lamyah na shafa bayan ta sai ji tai Farha na munshari, to an gaji, ga uwar rawar da ba a sa ta ba ta tiqa, dariya ce ta kwacewa Bala da Lamyah, aiki suka hau darawa, Bala ne yace" shi yasa nake son ta she is so innocent, ba ruwan ta da shirme, amma gaba daya a unguwa sun qi gane hakan, ka dan ne suka fahimce ta, akwai lokacin da aka ce za a kore fa a unguwa kar ta bata tarbiyyan yaran wajen, Farha ta musu hauka, tace nan nan wakilin mai unguwa da ta taba kai mai koken ya taimaka mata kwanan ta biyu ba abincin kirki neman ya keta mata mutunci yai, da ita din yar iska ce yan da take a yunwace ai da ta yarda, ke na taqaice maki a haka dai magana ta mutu, sai ga 'yar da suke cewa tafi kowa hankali a unguwar 'yar wani kamilin mutum Malam Sule, ta yi ciki, kaiiii ranar sun ga tijara wajen Farha" ya qarasa yana dariya sakamakon tina me ya faru ranar da yai, isar su gida ne ya katse shi, su kai ta dariyar rikici irin na Farha, har yanzu da suka girma suke jin suma manya ne tin da sun cika 20 da yan kai Farha bata barin shiririta, sai son girma, in Mubarak yace ma Lamyah mummy, ita kuma Farha yanzu zata kamo shi tace," to mara ta ido, in ka qara ce man Farha ba Aunty ba , ko Adda, ko Yayah zaka ga ya zan da kai sai na balle maka haqori daya," tin Mubarak na kuka har ya koma mata dariya, data sake shi zace Farha ya kwasa da gudu, ba ko zata tsaya bata lokaci wajen bin bayan shi ba.







*NIJER REPOBLIC*





Yau shekara hudu da watanni kenan da Baaba Mus'ab ya san mutuwar Amini kuma aboki sannan dan uwan shi El-mustapha, ran da suka sani dan qaramin hauka ya masu, Ameenullah kuwa, ya suma yafi a qirga, sai da ta kai an mai qarin ruwa tare sa allurar bacci, dan gudun kar wani abu ya same shi, satin shi biyu cif aka sallamo shi, ya rame yai baqi, baya umm baya umm umm, tinanin dake daga mai hankali, da ganin gawar yasan kashe mai Abiii akai, amma an hana su yarda da hakan, domin duk wani shaidar mutuwa yai sakamakon taka bawon Ayaba, da yai an gabatar, in ya mutu ne haka kawai ina Lamyan shi? Ina Mubarak? Sannan ya akai ba a ga komai na dukiyar shi ba? Dakko wayar shi yai ya bude, yana duba messages nan ya ga saqon , da Abiin shi ya turo mai, jiki na rawa yana hawaye ya ke qoqarin bude saqon,
Sallama ce sai gaisuwa, sannan ya fada mai yana cikin hadari, game da 'yan uwan shi, amma kar ya samu koma mene ne Lamyah da mubarak will be safe inshaa Allah, wasu hawaye ne masu zafi sosai suka zubo mai, "to ina take? Ina zan gan su? Me yasami qanwa ta, amana ta? Wace irin rayuwa suke? Ta ina zan fara neman su?" Tari ne ya sarqe shi, ya fara yi ba tsayawa, Mommaa Aisha ce ta shigo cikin hanzari, fridge din cikin parlorn shi ta bude ta dakko ruwa ta kamo shi jikin ta tana hawaye ta bashi , tare sa shafa bayan shi, a hankali ya samu nutsuwa, " ka yi hakuri Haerbeebee, ka kwantar da hankalin ka, ka ma Abiin ka addu'a shi da Ammiin ka, ita suke buqata a wajen ka ba kuka da damuwa ba, ba za su so ganin ka a haka ba, sannan ina son ka sa 'yar uwar ka a addu'ae itama Allah ya bayyana mana ita," kuka yake sosai kamar qaramin yaro, yana qara mannewa a jikin Momman shi, a hankali tana shafa bayan shi da kan shi yai bacci, gyara mai kwanciya tai cikin tausaya wa dan nata, dan ta san shaquwar dake tsakanij su, haka ta fita tana share kwalla..........





*celebrate with me Roumie na and Aisha Bixxisiou, kuna raina always, ku din daban ne, love u da yawa*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ 'YAR RAWA ๐Ÿ’…๐Ÿผ




BY HAERMEEBRAERH




*WOW ! i must say thanks to this wonderful and amazing people, u guys ar awsome, and i love u so so so very much u made my day so beautiful*


*My family i love u allโค My friends ku daban ne na zama ku kun zama ni, Widad Ummu Hafeezaโค My family freind, and so many others sunayen ku ba zai fadu a dan wannan page ba, amma ina mai tabbatar maku da naji dadin addu'oin ku jiya, Allah ya bar mu tare ya saka maku da alkairi mara yankewaโค*

*Mamu Novella*
*Bani nayi kaina ba G*
*Matsalolin Mata A yau G*
*Safaa & Marwaa Fans*
*Tabital fulaku G*
*Zahrah Surbajo G*
*Ummyn Yusrah G*
*Al'ummata G*
*Sophy And Vc novels*
*Sawwama Novel G*
*Matan Gidan Daraja G*
*Qasaitattun Mata G*


*Na gode da addu'oin kukuma, sosai naji dadi, Allah ya saka maku da alkairi mara yankewaโค*



Page 12:




Sai da Baabaa Mus'ab da Momma Aisha suka sha fama sosai, kafin Ameenullah ya daidaita, ya koma normal, amma ya rage yawan fara'a sosai, sannan ya rage magana, komai akai sai dai yai murmushi, ko ya bada amsa da kai, qasan zuciyar shi cike yake da soj ganin qanwar shi, da yanzu ta tabbatar wa kan shi son ta yake matuqa, so irin na aure ba soyayyar wa da qanwa ba, zuciyar shi na azabtuwa in ya tina har wannaj lokacin ba zai ce ga kamannin ta ba, muryar ta sai ta waya yake ji, abun na matuqar damun shi ba kadan ba, sannan ya zatai ta kula da Mubarak, iya wannan tswon shekarun, yakan yi kuka sosai, ya gode Allah, domin ya san tabbas suma suna cikin kadaicin rashin kowa nasu, cigiya kam a gidan redio da TV tare da jaridu duk sun.bayar, amma shiru kk ji. Yau ne Baaba ya samu Ameenullah, ya ke mai maganar komawar shi Nigeria aiki, don zaman ya isa haka, yana da kyau a ci gaba da kulawa da dukiyar da El-mustapha ya bari ko dan yaran shi, da ci gaba da yin sadaka da kyautukan da ya saba, ba dan Ameenullah yaso ba ya gyada mai kai, bayan ya fita ne ya kwanta yana kallon sama, sai tinani yale kala2, har aka kira sallar magrib, tashi yai yaje yai alwala ya tafi masjid, bayan ya dawo ne, ya fara shirya kayan shi kamar yanda ya saba, kiran abokin shi yai, Faisal,
" Yah Man ya akayi ne? Ina fatan dai gobe zaka zauna gida ba zaka wajen shegiyar rawar nan ta ku da kuka dorawa kan ku ba?" " yessss gobe zaka zo? Alhamdu lilLAAH, dama ina son ka zo akwai wata haja dana aje maka, wannan karon ko min qin kusantar mace da kk akan dalilin wata da ba ta san kana ma son ta ba, wannan karon sai ka dana, wannan kalar kuce, ta hadu iya haduwa, bata da makusa ko ta ina, matsala daya da za a samu shine, bata kula kowa, sannan bata cika magana ba, dan ina jin tin da muke bai fi sau uku na taba jin maganar ta ba, ita dai kawai ta zo tai rawa ta tafi kuma......." "Ya Allah, Faisal, me yasa kk min wannan dogon sharhi haka ne? Ni fa ban ce maka ina son kowa ba,hasalima kai kasan bana son hulda da mata, dan Allah ka aje surutun ka a wata ma'adana wataqila zai ma amfani, wanni karon" kit ya kashe wayar ta dayan bangaren Faisal ko da yake shirin shiga hotel din yai dariya kawai dan yasan halin abokin nashi.






Washegari da sassafe ya nufi Nigeria, bayan nasiha da Baaba ya saba mai wannan karon sai da ya qara akan na da, Momma ma haka tai ta mai nasiha tare da kwantar mai da hankali, cikin so da qaunar dan nata tare da kewar shi da ta fara tin kan ya tafi ta kai bakin ta goshin shi ta manna mai kiss, bayan ya tafi ne Baaba mus'ab yace " To sauran ni, dan na kula gaba daya hankalin ki ya tattara akan dan ki, tin da ya zo kk manta dani" ya qarasa cikin shagwaba kamar wani yaro, kwallar dake idon ta ta mayar nan da nan ta maye gurbin damuwar ta da farin ciki," Habaa Baaban Lamyah, da girman ka kk shagwaba, to matso ka gani," matsawa yai ya miqa mata fuskar shi, lips din shi ta kaiwa soft kiss, nan take ya lumshe ido, kan ya bude ta shige bedroom tana dariya, dariya yai shima ya bita yana," ai sai ki saya ki karbi tukuicin ki kema ko," " A'a ni kam na yafe Allah," dariya sukai cikin nishadi da nunawa junan su so.





Da magrib Lamyah na gani da guntun wando iya cinyar ta, kalar bby pink, sai riga da ta daga hannun ha ana ganin cikin ta, da cibiyar ta, ta daure gashin ta, hannun ta ya sha lalle da qafarta, an mata baqi da ja, sai naga ta dakko tirarukan ta tananta barin su sannan ta shafa powder, tana gamawa ta dora baqar abaya, kusan shigar da Farha tai kenan, Mubarak kuwa manyan kaya suka saka mai, dan shi wataran har kuka yake in an saka mai qananan kaya, sam.basa burge shi,in ba bacci zai ba ya saka na bacci, Farha kan kira shi saurayin qauye kawai, shi kuma ya murguda baki kamar budurwa harda fari da ido, in ta biyo shi ya gudu wajen Mummyn shi, yana mata gwalo," Lamyah yau gaskiya sai mun fi ruda duk wanda Allah ya sa yai tozali da mu, ni har na fara jin kunya, anya bamui shigar tsiraici da yawa ba?" " ke malama in zaki gama ki zo mu tafi ki taso, ai dai naga ba sai da jikin namu zamu ba ko, zamu ne dan nishadin mu kawai mu komo," " haka ne, to ni dai yanzu gaskiya jibi sai naje kasuwa, dan siyo pant da Bra na acuci maza, qawata Cutie kullum shi take sawa, kan na gano ta ba mai cewa ba nata ba, ni nqi ta tafiya zalau2 ba nama ke kuwa ko ina sai san barka," maganar ta ba qaramin ba Lamyah dariya tai ba, har tana kama ciki, "kin ga matakar ki dariyar tsiya dilla ni tashi mu tafi, nimq zan qibar ne ai, sai na baki mamaki, har sai kin nema min abun rage ta, kai kuma da kk guntse dariya ka sake kayi ta sai na zaune ka, ta shi kaje kace ma Bala mun gama," ta fada tana kunburi ita an mata dariyar bata da qiba, aiko sai da mubarak ya kai qofa ya juyo yace " Farha ni dai kk zaune ni sai na mutu, qashi zaki soka min," da gudu ya fita yana dariya zata bishi Lamyah ta riqe ta," haba princess din Bala, ina zaki da gudu haka ai sai Bala yace baki da aji," " to laifij waye in an ganni ban da ajin ? Ba ke kk fadan haka a gaban shi ba gashi nan yai hadda, ko batan wasali baya yi? Ni dai gaskiya asan ya za ai dani, ko kuma kema ki fara slimming cinyoyin da qirjin ki su dawo kamar nawa," ta qarashe maganar cike da shagwaba, Lamyah ce ta shanye dariyar ta ta kamo ta tana buga bayan ta," kar ki damu yanda kk so haka za ai, tashi mu tafi," miqewa tai cikin yanga, kamar zata balle, Lamyah ce ta saki tari, mqi hade da.dariya, aiko cikin fushi fuuuuu tai waje, zama tai gefen kujera tana ta tiqar dariyar ta, sai da tai ta qoshi ta gyara fuskar ta suka fita, lokacin tara ta kusa, a hanya ba mai kula kowa, Bala yayi iya qoqarin shi darling din shi tai magana taqi sam,Lamyah ya zabgawa harara ta madubi, daidai sun hada ido," Whatttt???? Me nai kk hararata," " nasan laifin ki ne koma me yasa Farha fushi, ga shi nan kin ja min," dariya take son yi amma bata son ta bata ma farha rai again,dan yanzu kam tasan tana gab da kuka, kuma tana son ba Bala amsa, haka ta shanye dariyar ta kawai ta koma gefe tana kallon titi, hannu ya sa ya riqo hannun Farha wadda ta zame da sauri, ta na kallon shi, da ma'anoni masu yawa, tsayawar motar a filin da suke parking ne ya janye hankalin ta daga kan shi, da sauri

Please Login or Register in order to submit comment