Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana ta fara mai," My love, ina neman alfarma a wajen ka, ina roqon ka da kome zasu ce maka ka tsaya ka nutsu ka amshi yafiyar su in sun nema, domin duk abin da suka maka nima ya shafen amma ni tin randa ta bar gidannan na ji ban ji dadin tafiyar ta ba, nai shiru ne gudun bacin ranka, amma ni gaskiya ina buqatar dawowar ta, ba dan bana jin dadin zama na da kai ba sai dan ina tinanin Momma bazata ji dadin barin diyar qawarta da kai ba, kuma kasan rashin jin dadin mahaifiyar ka akan ka ba a bune mai kyau ba a rayuwar ka duniya sa lahira, akwai matan da suke ma mazajen su abinda yafi na Naufaliyya kuma a hakura a zauna, plss my baby kai hakuri kaji," ta qarasa tana wani irin juyi a jikin shi, tare da motsa hips din ta, cikin hanzari ta qarasa riqe lips din shi , kamar jira yake, tana ji ya kama tai qoqari ta zare tana mai dariya, "je ka ka dawo zan maka wani abu" yana lumshe ido ya fita, kifewa tai a wajen tana kuka mara sauti, kishi ne danqare a cikin zuciyar ta, amma sai ta tina da Hadith din Rasulullah da yace" imanin dayan ku baya cika sai ya so ma dan uwan shi abin da ya so ma kan shi," ta haka ne kawai take ganin zata iya daidai ta su, in ba haka ba yanda Yah Amee ya dau fushi bata jin zai saurari kowa akan Naufaliyyah dan tin da ta tafi ko da batan hanya bai taba kiran sunan ta ba.


Bayan gaishe2 da sukai, idon shi ya sauka kan Naifaliyya da ta qura mai ido, tsaf ya gane irin kallon, dan guntsun tsaki yai ya kauda kai, dauke idon ta tai daya ciko da hawayen, ta cije lips din ta, " Ameenullah naji labbarin duk abinda yarinyar nan ta aikata, kuma a gaskiya na zo nan ne domin baka hakuri, domin duk abinda tai akwai sa hannuna ciki, da kuma gurbatacciyar tarbiyyar data samu daga wajena, mahaifin ta ya mana waazin da ya shiga zuqatan mu daga ni har ita, dan son Rasulullah kai hakuri, ka yafe mata, ka kira abokiyar zaman nata domin ta bata hakuri, tabbas mun cutar da ku," ta qarasa cikin tsananin nadama wadda ta kasa boyuwa a fuskar ta, jikin shi ne yai sanyi da yanayin su dika, tabbas akwai tsantsar nadama a tattare da su,miqewa yai ya shige bedroom din shi, kwance ya tadda ta, tayi kuka har ta gaji, fuskar ta tai ja,musamman hancin ta, dago ta yai yana bubbuga bayan ta, saurin miqewa tai tana yaqe, murmushi ta so yi amma tai failing,hawaye ne ya biyo baya, girgiza mata kai yai," in ina ganin hawayen ki zaki sa na koma na kore su dan ba zan taba aje abinda zai bata maki rai ba," da sauri ta share hawayen ta tace," kayi hakuri ba zan qara ba," murmushi yai ya ja ta toilete ya wanke mata fuska, ya bazo mata gashin ta ta gaba,yanda zai diga rufe fuskarta, sai dai idan ta mayar da kanta, kama hannun ta yai suka fita, tana ganin sun kusa wajen su tai qoqarin kwace hannun ta amma yaqi, a tsaye ya tsaida ta gaban Naufaliyyah," ke na fara aure kafin na ga qanwa ta farin cikina, kafin na samo alqawari na da na dade da burin samu, na aura kafin kowa, ke ce macen da ta fara kasancewa da ni a matsayin miji, kin yarda damar da kk samu da matsayin ki, in kina son zaman lfyr ku daga yanzu zuwa har abada, ki zauna lfy da ita, na san wacece Lamyah, ba ta da son hayaniya, in ba taba ta akai ba, ba ta da fada in ba janta akai ba, ke kuma na san halin ki, kowanne, dan haka ku zauna lfy da juna ku riqi Allah a zamab ku,kar kuna sani gaba a zaman ku, kuna saka Allah a zaman ku, domin in kuna saka ni a farko zaku na sabawa Allah,zakuna shiga haqqin junan ku, shi aure ibada ce, kuma ba kowa ake wa ibadar nan ba face Allah,dan haka in kuna son samun nasara duniya da lahira kuna tina Allah, ko sabani kuka samu, in da hali kuna warware shi a tsakanin ku, ta hanyar tattaunawa a junan ku, ku zama kuna ma juna uzuri, sannan kuna ba juna hakuri akan laifukan da kukaiwa juna,...." nasiha yai masu sosai da ya sa a cikin kaso % na kishin su kashi 50% ya fice, zuqatan su suka samu nutsuwa sosai da shi, hannu ya miqawa Naufaliyyah ta miqe ta isa gare shi,ya hada su ya rungume, Maman ta ce tai gyaran murya, sika sa dariya dika, cike da kunya,bayan ta masu addu'ar zaman lfy ne sai ta masu sallama ta tafi, zaunar da su yai akan doguwar kujera, " da farko dai kusan nace komai ya faru Allah ya qaddara hakan, amma tabbas akwai rashin bin dokokin Allah dake jawo komai ya tavarbarewa bawa, ya rasa dalilin faruwar abubuwa marasa dadi a rayuwar shi, a qa'ida ya kamata tin da akai auren mu da Lamyah yazama mun raba kwana atsakanin mu, amma bam hakan ba, muka ci gaba da zama na tauye haqqin ta, dan haka a yau ina son mui magana a tsakanin mu kwana nawa ya kamata muna yi?" Lamyah ce ta kalli naufaliyyah ta mata alama tai magana," da farko dai ina mai qara ba ku hakuri ku yafeni, akan soj zuciyar dana aikata maku, kuma ina ganin kwana biyu yayi, a gani na fa amma," ta fada cike da murmushi, dik sin aminta da hakan, Lamyah ce ta miqe ta fara takawa," to ango da amarya ni na shiga ciki, na barku lfy," Ameenullah ne ya sake baki, a ranshi ko gani yai wannan yarinyar ta gama da shi, tabbb, ina alqawarin da ta mai? Lallai za a yi ta, ya nuna bai yarda ba Naifaliyyah taga ba a kyauta mata ba, cikin yaqe ya juya ya hada ido da Naufaliyyah da ta gane kwata2 ranshi bai so ba, amma ya zatai itama tana buqatar shi.
Dare yayi Naufaliyyah anci kwalliya, an harde a gado Ameenullah ne ya shigo, " ya na ganki anan? Ai bina dakina zaki dan gaskiya ba zan din ga yawon bin dakuna ba ina da dakina, ai kamar jira take, har tana kusan kifewa ta miqe jiki na rawa ta kashe fitila ta ja qofa ta bishi, waiiiiiii makaranta kun san wace Naufaliyyah, ba sai na gaya maku budirin da aka sha ba ranar, dan ko abun sai su kawai, Ameenullah ya wahala🤣har mamaki yake wai ita wace irin mace ce? Komai tin anayi da dadi har a wahala? Gashi abin haushin ma in ba dan ta iya style kala2 ba sam bata kai Lamyah komai ba ta fannin ni'ima, ( makaranta kar ku manta fa ita gimbiyar kayan mata ne kala da kala, amma Lamyah ta fi amfani da natural abubuwa, bata yarda da shan kayan da bata sani ba, komai zatai da natural take yi, yanda zai gyara mata jiki, ba ya gyara ta na dan lokaci ba daga baya a bata ta ba, dan haka yana da kyau mu farka mu kiyaye binda zai amfane mu da wanda ba zai amfane mu ba).





*Bayan wata biyar*



" Masha Allah barakallah, wannan baby ba qaramib kyau yai ba, Sannu my sister, kin yi matuqar qoqari,ba mai cewa daga jikin ki wannan qaton baby ya fito ba," dariya sukai, amma banda Naufaliyyah, wadda gaba daya kallon da Farha ke watsa mata yake matuqar tsorata ta, amma tsabar hali irin na Farha ita zata juya ai dariyar da ita amma ta hana matar mutane sakewa, tin da suka zo Nigeria, Farha ta hana Naufaliyyah sakewa sam, yau dai Lamyah ta shirya yi wa Farha magana, " Sister ki bari mana, na fada maki komai yai daidai," habaaa dama jiran kadan take," eh amma da komai yai daidai ai ni ban fadi albarkacin bakina ba, baiwar Allah bari kiji, lokacinnan abinda ya hana ni zuwa na sumar dake da duk wani boka da malam tare da masu baki shawarar taba wannan gold din nawa shine wannan cikin, kwata kwata bari na fada maki gaskiya naji matuqar haushi da kk shiryu ban je na taba lafiyar jikin ki ba, amma bari kiji, alqawarin karaya da targade na kan ki a duk randa kk batawa 'yar uwata rai ina fatan kin gane," kamar wawuya Naufaliyya ta kada kai, cike da matsanancin tsoron Farha, " Gud now we can be freinds" miqa mata hannu tai sukai sallama, cike da ajiyar zuciya Naufaliyyah ta sauke hannun ta, Bala ne ya kira mai jego ta miqe ta fita, " Sistern kinnan can kill with only her look, ba qaramin tsoro take van ba," dariya Lamyah tai sosai ," qashi da ran kk tsoro?" " keee bar wannan qashi da ran cike zuciyar ta take da qarfida izza," " Allah yasa ba zance na naji ana yi ba," " Aaaa mu ba zancen ki muke ba mukacenyaro kyakkyawa da shi tubar kallah," Lamyah me zatai ba dariya ba, kyakyatawa taje kamar me, wayar ta ce tai qara ta dauka, "Yah Amee na" shine abinda aka rubuta a wayar, murmushi tai ta daga, tashi tai ta bar waje, bayan sun gaisa ya fada mata bayan suna da kwana uku zasu zo har Baaba suje Rimin gata dan ganawa da iyayen ta na can, gaban ta ne ya fadi da tinawa da tai da su........






*Sai nace Farha Allah ya raya baby boy, TEEM FARHA INA BARKA🤱🏻*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼






BY HAERMEEBRAERH





*Qarin bayani da magana akan abinda novel din 'YAR RAWA ya qunsa*





Page 30:






1- Neman ilimi abune mai matuqar mahimmanci, both western education and islamic one, dan in kana da ilimin addini dana zamani akwai abubuwan da dole zaka banbanta da mutane da dama.


2- kar mui wa mamatan mu kuka, kuka irin na jahilci, kururuwa da iface2, mu zama komai zamui mui amfani da ilimin mu, kuka dole ne, amma mu yi shi yanda islam ya nuna mana ba kuka irin na jahilai ba,mui kuka mai hade da nemawa mamaci rahamar Allah, shine asalin soyayyar mu a gareshi.

3- Yana da kyau kowacce mace ta zama cikakkiyar macen da zata kange kowanne lungu da saqo na zuciyar mijin ta, yanda ba zai so rabuwa da ita ba ko na secod daya sai da babbar lalura, in ko bata tare da shi zai ji matsanancin kewar ta, ba yaimurnar qaya bata nan ba.

4- ki zama matar rufin asiri, matar da ko wanne hali zaku shiga ke da mijin ki ba mai ji, zaki hakuri, har ki sama maku mafita, ko ki sama wa kan ki mafita.

5- Yana da kyau bawa ya kiyaye dikokin Allah a kan shi, a koda yaushe kuma a kowanne lokaci, in ka kiyaye dokokin Allah Allah zai kiyaye ka daga dikkan abun qi.

6- Mu riqe ibada, duk wanda ya riqe ibada da azkar na safe da yamma, Allah zai kare shi sannan zai mai katanga daga manyan kaba'irai, zai daukaka darajar shi duniya da lahira.

7- Bawa ya guji yin shirka ga Ubangijin shi, shirka ko wacce iri ce haramun ne, hukuncin shirka wutane direct, sai idan bawa ya tuba, shirka ta fara daga kan canfi ne, qin dayan ta Allah, zuwa wajen bokaye ko malaman tsubbu,neman biyan buqata a wajen wanda ba Allah ba, musamman buqatar da bawa ya san ba wanda zai biya mai wannaj buqata tashi sai mahaliccin shi.

8- MATA MU GUJI MUMMUNAN KISHI, mumkunan kishi na kai mata da dama wuta, wai shin mene ne a kishi ne? Kishi ni a tawa fahimtar shine, qoqarin kiyaye abinda kk so kar ya fada ga halaka,da kuma faranta ma abinda kk so ta hanyar halak, dan haka in kenan qarin aure a wajen mazajen mu zai zama ya fidda mijin ki daga halakar misali zina kenan zaki kishin shi ki bashi dama a duk sanda ya zo maki da batun qara aure? Sannan ba zaki zama mai fasadi a cikin gidan shi ba saboda kawai an maki kishiya? Zaki zama mai qoqarin faranta ma mijin ki ne kawai ba tare da kin cutar da abokiyar zaman ki ba, kowa ta shi ta fisshe shi, da dama abinda mata bamu sani ba shine,ki gama haukan kishin ki, da biye2n bokak ki, mijin ya kubce maki da kiftawar ido, sannan ki gama mai gatan in ba dan Allah kikai ba ke ko dan Allah kikai ya zo ya baki kunya gaba ga kishiyar taki, ko a bayan idon ki ya zage ki tas dan kawai ya samu wajen zama gun waccan, dan haka koma zaki na kishi ki yi shi bisa tsarin islam, ki kyautata zaman ki da abokan zaman ki, ki ba mijin ki dama ya halasta abinda Allah ya halasta mai.

9- In Allah ya sa zama ya hada mu da dan da ba mu muka haifa ba, mui mai riqo na tsakani da Allah, ruqon gaskiya, domin ba mu san me zai zama ba gaba da zamu mora, kai ko ba zamu mora ba ma zamui domin Allah ya bamu lada, ta wani bangaren kuma bamu sani ba muma zamu rayu da namu? Su waye zasu riqe mana namu? In kikai ma dan wnai riqo mai kyau aiwa naki mai kyau.


10- Komai qanqantar abinda Allah ya hore maka in kaga wanda bai kai ka ba yana buqatar taimako ka taimaka mai, kaima Allah sai ya duba abinda kai ya qara maka.


11- Riqon alqawari yana da matuqar mahimmanci da lada mai dimbin yawa.




*Wannan hasashe na ne a cikin wannan novel mai suna 'YAR RAWA, duk wadda take da nata hasashen qofa a bude take dan a qaru da ilimin da Allah ya bata itama na gode*

*Haermeen Haermmaerh na godiya da soyayayyar ku da addu'o'in ku na alkairi a gare ta, tana matuqar son ku itama*❤
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼






BY HAERMEEBRAERH




*I am so sorry fans, yesterday's chapter is awful, banda lfy ne, kuma ban da sha'awar rubutun kwata2, amma saboda yanda naga wasu na son nayi yasa nayi din abinda kuke so shi nake so,hope za a yafe ma Haermeen Haermmaerh*❤
*Ana uhibbukum katheeran*❤






Page 29:








Wasu larabawa na gani kyawawa su uku,sun sha dogayen riguna har qasa, a cikin garin lagos, da alama duk da kyaun su gajiyar da sukai bata boyuwa, yau kwanan su uku suna yawon neman Lamyah, da Mubarak, wanda suke amfani da hoton ta dake cikin wayar mahaifin ta, wasu maza suka samu su biyu a wata mota mai baqin glass, suka tsaya, El-Hussein shi ke jin turanci shine yai masu magana," Assalamu alaikum, pls do u know this gurl? Her name is Lamyah," hada kai sukai suna kallon hoton kamar masu nazarin ta, sai suka fara magana qasa2, dayan ya ce ma dan uwan shi," Oh boy this people rich oo, we fit collect there bag, and take them to Oga Mikel na him know wetting him go do with them abi?" " u don talk wetting dey for my mind," kada kai sukai dayan su ya amsa da ," yes i know her, let us take u to her," cikin tsananin farin ciki zuciyar su cike da mugunta da kwadayi suka shige, muhammad har wani kada kai yake, yana ayyana irin hukunta Lamyah da zai, sannan da abubuwan da zai da dukiyar in sun karbe, tafiya ake ba ta qare ba,dama gasu a gajiye, nan danan bacci yai gaba da su, a hankali daya daga cikin mazan nan biyu ya juya ya zare jakar hannun El- Hassan, rage gudun motar dayan yai,shi ya fice daidai wani gidan katako, da sauri ya bude qofar ya wurga jakar sannan ya rufe ya fito suka sa kai,wani tankamemen gida suka je, wanda kyaun shi ya wuce na tsaya fasalta shi a dan wannan novel, mak gadin gidan na leqowa sakamakon horn da ya ji, ya ga mazannan nan da nan ya washe baki ya bude gidan, shigeea sukai, wanda yai daidai da farkawar su Muhammad, a zuqatan su suna ayyana kudin El-mustapha, washe baki suka hau yi, suna murna, larabci suke ta zubawa, nuni sukai masu da su fito, fuskar su ba walwala, budewa sukai suka saka qafafun su waje, suna gaba suma su Muhammad suna biye, qara kallon gidan suke suna ayyana mugunta kala2 a zuqatan su, wani wawakeken parlor aka kaisu, suka zauna a kujeru na alfarma, kalle2 kawai suke basu ga kowa ba ko wanda suka kawo su basu sake gani ba, dan tin da suka shigo sukai wani babban qofa suka aje su nan basu kuma ganin su ba, leqa qofar nai ganin qwaqwaf👀 wani qasungurmin mutum na gani, mai cikar gashi a fuska, jikin shi ba riga sai wani zani daya daura, shima kamar ya balle, da wata sanda a hannun shi, sai uban sanqo, tubar kallah baqin shi kam ban isa misali ba, ji nai fitsari na neman kufcen da yai magana," weldone Sam and Emma, ur work dey do me well oo, go inside and take two box my boys," " Ahhh oga make am three na? Na three men dey there oo," " k make u carry three then," godiya sukai suka fito dauke da akwati suka wuce su,ko ci kan ku ba su ce masu ba,su kuma har da daga masu hannu, a zaton su Lamyah ce ta sallame su,wata qila sun mata bayanin yanayin su ne ta gane sune, Muhammad ne ya fara kitsa masu abun da zasui data bayyana, suna cikin qus2 suka ga wani jibgegen qato ga tsawo ga qiba yana takawa da kyar dan ko takalmi baya sawa," Ya Rabbiiiii," El- Hassan dake kallon qofar ya fada a matuqar tsorace, suma juyawa sukai,ai suna ganin shi suka firgice suna neman hanyar guduwa, masu gadin dake tsaye a kowacce qofa ce suka shigo suna muzurai, wannan baqin qaton ne ya barke da magaukaciyar dariya ya hau yarabanci, nan da nan na ga su Muhammad suna takurewa a hankali suna dunqulewa sai ihu suke, daga hannun shi sama yai, tini suka tashi sama a matsayin tsintsaye masu kalar fari da blue masu kyau, manya, dan ni kam ko sunan su ban sani ba, nan take wasu maza hudu suka fito ta wata siririyar qofa na gaba dauke da sharbebiyar wuqa, take na sake fitsarin da ya matsen dan tsoro, ta daidai bayan qofar dana maqale suka wuce, ukun ne suka dau tsintsayen nan dake ta kada kai, sukai waje da su,kowa ya bisu, na lallaba nabi bayan su, gani nai sun je gaban wani qaton gunki, sun danne tsuntsayen nan, wannan qaton mutumin ya karbi wuqa a hannun dayan su ya fara yanka kowanne tsuntsu yana surutai da yare, yana gamawa kowa ya daha hannu sama sukai yare sannan suka nuna gunkin, hankalina ne ya tashi ainun, ganin kudi na fita daga bakin wannan gunki, ai qafa mai naci ban baki ba, na fece,kan na zama na baddawa.
Shi kenan qarahen akewa qasa, qarshen mai kwadayi da mugunta tare da mugun hali kenan.😭😭

Anyi suna lfy inda Baby yaci sunan El-Mustapha, Lamyah ta yi kuka sosai ranar, wanda Farha da mubarak ke taya ta, dan sun iso a ranar kwana uku kenan da sunan, tai wa Farha godiya ba iyaka, Farha taso a sakaya sunan amma Lamyah ta roqi da su bar shi haka, tana son ta ji ana kiran sunan mahaifin ta, haka zata fi jin dadi sosai, a haka aka bar shi, aiko yaro yaga gata wajen Yah Amee, innace gata ina nufin gata, iya gata, har kudin da za su saka shi makaranta daga play class har University sai da Yah Amee ya bayar, dan yace komai yayi ba zai biya su sunan Abiin shi da suka saka ma dan su ba. A kwana na hudu ne da zuwan su suka shirya tsaf dan zuw Rimin Gata,sosai Farha ta so aje da ita ta qara ganin Inna dan bata hakurin dukan da tasha amma suka hana ta aka ce ta zauna da ita da Tani a ranar suke son dawowa, haka ta hakura, amma matuqa taso zuwa, sannan ta ci wa Delu mutunci, dan ta matuqar tsanar ta, haka Lamyah ta lallaba ta suka tafi aka barta da cizon yatsa tana ta saqa irin tsiyar d zatai da an bar ta.

Da misalin qarfe sha daya suka isa, inda Saddiqa na riqe da Lamyah qarama a hannu, Musaddiq ya dau zani ya saka alamar jira yake a saka mai ita ya goye, sukai sallama, leqowa Inna tai, taga su waye, ganin Lamyah ne ya sa ta zaro ido tana leqa bayan Lamyah taga ita da waye? Dan tabbas ba ta son qara haduwa da Farha ko a hanya, ganin ba farha ne yasa ta dan pito waje,fuskar ta ba yabo ba fallasa, dan yanzu ta gama gane komai game da Lamyah, tsananin kishi ne ya sa Delu ke kushe su ai ga shi nan ta ga ishara itama,sannu da zuwa tai mata ta shiga da ita daki, ta saka mata tabarma, su Yah Amee da Bala tare da Baaba da Mubarak na fadar mai unguwa, Momma ce ta fara zama, tana kallon gidan, a nan ne wai akai wa Lamyah wulaqanci? Sai kace wata uwar ke gare su, gaishe gaishe sukai, dai dai lokacin da Musaddiq da Saddiqa suka fito, dan suga su waye, kwata2 qin yarda yai Saddiqa taje gida inda dan ta'addan dan Delu yake balle aiwa iyalin shi irin na Delun, " Lamyah sarkin rikici, nikam Baban Lamyah anya 'yar uwata ba tai rikici ba tana qarama? Ka duba kaga yanda yarinyar nan ke hana mu bacci? Badan inna na taimaka mana ba," " ba wani riki......." maganar shi ta maqale sakamakon arba da Lamyah babba da yai zaune tana ta maka mai murmushin ta mai kyau, da sauri ya daga labulen ya shiga," Lamyah? Os that you?" " ni ce Yah Musaddiq," ta fada tana miqewa, kallon kallo sukai ita da Saddiqa wadda ta isa da hanzari ta rungume Lamyah, gam kamar za a kwace ta, idon ta cike da hawayen dadin ganin 'yar uwar ta,murna sukai sosai da ganin juna, gaisawa sukai sannan Lamyah ta tsokani Musaddiq," Yah musaddiq a ban takwarar tawa mana, duk da dai naji ana man sharrin rikici," ta maida kallon ta kan Saddiqa," Aaa yanzu ai dana gan ki na janye, sai dai gado tai wajennnnnn," tana kallon Musaddiq daya jefe ta da hararar masoyan da suka shaqu da juna su, hamdala Lamyah tai cikin ranta,dan da dikkan alamu burin ta ya cika, " Yah Musaddiq tare nake da Baaba da Yah Amee suna fada," inna ce da ta fitk daga gurya dauke da jug da ruwan randar sanyi ta ce," kash amma dai ke ma akwai wauta, da baki magana ba wannan yaron ya kai masu koda ruwa ne? Maza tashi ka je ka kai masu wannan bari na kawo maku wani, " yana qoqarin miqewa ne yaji shigowar su ciki da Mai Garin, dake babban parlor ne wajen dan haka zai ishe su dika, shimfida akai ma mai garin ya zauna, bayan gaishe2 ne, da ban hakuri, Baaba ya debo kudi masu yawa ya bawa Musaddiq yace a saiwa Baby kwalli godiya sukai sosai,inda Yah Amee yace ya dau nauyin karatun ta itama har University nan take ya rubuta cheque ya basu, dan yace yana son amaryar shi tai karatu sosai, nan akai wasa akai dariya,inda Yah Amee ya buqaci ganin gidan da aka haifi Ammiin shi, nan take mai gari da Inna sika kalli juna suka sadda kai qasa," ranka ya dade na sha fada maku, in kana jin tsoron wancan shashashan a matsayin ka mutanen ka

Please Login or Register in order to submit comment