Join Our WhatsApp Group

AMATULLAH ƳAR UNCLE Complete Hausa Novel Document by AMATULLAH ƳAR UNCLE


AMATULLAH ƳAR UNCLE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16493



AMATULLAH ƳAR UNCLE

Reading Time: 1 Hours

Added On: 16, Sep 2023

Author: Ummu Aisha ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS

Author Phone : 08107640933

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 90.27 kb

File Type: txt

Views: 1111+

Download: 381+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 1&2*

Yanayin garin na Kano yau cike yake da ni'ima, sai iskace mai sanyi take kad'awa a ko ina sakamakon hadarin da ya wuce, kowa ka gani yana harkokinsa cikin farin ciki da walwala.

A cikin unguwar ta Hausawa wata farar mota 'kirar........... ta tsaya 'kofar wani kyakkyawan gida, sau biyu matu'kin motar ya matsa horn mai gadi ya bud'e masu get sai matu'kin motar ya shiga ciki.

Bayan ya samu guri yayi parking wasu matasa ne guda biyu masu kama da juna suka fito, sai dai daga dukkan yanayi d'ayan zai girmi d'aya, babban ri'ke yake da yaro d'an kimanin shekaru biyu a hannunsa.

Daga bayan motar kuma wata mace ce ta fito sai wata 'yar budurwa da ba zata wuce shekaru sha biyar zuwa sha shida ba, sai wasu yara mace da namiji da suka fito duk daga bayan motar.

Cikin d'oki wannan 'yar budurwa tayi hanyar cikin gidan da sauri, d'aya a cikin mazan nan yana mata magana "ke Amatullah wa zaki bari da d'iban kayan" amma ina ko sauraronsa bata yi ba ta shigewarya cikin ginin gidan ta barsu a wurin.

Bayan shigewarta ne babban ya dube shi tare da cewa "ai kaima kasan Amatullah da Hajiya, yadda take d'okin ganin tan nan ban ce ta ji abinda kake cewa bama."

Murmushi kawai ya yi yace "barni da ita kawai Yaya, ai zan shiga gidan na same ta ne."

Daga haka ya zagaya ya bud'e booth ya fito da babban trolly da kuma 'karama, dole shine ya d'auki babban matar kuma ta d'auki 'karamin suka shiga cikin gidan gaba d'aya.

Ita kam Amatullah tana shiga cikin gidan da gudu ta nufi dattijuwar matar da ke zaune kan d'aya daga cikin kujerun da aka 'kawata parlour'n da su ta fad'a jikinta tana cewa "nayi kewarki Hajiyanmu."

Cikin fara'a dattijuwar tasa hannu tana 'ko'karinta ture ta daga jikinta tare da cewa "shiyasa kike 'ko'karinta karyani ki sa 'ya'yana garari, tashi min daga jiki ke da bakya girma."

Gyara kwanciya Amatullah tayi tana cewa "wata nawa ban hau cinyarki ba, kawai ki barni na more."

Sallamar da akayi a ba'kin 'kofar parlour'n ne yasa Hajiya ba ta ce komai ba ta mayar da hankalinta ga masu shigowa fuskarta d'auke da fara'a tana yi musu sannu da zuwa.

Haidar da ya shigo daga ''karshe ya hango yadda Amatullah tayi d'are-d'are a cinyar Hajiya, ai kuwa ya zabga mata harara tare da cewa tashi daga jikinta kafin ranki ya 6aci, uwar 'yan son jiki baki da aiki sai na zama a jikin mutane."

Zum6aro baki tayi yayin da Hajiya tace "to kai ina ruwanka? Jikinka ta hau ko nawa?

Ai kuwa nan Uncle Bashir da ke zaune shida Aunty Habiba suka sa dariya "Uncle yace kai matsalarka kenan Haidar baka gani ka 'kyale sai ka tanka, ka san dai ba'a shiga tsakanin Hajiya da Amatullah, duk wanda ya shiga kuwa shi zai ji kunya."

'Kara had'e fuska yayi yace "ai dama kai da Hajiya ba kwa son laifin Amatullah duk abinda tayi bakwa so a kwa6e ta, shiyasa takewa mutane sangartar da ta ga dama.

Gaba d'ayansu dariya su kai, ganin yadda yayi da fuska kamar 'karamin yaro.

Suna cikin gaisawa ne me aikin Hajiya ta fara shigo da abinci, abinda zai baka tabbacin dama an san da zuwansu.

Zuruf Amatullah tayi ta mi'ke ta isa gaban warmers d'in ta fara bubbud'ewa don ganin abinda ke ciki, ai kuwa tana ganin alkubus fuskarta ta cika da farin ciki da fara'a, tace "yauwa Hajiyata shiyasa nake yinki."

Nan take ta d'auki plate ta fara serving d'in Uncle Bash, ta kai gabansa ta ajje sannan ta zubawa Aunty nata, sai ta zubawa sauran yaran.

Ta mayar da kallonta gurin Haidar tare da cewa "Uncle Haidar a zuba maka?"

Harara ya zabga mata tare da cewa "a'a karki zuba, tunda kinyo guzirin abincin ne kin taho da shi."

Hajiya tace "wai me yasa kai ba'a yi maka gwaninta ne? Yanzu daga tambaya sai ya zama laifi? Ai sanin tsurfarka tayi, yanzu idan ta zuba ma in baka ga dama ba cewa zakai baka saka ta ba.

Ita dai Amatullah bata 'kara magana ba ta zuba masa abincin ta kai gabansa ta ajje, sannan ta d'ebi dai-dai wanda ta san zata iya ci ta zauna a gefe ta fara ci.

Bayan kowa ya gama cin abincin ta tattare kwanukan da su kai amfani da su, ta mayar kitchen, tana dawowa parlour'n ana kiran sallar la'asar wannan yasa mazan mi'kewa suka fita don yin alwala su tafi masallaci, su kuma matan kowacce ta nemi inda zatai alwala don gabatar da tata sallar.


*Ummu Aisha*
[8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 3&4*

Tun bayan da suka fita babu wanda ya dawo cikin gidan sai dai jin 'karar motarsu su kai, alamun dai dake nuna sun bar gidan, su kuwa su Amatullah kowacce parlour ta dawo har Hajiya, nan suka zauna ana ta hirar yaushe gamo, sai labari suke bawa Hajiya.

Wajen biyar da rabi na yamma Hajiya ta d'auko mukullai ta bawa Amatullah tace su je ita da Baba Mairo (wato mai aikin Hajiya) su share gidansu, ba sai an jima sun koma a tsaya sharewa ba.

Babu musu Amatullah ta kar6i mukullin, ta jira Baba Mairo suka fita, Muhammad 'karamin yaron Aunty Habiba sai rigima yake zai bi ta, ita kuma tace "babu in da zanje da kai, haka kawai ka hana ni aiki da 'kiriniyarka.

Gidan da suka shiga a Jere suke da gidan Hajiya, sai dai shi a rufe yake saboda babu kowa a gidan.

Duk da ba wani dad'ewa sosai sukai da barin garin ba, amma sun sami gidan yayi 'Kura sosai, kasancewar babu kowa a gidan, sun sha aiki sosai don sai da sukai sallar magriba sannan suka gama komai, suka rufe gidan suka koma gidan Hajiya.

Bayan sallar isha Alhaji Babba suka shigo gidan yana kan gaba, yayinda matsan 'ya'yan nasa ke biye da shi a baya.

Kai tsaye parlour'nsa ya wuce, ai kuwa da sauri Amatullah ta mi'ke zata bishi, sai Haidar ya kama harararta tare da cewa " Allah yasa naga 'kafarki a parlour'n Alhaji ki ga yadda zamu yi da ke, daga dawowarsa ba zaki bari ya huta ba zaki je ki takura masa."

Hajiya da ke fitowa daga d'aki tace "wai Haidar ina ruwanka da takwarata ne? Ka d'aurawa yarinyar nan zani da tsanani a gidan nan fa, wallahi za mu sa 'kafar wando d'aya da kai."

Aunty Habiba da ke zaune tana sauraronsa tace "ina ganin kishi yake ta zo zata tare masa fada tunda shine auta, yanzu kuma zata 'kwace duk kulawar da kuke bashi ku mayar kan......."

Kafin ta 'karasa ya katseta tare ta da cewa ashe kin gane inda matsalar take, idan yarinyar nan ta zo daga Hajiya har Alhaji mantawa suke da ni, komai sai dai kiji sun ce ita."

Bashir da har ya kai hannunsa jikin 'kofa zai bud'e yana son zuwa parlour'n Alhaji don su gaisa ya juyo ya ce "amma dai kai anyi babban banza mai kishi da 'yarsa."

Hajiya ce ta cewa Amatullah "kinga takwarata tashi ki je ku gaisa da Alhaji tun kafin ya fara cigiyarki."

Ai kuwa da sauri ta mi'ke don dama kad'an take jira.

Tana shiga bata zauna ko ina ba sai gefensa, sannan ta gaida shi, shima cikin sakin fuska ya amsa mata, abinda ke nuna akwai 'kauna da sha'kuwa tsakaninta da shi, nan yake tambayarta karatunta, ta bashi amsa da "Alhamdulillah."

Can ta d'anyi 'kasa da murya yadda Uncle Bash dake zaune a parlour'n ba zai ji abinda take cewa ba tana magana, dattijon ya d'ago kai yana kallonta sai kuma yasa hannu ya dungure mata kai, "ai dama nasan aikin kenan, tun da Kura ta zo, wai Sa'adatu yaushe ne zaki daina kwad'ayi?"

'Bata fuska tayi kamar mai son yin kuka, cikin muryar shagwa6a tace "ni dai ka daina ce min kura."

Shima ya bata amsa da cewa "sai ki daina zuwa cinye min kilishi."

A hankali tace "ni dai don Allah ka bani."

Hannunsa ya nuna mata zuwa inda yake ajje a cikin wani bocket mai kyau, ta tashi taje gurin ta bud'e d'an bocket d'in, tana bud'ewa ta ware takardar da kilishin ke ciki ta d'ebi son ranta, sannan tayi godiya ta fita fuskarta d'auke da farin ciki.

Tana fita parlour Hajiya ta ganta ri'ke da kilishi tace yauwa kurar Alhaji ta zo, yanzu zaki fara cinye masa kilishi, da sauri ta nufi hanyar d'akin Hajiya, ganin yadda Uncle Haidar dake waya yana hararar plate d'in hannunta, don ta tabbatar idan ya gama wayar tana nan sai ya kwashe kusan rabi, tunda dama haka suke da shi, kuma tayi magana yace zai d'auki mataki a kanta tun da shi 'kanin babanta ne.

Tana shiga d'akin ta samu guri ta 6oye abinta, sannan ta zauna tana cin kad'an da ta rage, ai kuwa bata dad'e ba saiga Muhibba ta shigo kiranta wai ta zo su tafi gida, sauran wanda yake hannunta bawa Muhibbar suka fito tare.

Idon Uncle Haidar a kanta, cikin had'e fuska yace 'ke d'aukko min plate d'in da kika fito da shi daga d'akin Alhaji."

Tace "na cinye fa Uncle, kad'an na d'ebo dama."

Ya 'kara had'e fuska tare da cewa "wai yaushe na fara wasa da ke?"

Muhibba da ke cinye guntun kilshin hannunta tace "Allah Uncle ta cinye, ka ga ni taba wa sauran ma, dole babu yadda zaiyi ya ha'kura, Hajiya dake sauraronsa tace " kai dai Haidar zanga ranar da zaka girma, idan so kake kaje da kanka ka kar6a mana, amma sai dai idan yarinya ta kar6o ka 'kwace mata."

Shiru yayi baiyi magana ba, nan su Amatullah suka tattara gabad'ayansu suka tafi gida tare da yiwa Hajiya sallama.
Suna zuwa gidan wanka aka yiwa yaran tun da gidan a gyare yake babu inda ba'a gyara ba, sai aka shiryasu cikin kayan barci, Baba Mairo ta kawo abincin da dare nan aka bawa yaran suka ci, sannan suka kwanta saboda gajiyar hanya.

Zuwa 'karfe tara da rabi kowa ya kwanta yayi barci kamar babu kowa a gidan,sai iya Aunty da Amatullah kawai da suka zauna a parlour suna hira, shigowar Uncle Bashir ne yasa Amatullah yi musu sai da safe ta shiga d'aki, sai da ta fara yin shafa'i da wuturi sannan tayi addu'o'in kwanciya barci ta kwanta.


___________________________________________________________


Washegari tun da asuba da suka tashi sukai sallah kowa ya koma ya kwanta, amma banda Amatullah, don bayan ta idar da sallah sai ta zauna karatun Qur'ani, kafin ta kammala zuwa lokacin gari yayi gaske sosai, sannan tayi addu'o'inta da azkhar, ta fito parlour ta fara gyarawa, sai da ta share tayi mopping, ta d'auko bunner ta saka turaren wuta sannan ta koma d'aki.

Nan ma bata zauna ba, toilet ta shiga ta wanke tas, tana fitowa Aunty Habiba na shigowa d'akin cikin kwalliya, abinda ke nuna alama ta dad'e da tashi daga barci itama.

Fuskarta d'auke da murmushi tace "Amatullah sarkin aiki, yanzu ko hutawa ba zaki zauna kiyi ba, saboda gajiyar hanya? Da sassafen nan mutum ya tashi ya kama aiki kamar engine."

Amatullah tace "kai Aunty, wai ina aikin yake ne?, kuma nifa wallahi bana jin gajiya, tafiyar da ba' a mota muka yita ba."

"Ai shikenan, ke dai ba kya son zama haka amma dai ya kamata ace kin d'an kwanta tun da kin san zai yi wahala ki samu damar hutawa idan ba dare ne yayi ba."
Aunty da kanta ta tashi yaran tayi musu wanka, ita kuma Amatullah ta shirya su, sai Muhibba kawai da tayi da kanta, sannan Amatullah ta shiga daga 'karshe, kafin ta fito har Muhibba ta gama gyara d'akin yayi fes kamar babu wanda ya kwana a ciki.

Itama shiryawa tayi cikin dogur rigar shadda, d'in kin ya zauna a jikinta, ba 'karamin kyau tayi ba, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin 'kamshi, ban da 'kamshi babu abinda take.

Tare suka fito parlour da Muhibba da take zaman jiranta, suna fitowa suka gaida Uncle dake zaune a kujera da kofin tea a gabansa, don Uncle Bashir mutum ne da baya wasa da cikinsa indai akan abinci ne.

Kai tsaye dining suka nufa, inda suka gano Aunty da sauran yaran a zaune suna karyawa, suma suka sami guri suka zauna, kowacce ta zuba abinci suka fara ci.

Bayan sun gama sai da suka kwashe komai suka wanke, sannan suka fara shirin barin gidan, don zuwa gidansu Aunty Habiba, ita kuma Amatullah zata je gidansu itama.



*Ummu Aisha*
[8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 5&6*


A 'kofar gidansu Aunty Habiba da ke unguwar tudun yola ya tsaida motarsa, gabad'aya yaran da d'oki suka shiga gidan, sai iya Muhammad ne kawai Aunty ta ri'kewa hannu suka shiga tare Bashir na biye da ita a baya.

Su Amatullah suna shiga gidan suka sami Umma mahaifiyar Aunty tsaye a tsakar gida tana bawa almajirinta kud'in cefanen da zata aike shi, da gudu Muhibba ta je ta rungume ta tana murnar ganinta.

Itama nan take fuskarta ta cika da farin cikin ganinsu cikin 'koshin lafiya, tare suka juya zuwa d'akinta da ya kasance ciki da falo, a parlour'n suka zauna kan carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin tsaf dashi, kasancewar Umma mace ce mai tsananin tsafta.

Suna cikin gaisawa da Amatullah su Aunty suka shigo bakinsu d'auke da sallama, dukkansu guri suka samu suka zauna, sannan Uncle ya gaida surukar tasa cike da girmamawa.

Bayan...


Read / Download AMATULLAH ƳAR UNCLE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album