Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kama murfin ta fice, Faisal da Ameenullah su kuma sun fito, suna hira, kawai sai Lamyah ta tsinci kanta da faduwar gaba, like wise Ameenullah, shi ko harda dafe qirjin shi yai, "Man lfy?" " ba komai haka nan naji qirjina na bugawa da sauri, kuma zuciyata ta tsinke sosai Allah ka jiyar da mu alkairi," amsawa faisal yai yana kallon gefen su, inda suke takowa cikin yanga da qasaita irin na hadaddun mata........
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA. 💅🏼






BY HAERMEEBRAERH










page 13:






Tunda suka qaraso da Ameenullah ya hada ido da Lamyah, gaban shi yai wani irin bugawa, wani irin abu yake ji daha qafar shi zuwa kan shi, itan ma hakan take a wajen ta, kallon kallo sukai, kafin su dauke kai ga barin kallon juna, Farha ce tai fari tace," Hey handsome, ya kk?," banza yai da ita bayan ya mata kallon tara saura kwata, wayar shi ya zaro yana daddanawa, yana kallon tsohuwar Numbern Lamyah, dan guntun tsaki Farha tai wanda ya sa Ameenullah ya kalle ta da wani irin kallon da yasa ta ja hannun Lamyah tai gaba, tace ma Faisal," ka same mu a ciki in wannan dan rainin ya barka, ni kwata, bana son yana dawowa gaba daya baida sabo, dan ma ya samu mace kamar ni tana kula shi yake wani basar wa, dadin abun ina da saurayi, ba a kasuwa nake ba ehe," ta fada lokacin da take kada yan qananun duwais din ta, Lamyah kam yau tana cikin dariya ne sosai, amma wannan karon duk da dariyar da take ji, gaba daya ta kasa yi, saboda yanda take jin mutuwar jiki, bayan sun shiga ne Farha ta kamo hannin ta ta fara cire mata Abayar ta, ," Gurl me ke damun ki ne? Gaba daya naga jikin ki yai sanyi, ko dai wani abi na miki?" " A'a ni kam baki man komai ba haka nan naji jikina ya mutu, amma ba komai da naji taken mu zan ware na san," ta qarasa cikin murmushi, Farha ce ta qarasa mata make up, zata ce Lamyah kenan Faisal ya leqo, sai ta sauya da sunan da tai register da shi wato, Laila, ," lokaci yayi me kuke yi ne har yanzu?" " gamu nan zuwa" miqewa sukai a tare suka fito, kida aka baza masu nan da nan Lamyah ta ware, rawa take kamar ba qashi a jikin ta, juyi take kamar wata tarwada, guqun nan kamar zai karye saboda girgiza shi da take, haka ma qirjin ta, ga gashin ta da ta baza in tana rawa yana gaba yana baya, ko ta maoda kai gefe, abun sai wanda ya gani, Ameenullah da ya leqo fadama Faisal zai kwanta ko ya dawo kar ya neme shi ya tsaya kallon ikon Allah, baki ya bude bai ma san yayi ba, kallon ta yake kamar idon shi zasu fado, wani iri zuciyar shi take kamar ya ruga da gudu ya dauke ta ya boye haka yaji, dukan kafadar shi yaji anyi, " Man ya dai, ko ka gano abinda na hango maka ne?" Faisal ya fada cike da tsokana, daure fuska Ameenullah yai," malam dama na zo fada maka ne ka wuce dakin ka kar ka damen in ka dawo, bacci nake ji," kawai ya sa kai ya wuce " Sunan ta Lailah," iya abinda Faisal ya fada kenan yai gaba, maimaita sunan Ameenullah yai tayi har ya isa dakin shi, kwantawa yai ringingine yana ayyana abubuwa da yawa a ran shi, " Lailah, Lailah kin bata sunan ki, na tabbata wannan ba zata wuce sa'ar Lamyah ta ba, Allah sarki Lamyah, duk in da kk Allah yare man ke, ya kiyaye ki daga fadawa halaka," hawaye ne ya gangaro mai, amma sai me rufe idon da yai hoton Lailah yake kallo, miqewa yai da sauri ya leqa window , aiko yana budewa tana daga kanta, hada ido sukai daidai zata shiga mota, saurin shigewa tai, dan bata zaci zata gan shi ba,saboda gaba daya da tinanin shi ta gama rawar ta, wurga ido take dama taga ina zata sake ganin wannan kyakkyawar fuska? Aiko yana sakewa ya dafe qirji yana murmushi, itama murmushi tai data zauna, Farha ce ta fara zuba kamar kanya, Bala na amsa ta cikin jin dadi, dan dazu ta tsume bai sami damar magana da ita ba, har suka isa gida Lamyah na tina handsome din da ta gani dazu.



A qa'ida kwana biyu suke a tsakani kan su koma rawa, Allah Allah Lamyah take lokacin komawar su yayi tai tozali da wannan kyakkyawa, haka ta bangaren Ameenullah, roqon shi Allah ya bashi ikon daurewa kar ya tambayi wannan sarkin surutun inda zai ga Lailah yake. Bayan ta idar da sallah ne ta yi karatun qur'ani, Farha da Mubarak ne suka zo da nasu qur'anan suka zauna suka tankwashe qafafun su, qari tai masu kamar kullum bayan sun kammala sukai ma iyayen su addu'a, bayan sun idar ne kowa ya miqe yai dakin shi, kwantawa sukai dan su koma bacci, amma kamar daren jiya,haka bacci ya kasa daukar ta, Farha ce ta juyo tace," Lamyah wai me ke damun ki ne? Gaba daya tin jiya na kula baki da walwala, ko wani abun na miki ne ki sanar dani dan Allah," ta qarasa idon ta ya cika da kwalla, Lamyah kamo hannun ta tai da sauri tana girgiza mata kai,idon ta cike da hawaye, nan da nan suka fara kwarara," Farha ban san meke damuna ba, amma ni dai nasan ina missing Abii na da Ammii ga Yah Amee shiru, ba mai nemana, in ma sun neme ni ba zasu ganni ba, zuciyata ta fara raya min na je neman dangin mahaifiyata , dan na samu wasu a kusa da ni da zasu zama majingina a garen ,"kuka take sosai, zuciyar ta na quna sosai, ga shi ba zata iya sanar da Farha me ke damun ta game da wannan Ajnabin da ta gani dazu ba, tabbas zuciyar ta ba wanda take so illa Yah Amee din ta, amma wannan baqon lamarin da take ji game da wannan bawan Allah yana bata tsoro, kukan ta ne ya tsanan ta, Farha sarkin surutu ba baki itama kukan take, haka Tani ta isko su," me zan gani haka yarannan ku sa juna gaba kuna kuka, ko mai yai zafi maganin shi Allah, ku sauqaqa wa zuqatan ku ko kun samu sauqin ko me ke damun ku," a tare suka fada jikin ta suna kuka, bubbuga bayan su tai har suka samu sukai shiru, " to yammatan Tani, ku zo muje a hada abin karyawa," miqewa sukai, suka bi bayan ta suna goge fuskokin su.

Tanj ta kasance tana koyar da su wasu abubuwan da ya zamana basu iya ba, dan kar au tashi ba su san komai ba, a da Lamyah tana ganin hakan a matsayin aikin wahala, tin da bata saba ba, amma da Farha parrot ta zauna ta mata bayani, a cikin bayanin nata ne, take fada mata a nan in ba ta iya komai ba, wata zata karbe mata miji, ko da Yah Amee din ta ne kuwa, habaaa tana jin haka hankalin ta ya tashi, kishin su na Larabawa ya motsa mata, a ranar ta wahala wajen koyon girki, ta yanke ta qone,amma duk bata ji, burin ta bai wuce ta ga ta iya komai da zai ja mata hankalin Yah Amee din ta, a yanzu tana matakin tsakiya, na koyon abubuwa, Tani kuma ta zage damtse tana koya mata abincin kala2 na qasashe daban daban.





*sai nace Lamyah girki adon mace wadda ta iya ta huta, wadda batabiya ba ta sha haushi, mata a dage a iya girki, da sauran abubuwan da suke saka mace ta zama qasaitacciyar mace a wajen miji da ko ina*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA. 💅🏼





BY HAERMEEBRAERH







page 14:





Yau tin safe Lamyah take cike da farin ciki, zuciyar ta fes, " Mummy why ar u so excited ? " " yeh what's new?" " kunji min mutane kawai ku sani gaba da tambaya akan mutum ba zai farin ciki ba kenan?, to nothing new, kawai yau ina jin nishadi ne saboda RAWA, kema kin san ita ke sani nishadi ko?" Farha tabe baki tai tace " Imm bari kiga na tafi wajen Bala mu sha hirar mu saboda jiya ya wuni school, bamu zanta ba, ina son fada mai how much i love him, ina son na ga kyakkyawar fuskar shi ko hankalina ya kwanta, qawaye na suna ganin a yanda nake bai dace da ni ba, ba zasu gane mene ne so ba, so ba ruwan shi da waye kai, wana matsayi ka taka a rayuwa, wace kala ce fatar ka, ya tsahon ka yake, ko ya jikin ka yake, da ya tashi shiga zuciya baya kwankwasa, fadawa yake cikin zuciya, ba notice," tabbas Lamyah ta fada tarkon son baqon da bata sani ba, dan na tabbata in da dane wannan cakwaikwaiwar take wannan zuba zamcen sai ta katse ta, ko ta bar wajen , amma wannan karon lumshe ido take tana jin tabbas in haka ake so to itama ta fada tarkon shi a farkon ganin ta da wannan bawan Allah da ko sunan shi bata sani ba, Farha ce ta katse ta, " Kar dai ki ce man tin da na fita har yanzu haka kk baki motsa ba, naje Bala baya nan Baba ya ake shi," ta qarashe cikin zumbura baki, kwantar da kan ta tai akan cinyar Lamyah ta juya bayan ta, Lamyah ce ta dora hannun ka akan ta tana shafawa," Farha me zai hana wani satin Bala ya kaini Rimin Gata? Na matsu na ga dangin Ammii na yanzu ko na gaggauta wucewa Niger neman Yah Amee, saboda Farha my heart us trying to betray me, tana son kuma ta ci amanar Yah Amee, tabbas in abinda nake ji ya tabbata zan shiga uku, Farha zan shiga matsananciyar damuwa, domin zuciya ta bata kasamce daga cikin masu adalci ba," Farga dake kwance tana lumshe ido jin kalaman Lamyah sai zuciyar ta tai sanyi, gaba daya tausayin ta ya kama Farha, musamman da taji ruwan hawaye a kafadar ta, miqewa tai ta zauna kusa da Lamyah sosai ta jawo ta ta dora kan ta a kafadar ta( duk da dai ba wani tsokar arziqi sai dai ma ta soke wa baiwar Allah kumatu da qashin kafada🙊) lallashin ta ta yi sosai sai da ta gama kukan ta sannan tace mata " Lamyah ki sani Allah baya dorawa rai abinda ba zata iya ba, wannan wa'azin ki ne, ina son kamar yanda kk fadakar da mu kullum ya zamana kema kina saka maganganun ki a cikin aiki inshaa Allahu zaki samu komai da sauqi, don Allah ya hore maki sanin daidai da kuma abinda ba daidai ba, sai ki gode mai ta hanyar amfani da su din, ina roqon Allah daya yaye maki damuwar ki Lamyah na," da Ameen ta amsa, sai taji zuciyar ta wasai, tashi sukai suka shiga daki, Lamyah ta fara fiddo masu da kayan da zasu saka da dare, wasu skirt ne masu hade da dan gajeren wando a ciki, skirt din iyakar shi guiwa, sai rigar da ba ta wuce masu cibiya ba, iri daga multicolor ne kayan, kusan kowacce kala akwai a jiki, amma ya sha adon stones, masu kyalli,n golden a jiki," wai ban gane ba kin kwanta?" " to mi zan, dan Allah barni na dan taba bacci kafin daten yayi, yau na gaji haka kawai nake jin gajiya , kewar Bala ta cikan zuciya, rabona da shi tin shekaran jiya fa," juyi tai ta kwanta abinta, Lamyah ta dakko masu takalman sunda zasu saka nan ma ta aje, sai abayar da zasu dora, tashi tai ta tafi kitchen ta dakko cucumber ta markade bata wani saka ruwa ba amma saida ta yanka qanana sosai, tana fara markaduwa sai ta debo madarar shanu, da zuma sannan ta saka kwai a ciki, sai dan tomeric powder da cinnamon powder da ta zuba, qara markadawa tai saida suka hade tsaf, sannan ta juyo a dan mazubi, dakin su ta koma ta dakko masu zannuwan da suka ware don gyara jikin su, dadawa Farha duka tai a yar cinyar ta da ihu kuwa ta miqe, dariya ta saka , ta miqa mata zanin, harara ta banka mata " dan cin zali kawai ina kwance har bacci ya fara dibata, ki makan duka a cinya sai kin lotsamin ita," dariya abun ya ba Lamyah sosai," me din zan lotsa kamar wata katifa? Ke ai sai dai a karya ba dai lotsawa ba," Farha ce ta biyo ta akan sai ta rama kuwa tun da abun haka ne, aiko suka fara zagaye dakin, da Lamyah ta samu dama sai ta shafawa Farha wannan hadin , sannan ta kwasa da gudu, a haka har suka gaji suka zube a gado, suna maida ninfashi, bayan sun sha dariyar su ne suka tashi kowa ta shafe jikin ta fea da shi," wai ni wannan kuma na meye, kusan kullum sai kin fiddo da sabon abu, duk lokacin gyaran jikin mu yai sai naga sabon abu kk fiddowa ina kk koya?" " a gaskiya a kwa wadan da Ammii na ta koyan, akwai wadan da da kaina na qirqira," " gaskiya na gode dan i want to look beautiful for Bala today, sai ya rasa gane wacece wannan, shin canjo ni akai," sai ta dira wani tsallen murna, Lamyah kada kai kawai tai tana murmushi, dan Farha na bata dariya, ko dake shima Balan ya mato akan ta ba kadan ba,dai dai sun gama ne Mubarak ya shigo, a duniya in yaga su Lamyah sun yi abunnan tsoro ke kama shi, aikk zaro manyan idon shi yai waje ya kama baki, juyawa zai da gudu ya fice aiko abokiyar fadan shi ta cafe shi, shafa mai tai a kuma tu, yana bude ido sika hada ido da fuskar ta da tashi, ya kwalla qara, yana qoqarin sauka, ta hana shi, sai tsorata shi take, Tani ce ta shigo ta karbe shi, " yaro gobe ma ka qara min rowar chocolate din ka, in ba sai na ma wanda ya fi wannan ba, ko kai kadai kk son yin qibar," " to laifi na je da komai kk ci baki qibar," ya fada cikin kuka sannan ga tsoro ar the same time, ai ko cikin fushi ta zabura zata damqo shi ya kwalla qara yace " Tani dauke ni kar ta kama ni," ba Farha ba har Lamyah dake gefe tana sha'anin gaban ta sai da ta sa dariya.






Qarfe takwas da kwata a bakin mota tai masu, wani irin kyau da qamshi ke fita a jikin su, fuskar su tai wani haske mai bam sha'awa, ga shi ba tabon komai tai smooth, Farha na ganin Bala ta fara karairaya har suna hada baki da Mubarak," Bala my baby,"cike da tsokana Mubarak shima ya karye qugu yana yarfa hannu, yanda take yi, ya maqe murya shima sannan ya fada, aikk juyo wa tai zatai magana Lamyah tace," haba ke kamar baki san Mubarak ba, so yake ya bata maki rai, ko hirar ma da Balan ya gagare ki," kwafa tai ta juya tace "zamu hadu ne ai watarana," Bala ne ya qaraso cike da Fara'a ya iso, aiko tin da suka shiga ba abinda ke tashi sai surutun Farha, Bala shi ko dadi yake ji a ranshi, dan muryar abar qaunar shi ba qaramin sanyaya mai take ba, amma Mubarak da Lamyah sun juya idon su ya fi sau a qirga, a haka suka isa, Lamyah ce ta fito cikin faduwar gaba,yau kuma me za ta tarar, haka suka wuce dakin da suke shiryawa, ko ta ina ta wirga ido bata ga Handsome ba, Farha yau cewa tai ba inda zata tana wajen Bala zasui qala'in hirar da ba sui ba tin shekaran jiya, Lamyah ce tai ma Mubarak kiss a goshi ta tafi, tafe take cikin yanga, ta isa dakin da suke kwalliya, Faisal ne ya leqo, "ya kyakkyawar kin shirya ne," daga mai kai kawai tai,kamar yanda ta saba bata magana yauma haka, " ina Farha? Na manta ba ma magana zaki min ba muje kawai," ya sa ta gaba suka isa filin, tafi da ihun mutane ne ya sanyaya zuciyar ta, ji tai wani nishadi ya kama ta, dan ita abinda ke burge ta kenan, hawa tai cikin qasaita da isa, ta fara rawar ta cikin tsantsar kwarewa, da gwanancewa a kowanne stape ta dauka, ta shagaltu da rawa sosai, in da wasu maza su uku suka hada kai, ni kaina saboda qarar kida bana jin me sike fada, tafawa naga sun yi, sannan suka isa gaban ta, kudi masu yawa sosai suka watsa mata, dayan garin watsa maya kudin sai da yai dabara ya taba cinyar ta da ta fito, aiko ji yar kamar ya saka hannin shi cikin buhun flour dan laushi, ji.yai he wants more, qara miqa kudin yai ya shafo gefen qafar ta, nan da nan jikin Lamyah ko ya dau rawa tsoro ya shige ta, a hankali ta fara rage takun ta alamar ta kusa sauka kenan, ta tafi, dan gujewa wadannann mayun da ta kula sun sa mata ido yau, wandon shi har wani dagawa yake dan tsabar jaraba, lashe leben shi yake, yana mata wani irin kallo haka ma abokan shi, nan da nan kuwa ta sauka, tai hanyar tafiya wajen kwalliyar su, binta suka so yi amma suka dakata, tana isa jiki na rawa ta janyo abayar ta ta saka, Faisal ne ya iso da kason ta wanda a yanzu suna karbar wajen dubj dari da ashirin, saboda manyan yaran dake zuwa kallon rawa, nan take ta karba ta saka a jakat, wani guntun murmushi ta sakar mas, ta sa kai ta wuce shi cikin sauri, magana yake mata ma bata kula shi ba, a hanyar ta ta fita ne ta ci karo da wadannan samarin, kan ta daga kai ta ankara da su har sun zo dab da ita, shafo fuskar ta dayn yai," kaiiii yarinyar nan amma ke jinin indiawa ce ko? Ko larabawa, ko turaw? Amma dai ba bahaushiya ba, to wataqila bafullatana?" Dariya suka saka daidai lokacin da dayan su ya janye mayafin ta, gashin ta ya bayyana, ya rufe fuskar ta, kuka ta fara tana qoqarin yin magana ta roqe su ne, sai ga Ameenullah, zai zo leqen rawar ta, sannan ya kira Faisal, yana ganin haka kuwa da gudu ya isa wajen, bai tsaya bata lokaci ba wani bahagon naushi ya sakarma dayan da ya kai hannun shi jikin ta, sannan ya kama hannun ya ja gaba ya mayar baya da qarfi saida yai qara, aikk take wannan saurayu ya kwalla ihu, jin haka yasa sauran saka gudu, wurgashi gefe yai yana bins hi da wani mugun kallo, jan hannun ta yai suka bar wajen, motar shi ya wurga ta, fuskar shi kamar a kai ake tutu dan yanda ya bata ta, kwatancen da Faisal ya mai na gidan su a jiya wajen surutun shi ya ke bi,mamaki ne a ranta amma kukan da take yaqi qarewa haka suka isa gidan su, suna isa ya bude pin din bangaren ta, budewa tai ta sa kai ta fita, kan ta shige gida ta juyo da niyyar mai godiya cikin bacin rai yace," in da kin san baki kware a yawon karuwancin da kk fito ba da zaman ki kikai a gida, dan gaba ba abinda zai sa ni taimakon ki haka ta sake faruwa," da gudu ya ja motar shi ya bar wajen, cikin kidima da kalaman shi, masu qona zuciya ta shiga gida da gudu tana kuka wiwi, ga muryar shi da ta riki ta ta, kamar ta san muryar? To a ina?.....




...





*Haermeen Haermmaerh na son ku da yawa, dan haka take sanar da ku cewar ko wacce mace ta iya creating abubuwan da suka dace tayi ba sai an zaunar da ita an koya mata ba, ke sa kan ki kina zaune zaki iya cewa bari na hada kaza da kaza na saka a miya naga yau ya zai, ko na hada kaza da kaza nai gyaran jiki na ko gidana ko dakina da dainsauran su, be more creative gurls, Allah ya hore mana fasaha da fahimta, Me Love u XX❤*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAN RAWA 💅🏼




BY HAERMEEBRAERH



Page 15:






Haka Lamyah ta kwana cikin tsananin baqin cikin kalaman wannan bawan Allah, da ko sunan shi bata sani ba, ga kuma baqar magana daya gasa mata, ga muryar shi da tai mata kama da ta san ta, to a ina? " kaiii this is so complicating," " meye yake complicating din sis na? Is it the fact that you run back home with out letting us know, or is the fact that i have come to understand cewar Handsome ne ya dawo da ke?" "Gurl pls kui hakuri, wani abu ne mummuna yaso samuna amma Allah ya kare wannan dan rainin ya taimakan," ta fada tare sa gyara kwanciyar ta, ," hmmmm kin san tashin hankalin da kk saka ni? I was so worried, ji nai kamar na sa hannu aka naita ihu, inna rasa ki a rayuwata ban san ya zan ba, na rasa kowa nawa, ina zan saka kaina," Farha ta qarasa tana kuka sosai, " kar ki damu my sis, kinji, qafata qafar ki duk inda zani, yanzu ma si nake ran asabar dinnan mu je dangin Ammiii mu ga ni ko za mu dace su karbi abinda ta haifa, wataqila sun sauqaqa min fayyace wa Mubarak mu su waye, in kin amince ko ina zani ke mai iya zuwa ce in dai ba Bala ne zai hana ki ba sai kui zaman ku anan,ke ko auren ki kina iya wa ki zaman ki nan," rungume ta farha ta yi tana mai zubda kwalla, dan yau surutun ta ya qare, ta samu sister from another mother, tabbas ta yard akwai masu kafa zumunci ba tare da sanayyar komai ba.


Yau farha da asuba bayan sin kammala komai da suka saba, karatu, addu'a, azkar, bata koma bacci ba, wanka tai wa Mubarak, ta hada kayan su,Farha ta so bin ta, amma tace su je ita ta zauna ta kula da gida, bayan nan ma ya kamata ta ci gaba da zuwa rawa, dan so take in auren ta ya tashi, tai ma kan ta komai, zataji dadin hakan,sosai, suna kuka kamar wadan da aka ce ba zasu sake haduwa ba suka rabu, Bala na ta aikin ban hakuri, ya rasa wa zai lallasa cikin su, a haka ya ja mota suka dau hanyar Rimin Gata, suna isa, suka nemi a nuna masu gidan mai gari, nan ko aka kaisu, bayan 'yan gaishe gaishe da kuma tambayar su waye? Lamyah zama tai ta labarta masu komai da ta sani game da mahaifan nata, hawaye taga mai garin na sharewa, duk ya yamushe ya takwarkwashe," oh ni Haladu, ashe ina da rabon ganin zuri'ar Malam Muhammadu ta kwarai kuma a rayuwata? Wadan can yara nashi da suka rage 'yan asara, wahalallu da uwar su ta tsaya masu sui komai da suka ga dama, ko ganin su bana son yi, ina takaicin ace wai zuri'ar Muhammadu ne su, 'yannan Allah ya miki albarka, ya raya mana ku da imani, Allah ya jiqan iyayen ki, sallama akai tare da jinkirtawa, sai da akai mai izinin shiga sannan ya shiga, " Barka da rana Abba, ya kufan jikin?" " barka dai Musaddiq, jiki da sauqi alhamdu lilLAAHi, daga ina haka da uwar ranar nan, ko an kammala bautawa qasar ne yasaka dawowa?"

Please Login or Register in order to submit comment