Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni kan na fito aike ya iskeni daga mai gari gaba dayan mu da yan uwana mu je fada akwai mahimmin abu daya taso, dan haka ina ganin ku da baku sani ba yanzu na isar muku, sai mu qoqarta mui hanzari mu kammala na nan mu je can muji me ya taso haka na gaggawa?" Gara zama tai ta ce " ba komai ne yasa na kira ku ba Lado face maganar auren yaeinyar nan da mai gari keson yi, ni fa ba na son marainiyar Allah ta bar gabana, ta bar garinnan kwata2,..... sai ta fara kukan munafurci harda fyace majina.... in ta tafi Lado ban san halin da take ciki ba akwai damuwa da zata sarqen, ina tsoron nima na rasa raina saboda rashin Malam da diyar shi, sannan mutumin nan da gani ba dan Nigeria bane, wa yasan sana'ar shi, kuma malam bai da rai bare ace ya tabbatar zai bada ita a yanzu, babban kuma wani abun dubawar yarinyar nan bata son shi, tana ganin shi ma kuka ta saka" tsagaitawa tai tana kuka sosai kamar na gaske, tausayin ta ne ya kama wasu daga cikin su, wasu kuma suna ganin anya??? Lado shi anashi bangaren ba ruwan shi da koma me zai sami yarinyar tinda Delu bata son auren to fa ba wanda ya isa daura shi, " kiran mai gari na da nasaba da zuwan yaron ya kamata ku hanzarta kar mai afkuwa ta afku, ku tai maken da yar ku da dan uwan ku" kuka ta qara sakawa mai cin rai ita a dole kar a cutar da marainiya, miqewa suka suka kama hanyar gidan mai gari suna tattauna yanda zasu bullowa lamarin.



A fada waje ya cika ba laifi dan sanar da jama'a me za ai da me gari ya saka a yi, suna isa mai gari ya shigar da su wani daki, harda Aminin Malam wato Malam Abubakar, sai kuma su El-mustapha da Mus'ab abokin shi, zama sukai mai gari yai addu'a suka shafa sannan yace" Malam Lado na sa an kira ku ne da yan uwan ka akan batun auren Ameeaatou, meye ra'ayin ku akan wasiyyar dan uwan ku na a a aura ma wannan bawan Allah ita ko bayan ran shi?" " Ranka ya dade ni na ke bin tsohon wannan yarinya, nasan abinda yake so da wanda baya so, dan haka gaba daya wancan karon wannan bawan Allah tilasta mai yai akan ya aura mai ita,ba dan ya so ba ya amince, kan ya mutu ni da shi munyi wannan maganar," cikin kidima El-mustapha ya ja baya yana zare ido da dafe qirji kamar wata budurwar da ta shiga damuwa, yace" Malam Ka ji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da Allah zai tsaidaka ka maimaita abinda kace, kaji kunyar ranar da zaka maimaita wannan qaryar gaban dan uwan ka, wannan abun da ka fada bai faru ba, ba a taba yin shi ba, yarinya bata taba cewa tana sona ba ni na ce ina son ta,amma da dikkan alamu itama tana sona, ni ban taba furta mata kalmar so ba, na kula qarama ce tai qanqanta da hakan, dalilina na zuwa nansamu mahaifinta kenan, dan hakan shine mafi dacewa, uba na da damar zabawa yarinyar shi mai auren fari miji, musamman wannan da bata san komai ba" sunkuyar da kan shi yai yana hawaye,badan komai ba ganin yau ba Malam Muhammad ana neman shiga tsakanin shi da abar son shi , baida kowa a duniya, ita yake saka ran ta zama mai komai, ta maye mai gurbin rashin iyaye da yan uwan kirki da yai, amma gashi komai na neman zama mai ba daidai ba, kafadar shi yaji an dafa da sigar lallashi, " ka kwakntar da hankalin ka, wannan aure kamar anyi an gama ne, ba wanda ya isa ya daga shi, domin kuwa ni ne aminin mahaifin ta.ni da shi ya tabbatar min ya baka ko bayan ranshi ka dawo ai wannan aure naku ga mai gari shaida n3 shima"mai gari ne ya qara tabbatar ma shi hakan shima,nan take kwanciyar hankalin shi ta bayyana " ammmm bayin Allah ban katse maku hanzari ba, amma in dai za ai auren nan ba yawun mu, ko shekara dari zamu sake.a duniya in dai akai auren nan ba mu ba Ameenaa ba zuri'ar ta, tinda mu yan uwan mahaifin ta an mai damu bamu da amfani," inji na Duduwalle kenan daya daga Bappanin ta, me gari ko sauraran su bai sake yi ba ya baza babbar rigar shi ua fito suma si malam Abubakar suka bi shi, nan take aka daura auren su, akan sadaki dubu 20k, cikin farin ciki, Malam Abubakar ne ya wakilce ta shi kuma Mus'ab shine ya wakilce shi, haka akai auren cikin saka albarkar mutane da yawa,kamar sun san za ai auren dama can yanda aka taru a wajen, fakam fakam fakam suka zo suka wuce suna huci, bayan an dunqula masu goro da alawa a ledoji, ba kunya suka amshe sukai gidan Delu, suna zuwa daga yanayin su ta gane an gama komai, hannu ta dora aka ta rusa kuka, " shikenan sun cuce ni sun cuci marainiyar Allah, in dai ina nunfashi yarin yar nan ba za ta bar gidannan ba, sun ganta marainiya za su cutar da ita?" Daidai nan su Malam Abubakar suka iso, " zamu cutar da ita ko kk cutar da ita kuma kk shirin qara cutar ta? Dwlu duk makircin ku akan idona kk aikata shi, tin fil azal, ki kiyayeni dan wannan karon ba auren aminina akan ki ba zan dau iskancin ki ba," " Malam Abu ka duba fa ka gani auren dole kuke son yi wa marainiya ko nace kukao ma marainiya"ta fashe da kukan baqin cikin halin hutun da ya zo wa Ameenee, ki ra Malam din yai ta banka mata, nan da nan ta iso da hanzari ta duqa kan ta a qasa, ta gaida su ta dada takurewa gefe, dan a yanzu duk ta fuskanci inda zantukan su suka saka gaba, " Ameenaatou, kina son wannan bawan Allah ko baki son shi, ki fadan gaskiya kamar yanda zaki fafa ma marigayi, ni ubane a wajen ki , ko da wadannan ubannin naki sun juya maki baya ni ina nan tare da ke har qarshen nunfashina" hawaye take sosai, na fahimtar kenan su Bappanin ta sun qi ta ne, gefen da gogan nata yake ta kalla qasa qasa, cikin sa'a idon su ya hadu, wani marairaice mata yai akan ta amince da shi, murmushi ne ya subuce mata shima hakan, ta qara sunkui da kai tana rufe fuska, malam ne ya ce" to Alhamdu lilLAAH ina ganin wannan kadai ya baku amsa dan haka Ameenee debo kayan ki mu wuce gidana da ke da mijin ki cam zaku kwana kafin tafiyar ku jibi, domin ni ba kowa garen ba kun sani iyalina ta mutu kuma Allah bai bamu haihuwa ba, akwai wajen da zai ishe ku ku kwana kai da abokin ka da iyalin ka, mu tashi mu wuce, ke kuma Allah ya shirye ki da ku baki daya ku gane meye ma'anar zumunci" Bappa Lado ne ya karkata baki yace" Ameeeen da bamu san akan me kk wannan rawar jikin bane da sai mu zaci kai ma dan zumuncin kayi" Malam bai kula shi ba, haka suka jira ta ta debo kayan ta suka wuce gidan malam din, daki daya aka ware masu mai katifa da ledar daki, shikenan sai dan bargo da zanin gado, anan aka sauke su, Mus'ab ma dakin nashi haka ne, bayan sun isa ne, El-mustapha ya sanar da malam gobe zasu wuce, malam ya musu fatan alkairi da addu'o'i Ameenee ta sha kuka sosai, inda tin yana lallashin ta shima ya saka mata kukan,tin da shima yau ce rana abar baqin ciki a tare da shi, yayi auren fari ba kowa na shi, ga matar da yake so itama tana cikin damuwar, rungume ta yai suka sha kukan su a hakan,.

Washe gari su Ameenee an dau hanyar tafiya Niger, a hanya ta sha bacci sosai, suna isa gidan su kuwa Mus'ab ya musu sallama ya tafi gidan shi, shima, nan take ya aika da driver aka kai ma su abinci da abubuwan dai da zasu buqata a ranar, sannan ya aika wata daga cikin masu aikin shi, yar dattijuwa yace taje ta kula da Ameenee, ta kuma koya mata abubuwan da duk ya kamata ta iya, dan shi mai suna, Ameenullahi ne ke ta kuka, sai ya bi Iya gidan da zata dan sun shaqu sosai, hakuri ta bashi tace zata dawo nan da kwana biyar su tafi, Ameenullahi mai shekaru 6 a duniya ga wayo, yasan ba ta mai qarya sai ya hakura amma hawaye bai bar zuba mai ba, tafiya tai, aka kaita tana zuwa,ta isa inda Ameenee take ta kwashi gaisuwa, nan da nan Ameenee ta zube a qasa itama, ganin babbar mata da ta kusa sa'ar Innar ta tana duqawa tana gaida ta, gaisawa sukai a haka, El-mustapha da ya shigo ya gansu dariya ta kama shi, yai tayi kuwa, isa yai gabam Ameenee ya dago ta ta dan jamye kadan ganin wannan dattijuwa na wajen, sannan ya umarci Iyan da ta tashi, tashi tai ta zauna akan kujera kamar yanda ya umarta " da farko dai Iya wannan iyalina ce, sunan ta Ameenaatou, Ameenee wannan ita ce zata na zama dake musamman in bana nan, kuma kina buqayar wani abu duk zata maki, zata na taya ki ayyukan gida, ta koya maki abubuwan da baki iya ba, ina fatan ba matsala, ke kuma Iya daga yau kina dauki Ameenee kamar 'ya, sai dai kawai ba zan lamunci muzguna mata ko bata ranta ba a wajen kowa, dan wannan girman da kk bata ita ta taso gian tarbiyya ba zata so shi ba ina fatan kin gane" kada kai tai tare da godiya, ya nuna mata bangaren da zata zauna ya ja hanun iyalin shu suka tafi, a yau din komai ya wakana tsakanin shi da iyalin shi, wanda ya danganci amarci da raya sunnar ma'aiki, su Ameenee an sha fama da maza😱🙊 tayi kuka hr ta gode Allah sai da yace mat " in kina kuka Iya zata gane me mukai, ki shiru kae kowa ya ji, a maki dariya ke raguwa ce, in miji na ma matar shi haka lada suke samu, amma in wanda ba miji da mata bane zunubi suke samu, na san a karatun ki kin san hakan ai ko? Daga mai kai tai yace yauwa Habibaty, ku daina kuka, daga yau ba zan qara maki wanda zai saki kukan wahala ba kinji" daga mai kai tai, nan take suka tashi suka tsarkake jikin su kafin suka koma bacci,( ana son mutum bayan ya kusanci iyalin shi sui wanka ba a son kwana da janaba) bacci mai dadi sukai.





Washe gari ta tashi da tsamin jiki,musamman cinyoyin ta, ruwan zafi sosai mai hadin kayan qamshi na musk, da magarya,sai yar bagaruwa kadan, da kaninfari iya ta kawo mata tace ta shiga ta zauna zata daina jin ciwon jiki, nan da nan ta zaro ido😳😳😳😳ko dai iya tasan me akai jiya ne,wata kunya ce ta kama ta ta daqe bakin ta ta kama tafiya a tsaye da sauri tana son ta gudu daki, yana hango su ta parlo dariya ta gama cika mai ciki,tashi yai ya amsa yai mata godiya ya kai mata ruwan, samun ta yai bakin gado tana hawaye " Ya salam me ya same ki Ameenee na? Wa ya bata ran sahiba ta,? Ko dan iya ta baki wannan ne baki so, bata gane komai ba fa, kawai tasan kin gaji tafiyar hanya ne yasa ta miki wannan hadin, da kin shiga robar kk zauna zakiji dadi a jikin ki," kallon shi tai da idanun ta masu kyau da sukai ja, kada mata kai yai alamar da gaske bata gane komai ba, cikin ran shi kam dariya ce cike, tqna shiga ko ya fashe da dariyar, yace " ikon Allah, ashe haka auren yara yake?" .........



*Ni ko Haermeebraerh nace ya ma fi haka wallah*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼




BY HAERMEEBRAERH





Page 4:







Kwana biyu na cika kamar yanda Iya taima Ameenullah alqawari, haka taje ta roqi El-mustapha da in ba damuwa zata dakko Ameenullah, dan ta mai alqawari, nan take ya yarda, domin shima yana son yaron akwai wayo da tarbiyya, sannan kuma in an kawo shi zai debe ma Ameenee kewa da zaman kadaicin da zata shiga in tafiya ta kama shi, nan take ya saka driver da Iya suka tafi dakko shi, ba wani jinkiri mahaifiyar Aminullah Aishaa ta amince, tare da bada saqon gaisuwa mai yawa a kaiwa amarya, da kayayyakin su na Niger,😉 Aminullah ya yi murna sosai da farin ciki dan zai koma kusa da mai renon shi, yana son kulawa sosai, domin ita mahaifiyar shi akwai son yara, amma ba ta son dawainiyar su, son jiki ne da ita sosai, in tana zune bata qaunar abinda zai daga ta, in ba ita tai ra'ayi ba ko mijin ta ne wato Mus'ab sai dai yai komai da kan shi, tin yana fada har ya hakura, sai ya auna abubuwan alkhairin da take mai , yaga sun fi wannan din yawa sai ya mai da shi a matsayin ajizancin ta, haka suke rayuwar su kamar ba wata matsala.


Kafin su zo ta gyara wa Aminullah daki babba mai kalar green da white, dakin ya yi kyau sosai, ko wanne daki a gidan akwai combination din kalar shi kuma kaloline masu matuqar kyau, gidane babba mai ban sha'awa ga kowa, suna isowa, da fari ya dan mata baqunta, amma yana ganin Uncle Musty,ya ware, wasan shi ya shiga yi sosai, in da da dare, El-mustapha yace suje shooping don a siyo mai kayayyakin wasa, da kuma wasu littafan makarantar kamar yanda yake da su a gida suna debe mai kewa, itama cewa tai a sai mata littatafan, tana son koyon bokon, amma bangaren turanci, tinda da shi ake amfani duk duniya, sai mata yai cikin zuciyar shi yaji dadi, dan matar shi na son koyon ilimi, ba qaramin dadi yake ji ba, idan ya ji ta tana karatu da asubah, ko kuma in tana zaune ita kadai yaji tana bitar wasu daga ayoyin qur'ani ko kuma wasu littafan addinin. Sun sai kaya sosai in da Ameenullah yai ta murna, ga ice cream da chocolate nan kala2 an sai mai, bayan sun kammala ya biya ne suka dawo gida, kafin ya shigo yai ma driver magana akan da safe zai na kai Ameenullah makaranta, amsawa yai cike da girmama wa da son ubangidan nashi, miqa mai wata leda El-mustapha yai shima yai kwalamar kar a varshi a baya, wajen mai gadi ya nufa suka bude suka hau cin gara suma, Ameenullah yai bacci a hannun ta tini, karbar shi yai, dan gani yai kamar ya mata nauyi, dan irin yaran nan ne masu jiki bulbul barakallah,ga hasken shi mai matuqar kyau da daukan ido, in ta qura mai ido gani take anya jinin Niger ne yaronnan???



Washe gari da kanta ta shirya shi ta hada mai abun karyawa da taimakon Iya, tinda ta iya girki na zamani ne dai bata iya ba, shima ta daura damban iyawa.




A hankali kulawar Ameenullah ta dawo hannun ta, ita ta take mai komai, tare suke kwana in tafiya ta kama El-mustapha, a hankali ya maida mata sunan ta Ammii, yana kiran El-mustapha Abee, iyayen shi suna matuqar jin dadin hakan ba kadan ba, kusan a duk bayan kwana biyu uku sai sun je, zasu yini ma Aishaa sosai, sai dare su koma, yana kiran Aishaa da Momma, Mus'ab kuma Baaba, ba qaramin gata Ameenullah ke samu daga iyayen nashi hudu ba, sai ga shi a shekara daya da yai da Ameenee ya kusa yin Hizif 30, wanda tana kyautata zaton yana shekara 8 zai sauke alqur'ani, mahaifan uku sunji dadin hakan, kuma sun jinjina ma Ameenee.


A kwana a tashi, yau shekarar Ameenullah uku a hannun su, Ameenee na hango kwance jikin mijin ta,Ameenullah na wajen qafar ta yana matsa mata, yana ta zubo haddar shi, Abee din shi na ta saurara yana lumshe ido, Ameenee na cin yalon da ta sa aka nemo da kyar, sakamakon tulelen cikin dake gaban ta, haihuwa ko wanne lokaci zata iya sallama, tana daga kwance ta miqe da sauri kamar an mintsineta, har tana buge Ameenullah, duk da bakin shi daya dan fashe bai damu ba, hankalin shi ya tashi ganin yanayin da Ammin shi ta shiga lokaci kadan, abu kamar wasa, sai ga Ammin shi na kuka, dan wata irin shagwaba take bugawa El-mustapha, riqe mai wuya tai ta qanqame shi, fuskar ta a girjin shi tana murza kanta dan azaba, " Haerbeebee je ka kirawo Iya da sauri," yana kuka ya fita tare da waigen ta, haka yaje ya kira Iyan, da hanzarin su suka shigo inda ta umarci El-mustapha da fuskar shi ta jiqe da gumi da hawaye da ya kai ta dakin da suka tanadi komai na haihuwa, zuwa yai ya aje ta agaban kujera ta durqusa tadan buda qafa kadan, Ameenullah ya je ya ba hakuri " Haerbeebee ka zauna anan kaji, kai tai ma Ammin ka addu'a Allah ya sa ta haifa maka qanwa ko qani lafiya kaji, kar kai kuka, ka zama namiji, " haka ya dan bubbuga fuskar shi, " To Abii kaima ka daina kukan, inshaa Allah zata haihu lafiya," rungume shi yai, ya dan yi kukan kadan, sannan yai kissing goshim shi ya shige dakin, Iya ta saka komai a qasan ta na tarba jariri, ta dafe kujera yaje ta gefen damar ta ya tsugunna, ya riqe hannun ta daya, dayan ta dafe kujera da shi, yana shafa bayan ta da daya, addu'a kawai take, tana yi ma iyayen ta da suka rasu addu'a, ko tai da qarfi ko tai a zuci, ganin wahalar da take sha ba kadan ba yace "ko asibiti zamu kaita Iya" " karka damu da ikon Allah zata haihu lfy, ni na karbi haihuwar Ameenullah, duk jikokina ni nake karbar haihuwar su," gyada mata kai yai, zai magana kenan yaji Ameenee tayi wani nishi mai qarfi, ta damqe shi kamar zata karya, sai da yai wata 'yar qara, Iya na qara mata gwarin guiwa, akan ta ci gaba da nishin, qoqarin zama take, ta ware qafa iya ta hana, a haka take son ta haihu( in mace ta haihu ta haka ba ta da matsalar samun qari wajen haihuwa, inshaa Allah) wani kyakkyawan nishi da tai sai ga Baby ta fado, ta saka kuka, cikin farin ciki iya ta duqa ta janye yarinyar, sannan ta umarci El-mustapha daya girgiza ta mahaifa ta fado, haka yayi ko, ta nuna mai yanda zai ya kwaso jini daya kwanta mata, cikin nutsuwa da tausayawa,yai hakan, nan da nan ya daga ta ya shiga da ita toilet, ya fara wanke ta da gasa ta, tin a ciki ta fara gyangyadi, suna fitowa waje yai qal, Iya ta gyara har Baby, ta mata wanka,ga qamshi da ke tashi a wajen, bayan ya shirya tane, suka bude wa Ameenullah qofa, fuskar shi tayi jawur, ga hawaye ga dariya, ya rasa wanne zai yi, yana shiga ya fada jikin Abiin shi ya fashe da kukan murna, da sauri ya qarasa jikin Ammin shi ya kwanta a jikin ta yana mata sannu, shafa kan shi tai tana murmushi, ta daga kan shi ta kada mai nata, alamar ya bar kuka,
Iya ce ta miqa mai qanwar shi a hannu, kasa tsaida hawayen shi yai, wata irin soyayyar ta ce ta dira a zuciyar shi lokaci daya, ya qara qanqame ta, yana kissing din ta, " Ammii ina son bbyn nan, tana da kyau, Ammii Allah ya sa tai halin ki, itama ta zama bata duka ko fada" dariya suka saka sosai, " Inshaa Allah ba zata zama me fada ba Yaya Ameenullah, dan kai zaka na koya mata komai" murna ce fal cikin shi har ya zama Yaya ," Abii yau she zata fara ce min Yayan?" Cikin murya ta dariya Iya ta amsa da" In dai ba ta da yanga gobe ma sai ta fara, amma in zata maka yanga sai ta kai shekara biyu zuwa uku" kallon yarin yar dake ta bacci a hannun shi tana tsotsar yatsa yai yace," dan Allah kar ki min yanga kinji qanwata?" Dariya suke tayi dika," zo nan haerbeebee, ba zata maka yanga ba, dan ko Ammii ba zan bari ta fara kira ba Yaya zamu koya mata, kaji yaro na" dadi ne ya kama shi sosai, ya kwantar da kanshi jikin Ammin nashi.



Ameenee ta yi kukan rashin dangi, ita daya a daki, dan ba zata so ya ga ni ba, gudun shigar shi damuwa shima, tinanin ta yanzu haka zata fara tara zuri'a da qanan shekaru, sannan ba ta da kowa, sai mijin ta, murmushi tai dan tina waye mijin nata, ya kasance namiji daya tamkar da ba iyaka, tasan yana maye mata gurbin yan uwa da ta rasa, amma gaba wa zata nuna ma yaran ta a matsayin dangin ta, Ameenullah ne ya shigo, ganin ta na kuka kan ya qaraso wajen ta idon shi ya cika da hawaye, zauna wa yai a kusan rabin jikin ta, yana tambayar ta meya same ta, cikin qarasa gangarowar hawayen shi," Haerbeebee, ka kula da qanwar ka, har girman ku kaji, kar ka bar qanwar ka ta shiga halin maraici, ko da yaushe ka zama kana tare da ita, ina nufin ka maida ta rabin jikin ka, ta zama ba inda zaka iya shiga ba da ita ba, har qarshen nunfashin ku, ka min al'qawari Ameenuna, duk da na san kana da qarancin shekaru amma na san kana da kaifin hankali, da kuma riqe abu,na san ka fahimce ni, kuma ka riqe abinda nake fada maka," gyada mata kai yai yana kuka, yace" Ammii na na miki alqawari zan kula da ita, har qarshen nunfahin mu, ki daina kuka," share hawayen ta tai ta dakko mai ita ta miqa mai, dai dai nan Abii n shi ya qaraso" ashe nan ka gudo ka barni da ball a hannu, " dariya ya mai yana mai gwalo,....
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼




BY HAERMEEBRAERH




Hey guys, ina roqon duk wanda suka tambayen novel dinnan ta pc da su min hakuri sakamakon rashin tura shi ta pc da bana samun damar yi, i am truelly sorry, ku dinga adanawa a wani wajen saboda daga baya in kunji ya maku ku karanta, na gode. ME LOVE U XX❤



Page 5:





Ran suna an sama yarinya Aishaa domin yi wa matar mus'ab takwara, amma shi Ameenullah na kiran ta da Lamyah, ( macen da take baqa kuma siririya) dan gaba daya Aishaa kamar ta daban ba baqa ba kuma ba fara ba kuma bata da wani girma, abu kamar wasa suna ya bita da wuya wani yace mata Aishaa in ba Ameenee ba.

A kwana a tashi har ta kai shekara hudu sai kuma kamanannin ta suka canja, ta fara qiba da haske, kyaun ta ba qaramin ban mamaki yake ba mutane ba, hakane yasa Ameenee bata wasa da mata azkar din safe da yamma, ba qaramin son juna suke ba ita da Yah Amee din ta, haka take kiran shi, duk da baya so amma baya nuna wa sai bata kusa yake ma Ammiin shi magana, " ni Ammii bana son wani Yah Amee, yarinyar nan da akama ramawa tai, dan na bata sunan yar baqa sai ta rama, ai naga tayi haske ta tashi daga baqa yanzu" dariya Ammiin shi da Abii suke mai suce " to ai sau ka canja mata da sunan masu haske maybe ta canja maka kaima," " A'a wannan zai fi mata dadi in ta girma, kuma

Please Login or Register in order to submit comment