Join Our WhatsApp Group

A DALILIN KA NE Complete Hausa Novel Document by A DALILIN KA NE


A DALILIN KA NE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 53938A DALILIN KA NE

Reading Time: 4 Hours

Added On: 28, Apr 2024

Author: Jamila Sama'ila Yusuf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08130193077

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 326.51 kb

File Type: txt

Views: 449+

Download: 238+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: [1/9, 22:19] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*```Wannan littafin na rabuta domin infadakar kuma in nishadantar da masoyana,Ina make addu'a tare da fatan alkairi arayuwarmu...

_Ba'ayarda wani ko wata suyi imitating din wannan buk ba batare da ixinin mai mallakin shiba,akiyaye...._


*Ina kaunarku tare da fatan Allah yabar qauna😘😘....*


*1-5*Mallam Umar ne yashigo gidanshi cikin farin ciki,hannushi dauke da takarda,cikin sallama yashigo,Mama dake bakin murhu ta'ansa,lokacin ina zaune bisa wata qaramar tabarma ina bakacen masara,nima sallar Baba na'ansa.

Cikin kulawa Mama tace"Mallam lfy naganka cikin farin ciki haka?"

Fuskarshi dauke da fara'a yace"Saratu ai ganinan zuwa ina kke,wani abin arziki yarinyar nan tasamo"


Cikin jin dadi Mama tace"Alhmdllh"

Nida nake bakace,saina saurara ina mamakin mike faruwa?"

Mallam Umar ya'isa ina Mama take yamiqa mata takardar,

Cikin jin dadi mama ta'ansa tace"tou malam nida ba'iya karatu nayi sosae ba,sae kamin bayani yadda zan fahimta"

Malam Umar ya gyara tsayuwa yace"tou albishirin ki"

Mama tace"goro"a hajarce sbd ta kosa taji me ke faruwa,ba mama ba harni Zuhra ji nake kamar intambayi Baba abinda ke faruwa.

Baba yagyara murya yace"zancen karatun Zuhra ne wannan gwamnati tadauka shine yanxu,Alh.kabir ya'aiko inje,da naje shine yyi min bayani"

Mama tace"Alhmdllh,amma Malam muda bamuda komae ya za'ayi mu iyakai Zuhra makaranta?"

Baba yyi murmushin jin dadi yace"saratu,bbu abinda ake buqata daga garemu,gwamnati zatayi komae,Admission ne na jami'ar Amadu Bello dake zariya"

Mama tace"ashe dai maganar da mai girma governor yyi gaskiyane,wlhy malam nayi tinanin irin abin nanne na yan siyasa"

Mama da Baba suka kalleni,ni kuwa babu abinda nake banda hawayen farinci sbd bantaba tinanin zanci gaba da karatu ba sbd iyayena basu da hali Baba bbu abinda yakeyi banda sana'ar wankin huluna,daqer nasamu nagama secondry dina,ranar da mukayi SANFORTH dimmu ne aka gayyaci governor din jihar kano irin qoqarin da nayi shine yace yadauki nauyin karatu na zuwa jami'a.

Mama ce tataso tazauna kusa dani tana lallashi da inyi shiru ae komae nufin Allah ne.


Baba yace"wani hanzari ba guduba saratu,gsky ina tinanin yadda zambar Zuhra tayafi uwa duniya tayi karatu,dukda Alh. Kabir yace komae iyama za'ayi ba'a buqatar ko kobom mu,amma inajin yadda zambar 'yata tatafi,jami'a inda bbu wanda zai sakaka bbu mai hanawa"

Mama tatausasa murya cikin lallashi tace"haba malam muda zamuyima Allah godia dayaba diyarmu wannan damar,kuma ai munsan halin Zuhra munriga munbata tarbiya kuma insha Allahu bazata bamu kunya"

Nida nike kukan farin ciki nada farajin bayani Baba sai nabar kukan,sbd naga murna zata koma ciki,kuma nasan halin Baba sarai yana iya hanawa.

Baba yace"hakane saratu,mutane da dama suna yabon halayyar Zuhra,amma ina tsoron rayuwar duniyar nan,dukda yanzu idan Zuhra tafiddo miji banida abinda zanyi mata aure kasancewarta bamai abun hannu ba"

Mama tace"insha Allah malam bazamu samu matsala ba"

Baba yace"Allah yasa,amma bari inqara shawara game da tafiyar nan uwa duniya tafiya tin daga Kano har Zariya gsky abin da kamar wuya"

Nikuwa naci gaba da kukan naga samu zanga rashi,gashi a dokar gidammu idan babba yana magana yaro bayasa baki.

Baba yafita wurin sana'arshi,ni da mama hankalimmu yatashi,naci gaba da kuka na,mama na lallabata.

Bayan sati biyu da kawo takardar,bbu wata magana daga Baba,ni kuwa kullum kuka nakeyi tin mama na lallabata hartafara yimin fada,itama hankalinta atashe yake.

Mama da taje gidan Alh. Kabir chairman acan take wanke wanke,shikuwa Baba yanayima Alh. Kabir wankin huluna,haka mamana tatari Haj.hadiza da maganar zuwa makaranta ta,mama tabaya lbrin abinda yafaru,Haj.hadiza tace"insha Allah zatayima Alh. magana sbd yyima malam magana yabarni natafi makaranta ta insha Allahu bbu abinda zai faru,gasu Sagir nan dake karatu BUK harsun fara lectures dinsu,sageer dan Alh. Kabir ne tare suka gama secondry da Zuhra saedai shi private school yyi.


Haka Haj.hadiza tayita lallabar mama akan tayi haquri insha Allahu tasan idan Alh.yyi mashi magana zai yadda.

Da mama tadawo gida lokacin ina islamiyar hadda,koda nadawo mama tasanadda ni abinda Haj.hadiza sae nafara tinanin kadadae ace baza'a ansheni ba sbd anfara lectures.

Mama tace min Alh.kabir zaiyi ma Babanki magana akan maganar zuwa karatunki insha Allah munsan zai yadda,nan mama farayiman nasiha akan inji tsoron Allah aduk inda nasamu daina,kuma idan nayi abinda ba daidai ba su za'a zaga,inriqe mutuncin kaina,banida kamarshi,intsaya inyi abinda yakaini.........

*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:19] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION🤝*


```I LUV MY FANS😘😘...```


*5-10*
Haka Mama tayita yimin nasiha kamar yadda tasaba,sannan nashiga nacire uniform dina,nayi sallar magrib.


Bayan kwana biyu,Alh. Kabir yakira Babana,da yaje Alh. Kabir yashiga yi mashi bayani akan karatu yadda zai fahimta,da lallashi da komae haka Alh.kabir yashawo hankalin Baba,harya yadda,Alh.kabir yace"akwai kudin da gwamnati naturo,wanda za'ayi mata provision da dai sauransu,zai aiko da su,upperweek zata tafi makaranta,Baba yace basae anbashi kudin ba duk abinda yadace suyi mani da su,sukayi sallama.


Bayan sallar magrib,Baba yadawo gida lokacin ina zaune tsakar gida bisa tabarma inacin tuwo,cikin sallama yashigo,na'ansa tare da yi mashi sannu da zuwa.

Lokacin mama tana sallah,kasancewar lokacin zafi ne nadauko ma baba tabarma nashinfida mashi yadauna tare da yimashi sannu da zuwa.


Bayan mama tagama sallah,tayi addu'o'inta kamar yadda tasaba,mama tayi mashi sannu da zuwa sannan tagabar mashi da tuwonshi shima,Zuhra tadauki kwanon tuwonta takoma cikin daki.


Kafin Baba yabuda langar tuwon,yafara magana kamar haka yace"Allah yyi Zuhra zata tafi makaranta saedai muyita yimata addu'a,Allah yatsare yakuma bata sa'a.

Mama tace"Alhmdllh,Ameen ya rabbi malam,gsky naji ddi Allah yabada sa'a"


Baba duk yyi mata bayani akan yadda sukayi da Alh.kabir wajen kudin da aka turo na sayayyar makaranta,mama tace"hakan da kayi kayi daidai malam,sbd gwamnati ita ta daurashi akan kudin"

Zuhra tunda taji wannan maganar bbu abinda take sai murna,ta'aje kwanon tuwon sbd ji tayi duk bata iyaci sbd murna,fitowa tayi tayi alwala tayi sallah raka'a biyu tare da addu'ar Allah yatsareta yakuma bata sa'a.


Da taimakon Alh.kabir akayi mata registration sakamokon wani lecturer abokin Alh.kabir daya temaka masu.


Haka Haj.hadiza tasaimata dogayen riguna na shago,atamfofi,lesussuka da mayerials tare da yadin hijabobi,akakai mata dinkuna.


Bayan sati daya,komae yazama ready,mama da Baba kullum sunayi mata nasiha akan tayi abinda yakaita kada tabiyema mutanan banza.

Ranar sunday,Alh.kabir yahadata da driver dinshi yakaita makaranta,har bakin gate din hostel,dayake lecturer din daya temaka masu wurin yin registration shi temaka mata wurin accomodation,da yafito yaturo maka lambar room dinsu.


Da taumakon yara yan dako suka kaimata kayanta har cikin room dinsu,dakine lafiyayye komae tsaf hada carpet aciki tare da toilet da bathroom,gado ne guda ukku sae kayan tea da akajera bisa wani qaramin freezer.

Da sallama tashiga room wasu yammata ne wa'anda bazasu wuce agemate dinta ba,su biyu da ganisu kasan twins ne sbd kamar da sukeyi........


*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:19] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝**10-15*Daya tana zaune bisa kujera hannunta dauke da qaramin kofi tanashan golden morn tadaura Laptop bisa cinyarta tana kallo,dayar kuma tana zaune bisa daya daga cikin gadon hannunta dauke da textbook na chamisry tana karantawa.

Zuhra tayi sallama cikin sakin fuska.

Yammatan dake cikin room din suka ansa cikin fara'a.

Ganin kayan da ake qoqarin shigowa da su,yasa suka fahimci room mate dinsu ce.

Da sauri dayar wadda take bisa gado tasauko,ta tari Zuhra kamar tasanta.

Tace"sis sannu da zuwa,mun dade muna jiran zuwanki wlhy"takama hannun Zuhra suka zauna gefen gado.

Zuhra ta'ansa da yawwa cikin fara'a.

Wadda ta tari Zuhra ita tasallami yaran da suka kawo mata kayanta,dayar kau saibinsu takeyi da kallo.

Wadda ta tari Zuhra tace"i'm Islam Khaleel Adam by name nd my twins sister Iman Khaleel Adam,mu yan kano ne,muna zaune a GRA"

Zuhra tayi murmushi tace"nd i Zuhra Umar Farouq,nima yar kano ce,muna zaune a zaria road"

Nan suka shiga murna ashema garinsu daya,kamar sunsan juna haka Zuhra da Islam sukayita labari,banda Iman da taci gaba da kallonta a laptop,Islam duk bataji dadi ba amma dayake tasan halin sis din tata dole tashareta.

Anan ne suka gano ashe course dinsu daya,BIOCHAM,ita Iman BIOMATH take,nan sukaci gaba da hirarsu.

Iman dakeshan golden morn tace"sis taso musha golden morn"

Islam tace"haba sis ina laifin ki hada mata wani"

Islam tace ma Zuhra"sis kinzo a sa'a muma bamu dade da dawowa daga kaduna ba,bamu dafa abinci ba,kuma daga hostel zuwa restourant da nisa,amma bari nahada maki wani abu"Zuhra tayi murmushi tace"Alhmdllh wlhy banajin yunwa".

Islam tafiddo time table dinta suka shiga dubawa,kamar sunsan juna,dayake su Islam sunyi sati ukku da zuwa yanxu sunsan venue din da sukeyin lectures.


Wayar nokia dinta tashiga ringing,da sauri Zuhra tadauka ganin sunan Baba,nan suka gaisa tate da yima mata sannu da zuwa har suka gaisa da Mama dayake Baban yana gida,suyi tayi mata addu'a har sukayi sallama......


*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:19] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*


*15-20*Islam tana mamakin irin kyau Zuhra sae kace barabiya,ita kuma Iman batada yawan magana ba kamar Islam,dama ita Islam kowa natane gata da wayau shiyasa yayansu yafi ji da ita.

Da marece suka tafi restaurant cin abinci,Islam ce tabiya masu kudin,da suka gamasukadawo hostel kamar dama can sunsaba da juna.


Bayan sallar magriba,Islam tafiddo jotting dinda sukayi Zuhra batanan,Islam tayimata bayani sosae.


Islam tace"dan Allah sis,Zuhra batayi maki kama da Sajeeda Abba?"


Iman tace"nima tinda tazo nake ganin kamarsu"


Zuhra tace"wa cece Sajeeda Abba?"


Iman tace"wata friend dimmu ce da mukayi Turkishi International college a Abuja,amma ita barabiya ce"

Islam tace"dan dae ke kinada dimple ita kuma bata da shi"

Itadae Zuhra batace komae sbd tasaba jin ace tana da kyau.


Da dare yyi Islam da Iman kowa yafiddo Laptop dinshi yana kallo,Zuhra tafiddo textbook dinta na Biology tana dubawa.


Islam tace"sis kizo muyi kallo gobe sae muyi karatu,yakamata ki huta yau kadae"

Dole Zuhra ta'aje littafin tatafi wani film ne zuke kallo mai suna MARLIN.


Washegari ranar monday,kasan cewar su Zuhra suna da lecture 8-10 ta chamistry,su suka fara shiryawa,Iman tahada masu breakfast tea ne tahada masu tare da soyayyen kwai.

Rayuwa kenan da ganin su Islam da Iman kasan 'ya'yan masu kudi ne,sbd yanayin shigar da suke da yadda suke kashe kudi,Allah yabasu kudi gasu da kyau ba farare bane sosae amma suna da kyau,wani ikon Allah sae santin kyauna suke.


Tsaf nagama shirina sanan nadauko hijabi ta tare da liqab nasaka,Islam kai doguwar riga ce red tasaka qirar bahrain sannan tayi rolling da bakin gyale tadauki jika da takalma bakake tasaka kamar zata biki,suna ganin Zuhra tasaka hijabi.

Islam tace"ae dole kirufe wannan kyakykyawar fuskar sbd kada kihada mamu goslow ahanya"


Iman yayi murmushi tace"sis da gaskiyarki wlhy"


Zuhra tace"kodae kuna da abin dariya sosae,yanzu zolayata zakuyi tayi?,bance zaki hada gslow ba sai ni?"

Islam tace"wlhy maganarmu bbu wasa sis"


Hadae suka fita,abakin gate suka hau adaidaita suka tafi venue.

Bayan sungama lecture 8-10,bazasu qarayin wata ba sae11-12,amma mutane da dama bbu wanda yatafi dukda yan course dimmu bamuda yawa sosae.


Mukaje cikin venue muka zauna first seat,ni da Iman munata labarimmu,tare da jajen Iman ko tataho,Islam tace"bari nakirata muji"


Islam tafiddo wayarta kirar Samsung Galaxy,tayi dialling din number din Iman.


Iman ta dauka,Islam tace"kin tahone?"

Iman da wulaqanci wai yanxu zata shiga wanka,Islam tace"ae kinfi kowa sanin halin yaya Rafeeq"sannan takashe wayarta.


Zuhra daga seat din bayansu taji wasu yammata na labarin Dr. Rafeeq.

Dayar tace"Aysha,Allah yaba Dr. Rafeeq komae,amma bayason mutane dan wulaqanci ne"

Wadda aka kira da suna Aysha tace"aeni yayimin daidai wlhy Maryam,sbd idan yyi wasa sae yammatan ABU su lalata shi"


Aysha tace"hakane kuma,amma wlhy maryam son Dr. Rafeeq yakamani"


Maryam tace"ki rufama kanki asiri,wlhy idan gimbiyarshi tajiki kingama yawo"


Zuhra tajuya wurin Islam da takeyi mata magana,Islam tace"sis tinanin me kike?"


Zuhra tace"bbu komae sis,amma yakamata mufiddo textbook dimmu na biology muduba"

Islam tace"hakane sis" suka fiddo textbook dinsu suna karantawa


Tsayawar motar da sukaji,shi yaja hankalin ko wani student yakama kanshi tare da natsuwa,har yashigo cikin venue din kamar bbu kowa.


Yaje gaban whiteboard yatsaya,kamshin tirarenshi mai sa natsuwa shiya dawo da Zuhra cikin hankalin dan tanatso duniyar karatu.


Lokacin da tadago idanuwanta sukayi tozali da kyakykyawan saurayin da ake kira da Dr.Rafeeq Khaleel Adam,sae tafurta ya salam,acikin zuciyarta sbd bata taba ganin kyakykyawan saurayi kamarshi ba.

Ashe dama haka Dr.Rafeeq yake?,dole yammata zasu haukace kansa,amma da ganinshi bashida wasa ga kasaita,cikin harshe turanci yafara lecture,dajin yadda yake silence kasan ba a Nigeria yyi karatu ba..............*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:19] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝**25-30*Zuhra dae batace komae dukda itama tanajin qishi,haka suka tafi office din Aunty hanan.

Wata tsadaddiyar mota ce akayi parking akusa da office dinta,qirar LEXUS LX 2017,baka sae faman daukar ido take dagani sabuwa ce.

Tin akofar office din nike jiyo kamshi yana tashi,cikin sallama suka shiga office din,wata kyakykyawar budurwa ce wadda bazata wuce shekara 25,farace sosae,daganinta yar masu kudice,kuma boko yazauna da kafafuwanshi.

Cikin fara'a ta'ansa, Islam da Iman suka gaisheta cikin harshen turanci,itama ta'ansa.

Zuhra tagaishe da ita,tana yamutsa ta'ansa kamar bataso.

Dama tinda Zuhra tacire niqab dinta,sukayi ido hudu da Aunty hanan,tindaganan take harararta.

Islam talura da irin kallon da Aunty hanan take yima Zuhra duk bataji dadi ba,Iman tabude freeze tadauko robar robar ruwan faro,tadauki daya taba su Islam,amma sukace sunkoshi.

Iman tace"Aunty hanan kinyi kyau sosae wlhy,nasan yaya Rafeeq duk zafin kanshi saeya yaba"

Aunty hanan tayi murmushi tace"yanxu muka gama waya da shi,sae muje mugaishe da shi ko"


Islam tace"Aunty hanan,Mummy tashigo school ne?"

Aunty hanan tace"a'ah ta tafi kano,nasan yanxu tana hanya"

Iman tace"Aunty hanan yau bazakiyi mana lecture ba ne?"

Aunty hanan tace"yau bazan iya lecture ba,nagaji,yau ni nayi driving tindaga kaduna,driver yatafi kai Mummy kano"tadan yamutsa fuska tace"ina kuka samo wannan"tana kallon Zuhra a yamutse.

Islam tabata fuska tace"friend dimmu ce,kuma room mate dimmu"

Aunty hanan tayamutsa fuska sbd ita batason bare tace"ae daman nasan ke keda kwashe kwashe"


Haka suka fito,lecturers sae wani girmamata suke,qaramin gyale tayafa,sannan doguwar rigar dake jikinta tayi tighting dinta sosae,gashin kanta har gadon bayanta bata rufeshi ba.

Bbu nisa sosae office din shiyasa muka tafi aqasa,fuskata bbu liqab nasakashi acikin shouldbag dina,mutane sai kallo na suke bansan me suke kallo ba,da nayi niyyar bazanje ba,amma Islam tanunamin mutafi da idonta.

Tin abakin office din kowa yashiga taitayinshi cikimmu hadda ita naga itama tanatsu sosae.

Sallama sukayi saeda yabamu umarnin shiga sannan muka shiga ciki.Komae ta office din tsaf sae qamshi yakeyi,kanshi bbu hula gashin kanshi sae shinnig yake baki wuluk kamar na larabawa.


Kanshi akan takaddimmu da mukayi test,yanata gyarawa,baidago yakallemu ba saeda akayi kamar minti biyar.

Aunty hanan tasamu kujera tazauna sbd tafara gajiya da tsayuwa,mu kuwa bbu ko motsi sbd tsoron shi.

Saeda yadago fuskarshi,suka shiga gaishe shi cikin harshe turanci ya'ansa.

Wayarshi ake bisa table tashiga ruri,cikin fara'a yadauka,ya gaishe da ita,cikin harshen turanci yake wayar dajin yadda yake wayar da mahaifiyarshi ne kuma naji ya'ambaci sunan Mami,harya fara yi mata shagwaba,sae suka canxa magana sbd da alama sirrice,akan sa ranar aurenshi.

Sae kuma suka koma maganarsu,Islam da Iman,sae yaya Rafeeq yace gasunan sunzo Mami,yaran da basu wani karatu.

Cikinsu Iman da Islam yamurda,sukagama maganarsu sannan yyi mata sallama.


Cikin harshen turanci,Aunty hanan ke tambayarshi maganar miye sukeyi da Mami?.

Baiko bata ansa ba.

Cikin harshen turanci yaya Rafeeq yafara yi masu Islam fada wai atest basuyi komae basu karatu.

Yace"wa cece Zuhra Umar Farouq?,ita dayace taci 8/10 a cikinku"

Islam ta nuna Zuhra bakinta na rawa tace"gatanan"

Dago dara daren idanuwanshi yyi yana kallon Zuhra,sae yace"mata weldone"


Haushi yakama Hanan tace"haba Dr.sumafa suna maida hankali"

Baiyi mata magana ba karo nabiyu.

Sae tafara janshi da surutu,amma bbu wata cikakkiyar ansa daga gareshi idan da sabo...


Read / Download A DALILIN KA NE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album