Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

RASHIN SAA Complete Hausa Novel Document by RASHIN SAA


RASHIN SAA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 43149



RASHIN SAA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 8061929616, 08033933642, 09032409668

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 223.8 kb

File Type: txt

Views: 536+

Download: 746+

Last download: 26 minutes ago

Description/Story: [2/29, 10:42 PM] Sis Asma: BISMILLAH
COPY BY ZAINAB BUTALAWA



🌄🌄RASHIN SA'A🌄🌄








1








Official






By
AsmaBaffa









Muna Godiya da Allah ya kawo mu sabon Novel Allah yasa mu Gama lafiya.

Ina gaida Fans Dina musamman masu Sharhi Allah ya biya.





Da ku Zan Fara mutanena ga page naku

MAMAN SAMHA
NABEET ABSA
MAMU GALADIMA
AMINA ABDULLAHI
MARCYCOOL and
FLOWER.



Gaisuwa me tarin yawa zuwa ga JIDDER ZARIA, ASYCOOL,AUNTY SUMEE,KHADIJA A HAMZA,HADIZA MUKHTAR,JANNAT,HAFSAT, HAFSY, KHADIJA DANDUME and FULATA LUV.









Katsina state cikin wani kauye sosai na Fulanin asali Rugar jabbama, wata Yar budurwa ce baza ta wuce 15yrs ba zaune take Bakin makarantar bokon wacce take guda Daya tal a kauyen itama ba wata ta kirki bace, kuka take rusawa iya karfinta abokan karatunta Yan Mata da maza sun taru akanta Ana ta Yi Mata dariya da ihu, Mikewa tayi jiki ba kwari ta dauki Yar Jakarta ta dauki hanyar gidansu tana bi ta lungunan kauyen har ta Karasa gidansu Wanda duk garin shi kadai ne na bulon siminti me kyau dashi dagwas dagwas,ciki yasha tiles Kamar ba a kauye ba,Dakuna Hudu ne da Palo sai Toilet biyu da kitchen,toilet Daya a cikin wani room yake daban Daya Kuma a tsakar gidan, Rijiya karama a tsakar gidan me dauke da Bishiyar Umbrella katuwa, gidan a tsaftace komai Neat ba tarkace.

Yar Budurwar kyakyawar gaske ta shiga da sallama tana murza idonta Dara Dara Wanda Suka koma jajir dasu,Wata Dattijuwa sosai me Kamala ta amsa Sallamar tana Aikin Wanke Kubewar Miya danya tace Husna Lafiya? Ke anyi Hutun makaranta Ana murna ke kina kuka kullum duk yanda akayi abinda kika Saba shi Kika sake samu a result dinki,duk yanda akayi term din Nan ma bakiyi kokari ba kin dauki dakon aji,ke kullum kece a karshe.

Wacce aka Kira da Husna ta Kara fashewa da Kuka cike da shagwaba tace yo Yafendo Ni ya ake so nayi sabo da Allah iya kokarina kenan kina gani kusan kwana nakeyi karatu Amma bana cin jarabawar Ni ban San me yasa ba,mu gani result din ta nawa kikayi? Yafendo ta tambaya,Husna tana turo Baki tace cikin Mu 95 nayi ta 94, tabe Baki Yafendo tayi tace aikin kenan mutum Daya Kika kayar Lallai Husna Allah ya kawo Baffanki ai zaizo daukanki birni na gaji da rufa Miki asiri sai na fada Masa,gwara ya tafi dake gabansa kawai.
Magiya Husna ta shiga yiwa Yafendo Kan karta fadawa Baffanta Amma Yafendo tace ta gaji wlh.

Suna Haka Suka ji sallama wata tsohuwa ta Fado da sauri tana Yafendon Husna maza kizo Tasalla tayi Bari, a rude Yafendo ta figi gyale tace Husna maza ki shirya kici Abinci ki tafi makarantar Allo Ni Bari naje Makwafta gidan Tasalla.
Husna Bata gane Mene Bari ba tunaninta Tasalla barin Kwanukan jere tayi ko kayan Abinci ta zubar ko wani garin tuwo ta zubar,tunda taji Ana gayyatar mutane tasan Barin Babba ne, sai ko tace wlh Nima baza a barni a Baya ba sai na gani watakil samirun jerenta ta barar suka rikito, sai da taci abinci tayi wanka ta shirya zuwa makarantar Allo sannan ta wuce gidan Tasalla lokacin tuni su Yafendo sun Gama komai sun fito daga gidan ma Tasalla fes da ita Ana zuwa dubata.

Husna da gudu ta fada Dakin tana zare Ido ta gani me Tasalla ta Barar sai taga ba komai sai sannu akeyi Mata tsaki taja tayi ficewarta ta tafi makaranta.
Ko da ta Isa makarantar Allonsu da kyar ta Kai Haddarta har sai da malamin ya zabga Mata bulala sannan ta tayi karatun da kyar sannan ya Kara Mata ta Iya.

Ko da ta dawo Gida Magrib har tayi Sallah tayi sannan ta dawo kusa da Yafendo ta zauna gefenta tare da daura kanta saman cinyar Yafendo tana Lumshe Ido zata Yi bacci, Sallama Me gidan yayi da Alama ya dawo daga kasuwa ne,Husna ta mike da sauri tana Sannu da zuwa Affa,da Fara'a ya amsa yace Sannu Husna, yawwa Affa ya kasuwa ta Furta tana amsar ledar Hannunsa shi Kuma ya shige Dakinsa tare da Yafendo Matarsa.

Wayar Yafendo ce tayi Kara ta daga da Fara'a gaisawa sukayi ta waya tace to Allah ya kaimu goben Zan hada Mata kayanta,Gama wayarta keda wuya Affa yace Baffan su Husna ko? Ae shine yace zai zo gobe ya tafi da Husna Birni tayi Hutu a can,to Alhmdllh ai yakamata wannan Hutun ya dauketa da wuri sabo da su shaku da Yan uwanta.
Husna kuwa tunda taji Baffanta zaizo farin cikinta ya rushe ita tana son Birni Amma abinda ake Mata yasa Bata son Birni sannan zaiji term din Nan ma batayi kokari a schl ba Kuma yace sai ya zaneta Haka Mamansu ma zata zazzageta a birni bayan Haka ma Yan uwanta ciki Daya suyi ta rainata suna ce Mata Yar kauye komai Bata iya ba sai sune suka iya, tsaki ta ja kawai tayi kwanciyarta tana takaici.


Wani azababben matashin Handsome ne, yaro ne matashi bazai wuce 29yrs ba Cikin shiga ta Alfarma Kamar yau Daurin aurensa sanye yake cikin farar shadda dinkin zamani Kamshinsa ya cika ko Ina, Yana sakkowa Daga steps Yana danna faskekiyar wayarsa Guards ne suke take Masa baya janye da Trolley dinsa da Alama tafiya zaiyi, daga part dinsa ya fito kafin yaje Daya part din sai da ya shiga mota Driver ya kaishi ya fito cike da Izza tare da shiga part din abinka da gidan masu hannu da shuni sallama kawai yayi ya shiga cikin hadadden Palon na masu hannu da shuni,saman Wata arniyar Kujera dattijuwa ce Kyakyawar gaske ba wata Babba bace can Fara kwal da ita kamar ka taba jini ya fito yanda Handsome yake da kyau Haka take har ma ya fita komai da komai, jikinta ya kwanta tare da narkewa a jikinta sannan da kyar yace Ina kwana Ummana? Amsawa tayi ka tashi lafiya Son,lfy ya Bata amsa kawai Bai sake magana ba Haka take ta Masa Hira Amma Sam ko kala Bai ce ba Kuma baiyi dariya ba ko kadan.

Halinsa Yana damun Umman tasa Sam Bata son Halin danta Haka ba magana baya harka da kowa kullum cikin kunci da masifa,da can ba Haka danta yake ba,kallonsa tayi tace Farhan? Kansa ya Dago daga jikinta kawai ya zuba Mata idanunsa farare tas kyawawan gaske abinka da farar fata komai kyau yake Masa, Farhan Bana son Halin naka da kakeyi yanzu ace Dan kawai Haneefa ta rasu sai ka damu kanka,dukkan Dan Adam lokaci yake jira ai,muma ba Zama zamuyi ba, ka Fara girma fa Farhan 29yrs ba Wasa ba,Haneefa Kuma nasan Dole nasan kaji mutuwarta sabo da Kun shaku har an kusa aurenku Allah ya karbi Abarsa ya kamata ka hakura ka koma normal.

Kallon Umman kawai yakeyi kawai yace Zan daina Ummana ki tayi min Addua ya kike so nayi? Addua Ina maka Amma ya kamata ka daina wannan Shuru Shuru da kunci,Hooo Umma nifa ba Haneefa bace tasa nake damuwa kawai Haka na koma Nature nane Haka nake,Mikewa yayi yace Zan wuce Qatar Umma,Hmm kaji Halinka ko yanzu ban San zakayi tafiya ba sai da ka Gama shirinka zaka ce wani zaka Yi tafiya,Anyway Allah ya kiyaye Hanya Amma Karka wuce 1mnth kaji na fada maka, matukar ka wuce Haka wajen Tsohon Ubanka wlh sai ranka ya baci, 2wks ma zanyi Ni na dawo Umma karki Yi fushi pls,Better cewar Umma, fita yayi Suka wuce da escort nasa zuwa Airport jere cikin motoci guda shida na Alfarma ka rantse gomna ne.

Husna fito mana naji Karar Mota ga Baffanku can Allah ya kawo Dan Uwana lafiya cewar Yafendo,Affa mijinta yace Alhmdllh shi yasa naki fita Ina Jiransa Ai daga Jin motar ta Alhaji Shu'aib ce, tabe Baki Husna tayi tare da cewa ko kadan bana murna wannan Jarabar Birni bana kaunarta birni ko jaraba gari kowa Iyayi da karya ba abinda Suka iya sai karya,Rankwashi Yafendo ta zuba Mata ba shiri ta fice da gudu kofar gida tana turo Kyakyawan Dan karamin lips dinta.

Kofar gidan ta leka kadan ta Iske motar Baffa Yar karama ta masu rufin Asiri,gaban Motar kanin Husna Ne Aliyu Dan Shekara 10, sai kanwarta Nusaiba a bayan mota Yar 13yrs,Da kyar Husna ta karaso jikin motar
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RASHIN SAA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album