Join Our WhatsApp Group

FIRST RAMADAN WITH HABIBI Complete Hausa Novel Document by FIRST RAMADAN WITH HABIBI


FIRST RAMADAN WITH HABIBI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36822



FIRST RAMADAN WITH HABIBI

Reading Time: 3 Hours

Added On: 08, May 2023

Author: Faridat Husein Mshelia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 186.45 kb

File Type: txt

Views: 801+

Download: 410+

Last download: 3 days ago

Description/Story: FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
  💔Heart touching story.💔




https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS


FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

TSARABAR RAMADAN.
*Manzon Allah (SAW) Yace:*
*“Dukkan aikin da ɗan Adam yayi to nashi ne, Duk aikin lada yana da guda goma makamancin sa, har zuwa a ninka masa sau ɗari bakwai. Sai Allah maɗaukakin Sarki yace: Banda Azumi domin shi na wane, kuma ni ne zan saka akansa. Shi mai Azumi ya kame daga Sha’awarsa, da abinci, da abin sha saboda Ni.*

LAMBA NA ƊAYA .
Baccin kirki ya gagara ɗaukata saboda cike na ke da zakwaɗi da mararin shirya ma Habibina girke-girken alfarma wanda na cika wayata da su,wasu na samo su ne daga Tiktok wasu daga group ɗinmu na Whatsapp wasu kuma na cirosu ne daga shafin manyan chef da ke Facebook dan haka sam na gagara sukuni babban burina yamma ta yi in shige cikin kicin saboda wannan shine farkon azumi da zan yi a gidan HABIBI(FIRST RAMADAN WITH HABIBI).
Duk na ji zaman ya isheni minti-minti nake duba agogo amma sai in ga kamar an rage ma lokacin gudu dan haka na janyo wayata na shiga cikin group ɗin mu na sababbin Amaren da suka yi aure daf da Ramadan,nan take aka goge min hadda saboda hango bidiyon da takwarorina Amaren group ɗin suke turowa na yanke-yanken da suka fara gabatarwa dan haka na zabura na miƙe na shige kicin,dankwalin turawa na ɗibo cikin faranti na fara fera wanda ya ɗaukeni fin awa ɗaya,ina kammalawa na janyo kabeji,karas,koren wake,kokumba na goge na gogewa na yanka na yankawa na sashi a freezer,wake na ɗebo rabin Mudu na hau surfe na wanke shi tsaf na sa a firinji,kafin na fara kokawar haɗa jus,ina kammalawa na ɗebo gyaɗan da Momi ta niƙa min na zuba farar shinkafa akai na yi blending na shi,kafin na dawo gurin Naman sa da kifi na ciri kaza 4 na fara aikinta,duk aikin nan da nake yi Inna kammala guda 1 ina yin video in tura group ɗin mu na FIRST RAMADAN gudun kar a yi bani ko kuma a ga gazawata dan duk  yawancinmu classmate ne mun san juna.

Jin ana kiran Sallan azahar ya sa na tsagaita da aikin na je na sauke farali,ji na yi duk jikina ya yi sanyi kasala na shirin rufeni amma haka na yi ƙarfin hali na shiga cikin kicin na fara aikina,dafa wannan,sauke wancan,soya wannan sai da ya ɗauke Ni fin awa 5 ina aikin dan hatta gyaran gida sai da ana gab da ƙiran magrib sannan na kimtsa falona tare da jera kuloli bila adadin banda Flask da lemummukan da na yi ma HABIBI,turare na sa na wuta , a gaggauce na faɗa bayi na watsa ruwa na fito ban bi ta kan kicin ba dan ba zan iya gyara shi ba a wannan lokacin ga himilin wanke-wanken dana tara dan kusan rabin tukwane na na yi amfani da su bayan ribobi,blender da na yi aiki dasu ban wanke ba.

Riga kawai na zura da Hijab na fara rama Sallan la'asar wanda ban samu na yi ba saboda aiki,ina idarwa na gyagygyara jikina kafin na shiga cikin Ƙayataccen Falonmu wanda abokan mijina suka yi ma ƙawanya,gaisawa muka yi cikin raha da barkwanci bakin su fal murnan yau za su kwashi ganima,na kai dubina kan HABIBI wanda yake jin kan shi a kumbure irin shima Allah ya kawo shi lokaci ya zama magidanci,murmushi na sakar mi shi mai sanyi shima ya maido min da tashi kafin na shiga Serving na su cike da son burgewa,Kunun gyaɗa mai kwakwa na fara zuba musu tare da madara wanda na kusa juye gwangwani ɗaya,sai alalen da yaji hanta da ƙwai tare da source ɗin naman rago a gefe,irish ball tare da wainan ƙwai a gefe guda,sai irian rice wacce ta ji kayan lambu tuttura musu gabansu ƙamshi duk ya cika musu ciki har wani tanɗe baki suke yi dan girkin ya sha spices,dakatawa na yi da zuba farfesun kifin jin sannu da aikin da suke min ya yi yawa sai gasashshiyar kaza da na mata gashin tukunya ganin suna ta godiya sai na sa juice ɗin karas na ajiye ma kowa a gaban shi nima na janyo kujera na zauna tare da ɗiban kunun gyaɗan ɗan kaɗan na ƙarasa juye madarar gwangwani,ƙasa-ƙasa na ga HABIBI ya kalleni tare da aiko min da saƙon harara,a cikin zuciyarsa kuwa yana jin kamar ya jawoni ya lakaɗa min dukan tsiya dan shi sai yau ya tabbatar da mahaukaciya ya auro ba mai hankali ba banda haka ina mai hankali zai aikata irin abin da(DIYAN SHi)ta aikata,ta soye rabin kiret na ƙwan da ya siyo a ƙiyasin shi,ta juye gwangwanin madarar gari a rana guda wanda yana ganin zai kai musu rabin azumi tunda yanzu kowa ya san halin da ake ciki a ƙasar nan,kifi,kaji,namomi duk ta dafe shi a lokaci guda babban takaicin shi ko mutane goma ya ƙaro za su ci abincin har ya rage wai me ta aikata haka ne?ina hankalinta ya tafi ne har ta yi wannan ɗanyen aikin?


Ji ya yi abincin duk ya fice masa a rai dan HABIBI riƙaƙken Kwamared ne wanda ke da dokoki da ka'idodi a matsayin shi na cikakken ɗan boko mai degree har biyu amma har yanzu ba takamammen aiki,

Ashe da sauran rina a kaba dan yana kurɓan kunu ya yi saurin fito da shi jin wani irin TSAMI da ya ziyarci harshen shi da sauri ya ɗibi Irish balls ɗin nan ya kai bakin shi sai dai jin wani irin zaƙin maggi,da gafin kori da ya baƙunce shi yasa ya miƙe a guje ya fice daga Falon da sauri DIYAN HABIBI ta mara mi shi baya sai dai tana tunkaro shi ya yi saurin hankaɗeta ya yi waje da mugun sauri gudun kar abokanan shi su ci wannan kwaɓar dan ya san ya riga da ya gama kunyata a idonsu sai dai ko kafin ya isa aikin gama ya gama,ba bu abinda ba su ɗanɗana ba dan haka marasa hakurin cikinsu har sun miƙe a gaggauce tare da shigewa cikin motocinsu dan yunwa na ƙwaƙwularsu masu hakurin ne kawai su biyu suka rage da shan lemo da abarban da suka shigo da su,takaici tare da baƙin ciki yasa ya ji kamar ya kashe DIYAN SHi  yau dan ta yi matuƙar ja masa abin kunya a cikin abokai dan haka ya tasota a gaba a kan dole sai ta cinye duk abinda ta girka bayan ya sallami sauran, ganin yanda yake huci ya sa ta ranta ana kare sai gidansu dan bai da nisa a tsakani.
Regegeniyar tambayarta lafiya aka fara tsakanin Amminta da Abynta aka yi, kuka ta ke tana ƙarawa ta gagara furta uffan,ganin yanda take ƙiran sunan HABIBI a firgice ya sa Mahaifinta kama hannunta ya maidata cikin gidanta,jan hannunshi take har suka iso falonta nan ta tadda HABIBI yana kuka dafe da kumatun shi biyu, ganin asarar data tafka mi shi (Yo abin ku da kwamared iyayen tsumulmula da tsumi da tanadi),tun kafin Abynta ya ce uffan HABIBI ya miƙe yana nunota da hannu cikin rufewar ido dan ko ganin sirikin na shi ne yi ba ya ce"Ni kika kunyata DIYAH(DEAR)a gaban abokanaina?,ji yanda kika almubbazzarantar da kayan abinci dana maƙulashe fisabilillahi to na yanke hukunci ba zaki ƙara soya ko da dankwalin Hausa ba a gidannan har azumi ya ƙare,zan auno masara da kuka da kuɓewa shi ne abincin da zaki dinga ci har sai Ramadan ya wuce"



Kuka ta fashe da shi tana ce wa"Dan Allah Abi ka bashi haƙuri Ni ban san mena yi ba."

Nuna mata dinning Area Abyn ya yi ya ce"je ki ci abincin da kika dafa"dan tunda ya ga HABIBI na kuka a gaban manyan kololi ya san kwanan zancen,

Cike da ƙarfin gwiywa ta isa ta fara kai kofin kunun bakinta ta ji tsami ya buwayi bakinta dan haka ta furzo shi,ja da baya ta fara yi cikin tsare gida Abyn ya umurce ta ta buɗe kowanne kula ta ji, cikin ɓata fuska ta ke taɓa kowanne daga wanda tsami yayi yawa,sai wanda yaji ko suga ko barkono ya yi yawa nan da nan ta fashe da kuka dan tabbas da ace ta yi koyi da mahaifiyarta bata biye ma Ramadan time table na social media ba da bata shiga cikin chakwakiyar ba dan tabbas ita ɗin gwana ce gurin girki,

Ƙawayenta na group ɗin FIRST RAMADAN WITH HABIBI sun cuceta duniya da ƙiyama ko kafin ta ce uffan Abynta ya juya bayan ya jinjina ma sirikin shi akan hukuncin da ya ɗauka.



Labarin gajere ne na rubuta shi ne saboda faɗakarwa akan Amare masu biye kawayen social media idan kuna buƙatar cigaba in ga comments.





Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS



FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).




TSARABAR RAMADAN.
  Manzon Allah (SAW)
Ya kasance yana yin buɗa baki da ɗanyen dabino kafin yayi Sallah, idan bai sami ɗanyen dabinon ba sai ya yi da busasshe, idan kuma bai sami busasshen ba sai ya ɗan kurɓi ruwa”.
[Tirmizi].




LAMBA NA BIYU.
A tunzure HABIBI ya mara ma sirikin shi  baya ya fice zuwa Masallaci domin gabatar da sallan Ishsha,ana idarwa aka kabbara sallan Asham jin yanda idon shi ke rufewa tsabar yunwa ya sa ya fice daga masallacin kai tsaye ya nufi wani madaidaicin gurin sai da abinci,

Layi ya bi har aka kawo kan shi sai dai yana miƙa Debit card ɗin shi domin a zari kuɗin abincin ba network, ƙoƙarin yin transfer ya yi ta cikin bankin shi na Opay da ke wayar shi nan ya nuna ya shiga amma mai gurin sam bata ga alert ba dan haka ta hana shi tafiya,abu ya haɗu ma shi goma da ishirin ganin ana niyyar karɓar abincin daga hannun shi yasa ya fizge a tsiyace ya samu gurin zama ya fara kwankwaɗar kunun tsamiyar da ya siya,sai da ya yi rabi sannan ya fara cin masan a yunwa ce ,wani irin mugun kallo ya wurga ma waiter ɗin da ke jiran alert ya ce"Matsa anan ko in barar da ke wallahi",

"Ba zan matsa ba,ka bani kuɗi dan ba mu ji alert ba."

"Sisi bana magani dan kin fi kowa sanin wuyar da cash yake yi kuma Bank ɗin ku ne ke da matsala dan Ni ya tafi."

Da wani bank ka yi Taransifar."ce War mai gurin,

"Opay"ya furta a daƙile dan ji yake yi kamar ya shaƙe su dan takaici banda shirmen da Diya ta aikata mi shi me zai sa ma har su gan shi a waje,

Shikenan ba damuwa ka tafi idan bai zo ba gobe za mu haɗu."ce War Hajiyar bayan ta ga receipt na transaction ɗin,

Wani dogon tsaki ya ja tare da ficewa sai dai me yana isa gida ya ƙara tadda wani kayan takaicin tun daga ƙofar falo in da ya hango throw pillows a zube a ƙofar shiga, tsallake su ya yi ya ƙarasa shiga falon in da ya tadda shi yanda ya bar shi sam Diyah bata kwashe kayan abincinta ba,tsaki ya yi ya shige cikin ɗakin shi domin ya watsa ruwa sam bai bi ta kan mashirmaciyan can ba a cewar shi.
  Diyah kuwa tsabar takaicin abinda ta aikata yasa ta ji yunwar cikin nata ma kan shi ya ɗauke dan haka ta rarrafa ta shige cikin group na FRWM(First Ramadan with HABIBI)janyo wayarta ta yi ganin takwas har ta gota ta san akwai labari daɗaɗa,buɗe datar ta ke da wuya ta ga akasin haka saboda dukkanin waɗanda suka aikata kalar haukarta ko mafiyin nata ma ba su ƙarke da mazajensu lafiya ba ,matsalar da ya fi jan hankalinta shi ne na aminiyarta wacce aka saketa sanadin Ramadan time-table na social media wanda ta rubuta shi a group ɗin SIRRIN YA MACE dake Facebook in da ta ce"Ina son mijina amma ya sakeni sanadiyyar na ɗauki kuɗin shi na yi siyayyar kayan ƙwalam da maƙulashe wanda na kwafo daga shafin sada zumunta,na tambaye shi kuɗin da safe ya ce bai da shi,yana fita na ɗauki Debit card ɗin shi na je na yi siyayya dan Allah ku bani shawarar yanda zan koma hide my id sister yau aurenmu ke cika sati biyu cif da aure."

Ai ban ƙara sa kai ƙarashen labarin ba na koma Facebook in da na shige SIRRIN YA MACE domin karanta comments kamar yanda na saba,

Cikin manyan baƙi na ga an rubuta"FIRST RAMADAN WITH HABIBI"sannan aka ɗauro post ɗin aminiyarta Laila wanda yawancin matan sirri Allah ya ƙara suke mata,sai masu kareta da sunan ƙaddara ne ai kuma mene amfanin bude gidan idan har ba za su ba ma juna shawara ba,dan haka sai ƴan abi yarima asha kiɗa suka fara bata shawara nan da nan na ji wani gamsuwa ya riskeni yayinda na haɗu da shawarwarin masu hankalin da suka ba da shawara dan haka nima na ce bari in gwada ko Allah zai sa HABIBI ya canza shawarar shi a kaina,

Ba tare da tunanin komai ba na yi post tare da tura ma mai girma admin domin ta yi hide ɗina,nan take kowa ta posta min dan na yi sara ne akan gaba tana online kuma ganin hukuncin da HABIBI ya ɗauka akaina  na cin tuwo ta san zai ja hankali dan haka ta yi min post aikuwa na sha zagi cin mutumci iri-iri kafin nagarin suka fara bani shawara,

Jin yanda idona ke min nauyi yasa na ajiye wayar a gefe sai dai ina rufe ido wani irin yunwa ya tasoni gaba dan haka dole na tashi a firgice tare da shigewa cikin kicin,

Haɗa shayi na yi tare da zabga Milo tunda madararmu ta ƙare,na sa sugar madaidaici tare da ɗaukan biredi da bota,sam yunwar ta rufe idona sam ban san da wanzuwar HABIBI a cikin madafar ba yana wanke kajin da na cika ma spices da yaji a gaban sink(Aikin Kwamared)

Har sai da naji ya ruƙo biredi da shayin cikin haɗe fuska ya ce"To be sencere ba zaki sha shayin nan ba almubazzara."

Ganin yanda ya yi maganan yasa na san he is serious dan haka cikin kuka na ce"Ni yunwa zata kasheni wayyo Ammina,ka bani ko in ƙirata Billah."

Wata muguwar harara ya doka min tare da komawa kan aikin shi na dirzan kaza da soson da yake yi duk kalar da na jibga mata ta fita,

Dariya ce ta so suɓuce min sai dai murɗawan da cikina ya yi yasa na fashe mi shi da kuka,cikin zafin nama ya damƙo hannuna tare da nuna min Iranian rice ɗin da na musu ya ce"Zo ki ci wannan in dai yunwa kike ji ko in maki bugun sakwara."

Ɗebowa na yi na kai bakina jin yanda shinkafar ta yi zaƙo-zaƙo tare da kayan haɗin na cabbage karas,green beans,da su gurjin yasa na haɗiyeshi da ƙyar nan da nan wani tari ya turniƙeni HABIBI ya yi saurin miƙo min ruwa a cewar "Bai gama fanshe kuɗin da ya kashe...


Read / Download FIRST RAMADAN WITH HABIBI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album