Join Our WhatsApp Group

TUBALI Complete Hausa Novel Document by TUBALI


TUBALI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 140485TUBALI

Reading Time: 11 Hours

Added On: 21, May 2023

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09097853276

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 805.58 kb

File Type: txt

Views: 11317+

Download: 10204+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: 11:10 Am

Monday/24/May/2021.


*TUBALI*
PAGE 1
NA

*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*Bismillahi rahmanirahim. Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani rai da lfy da damar fara rubuta wannan littafin nawa mai suna. TUBALI* *Ya Allah ka bani aron rai da lfy da konciyar hankali ka bani ikon rubutashi har ƙarshe bisa, lfy al'farmar Annabi da al'ƙur'ani. Allah kayi min tsari da abin hani, ka tsare min hannuna, tunanina, idanuna, al'ƙalamina, yatsuna, da rubuta wani abu da zai zamewa al'ummar Annabi sharri ko ya zama cutarwa ga tarbiyarmu.*
GEMBU MEMBILA Taraba State.

Wani irin hadari mai masifar ƙarfi da duhu ne, ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila ƙawanya tako wani sashi, gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami.
Yayinda Ya haɗe da duhun dare mai gauraye da duhun damina.
Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu ƙaƙƙautawa, kana kuma wata iriyar iska mai ɗan karen ƙarfi da sanyi ne ke ci gaba da kaɗawa da ƙarfi.

A dai-dai ya irin wannan lokacin kuma gaba ɗaya bani Adam mazauna cikin gidaje, sunyi nisan bacci kasan cewar ƙarfe ɗaya na dare ta gota.

Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske, wanda take nuni da mamalakinta wani ne ko wane, ta faso kai.
Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama.
Ma’ana gudu irin na ceton rai, shiyasa shi kansa bai san irin tuƙin da yakeyi ba.
Gaba ɗaya jikinsa kyarma yakeyi, duk da azabebben sanyin yanayin wurin, da kuma sanyin A/C’n dake cikin motar, amma hakan bai hanashi haɗa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da rayuwar duniya ba.

Tuƙi yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya, haikan-ƙadaran.
Da nufin bi ta kanshi ya takeshi, ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi.

Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa, kana yasa hannunshi ɗaya ya ruggume yaron dake bisa cinyarsa, yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi.
Dai-dai lokacin kuma suka iso, kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaɓan kogin Gembu wanda yake haɗe da kogin. Numan Adamawa. Dadin Kowa Gombe. kana da binuye.
Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya ziz-za.

Wayarshi ya zaro a cikin kiɗima ya fara magana da wanda ya kira ɗin, yana maganar muryarshi na rawa, magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana.
Sun zo gab da Rugar Rumo dake ƙasan hanyar can gefen kwazazzaɓan.
Dai-dai lokacin kuma, tirelar nan ta cim mishi.

Cikin tsananin mugunta ya danna motar da ƙarfi, ya ingizata, cikin ramin dake haɗe da manyan Koguna wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato.

Ji kakeyi k’uuuuuuhhhh, motar ta bada wani irin gigitaccen sauti.
Sai kuma ta ɗan tsaya daga gangarawar sabida karon da tayi da wata bishiya hakan yasa bata faɗa ciki kai tsaye ba.
Da ƙarfi ya kuma matsowa ganin bishiyar ta ƙare ƙaramar motar.
Ingizata yayi ta tafi cikin ramin.
Ji kakeyi fuuuuuuhhh zinɗim! Ta faɗa cikin ruwa.

Wanda sautin faɗawan yasa mafi akasarin mutanen Rugar Rumo farkawa.

Suna al'hini da tausayin sanin duk wanda ya faɗa ciki ya faɗa ƙabarinsa kenan...

Shi kuwa mai tirelar wani irin masifeffen dariya mara daɗin amo, yayi kana ya wuce cikin garin dan babu damar yin kwana a wannan wurin.

Tuƙin yakeyi wayarshi saƙale a kunne shi yana cewa.
"Sir na gama dashi, babushi a duniya.
Yayi ban kwana da duniya yanzu zan wuce cikin Gembu kuma zamuje mu kashe matarsa da yaranshi kab".
Ɗan jim yayi jin yadda Sir ɗin ke dariyar cin nasara tare da cewa.

“kuna kashesu.
Sauran cikon 2 million din ku zai shigo hannunku.”
Cikin zaƙuwa matuk’in tirelan yace.
"Yanzu kuwa".
Kana ya katse kiran, ya nufi cikin Gembu a cikin daren da wannan duhun damunar.


***************


Bayan wasu shekaru A kamar Ashirin da biyu 22.

Kano state.
Shiru hall ɗin taron ma'aikatan tashar Arewa 24 TV dake birnin Kanon Dabo yake, yayinda ma'aikatan ke zaune bisa kyawawan kujerun dake zagaye da babban table mai kujeru sama da hamsin.
Yayinda gaban kowa goran ruwan Faro mai sanyi ne da kuma Nutrimilk sai maltina da chii exotic, baya ga haka kuma glass cheers cups ne a gefe-gefe.
Kana sai abun sautin magana dake gaban kowa, mai ɗan tsawo.
Gefen dama duk manyan ma'aikata ne.
Kana gefen hagu mabiyansa.
Can baya kuma ƙananun ma'aikata.
Babban ogansu ne ke musu bayanin canje-canje tsarin aikin da suke shirin kafawa na forkon shekarar.
Gyara zamanshi yayi tare da kallon gefen damanshi.
Murya ya ɗan gyara tare da cewa.
"Ina mai Shirin baƙon mako?."
Cikin nutsuwa Jannart Idris Saleh Dakata. Ta ɗago kanta cikin tattausan muryarta mai cike da nitsuwa tace.
"I’m here Sir".

Sautin daddad’an muryarta ne kuma yasa, mafi akasarin mutanen dake wajen suka juyo suna kallonta.
Tabbas Nitsuwarta na daya daga cikin dalilan da suka sa aka bata ragamar wannan shirin.
Kasan cewar manyan mutane masu kamala da shahara ake gayyatowa, so ana buƙatar mai nitsuwar da zata martaba musu manyan baƙin su.
Cikin kula. Uban gidan nasu yaci gaba da cewa.
"Shirin baƙon mako, yana da manufa mai girma, ta samo manyan mutane ta tattauna dasu, su sanarwa duniya nasarorin su da kuma irin ƙalubalen da suka fuskanta domin.
Su kasan cewa matasanmu masu tasowa, Maduban gina TUBALIn rayuwarsu ta yadda zata inganta su, tsare kansu da lalatacciyar tarbiya suyi karatun da sana'a domin watan-wata rana su zama abun koyi abun so wa yan baya."
Shiru ya ɗanyi tare da kurɓar ruwan Lemun exotic din dake gabansa.

Ita kuwa Jannart na'urar maganar dake gabanta take ɗan sa fararen yatsunta wanda sukaji red henna tana sama tana ƙasa dasu a hankali.
Yayinda duk saura kuma sukayi shiru.
A nitse yaci gaba da cewa.

"But now I’m sorry to say Jannart, shirin ya raunata sosai. Yananin tsaron da kike ciki yasa bakya sakewa ki samu ki gayyato mana manyan mutane, shahararrun masu nagartan da zasu burge mutane.
Shiyasa shirin yayi rauni mafi akasarin ranaku sai dai aita maimaita program ɗin daya gabata.
Wannan dalilin yasa muka samu umarni daga sama.
Aka bamu zaɓi biyu."

Da sauri Jannart ta lumshe idanunta kana tayi ƙasa da kanta, saboda fahimtar inda kalamanshi suka dosa.
In ta gane ana gab da sallamarta daga aikin. Wanda nanne kaɗai duniyar farin cikin ta, in ta shiga cikine kadai take samun ta sake, tayi raha tajita mai eanci babu Escort, ba Yah Junaidu a kusa.
A hankali tasa yatsarta ta ɗan ƙara saƙala na'urar dake saƙale a kunnenta wanda shike ƙarawa jinta ƙarfi, yadda take ɗan taune lips ɗin ta na ƙasane ya bawa kyakkyawan Dimple ɗin ta damar lotsawa, yayinda jajayen lips din nata suke sheƙi dan lasarsu da ta ɗanyi.
A hankali A'isha Lawal dake gefenta tasa hannunta ta kama nata tana ɗan murzawa alamun bada ƙarfin guiwa.
Salman kuwa dake fuskantar ta, idonshi ya rumtse.
Da sauri ta buɗe idonta jin shugaban nasu yaci gaba da cewa.

“Umarni na forko wannan karon an bamu sunan mutumin da ake son mu gayyato, yazo ayi hira dashi.
Domin shi kadai ne zai ɗaga darajar shiri.
Sai kuma cewa in har bazaki iya samun dama da lokacin sakewa ki nemishi ba, to dole a sauƙeki kan shirin.
A nemo wata ko wani da zasu iya."
Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi kana a hankali cikin tsoron rasa aikinta tace.

“In sha Allah zan iya".
Da sauri ya kalleta.
Kai ta jinjina alaman.
"Yess zan iya".
Kai ya jinjina kana yaci gaba da cewa.
"Sai umarni na karshe, dole a nemishi, ya zama next 2 week's dashi za'ayi hira. Kinga kenan yau saura kwana goma kenan.".
Asiya ce dake masifar son amsar ragamar program ɗin daga hannun Jannart.
Ta gyara zamanta tare da cewa.
"Sir waye ne shi? A ina yake?".
Cikin ɗan ɗaga sauti yace.

*”Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne"*

Da sauri duk suka fara kallon juna, cikin kaɗuwa Aisha Lawal tace.
"Sir Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, shifa..."

Hannunshi ya ɗaga mata tare da cewa.
"Na sani, shi ba mutum ne kamar kowaba, ra'ayin shi da banne.
Ko BBC bata taba samun nasarar yin hira dashi bako!?".
Da sauri kab suka amsa da.
Yess! Yesssss!!".
Ajiyan numfashin ya sauƙe tare da cewa.
"Toh wannan itace nasararmu in har an samoshi.
Zai zama mujallar Arewa ce zata taɓa fidda hirarshi da hoton fuskarshi kana, Arewa 24 TV ce zata taɓa haska fuskarshi da surar jikinshi bayan sunanshi daya zama sananne a Africa baki ɗaya.
Wannan shine zai ƙara ɗaga darajar shirin.
Shin Jannart zaki iya? Ko dai kai tsaye asa Asiya?".
Da sauri Asiya tace.
"Sir Ni zan iya, tunda bani da wani tsaron nuna isar cewa ni ƴar wanice, aikina shine isata".
Mafi akasarin mutanen wurin ido suka zuba mata ganin yadda take mgna tana watsawa Jannart harara.
Ita kuwa Jannart glass din idonta ta gyara tare da ɗagowa jin shugaban nasu na cewa.
"Jannart zaki iya ko dai yanayin tsaron da mafahifinki ke baki bazai barkiba?".
Cikin sanyi da danne fargabarta tace.
"Sir zan iya in Sha Allah. A bani kundin bayaninshi".

Ajiyan zuciya Salman ya sauƙe jin cewa ta amsa zata iya, baya son rasa abokiyar aikinsa sabida yana jin daɗin aiki da ita.
A'isha Lawal kuma ajiyan zuciya ta sauƙe.
Shi kuwa MD’n su, wani file mara girma ya tura gaban Jannart tare da cewa.
"Gashi sai dai babu komai nashi a ciki, sai sunanshi, da sunan Company's ɗinshi, da garuruwan da suke. Da Hospital's ɗinshi. Da kuma foundation ɗin sa, mai suna Mainasara Foundation."

Jin yayi shiru ne yasa ta ɗan kalleshi kana a hankali tace.
"Ba phone number ɗinsane, ba picture dinsa? Ba address ɗin sane?".
MD ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
"Toh Jannart ai da akwai waɗannan abubuwan a ciki, toh da bazaiyi wuyar samuwa ba kuma da bazai zama mutum na musamman ba, kunsa duk abinda yake killace shine special."
Sai kuma ta juyo ta kalli mai kula da shirin nasu dake cewa.
"Babu number sa, ba hotonsa ba adireshinsa. Kana ko akwai number sa, ko sau 1000 zaki kira da layuka 1000 ma-ban-ban-ta bazata shigaba, sabida yana amfani da App ɗin nan da in dai bawai yayi saving number ki a wayarsa bane, kiran bazai taba shigaba.
Kuma koda ya ajiye ya shiga, zaki kira a ƙalla sau goma bazai amsaba, sai dai ace mikin ki ajiye mishi voicemail.
Sabida yawan aiyuka da uzurrukan da mahaifinshi ya ɗaura masa yasa bashi da isashen lokacin kansa ma, da yawan mutane suna matuƙar jinjina masa da mmakin kwazonsa, sabida aiyukan sun mishi yawa, kana matashine a tsakiyar dattijai.
To shiyasa bai cika samun lokacin amsa kiraba.
Sai dai a ajiye mishi saƙo, so nanne zakiji muryarsa, idan abinda ke tafe dake mai mahimmanci ne, kuma kinyi hikimar faɗa mishi number ki to shida kanshi zai kira".

Mafi akasarin su ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe.
Cikin karaya Jannart tace.
"My Aunty to Ina kikaji duk wannan bayanin?".
Dariya Hajia Rabi'ah tayi tare da cewa.
"Jannart yar jaridar gaske wato, tuni har kin fara binciken tun yanzu a kuma kaina".
Murmushi tayi tare da gyaɗa kai.
MD kuma kai ya jinjina sabida gamsuwa da hikimarta da nitsuwarta wurin aikinta.
Cikin girma Hajia Rabi'ah tace.
"Toh gsky nima wurin PA'nsa na samu wannan bayanin.
Ba kuma wurin PA din kai tsaye ba.
Akwai ɗan yayata, abokin ƙanin PA'n nashi ne, so nan naji wannan."

Cikin sauri ta miƙawa Hajia Rabi'ah wayarta tare da cewa.
"Samin number ɗan yayar taki".
Murmushi tayi ta amsa tasa mata number.
Kana tace.
"Sunanshi, Mahmoud".
“To” tace kana ta adana number.

Shi kuwa MD'n gyara zamanshi yayi yaci gaba da tsara musu sauye-sauyen programs ɗin nasu.

Sai kusan ƙarfe shida saura suka tashi a taron.

Suna fitowa, mafi akasari suka kama hanyar parking lot ɗinsu dan daukan ababen hawansu.

Wani irin kallo mai cike da tsana Asiya ke bin Jannart dashi lokacin da suka fito, a take Escort ɗin ta suka miƙe suka mara mata baya.
A hankali ta ɗan juyo jin Aisha Lawal na kiranta.
"Jannart! Jannart!!".
Juyowa tayi tare da bin tsakiyar hanyar da suka buɗa matan.
Da sauri A'isha Lawal ta iso, cikin sanyi tace.
"Zaki iya?."
Cikin jin tsoron rasa aikinta, ya zama dole taita zaman gidan da yafi na kurkuku muni da zafi.
Tace.
"Na'am A'isha zan iya, in sha Allah. In ban iyaba naci gaba da zaman gida, Yah Junaid zai k’arasa kurmatani da marukan da yake yayyarfa min a cikin ko wani mintuna, wurin aikin nan shine duniyata, shine TUBALIn ɗan y’ancina, ya zanyi sakacin rasa aikina".
Cikin rauni da ƙara yin ƙasa da murya Aisha tace.
"Okay Salman yace ince miki in sha Allah zaku iya, kuma zai roƙi a baku cikekken dama, da zai biyoki sai ya tuna waɗannan kattin dake zagaye dake wanda suke shirye da ilkata duk wani na miji in yazo kusa dake".
Kai ta jinnina kana sukayi sai anjima.

Wasu dalla-dallan motoci ne guda, uku.
Ta tsakiya itace a baya.
Ta baya kuma ƴan tsaronta, hakama na gaba.
Tana baya a zaune.
Yayinda driver'n ta ke janta.
A haka suka nufi gida tana mai jin tsoron me zata riska a gida, kasan cewar ta wuce lokacin dawowarta.

Anguwa ce mai zaman kanta Janbulo tsit anguwar ba hargitsi, da hayaniya, da kwata kamar ba cikin kano ba, sabida manya-manyan gidaje ba irin gidajen kanawa mitsi-mitsin nan ba.
A bakin wani tamfatsetsen gida mai ɗan karen girma da kyau, suka tsaya tare da danna hon.
Jiki na rawa mai gadi ya buɗe musu.
Nan suka ratsa cikin gidan.

Suna isa parking space ana kiran sallan magriba.
Wanda yayi dai-dai da fitowar Alhaji Idi Sale Dakata daga cikin gidansa tare da zaratan samari uku Junaid Azeez Abdul a bayanshi.
Da wani mutum wanda suke kama da juna Barrister Kabir Saleh Dakata kaninsa kenan.
Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe fahimtar Yah Azeez zai koma wurin aikinsa dan taga ana sa kayansa a mota, alamun ana idar da salla zasu wuce Airport dashi.
Murmushi Barrister Kabir yayi tare da cewa.
"Masha Allah, Ammina kin dawo kenan".
Da sauri ta matso kusa dashi tare da kaucewa mugun kallon da Yah Junaid ke watsa mata, cikin sanyi tace.
"Eh Abba na dawo, ina Aunty Dija".
Ta k’are mgnar tana kallon fuskar Yah Azeez d’in da yakeyi mata kallon mai cike da tausayawa,
Barrister Kabir kuwa wanda ta kira da Abba Cikin kula da tsananin tausayinta da danne wani abu can ƙasan zuciyarsa yace.
"Suna ciki shiga bari muje masallacin".
Da sauri tace to.
Kana tayi cikin gida su kuma suka nufi masallaci...


*Ethiopia Addis Ababa.*

Wani kyakkyawan matashine mai wani irin tsabtaceccen kyau mai masifar ɗaukar hankali, matashine mai jini a jika.

Wani irin kimtsestsen taku mai cike da nagarta, nitsuwa, kamala, haiba, yakeyi, yana mai...


Read / Download TUBALI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

3 Comments On TUBALI
avatar
khadija-dauda

7 months ago

Reply

Pls inason littafin tubali

avatar
taskar

7 months ago

Reply

Replying to khadija-dauda

ki karanta anan

avatar
fatima-muhammad-8-7

4 months ago

Reply

Pls ina Sauran chapters din tubali naga wanna chapter 30 ya tsaya kuma bai kai kar she ba

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album