Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞




paid book 200 only
wattsppt number
08101235739














🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم






Godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara rubuta wannan labarin har na wallafa shi ,, sallar i ga aminchi su wanzu shin fiyyayin hallita S, A,W.






Ya Allah yanda na fara shi lafiya kasa magana lafiya ka tsaftace min al'kalamin na daga aikata fasadi da ta'asa a doron 'kasa , kasa ya amfanin dukkan al'umma wannan labarin wani sashin ya faru da gaske ,kuyi Hakuri da kuskure da zaku iya samu a cikin ta , mai koyo ce ,,,








Godiya ta musamman ga Aunty Rumaisaaliyuinuwa da yakasance madubin dubawa ta…








Free page 1️⃣&2️⃣




Yau ya kasance ranar alhamis wanda yayi dai_ dai da 1 ga watan biyu ,shekara ta dubu ashirin dai-dai (1\2\2000) .




Ranar da Jahar Adamawa Yola ko nace har Nigeria gaba-d'aya da dukkan wata uwa ba zasu mance wannan bak'ar ranar da ya kafa mummunar tarihi a zu'katan bayin Allah ba.










Antashi da ruwan sama sosai tun daga fad'uwar rana har zuwa yanzu k'arfe goma na dare a jahar Adamawa Yola South.




Tun d'azun take ta faman nishi da ihu da duk wani addu'an da yazo daga bakinta yi kawai takeyi,
'"ya Allah kana gani kana ji ya Allah wallahi na wahala,


Ya Allah taimakon ka nake buƙata a cikin wannan yanayi, (summa sabila yassaarahu)", ga duk mace mai ciki ana so tana wannan addu'ah tana shafawa a saman cikinta ko ta tofa a ruwa tasha har lokacin haihuwa).






Tana rirriƙe ƴar uwarta tana kuka
"ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zaki haihu lafiya yanzu, ki cigaba da adfu'a kinga nima ina mike addu'a ko?,
kuma banson na gayawa Mama a waya kinsan hankalinta zai tashi tunda har mubi take,
yanzu hakan mun kusa isowa asibitin Genaral hospital specialist.




Nurse's ne sukayi kanta da gudun gaske haɗe da kawo keken marasa lafiya suka yi kama_ kama gun ɗago wannan baiwar Allah da ƙaton cikin ta wanda gaba d'aya cikin ma yafi ƙarfinta,






Duk da tana cikin mayuwacin halin hakan bai hana kyan ta na asali fitowa ba, fara ce fat doguwa mai dirrin jiki, duk da cewa ƙaton ciki gare ta,


duk abun nan dayake faruwa banga namiji agun ba face driver da ya ɗauko su cikin adai-daita sahu.
" Addah Salma kar ki tafi ki barni cikin wannan halin ina zaki je wallahi mutuwa zanyi, don Allah Adda Aalma ku yafe mun na rantse da zatin ubangiji ban taɓa aikata mummunar aiki ba".






"Haba mana kiyi haƙuri kiyi shuru ki kwantar da hankalin ki zaki haihu lafiya , kowa ma haka ya fara, ai ba wanda yafi 'karfin sharrin shaiɗan,
file zan kar'bo ku shiga da itah ciki ga hand card a hannuna zan ɗauki file" cewar Addah Salma.








Tana kakkaɓe hijjabi tana tafiya da waiwayen halin da ƴar uwarta Suhaima, malam Salihu ne ya ma rawa Addah Salmah,suka wucce cikin azama .




Tunda nurses suka shiga da itah take kuka sosai ba kajin komai sai addu'a da neman za'bin Allah gun ya sawwa'ka mata wannan wahalar da ta tsinci kanta acikii


Adda Salma ce zaune a ' kofar labour room ta zabga uban tagumi abun duniya ya mata yawa gaba-d'aya bata cikin hayacinta jira kawai take yi taji ance Suhaima ta haihu







Wata nurse ce ta fitto tace "ya kamata ayi gaggawa zuwa a sayi wannan" tana mi'kawa malam Salihu paper mai haɗe da gajeran rubutu, tunani yakeyi a ransa dubu d'aya ce a aljihunsa sai kuɗin balance da zaikai gobe dubu uku da d'ari biyar, cikin abinda bai wuce minti 20 ba malam Salihu ya dawo da leader a hannunsa.






tunda suka koma kan Suhaima baka jin komai sai kukan ta dake tashi a d'akin cewa taken" Allahu Akbar! Allahu Akbar!!! Subhanallahi!! wallahu akbar!!
Allah kawa yaro na gata, ka haɗa sa da Ubansa aduk inda yake,!!!Allah ka bayyana gaskiya cikin wanan DUHU CIKIN HASKE..










Cikin kururuwa da jarumta Suhaima tayi kabbara wanda gaba-d'aya wanda suke kusa wannan kabbarar ta doki dodon kunnen su, Adda Salma ce ta mi'ke tsaye kamar zata b"alla 'kofar labour room don taga meke faruwa da Suhaima kukan jinjiri ne ya shaida nata da cewa lallai Suhaima ta haihu .kafun ta ankara ta saki wani kabbarar da cewa Allah gani !gani!!gani!!!! ka yafe mun laifin dana aikata!!!Allah gafartamun domin darajar fiyyen hallita MUHAMMADU RASULLULLAHI SALLALLAHU ALAHI WASSALLAM !!!!"










Wani Yaron ne ya sake fitowa da cancara ihu ai shima na farin ya tsananta kukan sa gaba-d'aya sun rigid'a sashin da kuka irin na jarirai kyawawan Yara maza biyu masu kama da juna, hannunsu ɗaya ne suka fitoo da 'kyar aka 'ban'bare d'aya da d'aya hakan ke nuna cewa duk abinda ɗayan yakeyi shima ɗayan zaiyi ikon Allah kenan.






Tuni nurses suka fara gyarah Yara cikin azama wata ta fitto ta cewa Addah Salma" barka ta haihu lafiya ta samu tagwaye maza har biyu kyawawa kamar larabawa "




Addah Salma tace "cikin farin ciki godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai , mai yin yanda ya so a lokacin da yaso, fatan dai Suhaima lafiyarta ƙalau ko?"
kafun nurse ta buɗe baki tayi magana ƙarar bindigogi ya karaɗe illahirin Asibitin.






Ƴan ta'adda ne masu shigan baƙaken kaya riƙe da manya manyan makamai na bindigogi sun rufe fuskarsu da baƙin yade
suka shigo layen masu haihuwa suka kwantar da kowa mata da maza, security da nurses , doctors, majinyata, gaba ɗaya an kwantar dasu nan suka fara kwashe jariraiii suna bawa Ƴan uwan su suna fita dasu Yaran .


"Ƴarana ,ku taimaka mun ni sabuwar uwace,waiyooo Allah waiyooo Allah waiyooo rayuwa ta", wani daga cikin su ya hankaɗa Suhaima ta fad'i rub da ciki tana ihu tana " cewa Addah Salma malam Salihu ƴan sanda ku taimaka mun zasu gudu da Yarana!" ko zafin jikinta bata ji ba ,


kai ba ita kaɗai ba harta sauran matan da suka haihu suna cikin mayuwacin hali.






Cikin rashin Imani da tausayi wane ƙaton yazo ya bata mari biyu hakan bai dameta ba hannu tasa ta rige 'kafansa tana cewa "in kasan darajar manzon Allah ka dawo min da Yarana" naushi mai zafin gaske yakai mata a ciki ya toshe bakinta da gam ya d'aure hannunta akan wannan gadon haihuwar
mata gaba-d'aya sun rud'e ana ta kwashe jarirai ciki kuwa harda twins .






Haka wannan mutanen suka fita da yara a'kalla Yara 16 suka sace suka hau mashine suka gudu


Fittowar su da minti biyar Ƴan sanda suka iso bayan angama wannan 'barnar nurses ne suka hau jan marasa lafiya su masu jarumtar kenan.






Nan da nan Suhaima ta tsunduma kabbara da ya ruɗa labour room, da alama dai wani naƙudar ne ya taso mata nan ƴan sanda suka fita, suka cigaba da binciken su,




Suhaima ta haifu ta samu ƴa mace a wannan lokacin, cikin Ikon Allah Addah Salma ta farfaɗo daga suma da tayi


"Addah Salma?" cewar Suhaima tana kuka,
Addah Salma ga ƴata nan bansan me ubangiji ya ƙaddara a rayuwar taba, naga jarabawar rayuwa daban-daban, naga takaina rayuwa ta ta 'kare sun ɗauke mun Yarana yau yau, na haife su ko wahalar naƙuda bangama ba",


"Allah kana gani kanaji hakan tafaru!!!!
Allah nabar Yara na agunka,
Allah ka kubutar min da Yarana ,
Rabbi banta'ba zina ba,
banyi karuwanci ba,
bana shaye shaye ,bana sata, banyi kisa ba,
ya Allah nabi ka nabi manzon ka,
nabi addininka, nabi uwata nabi uba na , nayi zumunci,nayi sadaƙa,nayi kyauta,banyi hassada ba,banyi riya ba,banyi ribbah ba ,




Ya Allah kabani jarabawar rayuwa mai matuƙar wuya da sarƙaƙiya ,
Allah ka warware mun ka bayyana haske a cikin duhu,
Uwa bataji ɗumin danta ba?
Uwa bata bawa d'anta abinci shiba?
Uwa bata rungumi d'anta ba?
Uwa bata ga idon d'anta ba?
Allah ga wata sabuwar uwa!!!
kada numfashi na na k'arshe ya fita ba tare da sakayyar wannan azalluman ba!!


Allah ga uwa na zubda hawayen ta akan Yaranta da ta haifa yau, d'azun tana maƙiyar ka kubutar mata da Yaranta,








Cikin sarƙewar murya tana magana wanda gaba-d'aya Addah Salma ba komai yake shiga kanta ba don bata hayyacinta ma, kukan mata a 'kife ga 'yan sanda ana ta zuba bincike……








Ganin hakan Suhaima ta rige hannun Adda Salma da karfin gaske tace Yarana 'yan uku ne su uku na haifa, na bar miki amanar Yarinya ta kisa mata suna , Ruqayya sunan ba…….ban…..ta…..ah…….. "kawai ta fara rufe idon ta Adda Salma ce tayi ihu da gaske nurses da 'yan sanda sukayo kanta nan dai kawai aka bata kalmar shahada tace ga garinku…


Kullun nafsin zai'katul maut


Allah yayiwa Suhaima rasuwa.


So painful gaba-d'aya jikina yayi sanyi da wanan page ɗin gashi shine farkon page …
Allah jiƙanki da rahama Suhaima,Allah amsa miki adu'an ke ..R I P……..










Who is Suhaima?, mai tarihin rayuwarta ya 'kunsa har haka,da ƴar uwarta Adda Salma?,






Hakan yana nufin cewa Yaran da Suhaima ta haifa Yaran zina ne ko na halal?.






waye Uban Yaran idan Ƴan halal ne meyasa Adda Salma batasan Uban nasu ko labarin shiba?.








idan kuma Ƴan haram Ƴan zina ne meyasa Suhaima take neman gafara kuma ta rantse Yaranta suna da asali?.








oh my God wasu mutanen basu da imani ko kad'an raba uwa da Yaronta babban laifine , shin wace mataki government zata d'auka akan lamarin?.










Yaran nan zasu rayu kuwa kodai sun tafi da haka?, a sannu a hankali chaƙwakiya zata bayyana cikin littafin .








🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗
Dark in light
only 200 ki biya a saka ki a paid group.






A'kalamin ƙanwar soja ✍️✍️💞💞






















🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60% true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞
The writter of Mijin Mage ,and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗


paid book 200 only
wattsppt number
08101235739

















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم
👇👇👇👇👇👇👇


Page 3️⃣&4️⃣
2/2/2000








Gaba d'aya garin Adamawa state ya ɗauka akan ta'adance da akayi a Adamawa state , Nigeria kaff babu labarin da ake bugawa a gidan jaridu da gidan television's, gidan radio ya zama gidan da akafi tattauna wannan al'amarin mai rikitarwa,
kafafen sada zumanta, yanar gizo_gizo ,duniyar internet, ya rikice,
ranar da baza'a taɓa mantawa dashi ba a tarihin 'kasar Nigeria,
anyi satan jarirrai da a'kalla sunkai goma sha shida a jahar Adamawa state,,,,,,,,,,,,,,,,,










Gabaɗaya garin ya harkitse da jami'an tsaro ciki da waje ,birni da ƙauye ana neman abi sahun wan nan ƴan ta'addan.






Tunda suka kwashe jariraiii goma sha shida suka zubawa mashin nasu mai ƙafa biyu wutar gudu kawai suki daji daji, suna keta bishiyoyi da koguna, ba alamar tsoro a tattare dasu , basu huta ba, basuyi barci ba hakan yasa ba'aga ta inda sukayi ba.






JAHAR LAGOS




"Hooooooooooooooooooo
Hhhhhhhhhhhhhhhhhh
Hiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii
Huuuuuuuuuuuuuuuu


Sai oga ai ina gayama na zubawa Yaran nan kuɗi har miliyan goma su raba, burina kawai su kawo mana Jariran nan a yau ta jirgin ruwa, don mu shayar da Ƙungiyar mu jini, na tabbatar fushi take damu shiyasa har
yanzu bata mana ruwan kuɗi ba",






Daga ɗayan ɓangaren akace,,," ,"Akeeboo wulkusum, "
Ɗiff ya kashe wayan ya kurɓi ruwa mai sanyi ya koma barcin sa cikin kwanciyar hankali da natsuwa, da rashin fargaba.


murmurshi yayi domin ya ce miliion goma ne ogan ya tabbatar amman maganar gaskiya million biyar ce zai basu domin aikin da sukayi,




Lokacin da suka kusa isowa kusa da bakin kogi nan suka buɗe fuskokinsu cikin jindaɗin samun nasara suka gaisa da junan su tare da rungumar juna suna tsalle suna nishaɗi nan suka lura babu Bala acikin tawagar su take suka ɗimauce suka fara waige waige ganin lallai babu Bala babu labarin sa suka hau mashin da Jarirai sha biyar suka ƙara gaba basuyi baya ba duba abokin tafiyar su ba don a tunanin su mummunar masifa ce ta riskesa,








Lokachin da suka iso kogi suka tadda jirgin ruwa nan take suka duba Yaran sha biyar wani daga cikin Ƴan jirgin ne yace " ina yaro ɗaya??"






Babban cikin su ne ya ce " yana gun abokin tafiyar mu saida muka zo nan muka lura baya tare da tawagar mu, bamuyi yunƙurin nemosa ba domin kar muma murassa namu rayuwar".








Yana magana yana kallon ƙwayar idon sa , 'karya ne na rantse dole ku a cire kuɗin sa a maimakon jaririn d'aya salwantar wa ogah,,,,,, saboda banzan sakacinku, da shashanchinku", cikin kasƙantarwa ya basu wannan kuɗin da ya cire wani abun a ciki ya juya suka tayarda jirgin ruwan sai LAGOS……








Zaune yake yana ganin Jariraiii goma sha biyar da aka kawo musu babu guda d'aya duk da cewa ransa ya ɓaci matuƙar gaske,,, hakan bai hanashi kallon kyakkyawan Yaro cikin kayan sa na Yara ba cikin haka Yaron ya buɗe kyakkyawan idon sa charaf suka haɗa ido da Alhaji Ali cikin zare ido yake kallon sa hakan ya tunzura yaron nan ya fara cancara ihu da sauri wanda ya kawo su ya sa mai farin gyale ya kuma barcin dole.


Alhaji Ali ne yace: "akwai wanda ka gayama an rasa yaro ɗaya?"
ya ce "a'a oga kai kaɗai kasanj yanzu", "to duk wanda ya tambaye ka kace biyu aka rasa domin ina son wannan Yaron yashiga raina, zan baka kyautar miliyan 10 kai kaɗai amman yazama sirri ne, musa Ƴan tawagar nan a DUHU cikin haske ka aminchi????"








Cikin zaguwa samun kuɗi dewa yace "na yarda oga bawanda zaisan wannan labarin , Ina gayyama ko a lahira bazan tona asirin kaba".




Haka suka cigaba da hira kafun dare yaye ya ɗauki yaron nan ya raɗa mai sunah MUHAMMADU JAMALUDDIN
a cewar sa Yaro ne mai haske,.




Tunda dare ya tsala aka fara gudanar da taro kamar dai haka taron baƙaƙen matsafa ga dukkan alama Alhaji Ali yana cikin manyan masu bada shawara agun,




Manyan manyan mutane ne wanda suka amsa sunan su masu kud'i jeri gaban wane gunki tsirarra sun shafa jin da farin powder a saman 'koshin su suna sambatu suna girgiza wuƙa da manya manyan mazubin jini a kansu suna cikin wanan halin suka salwantar da rayukan yara har goma sha had'u (wa'iyazubiilah)..........










****************************************






Yaro ne mai kimanin shekaru goma sha ukku yana tafiya da shigar kayan fulani da sanda a hannun sa, yana i'yar wa'karsa tsakar daji da shannaye da yaki kiwo.


Kukan jinjiri yakiji tamkar daga nisa nan ya tsayar da wakar da yakiye ya kwaɗaitu da son jin me yafaru ( hande mi buɗi min Buba).


"yau na shiga ukku inje Buba" chan ya hango mutum kamar gawa na kwance ƙuda nabin gangar jikinsa cikin hantsari ya fara tunkaro sansanin kuka yaro ya ƙara mai kaimi gun isowa gun wanan…


"Ya subhanallahi wanga bawan Allah muguwar hatsari ya sameta a tsakar daji," cewar bafullatanin yaron da yaki magana cikin maganar hausar da bai ishishi ba.










Ganin cewa yana wahalar numfashi ya ɗauki ruwa daga gorar sa ya yayyafamai " cewa yaki na runtuma zunubi mai matukar munin gaske ka taimaka mun ga wanan jinjirin ka tafe dashi zuwa gidan ku lallai ne na kasance cikin taɓaɓu masu mantuwa da cewa Allah ba azzalumi bawan sa bane,


nakai bugu ga macce mai naƙuda ,na raba uwa da yaronta ,, lallai ban chanchanchi yafiyya daga garisu ba, na tubah Allah naga wuya mutuwa zanyi tafe da yaron nan amana na nar bar ma yaro,"


nan da nan yafara amai na jini mai muguwar wari ya mutu baki buɗe yana mai kallon wanan jinjirin"…..




Duk wanan bayanin Buba bai gane komai ba abinda ya fahimta kawai wanan bawan Allah yaye laifi agun Allah ne..






Nan buba ya lura da ƙaramin jinjiri yana rufe da idon sa alamar yaye kuka har ya gaji kyakkyawar jinjiri sabon haihuwa wahala ta sa fuskar nan tashi taye jawur abunka da farar fata.




Cikin azama ya runtumi jinjirin ya kora shanun sa zuwa gida cikin fargaba da tsoron hallin Innar su iddan yau tagansa da wanan yaron gwanda Baffa shi Allah ya zuba mai tausayi..







Me yafaru da Bala da yaro ɗaya?
Waccece Suhaima da Adda salma''?
Waye Alhaji Ali?
wane 'bangaren labarin nan true life story ne,
mujee zuwa kar ku manta yanzu muka fara wanan littafin,yanzu aka fara chaƙwakiyar triple's……………….




Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️ .
























🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60% true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞
The writter of Mijin Mage ,and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗






paid book 200 only
wattsppt number
08101235739















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم
👇👇👇👇


page 5️⃣&6️⃣




Cikin azama ya runtumi Jinjirin ya kora shanun sa zuwa gida cikin fargaba da tsoron hallin Innar su idan yau tagansa da wannan Yaron gwanda Baffa shi Allah ya zuba mai tausayi..








Isowar Buba cikin wani gida da aka kewaye da zana yayi dai-dai da sallamar wani bawan Allah da girma ya fara ziyartarsa, cikin shiga koɗaɗɗiyar shaddar da ta fara yagewa wahalar rayuwa itace zata sa kace mutum ne dottijo da tsufa tamai yawa ganin Buba da tsumma dunƙule tasa Baffa magana "me a hannayanka Buba?", cikin harshen fulatanchi Yaron ya mi'ka mai Baffa na ganin Jinjiri sabuwar haihuwa ya rikice kardai Buba ya sato Yaron mutane ne ,








"Kai Buba ina ka samo wannan" Buba ya kora mai bayyanin komai "Allahu Akbar anda ina Iyayen sa?" ,,,tashi Buba yayi da tsugunawar da yayi ya kora shanun su cikin k'arinsu nan ya dawo ya shiga cikin gidan da Baffa,,,








Gidane da aka kewaye da zana d'akuna biyu ne kacal irin ginin dacan na ta'bo mai k'aramar kofar shiga, tana zaune riga daban zani daba ko d'an kwali babu a kanta wata tsohuwace a tsakar gidan riƙe da fefeee tana gyraa maiwa sallamar su ne yasa ta zubar da yawun bakinta da ya canza launi zuwa ja sakamakon goron da take ci ha'koran nan nata zago-zago dayawa ma sun zube sai kallarsu daga fari ya kuma jan launi share dattin hannunta tayi akan zanin ta face majina, tafara zuba masifa kamar dai ita ta kawosu duniya .












"To yau kuma ina ka kwaso Jariri Baffa hala satan Yara ka fara banda labari?", "haba Lantana ke dube ni da girmata tunda uwata ta haife ni kin ta'ba jin labarin nayi sattar koda ' kwayar wake ce balle d'an mutum jikar mutuwa?".








"ohhhhu ne yo ina ruwana da wannan ita babbar taka wayasan yawan sirri ka da ta ɓoye har aka yarda aka baka aure na gashi na ' kare a gidan tsiya ,sata kuma ba yau farauwa ,ai in 'bera nada laife dadddawa ma da warinta"








Buba dake tsaye tsakanin su sun saba da irin zanttutukan Iyayen nashi don haka ko ajikinsa burinsa kawai ya amshi Yaron nan daga hannun Baffa, nan ya dauko ru'ba'bin tabarmar su da ta sauya kalla zuwa tsummar hura wuta ya ɗan buga ta da dutse ta mi'ke ya shimfiɗ'ar wa Baffa daga 'kifin k'ofar dakin ,sanan ya d'auko cinyayyin tsintachiyar sa ta duduge ya ture dattin da Inna ta bari batayi shara ba kaɗan daga halinta kenan tana jiran sa ko Baffa suyi mata ,,,,






Muryar Buba ita ta dawo dasu daga jiniyar kacamewar masifar da musayar magana a tsakanin su " Baffa ga tabarma chan na shinfid'a ma" ,cikin harshensu na fullanchi "Baffa yace yaro "Allah maka Albarka",wuff inna Lantana tace nikuma Allah tsini mun ko tunda ga sabuwar Ƴar tasha na magana"




shirin zama a bisa tabarma yayi bayan ya ciri diddugin silidaf nasa , "ihuuuu kwarankwatsa idan ka zauna da Yaron nan a gidan nan ubana shege ne", zare ido yayi domin ai ko ba komai ubanta ubansa ne tunda cikin ɗaya dukka suka fito maganar ta bashi haushi amman ya dake ya zauna "ohhh yanzu nagani ashe Yaron ne shege ubansa kwarto a ƙauye, ye kuwa jama'ar gari ga wanda kuka d'auke shi matsayin malamin ku ƙaruwar sa ta bashi Yaronsa domin bazata yi rainon ba ,,,,",







ko a gyalen sa kamar baya jinta ya yaye fuskar Yaron fari ne tass mai kyau da haske ga wane kwarjinin da haiba a tattare da yaron buɗi losa_losan idon sa yayi manya dasu da sukayi ja nan ya qare idon sa akan Baffa tamkar bazai janye ba nan Baffa yace masha Allah " Bala ma ya leqo yace Baffa na samu 'kani nima zamuyi karatu muyi kiwo muyi wasa muje rafi ko " murmurshi Baffa yaye ya kama kunnen Yaron ya rad'a masa suna Muhammad Kamaluddin , murmurshi Bala yaye ya ce" Kamal aboki na"
















Ba'kin ciki ne yasa ta zurma d"aki "jar uba kunga yanda Baffa ya juya akan wai an Yaron ana safiyar gobe zan buga sakamakon gun malam na gorkun ya duba mun wai Malam ina ya samu wannan Yaron tun kafin na ganshi ma na tsaneshi fa",fitowa tayi ta sauke abincin dawan data tu'ka tayi d'akinta dashi ganin hakan Baffa ya d'aura ruwan zafi ya umarci Buba da ya tatso nonon saniya, cikin minti ƙalilan ya haɗa komai yawa Kamal wanka da taimakon Buba suka bashi madara yasha sai barci da ajiyar zuciya,,,,,














To Kamaluddin Allah ya rayaka ko ya rayuwar ka zata kasance a gun wanan mutane guda ukku ,,




Chakwakiyah waye Baffa?!!!
wacce Ina 'kazamiya ???!!!
Me tarihin rayuwar gidan ya 'kunsa naga kamar komai bahago ne a gidan ???


Anyah kuwa shikkinan anan rayuwar bawan Allah Kamal zai kasance ???!!!








mujeee zuwa , Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️✍️✍️✍️💞💞💞💞




🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞






















🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60%true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞
The writter of Mijin

Please Login or Register in order to submit comment