Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma naga ba kowa ne yake da wannan sunan ba ai, zata zama daban a cikin mata kamar yanda take daban itama," sukan kalle shi da so da qauna a cikin ran su su rungume shi.



Wayar shi ce take ringing a gefen shi, suna parlo suna kallo, miqa hannu yai yace " wake kira da darennan?" Yana dubawa sai yaga no qasar su ce, ea mammaki yake nunawa Ameenee har ta katse, aka sake bugowa, nuna mai tai ya daga yaji waye? Daga wa yai ya amsa, yayan shi ne, da suke uba daya, yake wanar da shi cewar Bappan su ba lafiya kamar zai mutu, yana ta tambayar shi, akwai abinda yake son ya bashi, nan take zuciyar shi tai rauni, dan Allah ya saka mai son yan uwan shi, ba kadan ba, hankalin shi ya tashi matuqa, miqewa yai ya shiga daki ya zauna bakin gado, zuciyar shi ta kasu kashi biyu, wani bangaren ana fada mai ya qi zuwa, dan suma sun yada shi, wani bangaren na ce mai yaje ba komai, yaje domin zumunci kuma domin Allah, beside baida kowa nan , can ne tushen shi, yaje ko yar shi ma ta san iyayen ta da suka guje ta, wata qila ma su daidaita, su so Ameenee, kodan hai fa masu kyakkawar diya da tai, a haka ta isko shi, bata tambaye shi ba, saboda ta kula, gaba daya hankalin shi a tashe yake, zama tai dab da shi ta kwantar da jikin ta a bayan shi, ta jingina da jikin gado, ta kwantar da jikin shi a nata, tana ta shafa qirjin shi da hannun ta daya, dayan kuma tana shafa sumar kanshi, a hankali take kissing din wuyan shi, tana hura ma kunnen shi iska, runtse idon shi yai, tin yana jin zafi a zuciyar shi har yaji ba komai, a hankali ta rada mai kalmar" I love u" da murmushi ya janyo ta ta koma saman shi ya ce " iiyeee ashe dai da gaske ake koyon turancin nan" dariya tai tace" ai dole na koyi duk yaren duniyar nan just to tell u how much i lobe u" daga ta yai sama kamar bbyn roba yana dubawa anya da gaske ita ce, na farko ta samu wani courage, hqr tana iya fadan tana son shi, wanda kullum sai dai shi ya fada, in ya matsa ta fada mai sai dai tace itama haka, sannan ga mamakin yanda har wani slanks take a turancin, " tsaya a ina kk koyi wannan turancin ne" dariya tai kan tai fari tace mai " a wajen Haerbeebee" gyada kai yai yana murmushi, can ya tuno da maganar da akai mai a waya, sai yace mata, " Habibty, ina son in kin aminve zamu tafi Dubai nan da kwana biyar, Bappana ba lafiya, da ni da ke bamu da kowa a Nigeria, domin kowan ki ya kuje ki, ni kuma ina son mu je ko shekara mu samu, saboda yarinyar mu ta san yan uwana duk da rashin son da suke mata, ba a san gawar fari ba, a qalla dai ta je" " Zaujee kar ka damu kan ka da neman yarda ta, ni mallakin ka ce, a qarqashin ikon ka nake, ko me kk so, ni zan kasance mai biyayya da mana fatan alkairi" kissing din ta ya shiga yi dan bai zaci zata yarda ba.



A gidan Mus'ab kuwa duk jikin Aishaa da mus'ab din kanshi yayi sanyi, Ameenullah kam har zazzabi yai saboda jin wannan mummunan labarin, sosai labarin ya rikita shi, hakuri suka bashi, da alkawarin in ya gama secondary zai koma can in har basu dawo ba ya qarasa karatun shi, da kyar suka samu ya daina kuka,ranar da zasu tafi kam, kamar Ameenullah ba zai kai ba, sun so matuqa su tafi da shi, amma suna ganin ba zasui ma Aishaa daidai ba, tinda shi kadai gare ta, haka suka tafi kowa na cike da qunar rabuwa da dan uwan shi.



Sun isa dubai lafiya inda suka nufi gidan shi na asali da yake can, an gyara shi kamar wani babban mai muqami na zuwa, haka Ameenee tai ta mamaki dama mijin da take tare da shi kenan? Yaran shi na dane ta kalla ko wanne fuakar shi cike da annuri, cikin harahen larabci daya daga cikin su yace, bai zaci zasu sake ganin shi ba, ba dan aiken da yake masu ba akai akai sai suce ko ya manta da qasae gaba daya, murmushi kawai yai yace, komai lokaci ne ai, gashi da lokaci yai na dawo, maraba suka qara mai suka bat shi da iyalan shi, kowa kallon Lamyah yake cike da so da qauna, dan ganin kyakkyawar yarinya, mai cike da kuzari.

Bayan sun huta ne sun ci abinci sunyi wanka, sika shirya sai asibitin da aka mashi kwatancen a can aka kwantar da Uncle din nashi, isar su ke da wuya, ya hango yan uwan shi uku maza, kowannen su fuskar nan ba alamar walwala, iya abinda ya zata shine jikin uncle din su ne yai tsanani, abinda bai sani ba shine, baqar fatar matar shi ce basu so gani ba, ga tsarabar yarinya da suka gani, isa yai ya miqa masu hannu dan ya kula ko dan rungumar larabawan nan ma ba samu zai ba a wajen su, da kyar suka bashi hannu, da yatsa dayan su ya nuna mai dakin kama Ameenee yai ta qugu sannan ya karbi Lamyah suka shiga, a kwance suka tadda Uncle din nashi, kamar baya nunfashi,yana jin muryar shi ya bude ido a hankali, miqa mai hannu yai da nufin ya isa gare shi, kama hannun na shi yai, yai kissing, a hankali, a hankali ya mai nunu da qasan pillo din da yake kai, daga shi yai a hankali, ya ya dakko wasu takardu, yana ganin ya karba yai murmushi ya koma ya kwanta, shikenan rai yayi halin shi, cikin kidima ya leqa ya kira Doctor da yan uwan shi kowa ya shiga damuwa da tashin hankalin. Bayan an kai shi komai ya lafa ne yana zaune a daki shi kadai, Ameenee tana can dakin Lamyah tana mata wanka, ita kuma sai rashin ji take, tana tsalle2, dan Lamya ba dai son RAWA ba , gata qarama, amma yanda take son rawa abun na ba iyayen ta mamaki, dan dai in ba a TV ba ba ganin Ameenee tai tana rawa ba, dubawa yai yaga wasu takardu ne na dukiya mai tarin yawa, da wasiqa a ciki,wadda Uncle din shi ke neman gafarar shi akan tauye mai hakkin sa da yai, tin mutuwar iyayen shi, yayi kuka sosai shi daya inda nan take ya tina wata magana da daya daga cikin yan uwan shi ya fada mai, kan cewar, ko yaqi ko yaso sai dukiyar nan ta dawo wajen su, mamakin su yake sosai, amma ya yanke shawarar miqa masu dika, dan a yanzu ma yana da ninkin ta, dan haka ba komai dan ya mallaka masu, da gudu suka shigo Ameenee da Lamyah, in da ta biyo ta da rigar ta a hannu suna ta dariya, sai tayi nesa da ita sai ta tsaya tana rawa tana karya qugu, tana daga hannu sama, in taga Ammiin nata ta kusa amata sai ta diba da gudu, wajen Abiin ta taje ta kwanta tana daria, wurga masu rigar tai ita kuma ta kwanta tana haki, " ga shi nan ku qarata, wannan yarinyar sai an mata addu'a ita kenan rawa, na rasa in da ta ke gani, ina jin zamu daina kallon tashoshin rawa a gidannan," dariya tai tace " A'a. Ammii ina so plsssss" Abiin ta ce yace " Baza a canja maki, tasha ba, duk san da kk kallo kinji, abun da nake son da ke shine, ki zama mai yawan karatu da neman ilimi, kinji, in kina qoqari kika zama yarinyar kirki, to har wajen koyon rawa zan kai ki" Ameenee ce ta kama baki tana girgiza nai kai, dan gaba daya ba ta son wannan bangaren na shi na ba wa yarinyar su duk wani abu da take so mai kyau ko mara kyau, amma tai shiru dan ganin bai dace ta mai magana a gaban yar ta su ba.



Bayan shekara 11 a Dubai da sukai, kullum suna waya da ita da Yah Amee din ta da Momma Aishaa, sai Baaba Mus'ab din ta, cikin da Ameenee ke dauke da shi ya girma sosai, in da yanzu Lamyah mai shekara 16, kowa ya ganta sau daya sai yai saurin sake juyawa dan kallon ta a karo na ba iyaka, tsabar kyau, da shape din da take dauke da shi, ga gashin ta mai tsaho da cika, santsi da baqi, Lamyah ta zama yarinya mai matuqar kyau son kowa qaunar wanda ya rasa, ga ilimi dan tinj ta sauke qur'ani da sauran littafan da mahaifiyar ta ta koya mata, bangaren boko ba a magana, yare uku take ji, Turanci, Larabci, sai hausa, tana son koyon Frence amma Yah Amee yace sai ta koma Niger zai koya mata. A kullum Ameenee na bata labarin dangin ta,kuma tana fada mata babban burin ta bai wuce ta haihu su je wajen dangin ta ta ga iyayen ta maza ba, dan duk da sun yada ta suna da haqqin ta sada zumunta da su, kusan kullum sai ta fadi hakan, hakan ne ya sa Lamyah take matuqar son zuwa Nijeria taje itama taga dangin mahaifiyar ta, taga ya qasar take.



Ameenee ce ke naquda ba kowa a gidan lokacin,gaba daya ta galabaita, kafin mai masu wanki ta zo daukan wanki taji nishin ta, da sauri ta isa, Ameenee ko hanun ta bata iya dagawa, bakin ta ya bushe qaf...........😱
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ ' YAN RAWA πŸ’…πŸΌ




BY HAERMEEBRAERH




*Hey guys, i am so sory for the late update, i have been busy ne wallahi this days, kuma ban jin dadi, amma in komai yai normal zan dawo kamar kullum, ina godiya da damuwa da kuka nuna akan jina shiru da kukai, hakan ya tabbatar man kuna biye dani, and masu tambaya daga farko ina qara baku hakuri dan Allah ku tambaya a group.nasan ko daya ne baza a rasa mai shi dika ba,thank you so very much for the love and care. Me love u xx*



Page: 6





Waya ta dauka ta kira El-mustapha daga yanayin maganar ta, hankalin shi ya gama tashi, ko qarasa sanar da shi.batai ba ya kashe ya taho, da hanzari yaje ya kamota, a take Iya ta fado mai arai, yai tinanin ko gwadawa zai ya karbi haihuwae shima, can kuma da yaji tana jan wani nunfashi, bai san sanda ya dauke ta ba sai asibiti, a hanyar fita suka ci karo ra Lamyah tana dawowa daga makaranta, itama komawa tai tabi bayan shi ta rungume Ammiin ta ya ja su, yana yi yana waigowa yana mata sannu, bata san ina kanta yake ba sam, Lamyah kam tai kuka ta gode Allah, fatan ta bai wuce na Allah ya tashi kafadar Ammiin su ba, a haka suka isa, nan da nan Doctors suka taru akan ta aka fara bata taimakon gaggawa, kiran shi sukai akan ya saka hannu su mata aiki, da hanzari ya saka hannun, bayan sun shiga da iya ne, cikin ikon Allah da taimakon addu'ar da su Lamyah suke ta mata, Allah ya bata iko ta haihu da kanta, amma jini ya tsaya yaqi tsayawa,sai da tai awa daya da wasu mintunan tana zubda jini, da kyar suka tsaida shi, ta haifi yaron ta qato tubarkallah kyakkawa sosai, mai matuqar kama da mahaifin shi, take wata iriyar soyayyae shi ta kama zuciyar Lamyah, tana hawayen murnar samun qani ta rungume shi tana kissing din shi, Ammii da Abii suna murmushin kallon soyayyar data bayyana a fuskar Lamyah, a haka Ameenee ta kwana uku suka sallamo.ta.


A ranar da yaro ya cika kwana bakwai a ranar Lamyah ta dau hotunaj shi ta turawa Yah Amee din ta, ta rubuta mai " Yah Amee ga Mubarak qanin ka, na turo don ka gan shi,"
Yana gama gani ya bata amsa da,
" Woooowww masha Allah, wannan kyakkyawan yaro haka? Allah ya raya mana shi da imani, amma ina fushi dake fa"
" Yah Amee me nai" ta fada tana turo baki kamar yana ganin ta,
" laifin da kk saba yi ne yau ma kk qara,"
Murmushi tai dan tasan me yake nifi
" laifin me?"
" hmmm Lamyahhhh kina son bam wahala, wannan ai abun kunya ne ace ban san fuskar ki ba bayan kin girma, kina nufin dole wai sai kun zo na ganki, ni ina matuqar son ganin yanda qanwata ta koma,"

" ni dai na baka hakuri nafi son na baka mamakin sunan daka saka min na baqaqen mata sirara, kai dai kawai ka sa a idon ka zaka ga macen da baka taba tsammani ba, kuma nasan su Abii bazasu karya promise din da sukai min na hanaka hotuna na ba" ta fada tana mashi gwalo, da dariya irin mai hawayen nan, kawai" Hmmm" ya rubuta mata, sai ya sauka online, kiran shi tai tana bashi hakuri, yace ya haqura, hirar su suka ci gaba, mai qunshe da ma'anonij da su suka barwa kan su sani.


" My queen ni me kedamun ki ne, gaba daya wani irin fari kk kamar mara jini a jiki, ko dai qarin jinin da akai maki bai ba ne?"
" Hum Abiin Ameenullah, lfy ta qalaou, ka daina sa ka damuwa aranka, rayuwa da mutuwa na wajen Allah, kuma duk abinda yai farko zai qarshe, fatana kawai shine ka daure ka ci gaba da mu'amala da mutane yanda kk yi, 'yan uwanka ka ci gaba da kyautata masu, na san ka sune sama da dukiyar ka dan haka koda ka ga zasu so salwantar da ranka akan dukiyar ka ka miqa masu ita dan a Niger da Nigeria ka na da mafiyan su, kullum kasuwancin ka habaka yake, ka kula da yaran nan kamar ina kusa daku, ka......"
" Dakata wai me kk fada ne hak?" Ya fada cikin tashin hankali, da ganin kamar bankwana suke, take ya janyo ta ya rungume ta cikin wani irin runguma mai tsanani, da nuna bege da shauqi, hawayen da suke riqewa ne ya zubo masu kusan a tare, shessheqar kukan ta ne ya qara daga hankalin shi, haka sukai ta kuka ba mai rarrashin wani acikin su, sallamar Lamya ce ta katse masu kukan su, " Assalamu alaikum, na shigo?" Ta fada tana neman izini daga iyayen nata, Ammiii ce tace mata ta shiga, sannan ta shiga, kallon su tai taga gaba daya idon su alamun sunyi kuka, mamaki da tsoro ne ya mamaye ta da hanzari ta isa gare su ta zauna a tsakiyar su ta dora kanta a kafadar Ammii tace" Ammii na me ya same ku? Me akai maku idon ku dika alamar kun yi kuka? Ko baki da lafiya ne har yanz? Dan na kula gaba daya kin yi fari , kuma kin fada?" Kamo ta ta qarayi ta rungume sannan ta manna mata kiss a goshin ta, " Lamyah Haerbeebty, ba abinda ke man ciwo, kawai ina tinanin rayuwa ne, in yau mune wataran ba mune ba, ina roqon ki da ki ji tsoron Allah, ki kare mutuncin ki, kar ki sadaukar da darajar ki ta 'ya mace a banza, ki kamilantar da kan ki ga mijin da zai aure ki, ki kula da dan uwan ki, Allah zai kula da ke kema" cikib kuka sosai Lamya ta qanqame Ammiin ta, Abii ya qara rungume su dika " Ammii me ke damun ki, dan Allah ki fada mana matsalar ki, mu kadai kk da, bakinda wanda ya fimu, wannan maganganun naki na tsorata ni sosai" tashi suka ga tayi zata toilet,cikin kidima Abii yabi bayan ta ya juyo da ita, " Ameenatou me yasa baki fadan jinin nan na zuba haka ba? Me yasa baki sanar dani ba? Ameenatou in wani abu ya same ki bazan yafewa kaina ba, ina tare da ke am......" zamewa tai qasa zata fadi ya riqo ta, Lamyah ko kuka kawai take tana riqe da yar binjilallayir rigat ta da hannu daya dayan ta toshe bakin ta, ta sunkuya hawaye na zuba da gudu, Abii ne ya ce ta bude qofar suje asibiti, kafin ya taka qafar shi sai yaga.......





*dan Allah ku min hakuri da wannan*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAR RAWA πŸ’…πŸΌ




BY HAERMEEBRAERH



*BANI NAI KAINA BA FANS❀ this page is for u guys, i love ur comments, u guys ar awsome, and i love u XX, especially Ramlat Sani, Fateema Abubakar, Haleema Sahad, ina jin dadin comment din ku, dan ku na miqe yanzu na fara wannan page❀*




Page 7:



Har ta zube a wajen, da gudu ya ida taro ta suka fadi qasa, rungume ta yai tsam a jikin shi yana wani irin marayan kuka, sakamakon tabbatar da cewa ba nunfashi a jikin ta, Lamyah ko mutuwar tsaye tai nunfashin ta na fita da sauri da sauri, hawayen ta kamar na yi ruwa an dauke, daga baya ne Abii ya kula da halin da Lamyah take, nan take ya miqe ya daga Ameenee ya kwantar da ita a gadon, ya rufe ta, ya koma jikin Lamyah dan kar ai biyu, jijjigata yai nan danan ta zube a jikin shi, hakuri ya fara bata, yana ta taimake shi kar wani abu ya same ta, bai san ya zai da ran shi ba " Lamyah Haerbeebty pls say something, ki magana kinji, ki koka Ammiin ku ta tafi ta bar ni, ta barku, ta bar Yah Amee din ki, ki koka dan Allah Lamyah" wani kuka ne ya kwace mai mara sauti sai qunar rai, nan take hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta, ta fara kuka, da rarrafe taje ta kwantar da kanta jikin Ammiin ta " Ammii ina son ki, na so ace kin rayu damu, kin kula da Abii da Ni da Mubarak, ga Yah Amee na ya dade bai gan ki ba, a wannan lokacin da muka saka ran Zuwa Nigeria ki hadani da 'yan uwan ki ko bazasu karbe mu ba a wannan lokacin kk tafi kk barmu, Ammii Allah ya fimu son ki,Allah ka gafartawa Ammii na,ka kai rahama da salama kabarinta, Allah kasa ta tashi tana mai makwaftar Rasulullah, Allah ka sauqaqa mata kwanciyar qabari," kukan ta ne ya fara raguwa domin addu'ar da tai ma mahaifiyar ta sai take jin a ranta ta gama nuna mata soyayya, abinda ya rage ta ci gaba da nema mata Rahamar Allah, gefe ta koma ta takure ta hada guiwar ta da kanta tai shiru, Abii n ta na gefe yana matse kwallah, yana ma matat shi addu'a, sai daga baya yai tinanin yi mata duk abinda ya dace, miqewa yai ya fita kamar wanda ya sha abin maye, a haka yai waya ma abokan shi 'yan uwa da duk wanda ya dace sai dai ya ce kar a fadawa Ameenullah, ya fi son ya sanar da shi ga shi shima kuma ga shi, a haka Aishaa da Mus'ab suka fara shirin tahowa, Aisha tai kuka har taji ba dadi, Mus'ab tun yana rarrashin ta shima ya bige da kuka, Ameenullah na Nigeria wajen kasuwancin Abii da yake yi yakan dawo Nijer duk qarshen wata, sai kuma Baban shi ya tafi shima yai wata, wataran kuma suna tafiya tare, in suka je sukan sauka a hotel, har su gama abinda zasui su dawo.
Mubarak ne ke ta tsala kuka, a lokacin har an kai Ammii makwamcin ta na gaskiya,wajen qarfe biyun dare, daga Lamyah har Abii sun rasa yanda zasui, yaqi shiru, Lamyah ce ta koma qasan qado tai ta kuka, yi take tana kumawa, shima Abii sharcr kwalla kawai yake, kukan Mubarak ba qaramin taba zuciyar Lamyah yake ba, wata irin zuciya ce ta shige ta nan take taji wani qwarin guiwar, cewa zata iya kula da qanin ta kamar ita ta haife shi, she is 15 going on 16,kuma Ammii tace a Nigeria ana ma yara 'yan 14 ma su haihu su raini baby so why can't she do it? Fita tai ta damo madara a fida ta karbe shi, ta miqa wa Abii hannu ya bata shi, miqa mata yai yana kallon fuskar ta cike da tausayawa,tina wa yai yanda Aishaa tai tai tai akan su koma Nijer ta kafe ita bazata ba, a bar su anan, har suka koma, duk qiwar Aisha a qalla yasan zata na koyawa Lamyah yanda za ta na kula da qanin ta, bari ya sawa sarautar Allah ido yaga ya zasu qare,
Gani yai ta mai rungumar shan nono,ta saka mai fidar aiko kamar mai jira, nan da nan ya kama,ya dinga tsotsa ba jira, sai da ya shanye tass, sannan ta dora shi a kafadar ta yanda taga Ammii nayi, gyatsa yai sannan ya fara qoqarin bacci, sai me? Ji tai yana wata irin tusa mai qarfi, sai da ta tsorata, daga baya ita da Abii suka bushe da dariya, hannu ta saka a leben ta tace ma Abii " Shhhhhhhssshhh" shima yanda tai yayi, basu ankara ba suka ji Mubarak na kashi, aiko miqawa Abii shi tai, tana riqe hanci, dan dama ita a komai na reno bata son aikin kashi, hannu ya dage yana nuna kan shi, " Me me zan yi?" " wanke mai zakai Abii" ta fada tana daga gira, " Noooo pls u know i can't?" " Yes u can,me zai hana ka ma in the first place? Bayan kai ne Abii ni yayar shi ce kowa yasan ba zan iya ba i am just 15"ta fada tana daga kafada, kada idon shi yai sama yace," Fine" ya karbe shi ya daga shi sama, yai toilet da shi tana gimtsr dariya, juyo wa yai ya kalle ta yana hararar ta ta kama bakin ta tai dif, zuwa yai ya cire mai ya gyara shi,kan ya gama jariri yai baccin shi, rungumo shi yai ya dawo ua kwantar da shi a gadon nan suka kwanta dikan su da asuba ya tashe ta tai sallah ta koma, nan ma Mubarak ya tashi,kan ya shigo dakin ta hada mai madara ta bashi ta jijjiga shi sun koma bacci.

Yau Ameenee ke cika kwana 60 cif da rasuwa, El-mustapha yai niyyar dakko mai reno amma Lamyah ta qi sam, tace in dan gyara kashin da yake ne ya koya mata zata na yi, da wannan zancen ya hakura, dan kuka tai tayi sosai, a haka yai ta bata hakuri sannan tai shiru aka bar zancen, Mubarak yana samun kulawa sosai, wajen Lamyah, dan komai take mai sai taga kamar bata yi, in da Ammii na da rai da zai fi samun kula, ko makaranta ta aje gefe, fatan ta kar qanin ta yai maraici.

Watarana El-mustapha ya fita yaga wata mota na bin shi a baya, yai iya qoqarin shi ya bace ma motar, mamaki ne fal cikin shi, waye kenan? Me ake nema a wajen shi kuma? Take wani tinani ya ziyarce shi, na wayar da daya daga cikin 'yan uwan shi sukai mashi, sun tabbatar mashi da cewar, sun gano dukiyar da Uncle din su ya bashi ba ita kadai bace, ya boye wasu, saboda ko gezau arziqin shi bai ba, ya yi iya bakin qoqarin shi, na yaga ya fahimtar da su cewar shi fa dama wannan kudin baya gaban shi na gado, sannan dukiyar shi ta kasuwancin zannuwa da kayayyakin yadikan da yake siyarwa qasa2 ne ya tara sudan ba qanan kasuwanci yake ba manyan kasuwanci yake, amma inaaa sun tabbatar mai da in bai mallaka masu komai a hannun su ba zai fuskanci hukuncin da bai zata ba daga wajen su, yai rantsuwa ya kuma amma sam sun qi aminta da shi.



Yau suna zaune da Lamyah da ta dan fada sakamakon rashin bacci da kuma gajiyawa na reno, tausayin gudan jinin shi ne ya kama shi, dan ko RAWAR ta ta da ta zama mata farillah

Please Login or Register in order to submit comment