Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Eh Abba, nayi ta gwada layin ku jiyan na sanar da ku dawowa ta, sai inna kira yaqi shiga, nace kawai kun ganni," ya qarasa cike da fara'a addu'o'in alkairi mahaifin nashi yai ta mishi, shi kuma yana amsawa, gabatar masa da Lamyah mai gari yai sannan ya mai bayanin ta, dan yana da masaniya akan labarn Ameenee, da El-mustapha, daga kai sukai a tare dan su kalli juna su gaisa, Lamyah a kunyace ta gaida shi, shi kuma kasa amsawa yai saboda ganin tsabar kyau a tattare da ita, sai da mahaifin shi ya maimaita mai me ta ce sannan ya amsa baki sake kamar wawa, umarni mai gari ya mai akan yai leading din su ciki,Bala kuma zai koma a ranar, tare da mata alqawarin dawowa,shi da farha taga wajen, sallama sukai, Mubarak nata kuka, akan zai bi Bala, da kyar aka lallashe shi , Musaddiq ne ya dauke shi yana mai wasa, suka shiga ciki, shigar su ke da wuya, ya nufi dakin uwargida wato mahaifiyar shi da ita, qawa ce a wajen Delu, duk da halayyar su ba ta gama zama daya ba, amma kusan daya suke ta bangaren kishi, banda kishi bata da matsalar komai, bayan gaishe2 da gabatar da su Lamyah ne ya aje Mubarak yai dakin shi, yana shiga ya dafe qirjin shi, at d same time kuma ya daka tsalle ya fada katifar shi, " nayi mata nikam, ya Allah in wannan baiwa taka rabona ce Allah ka bani ita, innba rabona bace Allah ka musanyan da mafi alkairi," lumshe kyawawan idon shi yai, yana tinanin kyakkyawar fuskar ta, murmushi yai, yace " Lamyah" .





Lamyah bata samu matsala ba a kwana hudun da tai a gidan mai gari, sai dai abu biyu kr damun ta, har yanzu ba'a hada ta da dangin mahaifiyar ta ta ba, balle kakar ta, sannan wannan dan mai garin fa na takura mata, da nacin kallo da magana, yauma zaune take tana shan Tea, ita da Mubarak, ya shigo, " A'a qanwata, me kk ci haka, ba gayya , miqa hannu yai ya karbi cup din hannun ta, ya daidaici inda ta saka baki, ya sha, tare da lumahe ido, a ranshi yana ayyana wataran fa bakin ta zan ji a nawa, da sauri ya bude idon shi, dan gudun. Kar ai abin kunya, sai yaji ma kamar ta gane me yace, kauda kai yaga tayi, cike da kunya tace, " Yah Musaddiq, ragowa ta fa ka shanye, kuma ni ai ban qoshi ba," ta qarashe cikin shagwaba, daidai nan Inno ta shigo ta same su, wani kallo tai wa Lamyah ta kauda kai, ta shige daki, kwalawa musaddiq kira tai, ya miqe yana cewa Lamya ta bashi 2mnts, kada kai tai tana mamakin yanda yake rawar qafa akan ta, " kaii me nake gani a can, wanan yarinyar mai kama da 'yar tsana tana yi maka," hade fuska yai sosai, dan yasan in yai lakwa2 wannan karon ma ba yarda za tai da zabin shi ba, a kullum tana mata biyayya amma bata gani, sai tai ta manna mai jikar qawar ta, Delu, Saddiqa, har wani kirari suke mata na Saddiqa amanar Musaddiq, ita kuma tai ta yanga tana rawar kai, 'yace a wajen Hamza, wanda ba abinda ya sani sai lalata yaran mutane, qanana, shi dayan tsabar shaye2 bama a san in da yake ba yanzu, kwata2 Saddiqa bata ji, bin mazan unguwar su kuwa kamar karya, ciki ta zubda shi yafi a qirga, ga ta ba arabi ba boko, in musaddiq na wannan complain din, Inno na ce mai nima ban arabin ba ban bikon ba kuma na haife ka, ya kanyi mata kuka akan ta barshi da zabin yammatan da yake kawowa na mutunci amma sam haka zata qeqasa qasa taqi, ga shi mai garin ma shi kanshi shakkarta yake ji, " da kai nake magana ka hade gira, ko kaima kanzama dan zamanin ne?" " ni dai a gaskiya wannan karon Inno dole a barni na zabi abinda nake so, dan wannan ma ba kamar sauran bace, inna hakura a bayan wannan karon ba zai yu ba," ya miqe cike da fushi ya bar dakin, kama baki tai, amma shakkar dakatar da yaron ta shige ta, dan ta san shi yaro ne mai biyayya, amma yau akan mave gashi yana neman juya mata baya, a haka ta ji ta tsani Lamyah, tsana mai tsanani. Yau ne da yamma Mai gari ya sa aka kira mai delu da Hamza, dan su shaida dawowar Yar uwar su dan sauran qannen mahaifin ta wasu sun riga mu gidan gaskiya,masu taurin kan ne ke da rai, take suka ce ai su sun ma manta da waye Muhammadu bare zuri'ar shi, Malam Abubakar ne ya zo shima idon shi yai ja alamar yai kuka sosai, kukan tinawa da Aminin shi, sun halarta a wajen, in da mai gari ya masu bayani, Musaddiq na gefe, amma hankalin shi na kan Lamyah, wannan ne yasa daga Hamza har Delu sukaji ko suna da niyyar karbar ta sun fasa, dan da ganin wannan kallon na so ne, yanda Musaddiq yaqi diyar su da can, yanzu tsanar ta zai, duk ko da kyaun da Allah ya mata itan ma, haka su ma suka nuna to dangij uban ta na haqiqa sun qi karbar jikar su balle ita, meye hadin su, dan ta kuma ba yanda zai ya dau wannan balagaggiyar ta kai gidan shi, kuka kam Lamyah tin da aka ce Bappanayen mahaifiyar ta sun qita ta fara shi, Malam Abubakar kam yai kukan rashin aminin shi, sannan yai masu barka da zuwa sosai, ya karbe su hannu bibbiyu, haka aka tashi taro Lamyah bata da madafar dangin uba.





*Niger*







" Haba Ameenullah, kaifa na kasa gane alqiblar ka, kwanaki har ka amince zaka auri yarinyar nan amma yanzu sam kace a'a akan me, to bari kaji, ka sauya tinani,san ba zamu zama qananan mutane ba, Lamyah ko ko yau ta bayyana na maka al'qawarin aura maka ita, amma wannan yarinyar nan da wata biyu kamar yanda mukai alqawari za a aura maka ita, Naufaliyya ya rinyar kirki ce, kusan ni dai ban taba jin ance ga matsalar ta ba, dan haka kai hakuri ai wannan al'amarin," tinda Baaba ya fara magana bai ce komai ba, haka Momma ta dora da nata,itama bai tanka ba, ba abinda yake hangowa face kukan Lamyah dake taba ran shi,kalaman da ya mata yasan basui daidai ba koda karuwa ce, balle Faisal ya gaya mai ko wanne daga halayen ta, amma tsananin kishin da yake halittar shi ne ya hana ya kasa daina hango ta tana tiqar rawa a gaban qatti, wani ma yasan in ya je gida da tinanin ta yake bacci, yana tina hakan yaisaurin daga kai cikin tsananin kishi yace," Baaba ni ku auran koma wace, amma dan Allah ku nemo man Lamyah itace cikon rayuwa ta," ya qarasa cikin hawaye, dan ko so da kishin waccen YAR RAWAN zai kashe shi ba zai aure ta ba, ba zai taba zama inuwa daya da ita ba..........






*Readers i am so sorry for the late update, those that ar worried about not seeing my post here i comeπŸ’ƒπŸ» thank u so so so very much for the love, i have been busy this past 2 days, but inshaa Allah, i will try as much as i can to update it for u, thank u so much again. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON KU XX❀*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ ' YAR RAWA πŸ’…πŸΌ







BY HAERMEEBRAERH










page 17:





Jitai an ja ta baya, dubawa tai taga Musaddiq ne, saka yatsan shi yai a kan lips din ta, idon shi taf hawaye, " da gaske kk baki so na? Son yaya da qanwa kk min? Kin amince na auri Saddiqa? Ko da bana son ta? Ki duba wannan lamarin fa ki gani ba a min adalci ba kwata2, in aka hada ni da wannan yarinyar sauran mazan qauyennan, ni na san nayi 'yan mata kala2, kuma soyayyar da ake gudanar wa ta zamanin nan na taba a baya, amma daga baya da ilimi ya shigeni na tuba, dan Allah ki yarda na aure ki," " Yah Musaddiq ba macen da zata ce bakai mata ba, amma ni matsalar da aka samu zuciyata cike take da rudani, ka tausaya min nima kar ka qaran akan na da, ka barni na koma inda ake mutunta ni, kaima ka fada ka taba soyayyar zamani amma ka tuba, to itama in ka aure ta da ilimin da kk da shi zaka ribace ta ka daidaita mata rayuwar ta, ka taimaka min ka ceci 'yar uwata, ka tina ita daya nake da ita a dangin mahaifiya ta da nake saka ran zan iya hada kai da ita, in ta shiryu, mu na sada zumunci a tsakanin mu, wannan jihadi zakai, tinda in kyau ne itama ba a baya take ba, kusan da kadan zan fita, halaye ne kawai bata da su masu kyau kai kuma zaka iya taimaka mata, plssss for me?" Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, idon shi ya kada yai jawur, ga qirjin shi dake dagawa saboda tashin hankali, ji sukai an saka ihu, da gudu suka fita, Farha suka gani ta shaqe Inno, tana dima mata duka, " an gaya maki jaka ce ita da zaki mata abinda kk ga dama, meye hadin ki da ita da kk da 'yancin ci mata mutunci haka, tinda nake da ita nasha ganin kukan ta ban taba jin irin na dazu ba, jakar ki ce da zaki sata a wancan madafin baqiqqirin, sai ko yau kin shiga na rufe ki in yaso iya azabar da kk ji wataqila kin gane Lamyah tana jin fiye da haka, tinda ko risho bata taba kunnawa ba," kakari kawai Inno take, da kyar ta furta," 'Yannan daga ina kk diro kamar aljana kk dukana, in mutan boye ne kui min rai ba zan qara ba, dama da ganin yarinyar nan jinsun su ce, na dade da zargin hakan, dan kyaun ta ya fi gaban namu mutane, ku taimaka kui min rai," Musaddiq ne ya isa da gudu ya kwaci Inno da kyar, dariya a cikin shi dan jin kalaman ta kamar ta kashe shi,amma yasan bai isa yin su ba,Lamyah kuwa wajen Farha tai dake ta masifa tana yarfa hannaye, fadawa jikin ta Lamyah tai, tana kuka, ran Farha qara baci yai ta banbare ta kuma yunqurawa kan Inno da sauri Lamyah ta riqe ta tana girgiza mata kai, " Farha ya isa mana, Main tek hain, mu je gida, ku dauke ni a nan garin, kui nesa dani, bana son qara dawowa in da ba su qaunata, ina son zuwa neman Yah Amee, in na samu Yah Amee rayuwata zatai dadi, komai na zai daidaita, Bala ku zo mu tafi pls," kamo hannun Mubarak tai dake taya ta kuka, fita zasui Farha tai dan zburar nan a gaban Inno, tako kurma ihu tana a ceceta, Farha ta dan sa yatsan ta babba ta shafe hanci da shi, tana wani baubbudawa, gaba daya Inno ta tsorata da lamarin wannan yarinya, wajen mai gari Lamyah ta so zuwa ta mai sallama, amma sam Farha tace ba za a ba, da dake mata iskanci ba yazama mijin tace ba bai hana ba me zasu je mai? Da kyar Lamyah ta shawo kan ta sukai mai sallama, ya basu hakuri sosai, Malam Abubakar ma sin yi sallama, a take a gaban Lamyah Misaddiq yace a sanar da su Delu ya amince zai auri Saddiqa, nannda wata daya, kowa yai murna amma ban da shi, zuciyar shi kamar garwashin wuta haka yake jin ta, haka suka tafi bayan musayar lambar waya, duk da Lamyah taci alwashin ba zata qara sati a Nijeria ba Nijer ta nufa.




Bayan sun koma gida ne Lamyah ta qara basu labarin komai, da yanda 'yan uwan mahaifiyar ta suka ma qi saurarar ta, da yanda Delu ta qi amsar ta, da mutuntawar Musaddiq a wajen ta, sai yanda Inno ta wahal da ita bayan ta gano yanda Musaddiq din ke son ta, aiko kamar an sawa Farha barkono a duwais haka ta miqe tana" ni da baku raba mu ba na lallasa ta itama na danna ta a dakin girkin na rufe qofar taji ya abun yake, muguwa kawai, wayace dan ta ya nace maki," Lamyah ce ta kama ta ta zaunar da ita ta dora kanta a cinyar ta tai luf kawai, shafa kanta tai tayi ita kuma da sigar tausayawa, " Ya wajen rawar ki, kin ci gaba da zuwa kuwa?" " Eh ina zuwa, har Faisal ya sanar dani, Handsome yai aure a cannqasar su, nan da sati biyu zai dawo, mahaifin shi ne a nan yanzu," wani irin faduwar gaba ne ya kama Lamyah, yayi aure? To meye nata a ciki? Kaiii amma zafin da zuciyar ta ke mata in bata matse kwalla ba ba zata ji dadin zuciyar ta ba, ta shi tai tana masa fatan alkairi tai bandaki da sauri ta danna murfin qofar, kuka ne ya kwace mata mai cin rai, a ranta tana ayyana gwanda tai wannan kukan koma na meye, ko zuciyar ta ta huta, yi take tana sakewa, saida taji ranta yai fes ta wanke fuska ta fita, kwalli ta shafa ta bi lafiyar gadon ta kwanta.



" zaki je ne? In zaki ga kaya na sayo mana, ki sa naki, dan na fada wa Faisal kin dawo," miqewa tai ta fara saja kayan, dan gwara taje ta cashe ko ranta ya mata dadi, bayan sun kammala ne, Bala ya debe su, suka fice, yau shigar larabawa sukai wa Mubarak, kamar yanda suka saka Abaya suma, bayan sun isa sun faka motar su ne, suka wuce kamar yanda suja saba, barka da dawowa Faisal ya mata, yai leading din su wajen rawar as usual, rawa take cike da kasala, amma yanayin ta ba qaramin burgewa yake ba, tana cikin yi ne nishadi na shigar ta, nan da nan yanayin rawar ta na sauyawa, ihu ake kamar zasu tsaga wajen,
" Malam Sale dakkon jaka ta a mota ina jiran ka anan, na mance ta" ya kashe wayar, Mubarak ne da Farha ke guje2 kamar yanda suka saba, karo Mubarak yai da shi, aiko ya qanqame shi," pls ka taimake ni, wannan qashi da ran zata daken," dariya sosai ya ba bawan Allahn, aiko daha shi yai sama dan ya mai magana, me zai gani.......








😱😱😱😱😱😱😱πŸ˜ͺπŸ˜ͺπŸ˜ͺπŸ˜ͺπŸ˜ͺπŸ˜ͺπŸ˜ͺπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAR RAWA πŸ’…πŸΌ








BY HAERMEEBRAERH






Page 16:







An daura auren Ameenullah da Naufaliyya, yau ne tarewar su, a fuska da yanayin ta kowa zai budi baki abun alkairin ta yake fada, yarinya ce nutsattsiya. Ango da amarya na hango sun yi sallah ya mata addu'a kamar yanda sunna ta koyar da mu, sai nonnoqewa take, Ameenullah ne ya miqe ya je yai wanka a dakin da yake nashi, ya gyara jikin shi, futar shi ma amarya ta miqe ta dakko wasu turaruka ta saka amma ni dai ban hango ta tai wanka ba balle brush, haka ta saka kayan bacci ta miqe a gado, Ameenullah ne ya shigo dakin cikin sallama, tana ji ta qudundune tana wani noqe kai, bayan ya qarasa shigowa ne ya dage abun rufa ya shige, wasanni ya fara da ita, amarya ta fara miqa , tana gantsare jiki, tin tana jurewa taga inaaa, wannan kunyar bazata iya jure ta ba, Ameenullah ya hadu, shi kuma ta nashi bangaren wasanni yake da ita, amma zuciyar shi da idanun shi tare da ruhin shi 'YAR RAWA Lailah ce a idon shi, cikin tinanin da yake qoqarin kawarwa, ya fara addu'ar saduwa da iyali, yana shiga yaji sabanin abinda yake son tarar wa, amma wasannin da take mai, da kuma asirin da sukai mai ita da mahaifiyar ta na daya sadu da ita ba zai taba daga maganar budurcin ta ba, shine ya shige shi, qasan zuciyar shi yana jin zafin samun iyalin shi ba a matsayij budurwa ba, amma ya furta ko ya nesanta da ita ya kasa, sai ma ji yake sha'awar shi na qara rising, yi sukai tayi har wajen 4am na asuba, sannan ya miqe ya je wanka, zuciyar shi cunkushe da abubuwa, kwata2 ba farin ciki ko walwala, a tattare da shi, wanda ya kamata ya samu farin cikin ne a matsayin shi na ango biyo shi wankan tai, ba kaya a jikin ta, tana wani yanga, a wajen wankan ma sai da ta shagaltar da shi, kiran sallah yaji za a shiga masjid yana manne a HQ bai ma gama kusantar ta ba balle yai maganar wanka ko sallah, da hanzari ya zare jikin shi ya gaggauta wanka ya fita haushi duk ya kama ta, qunquni tai tayi kafin ta fito, madadin ta qarasa wankan tinda ta jiqe ta koma tai sallah in yaso tai baccin inaaa, gado ta koma a hakan, ta kwanta tana jiran ya dawo su dora daga inda suka tsaya,.ba shi ya dawo ba sai wajen 7am, dan saida ya kammala duk wata ibada da ya san yana yi da asuba, aiko ranta ya kai qololuwa wajen baci, ko da ya dawo yana mata maganar tai sallah? Banza tai da shi, ta juya ta kwanta, matsawa kusa da ita yai yana shafa bayan ta zuwa qugun ta, bakin shi akan wuyan ta, nan da nan ta juyo, ta hade bakin su, kamar mai jin tsananin yunwa, Ameenullah tsananin mamakin yarinyar da ake cewa saliha yake, zaro ido yai, yana qarewa bayan ta da take turawa baya sosai ido yai, " Anya yarinyar nan ba a hadani da wahala ba? Kar ta tsotsen jini a kwanakin da zan kan na koma Nijeria," shafashi kawai yaji tana yi ko ta ina, tin ba ya da sha'awa har sai da ya tsinci kan shi da son abun shima, da kyar ya samu ta kyale shi, sukai bacci. Ba su suka tashi ba sai wajen 1pm suna tashi yaje dakin shi yai wanka, yai brush, ya canja kaya ya tafi masjid, a sannan ne hakimar ta miqe taje tai wanka, tai brush, a saja kaya masu matuqar kyau da nuna tsiraicin ta, komai nata qarami ne, hatta gashin ta guntu ne, saidai fara ce kuma bata layin munana, sannan bata layin kyawawa, sadda sadda inji fulaniπŸ˜€, ba zancen sallah ita a tattare da ita, kitchen ta je ta dudduba abubuwan ciki, kwai kawai ta soya masu ta hada Tea, sai bread data sa masu a gaba, nan ko ta hau ci dan maida energyπŸ˜€ tana kammalawa ta muqe a wajen, bacci ne ya dauke ta, Ameenullah na shigowa yaga yanda ta ke bacci dariya ce ta kama shi, " Yarinya qarama sai jaraba, ga shinan daga cin abinci ta bige da bacci, habaa, ayi mutum bai san komai ba sai dai aita abu daya kamar cin kwan makauniya?" Shima jan plate din mai kwai yai ya ci ya hada Tea ya sha ya miqe ya dauke ta ya maida ta daki, shina ya kwanta, baccin su suka koma sosai, a ranshi yace" gwanda nai baccin nima kan ta farka, dan na kula wannan komawata Nijeria shine zai cecen, kan na koma ta zuqe ni," baccin su suka sha sadidan, a haka sai da sukai sati biyu masu kyau, suna shan amarci, gaba daya halayen ta ba wanda basu fitowa Ameenullah ba ya gan su,na farko bata sallah, sannaj ga ta da son xxx, ga rashin iya magana, gata da qazanta, rashi iya girki, kwalliya kam tana gaba, yanga ma haka, kwarkwasa da fari ba a barta baya ba, amma qazantar ta da rashin sallan ta yafi komai damun shi, dan abinci dama ya saba a gida ma Momma Aisha ba ta qaunar girki, masu aiki ke masu, to ita wannan tsabar kishi ta hana a dakko mai aiki, a wannan satikan mahaifiyar ta, ta zo kusan sau biyu, ba komai take kawo mata ba illa magungunan mata, sai na mallaka, su basa asiri akan komai ma miji sai dai su malleke shi ya zama nasu su kadai, a haka suke wanda shi cikin ran shi, sam baya son Naufaliyyah, Lamyah yake so, amma a qasan zuciyar shi, ya fi son kasancewa da 'YAR RAWA Lailah, dan ko kalmar so din ya furta ba wanda yake gani sai Lailah 'YAR RAWA, ko sha'awar shi ce ta motsa ita kawai yake son yai maganin komai da ita, ya rasa yanda zai ya cire yarinyar a zuciyar shi.








*NIGERIA*



" Ai sai ki fito waje ki kama min ayyuka ko? Dan banga amfanin zaman ki a daki ba, bayan dangin naki karankaf sunqi qiba," Lamyah ce ta fito tana share hawaye, fuskar ta tai jawurr kamar ta shafa wani abu, takalmin ta ta zira, ta isa gaban Innoo, " Gani inno me zan yi yanzu?" " au tambaya ta ma kk me zaki? To tashi na kai ki madafin ki ga me zaki," kitchen din gargajiya ta kai Lamyah, aiko suna shiga ta fito da gudu tana.nemk iska, hade da tari, " Laaaaa ji iskanci, kuga mun yarinya zata mun tijara, hayaqin ne baki taba shiga ba ko meye sabo wajen ki? Kun wuce kinje jun tuqe tuwon nan tas ko sai na yanke maki shegen gashin nan da kk taqama da shi?" Shiga ta qara yi tana kuka mai cin rai, data san haka ne da bata zo ba, gashi nan da Bala ya dawo ta umarce shi sai nan da wata daya, , gashi gaba daya kwanan ta takwas, kuka ta sake fashewa da shi, na tausayin kan ta, " Abiii, Ammiii da kuna nan da rai da ban shiga wannan wahalar ba, da ban soma ganin kalar wannan wajen ba ma, amma ya Allah ka shaida zan yi wannan wahalhalun da suka kunno mij ne domin ka, Allah ka bani qarfin iko ka sauqaqa min komai," " Qunquni kk min haka dan na saki aiki, shigowar Musaddiq kenan, aiko tana juyawa da niyyar dakko ruwa ta watsa mata ta gan shi sai ta wayance da goge fuska tare da sharce majina, ita a dole Lamyah ta sata kuka, qarasawa yai ya janyo hannnun Lamyah data fara tuqa tuwon, ya fiddo ta waje, " daga yau sai yau, na sake ganin kina irin wannan aikin sai na mugun saba maki , kinji ko baki ji ba?" Ya daka wata gigitacciyar tsawar da ta saka Inno dafe gini, dan tabbas Lamyah yake kallo yake magana, amma ta wani bangaren kuma ya tauna tsakuwa ne dab aya taji tsoro, Lamyah kuwa dan tsoro durqushewa tai a wajen tana kuka, kuka take sosai cike da tsoro shi, a hankali ya dago ta ya sa ta gaba zasu tafi , cike da kishi sai kace wani mijin ta, " Malam ai sai ka sake mata hannun ko? Tin da naga ba sarki ko limamin daya daura maku aure ko?" A sannan ne ya kula da yanda ya riqe Lamyah da ta gama tsorata, da firgita da shi, sannan ga tsoron shigar ta kitchen din nasu da bai sake ta ba, yaga tabbas in ya sake ta tana ma iya faduwa, shiru yai ya kyale Inno tana sababi, daf zasu shiga dakin ta ne taji Inno nacewa," kaqi sake mata hannun ko? To sai dai ka canja masu wajen kwana ita da qanij nata, amma ba dakina ba, munafukai, anya Musaddiq wannan aljanar yarinyar bata rude ka ba ka salwantar da kan ka a wajen ta?" Wannan furici ba Musaddiq ba har sauran kishiyoyin ta sai da ya daka, amma an tsoron iya inji 'ya'yan mayya, ba wanda yai magana sai ma shigewa dakunan su da sukai, Lamyah ce ta kwace jikin ta ta fada dakin da gudu, ta dakko wayar ta ta kira Bala, tana kuka ta kasa magana, hankalin

Please Login or Register in order to submit comment