Join Our WhatsApp Group

BURIN HAFEEZ Complete Hausa Novel Document by BURIN HAFEEZ


BURIN HAFEEZ

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39903



BURIN HAFEEZ

Reading Time: 3 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: Munay ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 245.27 kb

File Type: txt

Views: 704+

Download: 308+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: BURIN HAFEEZ
Complet Ebook
Created by Shuraih Usman
Published @ www.hausaebooks.com.ng

[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
Bismillahir-Rahamanir-Raheem.
Episode 1⃣
Tasss!! Kakeji ya wanketa da kyakyawan mari, cikin
hargagi da tsananin masifa yanuna ta da d'an yatsa yace
"ke dabbar inace? Kina gani lokacin da nake 'ko'karin
kauce miki amma saboda tsabar dabbanci da 'kauyanci
irin naki shine kike 'ko'karin shigemin, salon naje
nabugeki kijawomin zuwa asibiti"
A gigice ta ri'ke 'kuncinta wanda yakemata tsananin
rad'ad'i da azaban ciwo, batareda ta kallesa ba, cikin
sassanyar muryanta tace "kayi ha'kuri, nima ba a son
raina hakan yafaru ba, kaina ke tsananin min ciwo,
hajijiya ce ke d'awaniya dani bansan lkcn da na tunkari
motanka ba, kayi ha'kuri"
Tana fad'in haka tudu'ka tad'auki bokatin awaranta
wanda yazube a 'kasa, ta ratsa ta gefensa tawuce, sakin
baki yayi yana binta da kallo, cikin zafin rai yace "ke!!!!
Zonan"
Batare da ta kalli inda yake ba tajuyo jiki asanyaye,
qarasowa tayi gamida duqe kai cikin sassanyar muryanta
tace gani, wani irin iska mai d'aci Hafeez yafurzar gamida
xaro manya-manyan idanunsa fuska a hargitse yace ke
waye ubanki agareni nan? Da har adalilina xaki xubar da
kayan tallanki amma kikasa budan baki kice nabiyaki,
damekike taqama stupid grl?
Wasu irin xafafan hawaye ne ke kwaranya akan
kod'ad'iyar fuskarta, cikin nuna rashin jindadin
kalamansa tace" kai kuwa bawan Allah kai wanne irin
mutun ne? Naga tunfarko nabaka hakuri sannan kayan
sana'ata da suka xube bana buk'atar kabiyani" meka
dauki kanka?
Toh bari kaji niba irin yan'matan nan bane masu son
cece kuce akan titi ba, sannan kana mgnr cewa waye
ubana' umhm ubana shi ba kowa bane, kmr yadda
kasani baxai iyaja da mnya kmr Ku ba. Tana fadin haka
ta gyara jemammen silifas dinta wnda yake qoqarin fita
a qafarta tacusa qafarta ciki tafara tafiya cike da sanyin
jiki' cikin xuciyarta kuwa wani irin baqinciki da qunci
gamida d'umbin damuwa ke d'awainiya da ita.
Abangaran Hafeex kuwa ko k'wak'waran motsi yakasayi
sbd tsananin mamaki da ya kamashi kasancewar tunda
yake ganin yan mata kala-kala masu aji da marasa ajin
babu wacce ya tab'a ciwa mutunci ta maida mishi da
marta sai wannan jamammiyar talakar yarinyar" cikin
tsananin fushi Hafeez ya fara takawa da nufin isa gurin
wannan yarinyar, ae kuwa da sauri wata kyakyawar
matashiyar yarinya tafito acikin motar da sauri gamida
riqo hannunsa tace "plss Yaya Hafeex don't do dat 4god
sake, tundaxu ina kallonku fa kasanar da ita laifinta
Kuma wannan baiwar Allahn ta amsa laifinta har tabaka
hkri" plss yaya kaxo mutafi gda ni ynwa nakeji gabadaya
am vry tied,
Fuskan nan ta Hafeez kuwa kokad'an babu fara'a yace
look Balkisu pls ki k'yaleni inje inkoyama yarinyan nan
tarbiyya,sbd na lura kokad'an bata da manners, cike da
shagwab'a Balkisu tafara bubbuga qafafunta kmr xatayi
kuka "plsss yaya nidai ka kyaleta kaxo mutafi gda,"
Hafeez yasake waiwayan wannan yarinya amma tuni
tab'acewa ganinsa..wata uwar kwafa yayi gamida Jan
tsaki ba haka yaso ba dan haka bashida wani xab'i
dayawuce yashiga mota sutafi.cikin qasan xuciyarsa
kuwa wani irin haushine yacikasa sbd gabadaya haushin
knsa ma yakeji da bai qara marinta ba.
Al'asfar Restaurant yawuce da ita kai tsaye, sbd Hafeez
Sam bai qaunar ganin Balkisu na complain akan yunwa,
abinci kala-kala masu kyau da tsada yasa aka kawo mata.
Taci sosai"shikuwa Hafeez sbd b'acin rai koh abinci
yakasaci, babu yadda Balkisu batayi akan Yayan nata yaci
abinci ba amma Sam yaqi., hakanan Balkisu tadaure
itama tadanci abincin ba wai don ranta yaso ba..
Jiki a sa6ule suka nufi gda, shigarsu keda wuya Hafeez
yanufi sashensa cike da 6acin rai' abangaran balkisu
kuwa nadama ne gamida Danasani fal acikin
xuciyarta.domin kuwa ita kanta tasancewa itace silar
wannan fushin nasa
Sbd tahanashi aikata abinda take ganin shine dai-dai,
Acikin wannan dare kuwa daga balkisu har Hafeez babu
Wanda yaruntsa, sbd kowa da tunanin da yakeyi cikin
zuciyarsa. Abangaran Balkisu kuwa talashi takobi gamida
alqawarin sai tanemo wannan yarinyar a dukk indatake,
sbd tabama yayanta damar cikar Burinsa.
Da wannan tunanin nannauyan bacci yyi awon gaba da
Balkisu.
®NWA
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣
K'aran alarm din k'aramin agogon dake cikin d'akin ne
yafara amsa kuwwa, mai nuna alamar lkci yayi' Balkisu
nadaga cikin bargo tamiqo hannunta dan tsaida wannan
k'aran kasancewar agogon na gefen gadonta.hannu tasa
ta danna wani abu sannan k'aran yatsaya, a hnkli ta zuro
qafafunta daga kangadon datake kwance yayinda
idanuwanta ke lumshe, tanufi toilet, tana shiga ciki tayi
brush sannan tadaura alwala, bayan tafito tafara gabatar
da sallahr asubanta kasancewar lkci yayi
Balkisu na idar da sallah kamar wadda aka tsikara ta
tashi da sauri tafada toilet tayi wanka, dasauri-dasauri ta
shirya tsaf cikin atamfarta mai ratsin orange da lemon
green, Balkisu dukk da bawata doguwar kwaliiya tayiba
amma kayan sunmatuqar amsarta, gyalenta tadauko
Wanda yyi matchn da kalar kayanta tayafashi gamida
daukar handbag dinta tanufi hnyar falo.
Daniel! Daniel!! Whr ar u? Dasauri Wanda Balkisu takira
da Daniel yafito daga cikin kitchn sanye da kayanshi na
kuku' dasauri ya iso gaban Balkisu cike da rissinawa
Daniel yace yes madam gani, Balkisu tadubi Daniel
sannan tasake duban dining area kafin tace wani abu
tuni Daniel yafuskanci abinda takeson tambaya" dasauri
yace am very swry yau nadan makarane bnsamu na
kammala brkfst din da wuri ba. Balkisu tadanyi jimm
kmr baxatace komiba chan dai tanumfasa tace "it okey
ynxu dame dame ka kammala"? Daniel yace madam sos
din kwai ne sai ruwan xafi na tea ynxu ne nakeson daura
ferfesun, Balkisu tace okay jeka kawomin tea da sos din
its OK.
Dasauri Daniel yashiga kitchn yaxo gaban Balkisu yacika
umarninta nan da nan yahada mata breakfast, balkisu na
kammalawa ta dauki handbag dinta gamida kallon
agogon dake daure atsintsiyar hannunta 7:30am tagani
Dan haka dasauri takira Daniel tabashi umarnin yayi
sauri ya kammala brkfst din sbd ynxu Yaya Hafeez xai
fito yin breakfst...cike da bin umarnin ta yace okay.
Parkn space tanufa kai tsaye tadauki wata jar mota k'irar
jeep, dasauri mai gadi yabude mata gate ta fice a gdan"
Balkisu bata nufi ko inaba sai bolori anguwar da suka
hadu da wannan yarinyar, tanashiga cikin anguwar
tafara tunanin ta ina xataga wannan yarinyar tayaya
xata fara nemanta. Nan take dibara yafado mata, gurin
mai sai da biredi da shayi dake cikin unguwar tanufa
Wanda dukk abunda yafaru jiya a gabansa ne Dan haka
tayi tunanin xuwa gurinsa koh Allah xaisa yasanta.
Daga gefen hanya kadan tayi parking motarta bayan
takulle sannan tanufi garesa.
Balkisu na isa gurin mai wannan shayin yaganeta, cike
da rissinawa Balkisu tagaidashi kasancewarsa dattijon
mutum, Cikin sanyin mgn Balkisu tace baba Dan Allah
kokasan wannan yarnyar tajiya da wannan Abu yafaru
jiya, maishayi yyi shiru cikin ransa yace"anya kuwa
yadace nasanar da ita gdansu domin kuwa bnsan wanne
irin tashin hnkli xataje ma wannan baiwar Allah dashi
ba?" Mgnr Balkisu ce takatse mishi dogon tunanin da
yatafi, baba karka damu inason ganin yarinyar ne sbd
inbata hkri akan abinda yafaru jiya, mai shayi yyi
murmushi yace auu toh ae shikenan, nan mai shayi yyi
mata kwatance gdnsu wannan yarinyar "yace daxarar
kinshiga cikin kwanar kikace anunamiki gdan Yaganaa
mai awara toh babu wnda baisaniba, Balkisu tayi mishi
godia tanufi inda ta ajiye motarta dasauri tanufi cikin
kwanar da wannan mai shayi yyi mata kwatance, Balkisu
sai murmushin mugunta takeyi domin kuwa
ayau tayi alqawarin saitadauki wannan yarinyar takaita
gurin yayanta yacika burinsa koh xaisauqo daga fushin
da yakeyi.
Balkisu nashiga cikin kwanar tanemugun parkn, sannan
tafito daga cikin motar gamida kwalama wata yarinya
kira keee!!"xo yarinyar dake qoqarin wucewa tagaban
Balkisu tatsaya indatake batareda taqaraso wajen
maikiranta ba, ganin yarinyar batada niyyar qarasowa
wajenta yasa balkisu tafahimci akwai alamar tsoro
atattare da yarinyar, murmushi kawai tayi gamida
jehoma yarinyar tambaya tace kokinsan gdan Yagana
mai awara?? Yarinyar ta gyada kai gamida nunamata
gdan da danyatsa tace gashi chan gdan maibishiyar
mangwaron chan.
Balkisu tagyada kai gamida murmushi alamar tagane,
godiya tayima yarinyar dai dai lkcin tasa key tarufe
motarta sannan tanufi gdan cike da Burin son ganin
wannan yarinyar
. Balkisu nashiga gdan tafara jiyo ihun mutun alamar ana
dukanshi, Balkisu batasan lokacin dataqarasa cikin gdan
da saurinta ba gamida riqe hannun wannan mata dake
dukan wannan yarinyar. Dasauri yagana tadannawa
balkisu wata uwar harara gamida tambayarta kekuma
fa?? Waye ke daxakishigo min gda babu sallama bare
nema ixinina, Balkisu tayi murmushi gamida cewa kiyi
hkri nasan bankyauta ba.Amma wannan dukan
dakikeyima wannan yarinyar ne yad'agamin hnkli
banmasan lkcin dana shigoba, Dan Allah baiwar Allah
kiyi hkri kimata afuwa kidena dukanta haka.
Dasauri yarinyar da ake duka tamiqe tsaye Dan ganin
wacece tashigo cikin gdansu Dan cetonta daga hannun
yagana domin kuwa iya tsawon rayuwarta idan Yagana
nadukanta qa'idane babu wani mutum da ya Isa yaxo
yabata hkri ko yaceceta daga dukk wata axaba daxa'a
gwada mata, Dan haka tamiqe daga duqen datake don
ganewa idanunta. D'agowan daxatayi kuwa idanunta
sukayi toxali da wannan yarinyar wanda fad'a yahad'ata
da yayanta. nan da nan jikin wannan yarinyar ya hau
rawa bakinta narawar sanyi tadubi Balkisu gamida had'a
hannayenta alamar Neman gafara tace Dan Allah baiwar
Allah kiyi hkri inba haka ba kuma kawai kikaini police
station domin kuwa nasan abnda yakawoki kenan.
Abin yamatuqar bama balkisu dariya gamida tausayin
yarinyar, a hnkli Balkisu taja hannunta suka nufi waje,
yayinda jikin wannan yarinyar yacigaba da kad'awa
alamar sanyi domin kuwa gabadaya illahirin jikinta a
jik'e yake jagafff!.
®NWA
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣
Batare da Balkisu tace uffan ba,haka taja hannun
wannan yarinyar har inda tayi parkin din motarta,suna
isa Balkisu tadubeta cike da kulawa gamida tausayawa
gareta. Cikin nutsuwaa Balkisu tace "Baiwar Allah inasoki
kwntar da hnkli ki abinda kike tunani bashi naxo
aikatawa a gareki ba sbd kedin baki chan-chanci haka
ba"inaso kiyishiru, kidaina kuka,kisanar dani ya
sunananki"?Wata sassanyar ajiyar xuciya tayi sannan
tashare hawayenta tadubi Balkisu tace,"sunana
AMEENATU amma anfi kirana da Meena" Balkisu tayi
murmushi, mai k'ayatarwa cikin kulawa ta dafa kafadan
Meena tace"gashi sunanki mai dadi da ma'ana, ke kuwa
Meena mekikayiwa mahaifiyarki haka har takemiki irin
wannan mummunan dukan"???
Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, sbd tambayar
da Balkisu tayimata baqaramin tab'amata zuciya yayi
ba.Meena tasaddakanta qasa gamida hadiye wani
kakkauran yawu tace Dan Allah baiwar Allah kigafarceni
amma baxan iya sanar dake lbrina ba sbd sanin lbri na
babu abnda xaiqareki dashi, sai dai abinda kika
tambayeni baxanqi baki amsa ba sbd ko ba komai
kinceceni a lkcin da bantsammaci hakan ba,
Wani dogon numfashi Meena taja gami da qara tattare
xaninta Wanda yake ajiqe, tadubi Balkisu tace wannan
abun yafarune sbd laifin danayimata wanda cikin
tsautsayi awaranta yaxube wato ajiye da abin nan yafaru
toh shine tace lallai sai nabiyata kudinta nikuma gashi
banda kudin biyanta shinefa yau da safee Aleesha tayi
fitsarin kwance tadaura laifin akaina alhalin tasan cewa
baninayi ba shine tad'ebo ruwa masu sanyin gaske
takwaramin ajikina dukk dai hakan baimata bashine
taqara da dukana kuma nasan tayi hakane dan tafanshi
kudinta. Meena nafadin haka tadubi Balkisu da
murmushi maicike da baqinciki da qunci,"tace nayi
mamakin ganinki cikin gdanmu domin kuwa ni bantaba
ganin wani mutum yaxo da nufin ceto naba sai ke kuma
naji ddi ngd" Balkisu mamaki ne yagama Lullub'eta
domin kuwa acikin lbrin Meena tabbas akwai alamar
tambaya aciki? Dan haka Balkisu batayi qasa a gwiwaba
wurin sake tambayar Meena, a hnkli Balkisu tace amma
dai Meena Yagana ba itace aenahin mahaifiyarki ba koh?
Dasauri Meena tace a'a itace mahaifiyata banda wata
mahaifiya da ta wuceta, Balkisu ta jinjina kai cikin rashin
gamsuwa da mgnr Meena tace amma Meena ga dukkan
alamu sun nuna.....balkisu bata qarasa abinda takeson
fadiba Meena tayi saurin zame hannunta daga riqon da
Balkisu tayi mata,dasauri tafara barin wajen gamida Yiwa
Balkisu godiya tace Baiwar Allah ngde da taimakonki
gareni dan Allah kimin afuwa bayan abinda nasanar dake
ynxu bnsan komai ba.kiyi hkri nixankoma gda ayyuka na
nan najirana, Meena na nafadin haka tasa kai tashige
gda..
Balkisu kam shiru tayi cike da yin dogon nazari agame da
rayuwar Meena domin daga dukkan alamu yarinyar na
fuskantar k'alubalin rayuwa',cikin zuciyar Balkisu kuwa
taqudurta axuciyarta tabbas sai ta taimakawa Meena
domin kuwa yarinyar na buqatar taimako, Dan haka
yaxama dole insan komai agameda rayuwarki.
Balkisu nafadin haka tashige motarta, gda kawai tanufa
kai tsaye domin kuwa xuwa ynxu kwakwalwarta tagama
daukan xafi, dafarko tadauka abin xaixo mata dasauqi
amma daga bisani Balkisu taga sa6anin haka,
Domin kuwa har yanxu dan'uwan nata bai sauqo daga
dogon fushin daya dauka ba.
Tagane hakan ne sbd talura ko fitowa baiyi daga cikin
dakinsaba, dan haka dasauri ta ajiye handbag dinta
tanufi dining area tadauki plate tahad'a mishi breakfast
maisauqinci wnda tasan shiyafi so, dakinsa tanufa domin
kuwa tasan baici komai ba. Sanin halinsane yasa ynxu
taquduri anniyar qin biyemasa gwnda tabishi da lallashi
kasancewar tasan baida ishashiyar lfy...
Kai tsaye ta nufi dakinsa ta kwankwasa gamida tura
qofar' Balkisu nashiga cikin dakin tasaki plate din abincin
dake hannunta da gudu taqarasa cikin dakin tanafadin
inalillahi wa'inna ilaihiraji'un....
®NWA
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode4⃣
Cikin tsananin firgici Balkisu taqarasa cikin dakin,
hnklinta gabadaya ya tashe ganin Hafeez kwance a qasa
tamkar gawa. Dasauri taqarasa gareshi dakyar tasamu ta
gyara mishi kwnciyarsa kasancewar bisa hannayensa
yake a rigingine, Balkisu kam gabadaya tafita hayyacinta
sbd tsananin rud'ewa sai faman sharar kuka take
tanafadin"yayana plzz katashi dan Allah katashi kada
kamutu kabarni kasancewa bani da uwa bani da uba
kaine uwata kaine Ubana kaine dangina" plss Yayana
katashi, nan Balkisu tashiga jijjigasa tanata faman
sambatu' chan kuma ta tashi tafice waje da saurinta falo
tanufa tadauki wayarta hannunta na makarkata dakyar
tasamu tasaita kanta tak'ira family doctor dinsu, doctor
muh'd najin abinda Balkisu tafadi mishi yyi saurin katse
wayar gami da cewa gani nan tafe.
Dasauri Balkisu ta wurgar da wayan takoma dakinsa da
gudu, ruwa tad'ibo masu dan sanyi tafara shafawa
Hafeez a fuskanshi, Balkisu na cikin wannan halin tajiyo
sallaman Dr muhd dasauri taqarasa gareshi tana nuna
masa irin halin da yayan nata ke ciki.
Dr Muh'd ba tareda yace da Balkisu uffan yanufi kan
Hafeez da saurinsa, yar qaramar jakar da yashigo da ita,
ita yabude ya dauko abubuwan gwaje-gwajensa, Dr
Muh'd yajima yana wasu yan gwaje gwajensa akan
Hafeez Wanda daga bisani yadago kai yadubi Balkisu
yace "pls Balkisu stop cryn sbd wannan kukan dakikeyi
bashine zai basa Lpy ba hasalima sai dai yaqaramasa
ciwon dake tattare dashi" domin kuwa a hali ynxu
Hafeez baibuqatar kukanki, kulawarki kawai yake
buqata,"ki kwantar da hklinki insha Allahu babu abinda
xaisameshi" Dr Muh'd yaja dogon numfashi gamida cire
gilashin dake sanye a fuskarshi yace amma Balkisu ya
akayi kika bari hakan tafaru? Sbd nasha fada miki kidaina
barin hafeez na dogon wasu tunanin wnda xasuke jefa
xuciyarsa cikin mawuyacin hali, domin kuwa a Halin
ynxu xuciyarsa na daf da bugawa dan Allah kiyi qoqarin
bashi kulawa kamar yadda kika saba, Balkisu wadda kuka
yaci qarfinta tadubi Dr Muh'd tace "Dr wlh nikaina
wataran yaya Hafeez nafin qarfina akan irin wannan
tunane tunanen nashi sbd ba tare muke bacci ba dakinsa
daban dakina daban sbd haka wasu yan tunanin da Yaya
Hafeez xaikeyinsu wlh banda masaniya"
Dr Muh'd yadauki jakarsa yarataya gamida xuba
hannayensa cikin aljihunsa, yadubi Balkisu yace kuma fa
hakane but dearis only one way inaga idan har munbi to
tabbas Hafeez xai kasance cikin walwala da kuma samun
ishashiyar kulawa.
Dasauri Balkisu tace Dr plss sanar dani.
cikin nutsuwa Dr Muh'd yabar dakin, yayin da Balkisu
tarufa masa baya da saurinta.
Suna Isa cikin falo Dr Muh'd yadubi Balkisu yace"hanya
dayace asamu ayiwa Hafeez Aure" dam! gaban Balkisu
yabuga da qarfi, cikin tsaninin tashin hnkli ta xaro
mnyan idanuwanta waje tace "Dr kamanta BURIN yaya
Hafeez? Ni ina ganin wannan shawaran abune mai wuya.
Dr Muh'd ya danyi murmushin yaqe yace I thnk dix is d
only way out! Balkisu tace tabbas hakane amma insha
allahu xangwada sa'ata koh Allah zaisa adace.
Dr Muh'd yayi murmushi yace"any way nizan koma i'm
in hurry" Balkisu tayi mishi godia sosai. Daga bisani
takoma cikin dakin yayan nata don bashi cikakkiyar
kulawa.
*************************
Daren ranan nan Balkisu bata samu ta runtsa...


Read / Download BURIN HAFEEZ

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album