Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ya matuqar tashi, yana tare da Farha, da kyar ta labarta mai komai, tace karya bari Farha taji, bata san a kunnen ta akai komai ba, ta cika tai fammm, hawayen itama ke na jin rashin imani na wadannan mutane akan marainiyar Allah, aiko rufe qofar motar tai tace " muje" tare da jan hancin ta, ta share hawayen ta, Baka kam kasa mata musu yai, dan shina zuciyar shi tayi Rimin Gata.
Hankalin Musaddiq ya tashi jij wayar da Lamyah tai , tabbas yasan yau zai rabh da ita, cike da tashin hankalu ya isa gare ta, " haba Lamyah, in baki hakuri ba kin facing yanayin rayuwar da Allah ya tsara maki ba ta ina zaki fara cin jarabawar Allah a kan ki?" " Sam wannan ba rayuwar da tazo man bace ni na kawo kaina, sakamakon son dangin mahaifiyata, da ban zo ba da ina cikin walwala da nishadi, da ban zo ba da ina tare da masu so na ko da ba jini daya muke da su ba, a qarqashina suke, amma soyayyar su ta wadata a gare ni, ka je kawai musaddiq, yau Bala zai mai dani gida, ba zan zo na zama sanadin hadaka da mahaifiyar ka ba, kai mata biyayya ka auri Saddiqa, kai za ka iya gyara ta a matsayin ta na jini na , ka taimaken kai sanadin shiryuwar ta, Allah zai baka lada mai yaw, kar kai tinanij rayuwar da tai a baya, ka aure ta domin Allah, i am sorry to say,ni dama kaga tin fari ba wai ina maka son aure bane a matsayin yayana na dauke ka,..." kafin ta ci gaba ya fuce a dakin kamar zai kife, ganin haka yasa Inno farin ciki, ta shiga dakin, " habaa yarinya, ai wanda yace zai cituwon inno zallar muya kawai yake sha, ke a suwa, zaki zo rana tsaka ki sa dana ya fara bijireb sannan kuma na yarda ya aure ji? Ai ba zai yu bq, gwanda ki tattara ku bar gidan tin kan rai ya baci?" Cikin kuka Lamyah ta juyo ta kalle ta, ta mata wani kallo da bata san ta iya shi ba ma, ta juya ta hade kayan su tsaf, Mubarak ta dau maya fi zata leqa ta kirawo, tana leqawa soron ta............








😱😱😱😱😝😝😝😝😝😝😝
*lols just chill guys Lamyan ku na nan lfy tana gaida ku*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼








BY HAERMEEBRAERH










page 18:





"El-mustaphaaa?" Shine abinda bawan Allahn nan ya furta kawai, da sauri ya hau jujjuya Mus'ab yana kallon shi, ganin haka ne yasa Farha miqa mai hannu akan ya bata Mubarak, gaba daya ta tsorata da ganin canjin mutumin a lokaci daya, ga shi ya fara zubda hawaye sosai, a firgive tace," Malam bani qanina mu tafi meye haka, ko an fada maka nan wajen makoki ne?" Fizge Mubarak tai wanda shima a yanzu ya fara tsorata da mutumin, tabba Baaba Mus'ab ya san wannan yaro jinin abokin shi ne, to amma ina Lamyah, dan wannan ba ita bace, ya san Lamyah ta hanyar hotuna, da kuma zuwan da sukan yi Dubai lokaci zuwa lokaci, anan ne sukai mata alqawarin boye wa Ameenullah ita har sai yaje da kan shi ya ganta ko kuma ita taje Nijer, " hukumullahu laa ajabun, wannan yaro tabbas dan Aminina ne, baiwar Allah ki taimaken ki sanar da ni ina zan ga AISHAA LAMYAH,," jin ya ambaci haka ne, Farha ta matsa kusa da shi sosai tace," kaiiii malam dakata kaji, ni fa da kk ganina hakan nan kar ka nemi kawon raini, ko wani 419, karrr nake ganin mutanen duniya yanzu, in ma wani tuggun ka ke son hadawa to bari na fada maka ka kiyayen, dan in daki qato ni ba wani abu bane waje na, a ido ne zan maka kamar va zan iya aikata hakan ba, amma duk wanda zai taba Lamyah a shirye nake dana sadaukar da rayuwata dan kare ta ta," " tabbas kin cika masoyiyar gaskiya, amma baiwar Allah ki taimake ni ki taimaki Lam......." wata murya mai zaqi suka ji daga bayan su, an kwala kira da " Baabaa" juyawa suka qarayi dukkan su ,Farha tin kan ta juya ta san mamallakiyar muryar, Baabaa Mus'ab da gudu2 ya aje Mubarak itama da gudu sosai ta isa gare shi ta fada jikin shi tana kuka sosai, kuka suke ba qaqqautawa, Mutuwar aminin shi ta dawo mai sabuwa fil, ita ma mussing Abii din ta take, da Ammii sannan ga farin cikin ganin Baaban ta, tabbas tasan a yau ta gama ganin Yah Amee din ta, sannan ta san Allah baya bacci, Allah yana amsa addu'ar bawan sa da ya yarda shi Allah ne, ya yarda da ya roqe shi akan komai ya kwantar da hankalin shi ya jira sakamako daga mai dika, Lamyah imanin ta ya qaru akan na da, domin tai wa Allah godiya a wannan lokaci yafi a qirga, Farha ce ta je ta kama hannun ta," can u guys pls tell me what is going on here?" Murmushi Baaba yai dan ya san wannan tabbas ba a taba Lamyah gaban ta mutum ya sha, kuma a yanda ya kula tana da kusanci da Lamyah in ko haka ne to tabbas yasan ta san ko shi waye," 'yata ni ne mahaifin Ameenullah, Yah Amee din Aishaa Lamyah, " ai ko wani tsalle ta daka ta dane Lamyah, tana murna, sai ga hawayen taya Lamyah farin ciki na bin fuskar ta, tare da hawayen tinanin tabbas rabuwa da qawar ta kuma 'yar uwar ta yazo, kukan ta qaruwa yai da kyar Suka samu tai shiru, Faisal ne ya qaraso da kudin Lamyah," to ni da kk bar min kudin me zan da su, kin san yau kin fi burge kowa wajen nan dan haka ne kudin suka fi na kullum kar....." maganar shi maqalewa tai ya duqa qasa yana sosa kai," Baaba barka da zuwa," qasan zuciyar shi yana mamakin ganin Lamyah a jikin Baaban abokin shi, ga Mubarak da farha a gefe idon farha ta sha kuka, shima haka da Lamyah, ," kudin meye kk ba 'yata Faisal?" In ina Lamayah ta fara, ta amshe kudin tai wa Faisal sai da safe, a haka Baabaa yace ba zai bar Lamyah tafiya ba tare da yasan inda take ba, nan take yai ma drivern shi waya yazo ya shiga motar shi da Mubarak da Lamyah ita kuma farha suka tafi da Bala, tun da suka shiga motar Farha ke kuka, ba irin lallashin da Bala bai ba amma taqi shiru, hankalin ta ya tashi matuqa, dan tasan tabbas rabuwar ta da wani bangare na jikin ta ya sake zuwa mata, nan take kan ta ya dau ciwo, zazzabi ya rufe ta, Bala ma hankalin shi a tashe yake ga masoyiyar shi ba lfy, kuma komai kan idon shi ya faru, ya tabbata rabuwar shi da uwar dakin shi yazo, haka suka isa gidan kowa da abinda yake saqawa, bayan sun shiga ne, suka nufi ciki, inda Baaba ya kira Baba mai gadi, bayan sallama da yai ya sanar da su yana son nan da kwana sha daya zasu tafi da Lamyah, nan take wajen ya kaure da koke2 Baba mai gadi kan shi hawaye yake,anan Baaba ya fuskanci lallai Lamyah yarinyar kirki ce, tai halin iyayen ta, " kar ki tafi ki barni 'yar uwa ta,in kk tafi za sake komawa cikin maraici ne, ki tausaya min , ko aure na baki gani ba zaki tafi kwanakin sun mana kadan Baaba," kuka take sosai Lamyah ma kukan take, sun manne juna kamar wadan da aka ce tafiyar yau dinne, ," ku dakata, wannan kukan da kuje ba magani bane ba fa, ke an kusa auren naki ne? Waye manemin naki, na roqa a kusanto da auren, dan kuwa tabbas zan tafi da 'yata da dana, ba zan bar su anan ba ba su da kowa, ko me ake. Buqata a auren ki na dau nauyu, ke koda mijin ne bai shirya ba, domin ke masoyiyar diyata ce komai zan iya maki," Baba mai gadi ne ya nuna mai Bala a matsayin mai neman auren ta, ya sanar da shi matsayin karatun Bala, da aikin da yake a gidan, yaji dadin hakan sosai, yace to ai abu yai kyau duk gida ne ma, dan haka a na sauran kwana goma zasu tafi za a daura auren, ta tare a randa zasu tafi, in yaso sai su zauna a cikin gidan kawai, sun yi murna da hakan sosai, amma fa banda Farha, dan ita yanzu ba ta da sauran murna sai tashin hankalin rabuwa da Lamyahn ta, ko daga kai batai ba, Baaba ya fuskanci hakan ya sa yace," to ku naga sai murna kuke anaryar ma naji tace ta fasa a ba wa Bala wata ya aura," da sauri Farha ta daga kai tace," yaushe mukai haka da kai," cike da zaro ido, aiko nan take wajen ya kaure da dariya,kunya ta kama ta ta miqe daki da gudu, Lamyah ma bin ta tai, sukai ta dariya, tare suka dawo, kitchen suka shiga suka debo mai abinci da kayan motsa baki kala2, dama bai ci abinci ba nan take ko ya ci ya qoshi, sannan sukai sallama akan gobe zai dawo, bayan ya tafi ne suka zauna suna ta tattauna yanayin yanda komai zai tafi, Bala ne ya fara hamma yai masu sai da safe, kafin Lamyah tace," to amarya aiki ya samen ya kamata na fara gyara ki kamar Yanda Juwaireren mama na ga tana gyaran jiki kema haka zan din ga maki," miqewa Farha tai ta shige daki tana qunquni, " ba sai ki gyara nin ba tinda ni daya ce amaryar? Kema kina zuwa za sui ramm da ke a ba Yah Amee din ki, kunqara ta can," " Farha me kk cewa ne, kin san ban son kina magana qasa2 dan na san halin ki sai ki zage ni tass ta haka ina nan baki bude," Farha bata ankara ba taji duka a baya, dama a wuya take, kuma tafi Lamyah qarfi, kokawa suka fara cikin daren Mubarak da yau idon shi ya soye ya fara dariya yana " Yauwa qashi da rai, cika mata aiki, ke kuna kumburin buredi zaune ta," suna jin haka suka saki juna sukai kan shi, yana ganin sun yo kan shi ya zare ido ya dora hannu aka yai hanyar fita da gudu, sai dakin shi, kan su isa ya sa key, yana dariya, yana qara tsokanar su, kowa a cikin su ta tsani sunan da yake kiran ta da shi, a haka suka je sukai wanka sukai addu'a suka kwanta.









Shirye2n biki sosai Lamyah tai wa Farha, qawayen su na wajen RAWA suka gayyata, harda yan baqin cikin su, sai da suka gayyata, su kuma suka ci alwashin zuwa ko dan suga dame yaran ke taqama su ke nuna su wasu ne. Farha ta sha gyara wajen Tani da Lamyah, Lamyah kullum sai ta kwadan ta mata zogale danye da manyan timatir, da kuli , ai ko nan da nan Farha hips din ta ya fara fitowa, ita kuma Lamyah ta dage da gyara belly din ta dan so take a bikin Farha ta cashe rawar da bata taba yi ba, hakan ne yasa take shan gwalba wadda ake hadawa da nono amma bata sa nonoj haka take jiqa ta ta murje kwallayen tana sha bayan duk wanu cin abinci, nan da nan kuwa tumbin ta yai qasa, ya dada shigewa yai flat yai kyau, ita kuma Farha sai Lamyah ke bata kwalbar bayan ta saka mata madara a ciki, na musamman ta sa aka yo mata dakan hannu na busasshiyar aya da kayan qamshi a ciki, da minannas, sai dabino busasshe, da madarar shanu da zuma Lamyah ke hada ma Farha ta sha, amma wajen shan kullun sai an kokawa, dan Lamyah ma cewa take sai ta sha," yacin kk sha kema sai an miki auren,ke za a aurar ko ni, ni ban gane ba , in aka zo ci ko shan me dadi kina gaba, in aka zo masu daci da bauri ki noqe, kaji min yarinya , ni gaskiya Tani na min wariya," dariya suke sakawa sosai, aiki duk randa aka ma Farha hadin tsumi masu bauri baurin nan, sai ta danne Lamyah ta dura mata, in taqi taita soka mata guiwar hannun ta a cinya, ita kuma abun dariya yake bata, kamar cakulkuli, a dariyar nan zata samu ta dura mata, sai ta gama sha tai allah ya saka mata, " zai saka miki mana da alkairi randa Yah Amee ya same ki a matsayin mata," ai ko da taji haka farin ciki na kamata sosai.







A kwana a tashi a sarar mai rai( Allah ka bamu sa'a ka sa mu cika da imani, Allah ka sa mui kyakkyawan qarshe ya rahman) a yau aka daura auren Bala da Farha akan sadaki naira dubu hamsin, wanda Baaba Mus'ab yai ma Farha waliyyi, Baba mai gadi ya karba wa dan shi auren Farha cikin murna da jin dadi, mahaifiyar Bala ta halarci auren, bayan kowa ya watse ne, aka bat Lamyah da Mubarak, da Farha, sai Tani dan itama a gidan zata kwana yau, kuka kowa yake kamar wadan da akai wa mutuwa, yau Mubarak ne jikin Farha lafiya laou ba rikici bate doke2, ya qanqame ta yana ta ta aikin kuka, Tani ce tai jarumtar miqewa tace," ku mui hakuri,mu zamu ba kan mu hakuri, tafiya ai ba mutuwa bace, za a na gana wa duk sanda aka so, an bamu adireshin ku na can, ga lambar waya, sannan kuma gidannan dai yana nan ba inda zamuje dan zan ci gaba da aiki anan, duk sanda taso ganin munza ta zo gare mu, dan haka kumu tashi mu fara hada kayan nan, " miqewa sukai jiki a mace suka hau hada kaya, sai da suka gama tass Lamyah ta je inda ta adana jakar da Abee ya bata ta dakko, ta dora kan akwatinan kayan su, wankan kwanciya sukai, kowa taje ta kwanta, ranar farha da Lamyah a manne da juna suka kwana, cikn dare Farha tai ta masifa a cikin bacci wai ba za a tafi mata da qawa ba, Lamyah tai murmushi mai cike da hawaye a idota sauka gadon tai taje tai alwala tai nafil2 tai addu'o'i kamar yanda ta saba yi a duk sanda wani abu zai sameta, sai ta mai addu'ar neman zabin Allah.






Da safe kam an sha kuka da bori wajen farha, da kyar su Lamyah suka bar gidan, Bala ma sai sharce kwalla yake, ga tausayin amaryar shi,ga kuma tausayin su duka, na rasa uwar daki mai adalci.



*NIGER REPOBLIC*






...............................😝
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼








BY HAERMEEBRAERH










Page 19:










Da gudu ta qanqame Momma, a tare suka fashe da kukan farin ciki, kewa, da kuma rashi, Baaba bai hana su ba, sai da suka gaji dan kan su sukai shiru, sake Momma tai ta fara leqa makeken parlon tana kwala ma Yah Amee din ta kira cike da farin ciki da zumudin ganin shi, a sannan ne fa hankulan iyayen biyu ya tashi, dan tabbas in Lamyah taji yai aure ba zaman lfy, to amma ya zama dole su sanar da ita, kamo hannun ta Momma tai tana shafa fuskar ta cikin kulawa," 'yata ki ci abinci, ki wanka, ki dan huta mana sai kiji ina Amee din ki yake," girgiza mata kai ta soma, idon ta cike da kwalla sannan tace," A'a momma, ni ina son na gan shi yanzu, ina son na fara bashi daddadan labarin da ya dade kunnuwan shi na son su saurara, na gaji da aje wannan sirrin dake raina, abubuwa da dama na yawo akaina,ina cikin rudani, bana son wani matsala ta faru daga bangare na," a hankali Momma Aishaa ta share hawayen da ya gangaro mata dan tabbas ta san yau akwai daru, sun so just for today, Lamyah ta huta, kafin a bata labarin komai amma inaa........... ......




Ta bangaren ango da amarya kuwa ana nan ana kan aikin da aka saba, da kyar ya samu ya sulale gefen ta, yana maida nunfashi, kamar wanda yai gudu, zufa kawai yake kamar manomi, ita ko sai wani yauqi take, ta dora kan ta a qirjin shi qafar ta a kan tashi, hannun ta na wasa da gashin qirjin shi, a hankali can qasan maqoshi ya fara magana," ki shirya na kai ki gidan mu, ku gaisa da su Momma, dan ni nan da kwana hudu zan koma Nigeria, kuma nan gida zan barki, amma in kina so, zaki iya na maida ki gidan mu, ki zauna bangare na har na dawo, dan nan ke daya ba zaki so ba," wani irin a bu ne ya tokare mata wuya, yanzu duk dadin nan da take kwasa tafiya zai? Ita ya ma za ai ta barshi tafiya shi daya yai watanni baya nan? Ya zata iya sabo da rashin shi bayan ya saba mata da jikin shi? A gaskiya da sake, ko ya tafi da ita ko ya maida ta gidan su, kaiii anya zata iya zama kuwa? Wadannan tambayoyin ne ke mata yawo a kai, sai da taji ya shafo gefen cikin ta, wani dan juyi tai a jikin shi, yana ganin haka ko ya qoqarta miqewa, ya san halin ta so take su koma ruwa," ki shirya bari na je na shirya a dakina zan jira ki in kin gama ki mun magana," ai kan tai wani yunquri ya fice, yana shiga dakin shi yai ajiyar zuciya, ya danna key, toilete ya shiga, ya sakar ma kan shi ruwa, zuwa tai qofar dakin shi din ta rufe sannan ga qarar ruwa, tsaki ta ja mai qarfi ta juya ta koma, toilete ta fada itama ta shirya, cikin wani material mai tsada da kyau kalar baqi mai ratsin yellow a jiki, tai kyau daidai ita, ya gama shiryawa kenan suka jero suka dau hanyar gidan su.


......... " Baaba ku fadan ina Yah Amee na yake pls, i really want to see him," ta qarashe cikin hawaye masu dumi, sallama suka ji gaba dayan su suka juya, gaba dayan su su biyun ido suka zaro a tare suka nuna juna," kaiiime kk yi anan?" " keee me kk yi anan" nan take yace " ke zan tambaya," " ko dai na tambaye ka ba don nan gidan mu ne, ga Baaba na da Momma ta, kai fa me kazo yi?" Wata dariyar rainin wayo ya saki, sannan ya wuce ta ya kamo hannun matar shi sukai ciki suka zauna kan kujeru, qasan zuciyoyin su ba qaramin murnar ganin juna sukai ba,dan zuqatan su sun yi kewar juna sosai, Baaba ne yai ma Momma nuni da suma su zauna, zama sukai Baaba yai gyaran murya, sannan yace" yanzu dai na ga alama kamar kun san juna , amma ba damuwa, komai zai zo da sauqi da ikon Allah, ammmmmm Ameenullah ya iyalin ? Ina fatan kuna nan lfy?," kan su Lamyah ya kulle sosai, wannan ba abun da za ai shiru bane, a ina Baaban shi ya san wannan tijararriyar? Har take ikirarin su a iyayen ta? Amma zai bi yanda suke so, amsa mai yai, da tana lfy, suka gaisa da Momma da itama abun ya mata daban, kamata yai a zauna ai ma kowa bayanin juna, sannan a warwarw komai amma Baaba ya kawar da zancen, bayan gaishe2 ne da akai, wanda in da sun kula da Naufaliyya zasu ga yanda ta cika tai fammm,dan zuciyar ta ta gama amince wa zama anan in yai tafiya, a da kam tana tantama, amma yanzu ta amince, musamman da taji Baaba na duqunqune zance, wannan mace da kyau kamar ba jinsin mutane ba, ina za ta yarda ta zauna a gidan su mijin ta, salon mijin ta ya na zuwa gaida iyayen shi tin bai son ta ya kyasa? Inaaaa ba da ita ba gada a qabari, sannan ga dikkan alamu sin san juna ma, tabota taji an yi, ta juya sashen shi, taga yana mata nuni da Momma, duqar da kai tai ta gaida ta, itama amsawa tai, idon Lamyah na kan na Ameenullah, shima haka, ko wanne da abin da ke saqawa, shi tashi cike take da farin ciki zullumi, fargaba, da rudani, ita kuma tata cike take da tsananin tsoro, kar dai ace wannan ne Yah Amee din ta, ga shi da mace, lallai da ta mutu, abu biyu sun hadu mata kenan, ga shi shine Yah Amee din ta, sannan kuma mutumin da yai mata satar zuciya ba zato ba tsammani, "Oh yau ya zan yi" shine a bin da ta furta ba ta san ya fito fili ba, kallon ta kowa yai, nan take ta tsume ta dau jakar hannun ta ta koma kusa da Momma, kwantar da kan ta tai kafadar ta tana shagwaba," Momma zan shiga na watsa ruwa ina ne dakina?" " Ya kama ta kam tashi mu je na nhna maki," tafiya suka kama, mamaki ya kashe Ameenullah, na ina suka samu wannan daha zuwa ji uanda take neman kwace mai waje, tabbb inaaa ba zai yu ba,da sake, to shi in ya tashi shagwaba yai a ina, wannan baligar da ta yi a kai ta daki ta cinye mai waje( ni kuma nace kai baka ji kunya ba risheshe da kai kace an cinye ma waje😂😝)bin su ya tashi zai yi Naifaliyya ta riqe hannun shi tare da murza cikin tafin hannun shi tana wani kashe ido, da lasar lebe, nan take yaji kasala ta rife shi, ya koma ya zauna, Baaba da ya kula da me ya faru ya girgiza kai yai layar zana.





Baaba ne da wasu abokan shi biyar, sun taru, shigowa ta qarshen zancen su naji, inda naji Baaba yana " Alhamdu lilLAAHi, yanzu da ya dawo tinda an daura, sai a kai mai amaryar shi," sauran ma murna suka taya Baaba na dawowar Lamyah da kuma daurin auren da akai kan in iso na Lamyah da Yah Amee ba da sanin shi ba, ba da sanin matar shi ba, sannan ba da sanin Amarya Lamyah ba. Sai dai nace Allah ya bada zaman lfy kuma a wanye qalaou.




Kwalliya ta ci ta kece raini, ta fito dakin ta zuwa kan dinning, inda Lamyah ta fito itama cikin qamshi da hasken fuska, dan ko mai bata shafa ba sakamakon yunwar dake addbar ta da kyar tai wanka, tai brush ta fito daga ita sai riga da wando iya kwaurin ta, gashinnan ta daure ta baya, yana lilo,sai agogo dake hannun ta, zama tai taja kujera,sannan ta fara zubawa kan ta abinci,ko kula da Naufaliyya batai ba, amma ita tin bude qofar ta ta qurawa hips da boobs din Lamyah ido, sannan ta. Kalli yanda cikn ta yake a shafe, kamar zai hade da baya, sai ogon gashinta da fuskar ta mai cike da kyau da kwarjini, kai lomar farko da Lamyah zatai tana daga ido sukai ido biyu, saurin kauda kaiNaufaliyya tai, amma dole ba yanda zatai Lamyah ta kama ta, yamutsa fuska tai, ta kalli Lamyah tace," ke a garin ku haka ake in aka tashi a bacci, baki san ki gaida manyan ki na?" Wani kallo Lamyah ta bita da shi, dan tabbas Naufaliyya zata girme ta, amma ba zai wuce da 'yan shekaru biyu uku ba, a ganin ta su kuma ba komai bane, dan ko Farha ta bata daya da kadan, " a garin mu ba a koya mana gaida wadan da zasu zauna si qurawa wani ido ba har wanij ya dinga zaton ko ba kowa a wajen ba, har sai ya tsargu daga kallon maitar da aka bi shi da shi," miqewa Naifaliyyah tai," ke har ni zaki kalla ki cewa mayya, nawa kk? Wacece ke a gidannan? Waya tsaya maki da zaki kallen matar da a cikin gidannan ki zagen," da

Please Login or Register in order to submit comment