Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DUHU CIKIN HASKE Complete Hausa Novel Document by DUHU CIKIN HASKE


DUHU CIKIN HASKE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Hadiza Usman chukkol

Total Words: 54042



DUHU CIKIN HASKE

Reading Time: 4 Hours

Added On: 31, Aug 2023

Author: Khadija Kanwar Soja ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Adventure novels

File Size: 325.85 kb

File Type: txt

Views: 1607+

Download: 1419+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: hakan bai hana kyan ta na asali fitowa ba, fara ce fat doguwa mai dirrin jiki, duk da cewa ƙaton ciki gare ta,


duk abun nan dayake faruwa banga namiji agun ba face driver da ya ɗauko su cikin adai-daita sahu.
" Addah Salma kar ki tafi ki barni cikin wannan halin ina zaki je wallahi mutuwa zanyi, don Allah Adda Aalma ku yafe mun na rantse da zatin ubangiji ban taɓa aikata mummunar aiki ba".






"Haba mana kiyi haƙuri kiyi shuru ki kwantar da hankalin ki zaki haihu lafiya , kowa ma haka ya fara, ai ba wanda yafi 'karfin sharrin shaiɗan,
file zan kar'bo ku shiga da itah ciki ga hand card a hannuna zan ɗauki file" cewar Addah Salma.








Tana kakkaɓe hijjabi tana tafiya da waiwayen halin da ƴar uwarta Suhaima, malam Salihu ne ya ma rawa Addah Salmah,suka wucce cikin azama .




Tunda nurses suka shiga da itah take kuka sosai ba kajin komai sai addu'a da neman za'bin Allah gun ya sawwa'ka mata wannan wahalar da ta tsinci kanta acikii


Adda Salma ce zaune a ' kofar labour room ta zabga uban tagumi abun duniya ya mata yawa gaba-d'aya bata cikin hayacinta jira kawai take yi taji ance Suhaima ta haihu







Wata nurse ce ta fitto tace "ya kamata ayi gaggawa zuwa a sayi wannan" tana mi'kawa malam Salihu paper mai haɗe da gajeran rubutu, tunani yakeyi a ransa dubu d'aya ce a aljihunsa sai kuɗin balance da zaikai gobe dubu uku da d'ari biyar, cikin abinda bai wuce minti 20 ba malam Salihu ya dawo da leader a hannunsa.






tunda suka koma kan Suhaima baka jin komai sai kukan ta dake tashi a d'akin cewa taken" Allahu Akbar! Allahu Akbar!!! Subhanallahi!! wallahu akbar!!
Allah kawa yaro na gata, ka haɗa sa da Ubansa aduk inda yake,!!!Allah ka bayyana gaskiya cikin wanan DUHU CIKIN HASKE..










Cikin kururuwa da jarumta Suhaima tayi kabbara wanda gaba-d'aya wanda suke kusa wannan kabbarar ta doki dodon kunnen su, Adda Salma ce ta mi'ke tsaye kamar zata b"alla 'kofar labour room don taga meke faruwa da Suhaima kukan jinjiri ne ya shaida nata da cewa lallai Suhaima ta haihu .kafun ta ankara ta saki wani kabbarar da cewa Allah gani !gani!!gani!!!! ka yafe mun laifin dana aikata!!!Allah gafartamun domin darajar fiyyen hallita MUHAMMADU RASULLULLAHI SALLALLAHU ALAHI WASSALLAM !!!!"










Wani Yaron ne ya sake fitowa da cancara ihu ai shima na farin ya tsananta kukan sa gaba-d'aya sun rigid'a sashin da kuka irin na jarirai kyawawan Yara maza biyu masu kama da juna, hannunsu ɗaya ne suka fitoo da 'kyar aka 'ban'bare d'aya da d'aya hakan ke nuna cewa duk abinda ɗayan yakeyi shima ɗayan zaiyi ikon Allah kenan.






Tuni nurses suka fara gyarah Yara cikin azama wata ta fitto ta cewa Addah Salma" barka ta haihu lafiya ta samu tagwaye maza har biyu kyawawa kamar larabawa "




Addah Salma tace "cikin farin ciki godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai , mai yin yanda ya so a lokacin da yaso, fatan dai Suhaima lafiyarta ƙalau ko?"
kafun nurse ta buɗe baki tayi magana ƙarar bindigogi ya karaɗe illahirin Asibitin.






Ƴan ta'adda ne masu shigan baƙaken kaya riƙe da manya manyan makamai na bindigogi sun rufe fuskarsu da baƙin yade
suka shigo layen masu haihuwa suka kwantar da kowa mata da maza, security da nurses , doctors, majinyata, gaba ɗaya an kwantar dasu nan suka fara kwashe jariraiii suna bawa Ƴan uwan su suna fita dasu Yaran .


"Ƴarana ,ku taimaka mun ni sabuwar uwace,waiyooo Allah waiyooo Allah waiyooo rayuwa ta", wani daga cikin su ya hankaɗa Suhaima ta fad'i rub da ciki tana ihu tana " cewa Addah Salma malam Salihu ƴan sanda ku taimaka mun zasu gudu da Yarana!" ko zafin jikinta bata ji ba ,


kai ba ita kaɗai ba harta sauran matan da suka haihu suna cikin mayuwacin hali.






Cikin rashin Imani da tausayi wane ƙaton yazo ya bata mari biyu hakan bai dameta ba hannu tasa ta rige 'kafansa tana cewa "in kasan darajar manzon Allah ka dawo min da Yarana" naushi mai zafin gaske yakai mata a ciki ya toshe bakinta da gam ya d'aure hannunta akan wannan gadon haihuwar
mata gaba-d'aya sun rud'e ana ta kwashe jarirai ciki kuwa harda twins .






Haka wannan mutanen suka fita da yara a'kalla Yara 16 suka sace suka hau mashine suka gudu


Fittowar su da minti biyar Ƴan sanda suka iso bayan angama wannan 'barnar nurses ne suka hau jan marasa lafiya su masu jarumtar kenan.






Nan da nan Suhaima ta tsunduma kabbara da ya ruɗa labour room, da alama dai wani naƙudar ne ya taso mata nan ƴan sanda suka fita, suka cigaba da binciken su,




Suhaima ta haifu ta samu ƴa mace a wannan lokacin, cikin Ikon Allah Addah Salma ta farfaɗo daga suma da tayi


"Addah Salma?" cewar Suhaima tana kuka,
Addah Salma ga ƴata nan bansan me ubangiji ya ƙaddara a rayuwar taba, naga jarabawar rayuwa daban-daban, naga takaina rayuwa ta ta 'kare sun ɗauke mun Yarana yau yau, na haife su ko wahalar naƙuda bangama ba",


"Allah kana gani kanaji hakan tafaru!!!!
Allah nabar Yara na agunka,
Allah ka kubutar min da Yarana ,
Rabbi banta'ba zina ba,
banyi karuwanci ba,
bana shaye shaye ,bana sata, banyi kisa ba,
ya Allah nabi ka nabi manzon ka,
nabi addininka, nabi uwata nabi uba na , nayi zumunci,nayi sadaƙa,nayi kyauta,banyi hassada ba,banyi riya ba,banyi ribbah ba ,




Ya Allah kabani jarabawar rayuwa mai matuƙar wuya da sarƙaƙiya ,
Allah ka warware mun ka bayyana haske a cikin duhu,
Uwa bataji ɗumin danta ba?
Uwa bata bawa d'anta abinci shiba?
Uwa bata rungumi d'anta ba?
Uwa bata ga idon d'anta ba?
Allah ga wata sabuwar uwa!!!
kada numfashi na na k'arshe ya fita ba tare da sakayyar wannan azalluman ba!!


Allah ga uwa na zubda hawayen ta akan Yaranta da ta haifa yau, d'azun tana maƙiyar ka kubutar mata da Yaranta,








Cikin sarƙewar murya tana magana wanda gaba-d'aya Addah Salma ba komai yake shiga kanta ba don bata hayyacinta ma, kukan mata a 'kife ga 'yan sanda ana ta zuba bincike……








Ganin hakan Suhaima ta rige hannun Adda Salma da karfin gaske tace Yarana 'yan uku ne su uku na haifa, na bar miki amanar Yarinya ta kisa mata suna , Ruqayya sunan ba…….ban…..ta…..ah…….. "kawai ta fara rufe idon ta Adda Salma ce tayi ihu da gaske nurses da 'yan sanda sukayo kanta nan dai kawai aka bata kalmar shahada tace ga garinku…


Kullun nafsin zai'katul maut


Allah yayiwa Suhaima rasuwa.


So painful gaba-d'aya jikina yayi sanyi da wanan page ɗin gashi shine farkon page …
Allah jiƙanki da rahama Suhaima,Allah amsa miki adu'an ke ..R I P……..










Who is Suhaima?, mai tarihin rayuwarta ya 'kunsa har haka,da ƴar uwarta Adda Salma?,






Hakan yana nufin cewa Yaran da Suhaima ta haifa Yaran zina ne ko na halal?.






waye Uban Yaran idan Ƴan halal ne meyasa Adda Salma batasan Uban nasu ko labarin shiba?.








idan kuma Ƴan haram Ƴan zina ne meyasa Suhaima take neman gafara kuma ta rantse Yaranta suna da asali?.








oh my God wasu mutanen basu da imani ko kad'an raba uwa da Yaronta babban laifine , shin wace mataki government zata d'auka akan lamarin?.










Yaran nan zasu rayu kuwa kodai sun tafi da haka?, a sannu a hankali chaƙwakiya zata bayyana cikin littafin .








🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗
Dark in light
only 200 ki biya a saka ki a paid group.






A'kalamin ƙanwar soja ✍️✍️💞💞






















🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60% true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞
The writter of Mijin Mage ,and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗


paid book 200 only
wattsppt number
08101235739

















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم
👇👇👇👇👇👇👇


Page 3️⃣&4️⃣
2/2/2000








Gaba d'aya garin Adamawa state ya ɗauka akan ta'adance da akayi a Adamawa state , Nigeria kaff babu labarin da ake bugawa a gidan jaridu da gidan television's, gidan radio ya zama gidan da akafi tattauna wannan al'amarin mai rikitarwa,
kafafen sada zumanta, yanar gizo_gizo ,duniyar internet, ya rikice,
ranar da baza'a taɓa mantawa dashi ba a tarihin 'kasar Nigeria,
anyi satan jarirrai da a'kalla sunkai goma sha shida a jahar Adamawa state,,,,,,,,,,,,,,,,,










Gabaɗaya garin ya harkitse da jami'an tsaro ciki da waje ,birni da ƙauye ana neman abi sahun
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DUHU CIKIN HASKE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album