Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SANGARTA Complete Hausa Novel Document by SANGARTA


SANGARTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 89651



SANGARTA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Zulaihat Rano ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 468.67 kb

File Type: txt

Views: 1209+

Download: 1262+

Last download: 3 days ago

Description/Story: Compiled By Umar Dalha Funtua.

Copied By Zulyheart Rano

[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

```Wannan page din sadaukarwa ne ga MARYAMERHABDUL (KWAISEH), fatan Alhairi na ke maki a dukkan rayuwar ki, Ubangiji ya kareki daga sharrin makiya da masu yi maki hassada, Wallahi Allah ina kaunarki har cikin raina, Allah ya kara maki basira da kafin k'wak'walwa.

Ina yinki sosai marubuciyar DUHUN DIMINA```😍😍


_*MY BESTY KHADIJAH S MUHAMMAD, HMMMM BA SAI NA FADA MAKI IRIN SON DA NAKE MAKI BA, DON KE DIN SHAIDA CE*_💞

*27*

Wani sansanyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe ido ya buɗe su fes a inda yake, sosai ya ke jin dadi na kewaya duk ilahirin jikinsa a fili ya furta

"Alhamdulillah! Na sauka a kasar haihuwata Nigeria kasar mu ta gado."

Duba ya kai ga agogon da ke manne a hannunsa, in da ya nuna masa karfe biyar harda mintina, sanye yake cikin kananun kaya wanda suka amshi jikinsa, ya yi kyau a ɗan zaman da ya yi na kwanaki bakwai a can, ji ya ke kamar ya yi tsuntsu ya gansa gabanta, babu abin da yake buk'ata a wannan lokaci sai ganin kyakkyawar fuskarta da daddaɗar muryarta, murmushi ya sauke ma kyau a fili ya ce

*I LOVE YOU AMEESHA*

Muryar direban su ne ya sa shi dawowa da hankalinsa sa kan shi, murmushi ya saki tare da fadin

"Har ka iso?"

"Eh! Yallaɓai."

"Madallah! Mu je kawai."

Shigo ya yi cikin motar, sannan direban ya ja, mintina ƙalilan suka isa gidan, a parking space direba ya faka motar sannan ya fita, da sallama ya shiga falon

"Assalamu Alaikum!"

Mummy da ke kai komo tsakanin falo da kicin ta amsa masa

"Wa'alaikumus salam! Barka da isowa NAJEEB."

Murmushi ya saki yana ci gaba da takawa har inda Mummy take, ya ce

"Yawwa Mummy na, *I miss you* ."

" *I miss you too my son*" Mummy ta faɗa cikin jin daɗi.

Zama ya yi akan kujera ya soma gaidata, da kulawa ta amsa tana tambayarsa yadda ya baro garin

"Ka ga kar ka zauna surutu, ga dukkan alamu akwai yunwa a tattare da kai, don haka tashi ka yi wanka sai ka zauna cin abincin."

"Wallahi kamar kinsan na yi missing ɗin abincin ki mai daɗi, bari na fito wanka sai na zauna." Ya yi maganar yana soma tafiya.

"Najeeb! Mummy ta kira sunan sa.

Dawowa ya yi yana faɗin " gani mum."

"Ka bar wankan nan, bari na hada maka kawai ka je da shi gidan ka, tunda yau kwana biyu kenan da aka kai maka amarya kuma ba ka nan."

Kallon Mummy ya yi mamaki kwance a fuskarsa ya ce

"Mummy Ameesha ta tare ne?"

Girgizar kai ta yi ta ce ya zauna, zama ya yi duk jikinsa ya yi sanyi, nusiha Mummy ta fara yi mu mai tsuma jiki

"Kana ji ko Najeeb! Ina so ka yadda da komai na duniya sai da Allah ya tsara shi, ka yadda wani ba zai taɓa auran matar wani ba, haka duk inda ka kai ga son abu matukar ba Alhairi ba ne bazaka taba samunsa ba, ka yadda Ameesha ba matarka ba ce, Rufaida ce matarka ina son ka yi hakuri da canjin da ka samu." Mummy ta dakata tana kallon wani yanayi Najeeb ya shiga, sai ta ga ya saki murmushi ya ce

"Mummy na fahimci inda nusihar ki ta dosa, wallahi na yadda da kaddara kuma insha Allahu ba zan bijirewa ikon Allah ba."

"Yawwa ɗan albarka, Allah ya yi maka albashi ya baka zuri'a dayyaba."

"Amin." Ya amsa cikin ɗan dariya, duk da zuciyarsa tana kuna da rashin Ameesha, sai dai hakan ba zai hana shi kula da Rufaida ba domin kuwa ita ce farkon masoyiyar sa.

"Mummy haɗa min in tafi." Najeeb ya yi maganar yana mik'ewa tsaye.

Tashi Mummy ta yi tare da nufa kicin ɗin, sai da ta haɗa masa komai sannan ta kawo masa, tana faɗin ƙasa Rufaida ta ci abinci da yawa, domin na kulla bata son cin abinci." Da yake tunda aka kai Rufaida kullum sai Mummy ta aika mata da abincin.

"Insha Allahu Mummy zan sanyata."

"Yawwa to ka gaidata, idan ka huta ko zuwa jibi ne sai ka kawo min ita." Don lokaci ɗaya Mummy ta ji son Rufaida, domin dai Allah ya yita da nutsuwa ga kunya.


******

Dr yana fita gida ya nufa, lokacin da ya shiga falon babu kowa, don haka bedroom ɗinsa ya shiga, shirin wanka ya yi cikin sauri sauri, bai wani jima da shiga ba ya fito, shiryawa ya soma yi cikin wasu kananan kaya wanda suka karbi jikinsa, sosai kayan sun yi masa kyau jikinsa yana fitar da wani sansanyar kamshi mai sanya nutsuwa a jikin dan Adam.

Rigar kalar ja ce an yi mata rubutu da kalar golden *Special one* sunan dake manne a jikin rigar kenan, ya yin da wandon kuma baƙi ne, wayoyinsa ya kwasa tare da key ya yi waje, har ga Allah ya manta da wata Aneesa, don burinsa kawai ya yi arba da Ameesha farin cikinsa, motsin da ya ji shi yasa shi saurin waigawa

Gabansa ya yi mummunan faduwa ganin yadda fuskar Aneesa ya kumbura, cikin sassarfa ya k'arasa inda take yana faɗin

"Anee lafiya?" Ya yi maganar yana kai hannu jikinta.

Harara ta watsa masa tare da kaucewa don bata son hannunsa ya sauka jikinta, juyar da kai gefe ta yi ranta yana tafarfasa ji take kamar zuciyarta zata faso waje muryarsa ta kuma shiga kunnenta

"Tambayar ki fa nake yi, ni yanzu bani da yancin taɓa jikinki kenan?"

Da masifa ta kalleshi ta ja tsaki tare da tabe baki ta ce

"Ina ruwan ka da lafiyata, maganar taɓa jiki kuma ai ina ga ka yi sabuwa sai ka je ka ci gaba da taɓa nata na bar mata, yanzun ma wajenta ka nufa ko? Wai don Allah Hamma dama haka kake ko kuwa dai zumudin amarya yasa haka?" Cikin kunar rai ta k'arasa maganar.

Murmushi ya saki ya ce

"Bari na dawo zan baki amsa, amma Please ki daure ki bar kuka haka, ki dubi yadda kika koma fa?

"Ina ruwanka da yadda na koma? Duk yadda na zama ai ina ga ba matsalar ka ba ce ko?"

"To ki daure ki ci abinci, kar ulsa ta kamaki."

"Ba ulsa ce zata kamani ba typoid zaka ce, kaga Hamma bana son *kankamba cirani ba miji a tafi ba ciki a dawo da goyon* ba zan ci ɗinba." A fusace ta dire maganar.

Girgiza kai ya yi cikin takaici da halin Anee, karin maganar ta ta karshe ce ta bashi dariya, har ya kusa yin dariyar sai ya yi saurin kumshe dariyar don kar ya kuma kular da ita sai kawai ya fita, tana ganin ya nufi fita ta ruga ɗaki da gudu bedroom ɗinta tare da sakin wani kukan.

Shi kuma yana fita motarsa ya shiga tare da bata wuta cikin gwaninta da kwarewa yake juya kan motar, har ya isa unguwar su Ameesha, farin ciki ke kwarara zuciyarsa har ya ɗan gana da get din yana hon maigadi ya buɗe masa, shi kuma ya cusa hancin motar cikin gidan yana gaida maigadin.

A parking space ya faka motar ya fito, jingina ya yi tare da harde hannunsa a kirjinsa yana tasbihi ga Allah, a hankali ya zame hannunsa ya zaro wayarsa ya yi dailling Number ɗin ta,

Lokacin wayar tana hannun Meena don ita ke amfani da shi, ganin Number din babu suna sai ta yi kamar kar ta ɗauka, har tana daf da katsewa sannan ta dauka

"Hello."

"Assalamu Alaikum! Dr ya faɗa yana gyara tsayuwa.

Amsawa Meena ta yi tana dan zaro ido jin muryar kamar ta Dr. Maganar sa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta faɗa. "Meena Dr ne gani a cikin gida, ki yi min iso a wajen Ummi."

"To." Meena ta amsa tana nufa bangaren Ummi, a falo ta samu Ummi Ameesha ta yi filo da cinyar Ummi ɗin, zama ta yi kusa da Ummi sannan ta ce

"Ummi Dr ne fa yazo!

Murmushi ta saki tare da shafa kan Ameesha ta ce

"Barkan shi da zuwa, a kawo shi nan bari in koma bedroom ɗina." Ta Kai karshen maganar tana mik'ewa.

Meena ma hannun Meesha ta ja tana fadin

"Mu je ki shirya tarbar Dr ga shi can a harabar gida." Tana maganar ne suna tafiya, suna shiga bedroom din Ameesha, Meena ta fara gyara mata kwalliyar fuskarta, domin bata wani dade da yin wanka ba, ko kayan jikinta bata canza ba domin dai doguwar riga ce baka, wacce ta sha adon duwatsu, sosai rigar
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SANGARTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album