Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri ta cire hannu za ta kaiwa Lamyah mari, Lamyah riqe hannun tai tace," ko da wasa, ko da mantuwa, hannun ki ya taban jiki, da sunan duka bada niyyar tausa ba ko wani abu makamancin haka zaki sha mamaki, dan ni ba komai nake dauka ba, ina da son mutane amma daga lokacin da idona yai arba da naki naji bana yin ki sammm, dan haka ki kiyaye" jan kujerar baya tai ta wuce cikn takun isa da qasaita na macen da take taqama komai yaji a jikin ta, daki ta koma, abincin da bata ci ba kenan, yunwar ma sai taji babu, ita ko uwar gida an barta baki sake kamar qawuya, Lamyah bayan ta koma daki, ta sake nunfashin da take riqewa mai qarfi, " Dama na iya fada? Dama zan iya rama abu in an min? Ko dai tsabar kishi ne kawai ya ja hakan? Don hae ga Allah ni tinda na ga wanda nake wa son da ban san sanda ya shigen ba da wata naji gaba daya na tsane ta," juya kai tai ta kwanta a hannun dama, hawaye ne masu zafu ke bin kuncin ta, kaiii jama'a yau ina zata saka kanta? Komai sai tayi kamar zata same shi sai ya kufce mata.



A wannan yanayi kullum Lamyah da Naufaliyyah suke, har Naufaliyyah ta gaji, ta ce zata koma gidan ta, su momma basu hana ta ba, ta tarkata ta koma, Lamyah kam zuciyar ta kamar ta fashe, dan gani take ta koma suna tare da Handsome din ta, " Handsome dina? " wata dariya tai ta gefen baki, dan ganin wautar kan ta da kan ta, a haka dai lokaci na ta ja har Ameenullah ya dawo, inda nan gidan su ya fara sauka, ya isko Momma bata nan da Baaba, Lamyah ce kawai a gidan..........








*Readers ga ango ga amarya fa*😱
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼







BY HAERMEEBRAERH





*This page is for u Aunty Rumaisa, thank u so much for everything, I heart u da yawa, kin cancanci yabo mai yawa, kina matuqar taimaka min da an tambayi novel kina kusa an samu. Love u XX❤





Page 20:






Waqa ce ta Arabs kawai ke tashi, mai cike da matuqar dadi, ga duk mai sauraro, gaba daya ta cika parlon da kidan ta mai ratsa zuciyar masoya waqe2, ko Ameenullah da bai cika son waqe2 ba yau ya yaba wannan, ruwan da ta dakko daga fridge a kitchen ta ruqo tana qoqarin budewa, at d same time tana rawa, qugunnan kamar ba a jikin ta yake ba dan juyin da take da shi, ga rigar ta dake dagawa, sai dogon wandon da ta saka wanda ya matuqar matse mata qugun, ga gashin ta dake baje a bayan ta, amma tana rawar tana jujjuya shi, sake baki yai kamar dolo, qoqarin zama yake a kujera ashe bai ida qarasawa daidai wajen zaman ba, qarar faduwar Ameenullah ne ya firgita ta, ta kula da shigowar mutum, ihu ta kwalla, ta sake ruwan, nan take ruwan ya zube, shi kuma ya tashi yana wani basarwa, kar ta raina shi, gudu zata sa ta fada cikin ruwan, aiko ta bare baki ta fara kuka, da sauri ya isa gare ta, dan taimaka mata, ashe ma matsoraciya ce, ya ayyana a ranshi, wani murmushi ya sake, daga ta yai, tana ta faman kuka," ke ki wa mutane shiru, kin kunna kida kamar kina gidan RAWAR taku, ko an gaya maki gidan mu gidan RAWA ne?" " sadda kai tai qasa dan gaba daya yanzu wani nauyin shi take ji, bata kuma san meye dalili ba, sannan kullum hasashen ta na qara tabbatar mata wannan shine Yah Amee din ta, amma yau ta yanke shawarar tambayar shi ko shine Yah Amee din ta? Bata kula shi ba dingisawa tai zata kujera ta zauna, haba wani qara ta sake, saboda azabar da qafarta taji ta mata, dafe gini tai tana hawaye, sosai ya tausaya mata amma ai ita ta jawa kan ta, kama hannun ta yai yana bata rai, wani irin lantarki take jin na bin jijiyoyin ta, shi kuma ji yake kamar da dai duniya bai taba jin hannu ko jiki mai dadin tabawa irin na Lamyah ba, tinanin shi ya kawar, can qasan zuciyar shi na ci gaba da tuhumar wace ita? Dan in da wata mai mahimmanci ce a rayuwar shi da iyayen shi sun sanar da shi wacece, amma zai jira ya.ga zasu mai bayanin wanan mara kamun kan?zaunar da ita yai zai fice a gidan dan kula da yai ba kowa, ga Naufaliyyah da ta dame shi da kira, dada kama hannun shi tai ido na kwalla sosai, ta daga manyan idon ta dake zubda hawaye tace," Yah Amee?" Muryar ta cike da rawa, a gigice ya juyo, yana kare mata kallo, yanayin yanda yake kallon ta ne yasa ta tabbatar wannan shine Yah Amee din ta, hawayen ta qaruwa sukai kamar panpo aka bude, shi kuma jikin shi har rawa yake ," Lamya" amsawa tai kuma a lokaci daya ta miqe ta fada qirjin shi da gudu,rungume ta yai sosai suna kuka, Ammii n su da Abii suke tinawa sosai, kamar wadan da a kaiwa mutuwa a lokacin , sallamar Momma da Baaba ne ya katse su, da gudu Mubarak ya je gare su ya kama qugu yana kallon Ameenullah , irin kallon ina jiran qarin bayani akan abinda ka mata, da Ameenullah ya gane nan take ya daga hannu sama da nufin kare kan shi," ba abinda na mata," amma Mubarak bai dai na kallon shi ba, sai ma daga gira daya da yai ya gyara tsayuwa," na rantse ban mata komai ba, rawa take ta dakko ruwa ta fadi, shine na taimaka na kawo ta nan, zan tafi ta riqen hannu ta kira suna na a nan na gane Lamyah ta ce shine ta rungume ni muke kuka, kuma ita ta fara riqen hannu, ta rungume ni, wait a minute, why am i even explaining my self to a kid?" "Whatch it man i am not a kid,nan gaba kadan zan iya zama Yayan ta, haka Uncle Bala da Farha sister suka ce,"Baaba da Momma da suka dade da fara dariya, tun Ameenullah na zuba bayani ne suka fashe da dariya sosai, Lamyah kuwa ba abinda take face kallon Amee din ta, shi kuma yana tinanin me ya hana iyayen shi sanar da shi ita ce? Amsa aka bashi," Saboda ina son na aura maka ita kamar yanda na maka alkawari, amma ganin yanda kuka nuna kun san juna, kuma na san halin ka, tinda na ga inda ita da Farha suke RAWA, dan kan na dawo sai da na bincika komai, kuma an tabbatar man da irin tsanar da kk wa halayen ta, wannan dalili me yasa aka daura auren ku, ba da sanin ku ba," wata zabura sukai, Lamyah yar qara ta saki saka makon fama in da ta bige dazu da tai, kallon ta Ameenullah yai da sauri, zuciyar shi bai san me take qunshe da shi ba, farin ciki ko disappointment ne? Dan gaba daya a yanzu ya rasa wa yake so ma, shin Lamyahn shi ko Laila YAR RAWA? ya zai yi , wannan dake gaban shi gaba daya baya son halayen ta, dan gani yake kamar ta gama biyewa mazan dake wajen rawar tasu, sannan kuma yana son ta a qasan ran shi, dan itace mace ta farko da ya fara jin komai akan ta, ha kuma natural son da yakewa Lamyahn shi, kai everything is complicating.


A nata bangaren kuw, banda mamakin wannan aure da aka hada ba abinda take, tabbas Yah Amee ne burin zuciyar ta, shi take son kasancewa da shi, in da so samu ne ma, yau ace an hada su su tafi gidan su tare, amma inaaa son da take mai ba zata iya zama da shi da kishiya ba, ace su biyu suke morar shi, musamman in ta tina wace a matsayin mayat shi, wani kuka ta sake mai cin rai, ta hau dingisawa tai dakin ta, gaba daya tana tafe albarkatun jikin ta na motsawa, ko dan wannan jiki Ameenullah zai
yarda da auren ta,
amma tabbas bai san ranar da zai daidaita zuciyar shi akan ta ba.

Bayan ta tafi ne suka qarasa tattauna komai da Baaba, sannan suka saka lokacin biki da tarewa, nan da sati biyu, sallama ya musu ya tafi gida cike da tinanin da ya rasa ina zai saka su, yau duk maitar Naufaliyyah bata gane komai daga wajen shi ba, a haka ta hakura ta barshi, dan ta kula yau ba a daidai yake ba, gashi ita ko dan tarairayar nan bata iya ba, abinci wannan siyowa tai ta aje mai acikin abin take away din ko ta dan mayar wani wajen duk da yasan ba ita tai ba, dan bata iya din ba.

Tana shiga daki wayar ta ta ratumo ta hai kiran Farha,Farha ana can ana zubawa Bala shagwaba , taji waya na ringing, miqa hannu yai ya dakko mata ya amsa ya kara mata,da kyar ta amsa da " Hello" " ke dalla tashi zaune Lamyah ce," ai da hanzari ta miqe har tana kusa kifawa dan murna, tsalle ta daka ta dale Bala, suna fuskantar juna, saka wayar tai a Handsfree, aiko Lamyah ta fashe da kuka, nan da nan jikin Farha ya hau tsuma kamar mazari," wane dan kan uban ne ya taba ki a gidan, kaf din su ki min bayani, bana tsoron ko wanne gauta a cikin su, ni rana ce dafa su zan, maza ki min bayani," Lamyah na jin haka ta tsagaita da kukan," Dalla uwae mafadata ni ba abin da kowa ya min," " to me kk wa kuka?" " Baaba ne ya... ya.... auran Yah Amee, "wata shewa Farha tai tana ta murza Bala, gaba daya Allah 2 yake ta aje wayar ," to in banda ke meye na kukan,bayan mafarki ne ya zama gaskiya," "a da ba? Yanzu yanda nake ji a zuciyata ba zan iya zama da shi ba" " baki da hankali ne, me yasa ba zaki iya zama da shi ba?" " yana da wata matar fa," kuka ta fashe da shi, ta hadiyi wani abu mai daci a wuyan ta, Farha ce ta sake wani ashar, " aure fa" daga Bala tai ta koma gefen shi,"wane qaton ne ya mai aure bayan an san ko ba jima ko ba dade zaki bayyaa agare su, to bari kiji kar ki yarda ki zaina da kishiya, ko ya sake ta ko a raba maku gida, ko kuma ya san abin yi, yo ni mutum ya min kishiya ma ba sai na babballa shi ba," ta qarasa tana huci sosai, wayar Bala ya amshe yana gimste dariya, gaisawa sukai da Lamyah sannan ya fara mata nasiha mai ratsa jiki da jijiya, nan take Farha da ta cika tai fam ta sauka," but still is not fair, yaushe ma Lamyahn tai girman zama da kishiya," daga qarshe suka mata addu'a suka mata fatan alkairi, da alqawarin zuwa bikin nata, kashewa tai ta zame ta kwanta, hankalin ta gaba daya a tashe yake, sai dai kawai a kaso dari t samu sauqin ashirin.



Gyara ta sosai Momma ta fara,ba qaqqautawa, sai dai komai zata bata tana amfani ne da abubuwan mu na gida, kama da ga kayan lambu zuwa kayan marmari, sai kuma dangin aya, dabino, kwakwa, cukui, da zuma, ko gyaran jiki da natural abubuwa Momma ke wa Lamyah amfani, nan da nan ko kyaun ta ya qara fitowa, jikin ta tsabar kyau wani sheqi yake kamar macijiya, gaba daya Momma kanta ta san dan ta ya gama dacen mace anan.





Tin saura kwana uku Farha ta dira a Nijer, sun sha murna sosai ita da Lamyah da Mubarak, sai kace zasu tsaga gidan da murna, dangin Momma sun fara zuwa suma, kowa sai son barka yake da amarya Lamyah, a gefe kuwa amarya zuciyar ta cunkushe take, duk yanda farha ta so mantar da ita baqin cikin ta abun ya faskara, tayi iya yin ta har saida itama ta koma yin shiru, Mubarak ne ya shiga tsakiyar su ya zagayo da hannun shi ta wuyan su" kaiiii shirun nan naku ya burge ni, for the first time Kumburin buredi, da Qashi da rai sun nustu ba fada, ba hira ba hayaniya," ido suka hada a tare sukai kwafa, ai ko kan ya ankara sunyi ram da shi, ihu yake yana neman taimako, dakin rufe yake, sai da suka gama yamutse gadoj kamar wasu yara, sannan suka kwanta suna ta dariya suna maida nunfashi," God i am gonna miss all this," hawaye ne ya gangaro ma Lamyah, Munarak ne yace," My goodnee really, Lamyah? To ba dani ba ni na gudu wajen Mommana, ta hadan abinci duk kun yashen ciki," fita yai a guje , su kuma suka saka dariya, Farha ce tace," yaron nan in yana abu kamar wani babba, he is just 5 to 6 yanzu fa, amma maganganun shi da wayon shi kamar dan 8 ko 9, Allah ya raya shi, tabbas ta bakin nashi ne tin da da yakan ce zai zama yayan ki,in Bala na kitsa mai hakan nakan musa kullum," murmushi sukai suka miqe zuwa sallah.








An ci an sha, an kuma yi biki lfy, in da Farha taso tai rawa amma aka hana ta, taji haushi sosai, tai qunqunin ta ta gama tace aiko yau ko a gidan amarya ne sai ta dance, ile ko bayan an kai amarya, mutane an tattafi, daga Lamyah dake ta kuka, sai ita Farha, sai wata yar uwar su Momma, da ta kan zo, mai suna Rahama, kida Farha ta kunna, tin Lamyah na daurewa ai sai ga amarya ta cire mayafi tana takawa, suna yu suna ihun jin dadi, a haka Ameenullah ya dawo, shi daya ya shigo, dan a nan su Farha zasu kwan, ita gobe zata wuce, shiyasa Lamyah ta dinga kuka sai abar mata ita, da kyar Momma ta yarda, dan gaba dayan su kuka suka sata gaba suna yi, Ramla ma gobe zata koma gidan Momma, leqowa yai ta yar hanyar da basu rufe ba,yana ta qarewa Lamyah kallo, gaba daya hankalin shi ya ma tashi, burin shi kawai ya gan shi kusa da amaryar shi.....





*Sauran qiris wayar nan ta ja na aje rubuta 'yan rawa sai bayan kwana biyu ko uku, inna huce daga faduwar gaban da ta ja min, nai rubutu mai yawa na fice hankalina ya tashi dana tina ban saving ba, ina komawa naga ashe bai gogu ba, da wallah sai na warke na dawo*😭😂😂😂
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼










BY HAERMEEBRAERH









*I dedicated this sweet page to all MAMU NOVELLA members, especially the active 1s, Yan labe layi daya ne naku*😙 *I heart u da yawa, mun zama sisters from another mother, Allah ya qara mana hadin kai da so da qaunar juna, My qawalliya rabin duwais ( Mamu Autar Hajiya) Maryam Alqali,ina roqon Allah daya baki ladan hada zumunci da kikai mai qarfi*







Page 21:





Wani juyi Lamyah tai hade da banqara qirjin ta, sannan at the same time qugun ta ta maida shi gefe, ta saka hannu ta tattaro gashin ta gefe, tana kada qugun ta a hakan, wata ajiyar zuciya mai qarfi ya aje, bai san da zuwan Naufaliyyah ba sai ji yai ta daki kafadar shi da dan qarfi, a firgice ya juyo, wani mugun kallo ta ke bin shi da shi, gaba daya idon ta yai jawur, fuskar nan tai jawur, haka ma hancin ta, sunkuyar da kai Ameenullah yai yace," shigowa ta kenan zan miqa masu wannan naga suna shashanci, ni kuma bana son shiga," harar shi tai dan a tsaye take tin shigowar shi, har matse qafafun shi da yake da komai a idon ta, qwace ledar hannun shi tai ta dauki hanyar dakin, zata kai masu, tinawa da yai ba Lamyah kadai bace a dakin, da qawar ta masifaffiyar nan, sannan ga Rahma kar ta fadawa Momma , bayan nan ba zai so wulaqanta Lamyah har haka ba ace a first nyt din ka kishiya ce zata kawo ma kazar amarci ba kuma da arziqi zata ba da fada zata je, shan gaban ta yai ya jawo ta jikin shi, sannan ya hade ta da gini, nan da nan jikin ta ya hau rawa, miqa mai jikin ta take gaba daya tana aje nunfashi, yana ganin haka a ranshi yace," yau na shiga uku," kiss daya ya mata a goshi, ya shafi gefen fuskar ta, sannan ya kauce, idon ta arufe yake amma jin da tai kamar baya nan ya sa ta bude ido, aiko nan take wasu hawaye masu dumi suka fara bin fuskar ta, ta durqusa a wajen tana kuka, mai cin rai, yau Ameenullah din ta ya zama na wata, yau da wata zai kwana ba da ita ba, a qa'ida ko bai kwana da wata ba lokacin waccan ne ba zai kwan da ita ba, aiko yau za a yi ta, dan maganin matan da ta dirkawa kan ta, ba qaramun damun ta yake ba, miqewa tai tai dakin ta, wasu arnan kayan bacci ta saka, ta feshe jikin ta da mayun turarikan ta,wanda a ciki harda hadin na asirin su na mallake Ameenullah, murmushi tai na gefen baki, sannan ta tura qofar dakin Ameenullah dan ta kai mai ziyarar ba zata, me zata gani.....
..




Wucewar Ameenullah, dakin Lamyah ya fada da sauri ya rufe qofar, kamar wanda aka kora ciki, ajiyat zuciya ya sauke kan ya daidaita kan shi, Lamyah da farha masu rawa tare da Rahma yar kallo ba qaramin firgita sukai ba dan ganin yanda ya fado kamar an biyo shi," wayoo Allah kai da waye?" Farha ce ta watsa mai wannan tambayar ta maqale a qarshen gado tana wulla idanu, Lamyah kam har ta fara kuka, sai Ramla data kasa magana jiki na karkarwa, bata rai yai ya harari Farha da take jiran amsa yace," Nida aljani ne," aiko a tare suka zunduma ihu, kowa ta qara qanqame yar uwar ta, dan tabbas da gaske yanda ya fadi akwai abinda ya biyo shi, dariya ce ta kwace mai bai shirya ba, " dalla malamai ku nutsu, wannan uwar Rawar da kuka me ai ta isa kira maku aljanun ba sai na zo da su ba, ke gaki jiki ba nama, a bushe amma kin dage wai ke rawa kk, to gwanda ma ita, tana da abun girgizawar, ba ma wannan ba Lamyah ki zo dakina ina son magana dake," idon Farha ne ya qanqance da masifa, ta miqe kenan tana tattaro kalamai da maganganun wassafa mai ta ga ya kama hannun Lamyah sun fice," Bashi, sai kuma ka biya," shine abinda Farha ta fada kenan ta sakko daga gadon tana ta mitat tsoron daya basu.




...........suna shiga dakin, auran ledojin ya aje a qasa dan dama uku ne ya aje ma su Farha daya ya zo da sauran nan, daya ta Naufaliyyah, daya ta Lamyah da shi, yana ajewa kuwa ya juya kan Lamyah data takure, a gefe tana watsa ido a dakin, kallon ta yai kamar ace fir ta gudu, ," sai kace wata ta Allah, dalla malama ki qaraso , ni magana nake son muyi dake," qarasa wa tai kanta a qasa, tana wasa da yatsan ta,duqar da kan da tai ne ya bata damar ganin kayan jikin ta, aiko wata kunyar shi ce ta kamata, dan laffaya aka nadota da shi, kayan qasan wasu fitinannun kaya ne irin yadin nan me mannewa a jiki, sannan doguwar riga ce iya cinya amma an tsaga ta ta gefe, sannan an matse ta daga sama, bata taba jin kunyar zama da irin kayan nan ba sai yau, Ameenullah kuwa duk inda hankalin shi ya ke ya kai qololuwae tashi, amma daurewa yake kar ya ja musu masifar Naufaliyyah, zama tai a darare, ya daka mata tsawa," ni dalla ki matso ko magana kk son nai ta daga mury ne?" Kada kai tai alamar A'a, matsawa tai sosai, shi ma qara matsawa yai jikin ta sosai, ledar hannun shi ya dakko, ya bude, kaji ne manya, masu laushi, guda biyu, sai drinks, da snaks, janyo dan qaramin table din gefe yai,ya dora su, umartar ta yai da su ci ta tashi ta bace mai a daki, ci ta farayi, dan ko tana jin yunwa, after all Yah Amee din ta ne, bata ga abin jin kunya ba, zagewa tai ta ci sosai ta sha abin sh, suna gamawa tai qoqarin miqewa, juyawar da tai, yai ido biyu da shape dinta nan take ya kware ya hau tari, ba qaqqautawa, da sauri ta juya nan ma ji yai kamar an qara kware shi, dan yanda ta sunkuyo qirjin ta ya bayyana mai jiyai kamar nunfahin shi zai dauke, jus ta zuba a cup ta zauna daf da shi,jikin ta na gogar nashi,ta kai mai baki, tana ta faman zuba mai sannu, idon ta fal hawaye, kurba yai, a hankali nutsuwar shi ta dawo, jan ta yai ya aje cup din hannun ta ya hau kissing din ta ba ji ba gani, suna a hakan ne Naufaliyyah ta shigo, kusan suma tai dan tsabar kishi, ai ko yaja jin qamshin ta bai san sanda ya ture Lamyah ba ta koma gefe, wani kallon mamaki ta bishi da shi, sannan ta bi inda yake kallo itama ta ga meke faruwa? Naufaliyya ce ta cika tai fammm, idon ta har qanqancewa yake dan masifa, " Lamyah sai da safe, ki addu'a kan ki kwanta," wani kallo ta bishi da shi na lallai ka rainan wayo, duk da ba tsoron first nyt da take ji tabbas she really want to experience it at her own first day, in her matrimonial home, amma da dikkan alamu wannaj matar tashi bazata taba bari su sake ba,duk da soj da suke wa junan su, tabb ashe akwai yaqi gaban ta," bakiji ance ki fitsari ki addu'a ba kan ki kwanta,yara qanana sai jarabar tsiya," inji uwar gida amanar Ameenullah, wani mugun kallo Lamyah ta bita da shi,tana son bata amsa taji an kama hannun ta ana leading din ta waje, juyawa tai taga Yah Amee din ta ne, suna kaiwa qofa yace mata a hankali,"My Lamyah sai da safe sleep well, and i love u so much," daskarewa tai a tsaye, yau me take ji, itace fa amrya, sannan kuma ita bata taba tsammanin zai hakura da kasancewar ta YAR RAWA ya aminta da ita da wuri haka ba, amma gashi har kalmar love ya furta mata, wani murmushi ne ya kwace mata,haushin da ta qunsa gaba daya sai taji nafila ne, tin da an bata farilla ai shikenan, ita kuma waccan jarababbiyar taje ta cinye shi, dama ita bata san komai ba ai, hanyar dakin ta tai ta isko mutanen ta na ta hira,Ramla na jin bacci amma iya surutu ta hana ta sai zuba take, kashe fitila tai ta qarasa gadoj ta haye, a hankali ta furta masu," sai da safe, a hakura da hirar nan haka Farha," haushi ne ya kama Farha sannan kuma taji wani iri game da yanayin Lamyahn," me ya miki? Ki sanar dani in wani abu mara dadi ya miki tin kan na tafi na mai tass dan ba wai mun baki shi bane dan ya na bata ranki," " cikin dan murmushi mai sauti Lamyah tace," Ammiii kwantar da hankalin ki, ba abinda ya min, kin hane?" Farha ce ta kada ido sama tace," au nice ma Ammii din yau," " to u ar being over protective,ba fa abinda ya min, da yamin wani abu kin san halina da kuka zaki ganni," ta qarasa cike da dariya, Farha ce tace " kuma fa haka ne," gyara kwanciyar ta tai,ta dan dago kai zata fara zubar ta ta, taji sun hai munsharin qarya,dan ta san Lamyah bama ta munshari ko

Please Login or Register in order to submit comment