Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR SADIQ Complete Hausa Novel Document by MATAR SADIQ


MATAR SADIQ

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 44261



MATAR SADIQ

Reading Time: 3 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Fatima Xarah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 255.06 kb

File Type: txt

Views: 663+

Download: 621+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [7:21am, 7/30/2016] 鈽凞EENY鈽凷HOMAR鈽�: *Pherty馃懐*

*MATAR SADIQ*馃拺

*Na fertymerh xarah*馃挐

1 to 10

Zaune yake babban gurin hutawarsa na cikin gidansa wnda dama an ware wurin domin hutawa, yar bukka ce gwani shaawa irinta turawa, wurin shirye yake da kujeru na hutawa irin gidajen masu kudi, an shirya wurin da fulawoyi masu kyau da tsada,kallo daya xakayiwa wurin ya nishadantarda kai domin gurin ya tsaru dole yayi dadin hutawa, sojoji ne birjik a wurin kowane dauke da bindigarsa suna gadinsa,

a hankali ya janye jaridar dake hannunsa cikin qosawa da karatunta ya cillar da ita gefe bayan ya tashi lokaci daya duk suka qame hade da sara masa suka bashi hanya ya wuce,

yana tafe suna biye dashi, taku yake irin na qasaitattun maxan nan masuji da mulki da kudi, ynda yake tfy ma abin birgewane sanda ya iso qofar falonsa anan duka sojojin suka ja suka tsaya tare da sara masa, batare daya kulasuba yayi shigewarsa ciki....

xuhura na ganin shigowarsa ta taso da karairaya fuskarta dauke da murmushi ta rungumeshi hade da kai masa kiss a kumatu

welcome my beloved husband,

murmushi yayi hade da rungumota xuwa jikinsa

yace kishirya jibi friday xamuje gida gaida umma acan nakesonyin wk end dina.....

tayi shiru xuciyarta na bugawa abinda ta tsana kenan xiyarar mahaifiyarsa kasancewar bata qaunarta dalili kuwa shine bata haihuwa bugu da qari tana wulaqanta danginsa da nuna fifiko akansu shiyasa ummansa ta tsaneta...

ya tsuramata ido yasan dalilin sauyawar yanayinta duk bai wuce ummansaba, ummansa na matsa masa akan ya qara aure saboda haihuwa as his age 34 ace bayada yaro kuma shekara biyar kenan da aurensu,yana son matarsa sosai saboda auren soyayya sukayi shiyasa yake matuqar tausayinta cikin wani irin yanayi ya kaimata kiss a wuyanta yasan shine weakness dinta ya dago yana kallonta itama shi take kallo idanunta sun sauya

yace meke damun *MATAR SADIQ?*

tayi murmushi cikin qasaita jin ya ambaci abinda takeso kamar ranta wato ace mata matar sadiq,ko a gurin aikinta da wannan sunan ma'aikatan kecin galaba akanta, tariga ta yardarwa xuciyarta tasanya a ranta babu wata sai ita ita kadaice matar sadiq batajin xata jure jin wata na amfani da sunan matar sadiq......

tace ba komai mijina muje nayima tausa naga alamar gajiya a tare dakai.......

Dariya take tana qarawa xuciyarta fal cike da farin ciki batada sauran damuwa ko matsala a rayuwarta tunda tana samun gata a gun mahaifiyarta kasancewar ta taso tasami mahaifinta ya rasu tun tana qanqanuwa,

ta soma jidar kayan datasamu a jiya wurin bikin saukar Al'qurani da akayi masu tana zubawa sirf tana dariya,

ta juyo tana kallon mahaifiyarta

tace momy kinga umma bataxoba kuma bata aikomin gift dina ba,

tace gift din umma daban yake a wurinki ummy,she promise you kuma nasan xata baki inbanda abinki duk wadannan kayan dakika samu basu isheki bane,

ta tunxure bakinta bayan ta jefar da swiss les din dake hannunta wanda faruq(qanin sadiq)ya bata amatsayin kyautarsa ga qanwarsa data sauke da shekara 12 a duniya.

tace momy tor yaushe xnje inda take?

tace gobe xamuje sai ki dauki kayanki da uniform dinki dan acan xn barki kafin na dawo india matsalar qafafuna ta matsamin ummy....

abinka da qurciya sai ta soma murna tanajin dadi batare da ta damu da ciwon mahaifiyarta ba

tace momy sati nawa xnyi acan?
tace bnsaniba ummy duk ynda hali yayi.....

*
Washe garin ranar sukaje inda umma,sojoji biyu ne masu tsare da gidan abinda ta tsana kenan a rayuwarta haka kawai Allah ya sanyamata tsoron soja a xuciyarta ta kuma tsaneshi...

suna isa taje da sauri ta rungume umma da kyar ta cirata sama tana mamaki

tace ummy ta soma nauyi ynxu hajiya nan gaba kadan baxan iya cirata ba,

momy ta sanya dariya bayan ta xauna tace kema dai kin fada ummy ta wuce dauka ynxu,

umma ta sauketa tana kallon ummi data maida hankalinta ga wani qaton hoton sadiq dake manne a falo,yana sanye da farar shadda yayi matuqar kyau sai ta juya tana kallon momy hade da nuna mata pic din sadiq

tace look momy, he is beautiful as u are,(dayake kamanninsa duka na momy ne qanwar mamansa umma,idan bakasan ummansaba baxaka taba cewa ba momy ce ta haifesaba saboda kamaninsu)

umma tace shima yayanki ne sunansa sadiq,yayan faruq ne,koda yabar garinnan baa haifekiba kuma sanda yake xuwanan bakyanan shiyasa baki sanshiba,

tayi murmushi tana kallonta
tace yanada kyau umma ina sonshi

umma ta bude baki lalalala ai wannan ya haifeki ummi ba sa'ar aurenki bane keda nayiwa autana faruq kamenki ko bakyaso kixama matar faruq?

ta girgixa kanta
ni *MATAR SADIQ* ce banason yaya faruq yana da wata mai kyau munje ranar ya kaini tabani chocolate da yawa ko momy,ta fada tana kallon momy

mamaki da tsoro ya dirarwa momy,a shekarun ummy 12yrs bata tsammanin tasan so tasan abinda takeso sai ta kauda xancen da gaggawa hade da cewa kije ki kira talatu ta shigarmiki da trolley ciki,

momy ta juya tana kallon umma
tace Anty ina tsoron faruwar wani abu yau ummi tabani mamaki hrtasan tace tanason wani namiji, ko ina tasan wannan? taya tasan akwai wata dangantaka tsakanin namiji da mace?

umma tace kema da wani batu kike sadiya,kimanta yaran ynxu ballantana irinsu ummi dana bude idanuwa da kallon films bugu da qare kina xuwa da ita qasashe tana ganin ynda abubuwa k wakana,ranar a gabanki kinkaji tana karatun what is marriage?abinda an riga an karantardasu a skul kuma yau da gobe suna ganin ynda mutane k tfyr da rayuwarsu sannan kinji hr faruq k daukanta xuwa inda budurwarshi anan ma xata fahimci abubuwa,ki bar ummy akwai qurciya da yawa a tare da ita inbanda wannan baxata dubi faruk tace tana soba saboda kyawunsa kawai.

momy ta tabe bakinta tace Allah ya kare mana yaranmu, ni gobe xn wuce india xnje su qara dubamin qafafuna hr ynxu sunamin majirya tun wannan accident din damuka samu,bana iya tsayuwar minti biyar xuwa goma

tace tor Allah ya qara sauqi,gashi gobe sadiq xaixo da hatsabibiyar matarshi,inajin haushin kasancewarsa da ita yarinya inbanda iyayi da rashin mutunci bata ajiye komai ba duk ta rabashi da danginsa koda yaushe yana can manne da ita duk ta asircesa...

momy tace nima tunanina kenan babu haihuwa babu komai yakasa nemawa kansa mafita ya laqe mata kamar rai da ajali,rabona dashi tunkafin na haifi ummi kullum sai waya tun ina fushi hrna daina....

mtseww umma taja wani dogon tsaki cike dajin haushi tace wannan karon xnyi maganinsa dole ne nayi masa aure......

SATURDAY, bayan ummi ta wuce islamiya.

A hankali yake saukowa daga.matattakalar jirgin cikin wani irin taku na qasaita kamar bayason saukowa

wankan tarwadane dogo mai tsararren tsayi ma'abocin ingarman jiki,cikakkiyar fuska mai yalwar dara daran idanu da wadatar dogon karan hanci xurrrr

maabocin yalwar girar idanu kwantacce gami da gargasa na gashi a kowanne gaba mai buqatan haka

dogo ne sosai mai nitsatsen taku da ingarman jiki daka ganshi kaga babban mutum as d age of 34

idanuwansa masu sheqi fatar jikinsa shine bayyananen kyawun da Allah ya mishi hasken jikinsa mai nuni da gogayya cikin xurfaffen ilimin boko, dagani babu tambaya daga duba na farko kaga bazamfaren usuli.

xuhura a gefensa ta kwanto ta kafadunsa kamar mai tsoron wani xai amshe mata shi,

basu bata lokaciba suka shiga motocinsu suka bar harabar airport din,

tym din da suka iso harabar gidan xuciyarta na soma bugawa badan komai ba sai dan haduwarta da umma.

*Pherty novels*馃摎
[1:56pm, 7/30/2016] 鈽凞EENY鈽凷HOMAR鈽�: [11:49PM, 6/15/2016] Pherty馃帳馃懐: *MATAR SADIQ*馃拺

*Na fertymerh xarah*馃挐

11 to 20

Sanda suka isa cikin gidan umman na xaune a tsakiyar katafaren falonta, takardune xube a gabanta tana dubawa na campany, idanuwanta sanye da siririn farin glass, sallamarsu ta katse mata rubutun da take amma bata dago xuwa dubansu ba illah ta amsa sallamar a taqaice.

zuhura ta sami wuri ta xauna a takure hade da fadin barka da aiki umma ya gida, kanta a sunkuye har lokacin bata dago ba ta amsa, yayin da sadiq ya xauna kujerar dake fuskantarta

yace mun sameku lfy umma? sai alokacin ta dago manyan idanuwanta ta xuba mishi hade da xare madubin glass dinta

tace inace kaga alamar haka,baka sameni da wata matsala ba.

cikin dakewa da nuna jarumta irinta sa a matsayinsa na babbbn soja mai rank uku a riga

yace haka nake buri a koda yaushe na sameki lfy, ta tabe bakinta bayan ta kauda kallonta garesa tana kallon takardun gabanta

tace munyi dakai xakaxo jiya a friday ko miye dalilinka naqin xuwa sai yau saturday ko umarnine uwargidan taka bata baka bane?

ya juya yana kallon xuhura a raunane data tsurawa umman ido cike da takaici

yace ba haka bane umma,meeting ne ya tsaidani kan sojojin da xaa tura iraq aiki,a matsayina na babba dole ina wurin shiyasa yau nayi sammako nabiyo ta jirgi amma ayimin afuwa umma.

tayi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR SADIQ

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album