Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KUSKURE NA Complete Hausa Novel Document by KUSKURE NA


KUSKURE NA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 119393



KUSKURE NA

Reading Time: 9 Hours

Added On: 10, Aug 2024

Author: Fenerh ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 652.01 kb

File Type: txt

Views: 533+

Download: 1319+

Last download: 4 days ago

Description/Story: 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_*KUSKURE NA*_πŸ™†
_Love & Destiny_


*Written by Fenerh*

✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍

❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


_Am back again my fan's , da fatan anyi Salla lfy ina Addu'ar Allah ya karbi ibadun mu Albarka cin Annabi da Al Qur'ani Ameen_

_Alherin Allah ya kaimu ku masoya littafai na ina Alfahari da dukkan masoyana dafatan zakuci gaba da karfafamin guiwa kamar koda yaushe'_

_"Kamar koda yaushe Na kuma dawo muku cikin wani sabon littafi Na mai suna KUSKURENA Wanda yake kunshe da zazzafar soyayya da kuma kaddara, dukkan cikakken musulmi dole ya dauki kaddarar rayuwar shi mai kyau ko Mara kyau sai dai muce Allah ya bamu i kon cinye namu jara bawoyin Ameen'_


_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah s.w.t da ya bani ikon ci gaba da rubuta muku sabon littafi na Allah ka kara dad'in tsira ga Annabin Mu Muhammad s.a.w_





*Da sunan Allah mai Rahama mai jink'ai*


πŸ…Ώβž‘1⃣
"Ummu Ummu""""' shine kiran da yayi sanadi yar farka warta da ga d'addad'an baccin da takeyi mai cikeda mafarkai masu dad'in gaske'


" Ahankali ta ke ware idanunta tana kallon wadda ke tsaye a kanta"


"Cikeda shagwaba tace " kai Hajiya yanzu bazaki barni inyi baccin ba bayan jiya dak'yar mutanen ki suka barni na runtsa"


"Hajiyar tace " ke wai bakya gajiya da bacci ne A rayuwar ki Ummu? Ta turo dan bakinta "Hajiya Ummu Ruman meye wani Ummu? Bawani dadi Kamar tsohuwa'


" toh naji yanzu dai kitashi ki shirya ko bazakije maka rantar bane yau?

"wani irin zaburowa tayi Kamar zata tun tsira tunawa da yau tanada lecture karfe bakwai kuma lecturer din ba mutunci ko kadan'


" Ta dubi a gogo ' na shiga uku Hajiya kika ki tashina da wuri gashi zanyi latti. " sarkin mita yanzu inace cewa kikayi bana son ki huta ?


"Nidai ki zabomin kaya kafin in watsa ruwa ta cire hijabin dake jikinta ta wurgar tareda kwasawa a guje tayi waje Hajiya na faman cewa'


" kinsan Akwai jama'a ko idan wani ya ganki Kamar diyar arna fa Gaki tubarkalla duwaiwai Kamar masaki 'daga wajen tace " wurin ki na gada ai keda ke tafiya dakyar saboda kiba'


"Nagode kya fito ki zabo kayanki shiryayya ' bata dai fitaba ta zabo mata Riga da zani shiga dai ta hausawa tareda hijabin da zai shiga da kayan ta fara gyara mata gadon tareda nannade hijabin data wurgar a kasa


" A guje ta shigo daure da towel Wanda ko haduwa bai gama yiba a kirjinta " Hajiya tace " Amma Ummu kun raba hanya keda kunya ' yanzu a haka kika ratso tsakar gidan nan?


"Idan wani ya ganki fa kuma kinsan gidan mu kowa shigowa yakeyi tunda ina Sana'a'

" toh ni ina ruwana da mutane nida gidan mu zanrika kame kame' ""aa Ummu gidana dai gidanku ai kinsan inda yake'


" Ni dai nan ne gidan mu tunda gidan kakata ne mai sona " ta rungumota cikeda so irin na jika da kakan da suka shaku '


"Cikin minti da bai wuce biyar ba ta shirya tareda daukar Jakarta ta rataya ta kuma zura hijabin ta

Hajiya ta zaro kudi a gefen zaninta ungo ki hau achaba Allah ya tsare ki daga sharrin mutum da Aljan


Ta karba tareda godiya bata tsaya wata kwalliyaba mai kawai ta shafa tadan murza powder tafito abinta shar Kamar ba jami'a zata ba takalminta plat ta zura tafita cikeda sauri duk da tasan tayi latti batason lecture ya wuceta'


"A kofar gidan kuwa mutane ne dankam masu jiran Abinci kasan cewar sana'ar kakar tata kenan wadda da ita suke samun rufin Asiri kuma Allah yasa ma lamarin ta hannu komai basu nema sun rasa ba'


*JIGON LABARI*

Hajiya kaka mai Abinci tsohuwa ce da Allah ya jarabceta da haihuwar da daya tilo Wanda shine mahaifin Ummu Ruman Wanda mahaifin shi yarasu tun yana karami Hajiya kaka ita tayi ta dawai niya da danta batareda gazawa ba tayi wani Auren bayan rasuwar mijinta Wanda suka dauki kusan Shekara Ashirin batareda ta kuma haihuwaba har Allah ya dauki ranshi shima A lokacin ta Aurar da tilon d'an nata hadin zumunci ne da y'ar kanwarta wadda itama Allah ya dauki rayuwarta a sanadiyyar haihuwar Ummu Ruman '

Sunji mutuwar baiwar Allahr nan sosai kasan cewarta mace mai hakuri domin mijinta yayi Alfahari da Aurenta mace mai tawakkali da kaunar mahaifiyar shi'

Alhaji Muhammad saida ya dauki shekaru kafin ya kara Aure don gaba daya kaurace ma Garin nasu yayi wato Zaria ya koma Kaduna da zama yaci gaba da kasuwancin shi kafin daga baya ya samu wata mata sukayi Aure A halin yanzu yana da yara kusan biyar tareda ita


"Tun lokacin da Alhaji Muhammad ya Auri bilkisu komai ya canja A rayuwar Hajiya kaka don gaba daya mantawa yayi daita da tilon marainiyar y'ar shi,


A dole ta mike tafara Sana'a domin cikawa jikanyar ta burin ganin tayi karatu mai zurfi,

" Hajiya kaka tana zaune ne a layin Banaden dake kusa da kwango A cikin tudun wadan Zaria


Gidane mai dan girma irin na talaka mai daukeda da kuna kusan goma Wanda take zuba dalibai suna biyan haya Amma dakunan duk suna kallon waje ba sosai sukan shigo cikin gidan ba kasan cewar su dalibai sukuma suna zaune a ta cikin gidan mai daukeda ciki biyu da falo Wanda daya Ummu Ruman ke zama daya kuma na Hajiya kaka

Ba laifi komai suna samu najin dad'in Rayuwa da sana'ar Abincin da takeyi tanada tsofaffi masu tayata yin komai suma tana biyansu

Arayuwa Ummu Ruman ta tsani wannan Sana'a ta Abinci domin irin kattin dake taruwar musu akofar gida wai su suna siyan Abinci saboda Akwai runfa an jera kujerun katako tako ina Kamar wani restaurant


"A kullum Addu'ar ta tazama wani Abu idan tagama karatu ta taimaki y'ar kakarta

Ummu Ruman yarinyace mai diri chocolate colour mai tsada tanada dan tsawo fatar ta sumul sumul Kamar mai Rayuwa a cikin A.c ga wani dimple mai zurfi Wanda ko motsa bakinta tayi sai ya zurma kyakkawa ce tubarkalla wadda mafi yawan cin kawayenta ke kiranta da African Queen saboda kalar fatar ta mai sheki,

" Tayi karatunta a zenith primary & secondary dake unguwar kaya cikin ikon Allah tasamu sauke qur ani kafin ta fara zuwa F.c.e Zaria


Abu biyu yake ci mata tuwo a kwarya A rayuwar ta rashin kulawar mahaifinta da kuma rashin mijin da zata iya Aure ita kadai tasan irin damuwar datake ciki bawai ta rasa masu sonta bane aa ita kawai har yau bataga irin mijin datake buri bane don ita Sam ta tsani Auren karamin yaro gwara dan talatin da wani Abu zuwa Arba'in


"don gani n take yi tafi karfin karamin yaro ita kam shiyasa duk Wanda ya nemi kulata bata bashi fuska Sam saboda gudun raini

" Damuwar ta babbace domin Allah ya jarabceta da muguwar jaraba wadda ba kowace ya mace bace zata' iya daurewa ba ta kuma kame kanta musamman ita dake goyon kaka Ummu nada tsananin kula da kuma kiyayewa domin tana gudun Abinda zai janyoma kakarta shiga damuwa,
Karfin feelings dinta bai janyo mata fadawa cikin halaka ba saima kara kusanto ta da ubangiji Wanda a kullum take kokarin yin Azumi tareda Addu'ar Allah ya yaye mata wanna damuwar da ba maiyimata maga ninta sai Allah


"wann matsalar ko Hajiya kaka bata San ta da itaba domin duk rashin kunyar datake nuna mata bazata iya bari tasan wannan ba'

*Cigaban labari*


Allah ya taimake ta har ta isa bai shigoba tafada cikin kawayenta masu faman kwala mata kira Queen"""


"Daya daga cikin su wadda duk kusan sa anni ne da Ummu duk bazasu wuce Shekara Ashirin ba mai suna hajara tace " kai guys yau naga wani lafiyayyan yaro under twenty ya jiku da kudi da kuma tsantsar kyau kana ganin shi kaga Hutu da kuma class ina fada muku gayen first class ne wlh kai banma tunanin bahaushe ne dan nijeriya ,


"Gaba dayansu suka juyo domin jin zancen saurayi dan karami mai kuma kyau da kudi suna rige rigen tanbayarta " kai Sumy A ina don Allah ita dai Ruman juya musu baya tayi don basuda zance saina kana nan yara masu sauke wando a duwawu'


"Kudai kubari wlh a kofar shigo wata nan naganshi ya tsaya a jikin wata Arniyar mota harda body guard dinshi kai wallahi yaron ya hadu ban Masan irin kwatancen da zan muku ba gashi a lambar motar an rubuta *J 3* wlh nayi karshen gani yau"


"Shigowar malamin yasasu yin shiru domin baya
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KUSKURE NA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album