Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mage ,and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗






paid book 200 only
wattsppt number
08101235739















👇👇👇👇👇


page 7️⃣&8️⃣
LAGOS




Security ciki ma'kil manyan motoci ne suka tsaya a cikin airport dake Lagos bud'e marfin motar akayi ya fara fitowa cikin isa da ƙasaita dogon mutum ne chocolate colour mai matsakaichin jiki, a 'kalla zaikai shekaru arba'in da biyar a rayuwar shi , sanye cikin farar gezina, d'auke da tawol da ke da'uke da sabon Jinjiri MINISTER OF AGRICULTURE NA NIGERIA kuma mai 'korarrin bussines wanda ya shahara da neman hallak gaba d'aya Alhaji Aliyu Jafar marafa kenan, wanda duniya ta sanshi da taimakon marayu da nunawa talakawa tsantsar ƙauna da tausayawa, hakan yasa ake mai la'kabi da baya goya marayu, mutum ne mai dukiyar gaske a cikin Nigeria gaba-d'aya hakan yasa yake gudanar da ayyukan sa bisa tsari da jajircewa, da kuma hankin nisa,










A ruyawarshi Allah bai bashi haihuwa ba matarshi d'aya tak a duniya Hajiya Maryam wacce take matakin Senator a birinin Abuja masaniya kuma kwararroyar ƴar siyasa wacce take Jan zaren ta a cikin ƴan majalisan 'kasa, zamansu ba wani dad'i gareshiba kowa na harkar gaban sa ne shiyasa basu da matsala duk lokacin da bukatar aure ta kamasu akan iya had'uwa a kowanne hotel, Alhaji Aliyu bai kansance mayen mata ba, don haka neman kuɗin sa yasa a gaba,
















Gyarah tawol ɗin hannunsa yayi ya ce "oh my boy yanzu zamu koma Abuja hope ka shirya shiga jirgi?" kamar yana jiran ya amsa mai ne "Allah kad'ai yasan son da nake ma Jamal" , murmurshi yayi ya shiga jirgi tare da rungume Jamal a ƙirjinsa domin jin bugun zuciyar d'an nasa,,,,














Big cars 'kirar Prado dozin d'aya su suka tarbi shi daga airport direct ya shiga ta tsakiyar car suka tsula cikin minti tallatin motor cin suka yi parking a zone two dake makikin gate ne 'kirar ruwan gwal da aka kewaye da flowers masu launin green da pink sai white a 'kife mai gadi ne cikin rawar jiki ya wan'kala gate ɗin gidan , Masha Allah shine abin da na furta , ,,,








Kasancewar yasan Hajiya Maryam na gidan, lifter ya shiga ya haura zuwa sama ta uku babban falour ne da ya had'a kayan alatun mori rayuwa sai 'kamshi da yake tashi da sanyin Ac dake buga lafiyayyun chairs da suka kai set ukku, zaune take da glass a idon ta 'kafa 'daya akan d'aya tana karanta news pepper , sallamar da
yasa ta ajiye ta amsa ganin Yaron a tawol ba 'karamin girgiza tayi ba tace "umm dear sannu da dawo wa", "yauwa sannu ohh yaushe rabon dana ke zauna a nutse haka a gida?" murmurshi tayi "ai na gaya ma kayi babban sa a domin gobe haka a can house of assembly nake domin muna da ganawa da sauran senotors kasancewar za'be nan da one year", "to Allah bada sa'a", ameen ta amsa.



Ta mi'ka hannun tayi ta bud'e tawol nin hannu "dear what is this what is happening, ina ka samu wanan abun?", "calmdown dear Yaro na ne ".






Wane uban tsalle ta buga "Yaron ka you mean aure kayi?" ajiye Jamal yayi ya rungumota "no ya zanyi aure kuma yanzu bayan gaki nan a gefe na , please ke fahimci ni Yaron nan maraya ne bashi da kowa Iyayen sa sunyi hatsari acan garin Minna to da yake harda wani driver na a ciki shine ya tsira da wannan Yaron ni kuma na amshe shi matsayin Yaro na , please ina fatan zai mana amfani a gaba,








Kuma Kinga namiji ne ba laifi bane idan mun riƙeshi matsayin Yaro, ina son ke fahimci abunda naki hasashe shi ka'dai ne zai kasance ya fidda Duhu CIKIN HASKE a rayuwar mu ta aure dake" , " tsura mata ido yayi don ganin hawaye fall a idon ta ta juya inda Yaron yake ta share guntun hawayen da ya ma'kale a 'kasan idon ta ,ganin hakan yayi murmurshi a zuciyar sa yace "tarko na ya kama " d'aukan sa tayi murmurshi tayi lokacin d'aya annurin fuskar ta ta dawo "Allah sarki ashe maraya ne dube shi kyakyawar Yaro dashi, nayi alkawarin zan d'auki ka matsayin Yaro na da na haifa tunda Allah bai ban haihuwa shi ka'dai yasan dalilin hakan" shafa fuskarsa tayi da yake barci hankali kwance, matsowa Alhaji Aliyu yayi ya h'ada da ita da Jinjirin kaf ya runguma a ƙirjinsa .












" Ina godiya uwar da'kina shiyasa naki 'kara sonki a kowacce da'kiƙa dake buga agoggo" d'an dukan sa a kirjin tayi "zaka fara ko , yanzu wane suna yafi cancanta musamai dear? " ajiye hular sa yayi akan stoll chair ya ce " Muhammad Jamal", "wow nice name dear Jamal Allah raya minkai ka fidda Duhu cikin haske na rayuwata zanyi waya dear a turo min special nanny daga can headquarters na school of Nanny's da zata kulla mana dashi tunda duk bama zama and then ya kamata muyi masa shopping a babban plaza you know aljihun ka ne kuma zaiyi aiki " , dariya yaye sosai "to senator don't worry duk ba abun da'ga hankali anan,




Akaiw company furniture da zasu zo nan da two hours domin gyarah wancan d'akin ya zama na Jamal sai ke gaya musu colour da kikiso ayi using dashi right after two days zan kira Ƴan jarida domin duniya tasan cewa ina da Magaji", " that's is my husband i love you so much dear sumbata ta kaimai a saman goshin sa cikin rashin sa'a ya janyota jikinsa ruff ta zube ya fara romance nata kamar baisanta ba duk da cewa ba laifin sa bane domin yanzu haka rabon da yakassance da ita haka zaikai seventh month.






Kukan Jamal shi ya dawo dasu daga duniyar da suka shilla , "ohhh ashe fa na zama big Daddy yanzu" shuru abunka rige-rigen d'aukan sa sukayi abun ma ya basu dariya ,,,,,,,,,






Nan Alhaji Aliyu ya hau lefter domin haurawa part nashi da al'kawarin zai Kira i'yan jaridu domin sanarwa duniya ya samu haihuwar namiji Muhammad Jamaluddin.








To Jamal Kai Kuma anaan cikin Abuja Allah ya kawoka ko ya rayuwar ka zata kasance a cikin wanan gidan Alhaji Aliyu da senator Maryam ,




ku chigaba da kasancewa cikin wanan ✍️✍️..👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇








🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60%true life
story
by


'kanwar soja ✍️💞

The writter of Mijin Mage ,and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗






paid book 200 only
wattsppt number
08101235739














*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم


👇👇👇👇👇👇
page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣




ADAMAWWA STATE,






Adda Salma ce a gaban Mama a k'aramar hukumar Mubi ta Arewa zaune da santaliliyar Jariyayya kyakykyawa fara da aka nad'eta cikin wanei zanin Atamfa sai barci takeyi hankalin ta k'wance gyara zama Adda Salma ta gyarah murya " Mama bakice komai ba akan maganar da na miki har yanzu kin barni cikin mayuwacin hali' "

" tura d'ankwalin kanta tayi wai ture kaga tsiya ta karkata baki "Salamatu kenan don takalmin ubanki da ita Suhaima taji gidanki da shegen cikin nata kin gayamun ne?, wai ke gaki mai 'yar uwa kun mai dani i'yar iska wacce bata san zafin haihuwa ba ,to ko baƙin cikin cikin shegen da tayi ai ya isa ta mutu kafurar Yarinya mai zubin mayu gwanda da Allah yasa ma aka sace Yaran aje can akashe 'Ya'yan shegu to ma ubanwa zai zauna da shegu a gidan sa rahamar Allah ya'ki zuwa idan anan rabon ni'ima a wuce gidan sa baza'a bashi ba" , "haba Mamma" don Allah chan rufemin baki kedai Salamatu badon a gida na haifeki ba sai nace an sauya min ke to kamar ba nono na ma kika shaba wayasani ko uwar Suhaima ta baki nononta ni bansaniba tunda tana baƙin cikin rashin haihuwa a lokachin "








tashi taye tsaye tayi tasa hannu bisa kwankwaso "to bari kiji da kyau ko Ubanki dake kwance a cikin kabarin sa bai issa yace ke raini wannan shegiyar Yarinyar da bata da uba ba , can ta kwaso dangin uwarta da yawace-yawace ".






_"Don Allah Mama Yarinyar nan bata san komai muna da ha'k'ki akan kula da ita marainyar Allah ce ,wallahi Allah zai tuhumi akan Suhaima da 'Yata ranar tashin al'kiya,,,,,"






"can bakinki ya sari d'anyen kashi Salamatu indai nice Uwarki dana haifeki kika yarda kika ɗauki wannan Yarinyar da niyyar shayarwa ko raino Allah ya tsine miki Albarka, shigiyar sakarya mara hankali,,,, "








Da sauri ta ajiyi Ruqayya dake cancara ihun masifa sakamakon hayaniyar su,da sauri sallamatu ta dur'kusa kusa da ƙafar Mama ta ta'ba 'kafarta ta fashe da kukan bala'i , "Mama don Allah don darajar manzon Allah kiyi hak'uri ki yafemun ki janye kalamai ki a gareni , Suhaima 'Yar uwa tace kuma 'Yar Suhaima 'Ya tace ke kuma uwace a guna , zanbi umarnin ki amman Mama ki sani abu guda d'aya tabbas Allah baya barci ,shi ya hallici Ruqayya don haka shi yasan makomar rayuwarta nabarta a hannun Allah ba hannun kowa ba zan d'auketa na fita bayan gari na ajeta,"










" barka salamatu ashe kin fara hankali to na janye maganata idan kika rabu da wannan tsiyar don gyatumin uban ki baki isa kimin wa'azi ba izu d'ari ba d'aya ne akai na", murmurshi mai 'kuna da ba'kin ciki Adda Salma tayi ta share hawayenta ta d'auki Rukayya ta bar gidan bata wuce ko ina ba sai tashar Mubi , ta Shiga motar dawowa gidan ta Jumeta, sautin kukanta shi ka'dai ke tashi a cikin motar bus da ya chika da mutane ma tafiya share hawayenta sannan ta zaro wata sarƙa da Suhaima ta bata shi domin ta baiwa Yarinyanta ko Yaronta duk randa ta haihu sanya mata tayi a wuyanta ta zaro fida mai kunun yara tabawa Rugayya tasha sosai ta 'koshi har tayi barchi.






Nan suka iso gida lafiya wanka tayi da Rugayya ta shafa mata mai da powder kana ta ware mata 'kafanta ta bud'e gabanta ta karanta , suratul nur da ayattul kursiyy da alwazaitan la'kad ja'akum ta rufe da amanar rassulu, da nufin Allah kare mata Rugayya daga sharrin zina a duk inda ta tsinci kanta.




( wanan babban magani ne ga jarirai mata , Allah kare Mana yaran mu da 'kannenmu daga afkawa matsalar fyad'e da taa'adanchin zina ameen 🥰).












Shinfid'e ta tayi sannan ta shirya domin fita 'karar adai-daita sahu shi ya dawo da ita duniyar tunanin ta, Malam Salihu ne yayi sallama da ganin fuskar Salma yasan akwai gaggarumin matsala domin tace a Mubi zata kwana sai dai a rashin sa'a gata ta dawo zama sukayi bata 'boye masa komai ba dangane da abunda ya faru fashewa da kukan tayi haka ya rungumi ta yana lallashinta har ta nitsu yanzu wane shawara kika yanke "to mallam kasan bansan inda dangin Mahaifiyar Suhaima suke ba asalima lokacin da babban na da rai yakance mana buzuwa ce ita daga 'kasar Niger take to kuma bata gayawa kowa labarin ta ba har ta rasu kaga kenan bamusan mafita a nan ba" , shiru yayi ya nisa yace "abu d'aya ne mukaita gidan marayu mafi kusa duk wata muna kaimata ziyara ko ya kikace zanwa abokina Jauro magana tunda naga Yana committee na marayu", " yauwa mallam ka kawo shawara mai kyau hanzarta kaji yanzu domin wallahi Mama cewa tayi kwana d'aya na 'kara kwana da Ruqayya Allah ya isa ce kawai tsakanin mu", girgiza kai yayi cikin takaicin halin surkartashi ya fita gida badon yana son rabuwa da Rugayya ba Yarinyar marainyar Allah,,










Koda ya samu Jauro da wannan maganar ya jinjjina matuk'ar gaske sannan kuma ya bashi shawarar cewa gidan marayu ba zasu amsheta ba kasancewar ga Y'ar uwarta da kuma kakanta mafita d'aya ce akwai gidan marayu dake jahar gombe idan ya aminci ya bashi Yarinyar ya wuce da ita da cewar bata da dangin kuwa a duniya hakan ne zaisa su amsheta, daga baya zan na kai mata ziyara ina baku hoton ta" ,cikin sauƙi mallam Salihu ya amince da abokinsa Jauro , da k'yar da kukan da rarrashi aka raba Salamatu da Rugayya, asubar fari Jauro ya d'auki hanyar gombe , gombawa ɗiban fari ,ba'a kwana daku ba antashi daku,,,,,,
















Inallillahi wa Ina illahin raji'oun wacce irrin annoba ce Mama, wacce irrin hali' garita ?












Allah sarki Adda Salma ,zamuso ace kibamu labarin rayuwar gidan ku, bayan kin gama jimammin rabuwarki da i'yar ke rugayya!!!










Hummmmm ga Jauro dai da Ruqayya a hanyar gombe ko ya zata kaya cikin wanan sansanin ya'kin ????






Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞


















🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60% true life
story
by
'kanwar soja ✍️💞

The writter of Mijin Mage ,and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗





paid book 200 only
wattsppt number
08101235739


Page
👇👇👇👇👇

1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣



page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣
************BAUCHI************
WAIWAYE ADON TAFIYA,,


Malam Baffa bafullatanin garin Adamawa makiyayin mai adalci a cikin aikinsa, su biyu Iyayen su suka haifa dashi da ƙanwar sa wacce ta rasu a yayin haihuwar ta anan ta haifi ɗa namiji aka samasa sunan Baffa wato Abubakar sadiq, a inda ake ƙiran Yaron da suna Buba ,bayan Allah ya mata rasuwa ne ya ɗauki Yaron da niyyar shi zai rufi Ɗansa, hakan ya faskara domin Iyayyen sun ƙi amincewa da buƙatar da yazo dashi kasancewar tunda matarshi ta rasu tsawon shekaru goma bai kuma aure ba idan ya tafi kiwo a garin Bauchi yakan d'ibi lokacin mai tsawo kafin yazo duba Ƴan uwa da abokan arziki tunda Iyayyen sa duk sun mutu a gaggauce Baffa ke don daukan yaron sa buba shi kaɗai ya riƙe wanda zai gani ya tuna Ƙanwarsa da Iyayensu kwatsam ya bada sanarwa a cikin rugarsu da a bashi mata cikin kwana biyu ya aureta domin ya samu a bashi Buba, cikin rashin sa'a limamin unguwar su ya sanar da cewa ansamu bazawara mai Yara biyar tayi aure har sau biyar mazan duk rabuwa suke yi kuma ma i'yar dangin suce na kakkaninsu koda aka tambaye ta da farko tace bata so jin har Bauchi zata kuma zata rabu da Yaranta, amman tunda taji labarin Mallam baffa ne tayi saurin komawa gun Baban ta tace ta amince da auren kasancewar mutum ne mai dukiyar shanu da baisan iyaka cin suba, yakan baiwa wasu makiyayan garke guda domin suje garuruwan mabanbanta domin sukai kiwo ,,,,,



Ranar wata juma'a ana saukowa daga sallar juma'a aka ɗaura auren Abubakar Baffa da amaryar sa Maryam wacce aka fi sani da mario 'kazamiya.


# **** waccce ce mairo 'kazamiya *****************************_******

Ƴar mai unguwar 'kauyen tangad'i kenan wacce masifarta ke hargitsa unguwa, tsantsar makircin ta da k'azanta, takasa zaman gidan aure duk inda ta shiga zata haihu d'aya ta fito ba namijin dake iya control nata gata da yawon bala'i Yaranta biyar don haka aure biyar tayi a Rayuwar ta ,,.
tunda aka gayawa Malam Baffa halayen ta ya ce yaji ya gani domin idon sa a rufe yake kunnuwansa basajin sautin maganar kowa, babban burin sa ko aljanna ce indai an samu to a aura mai kawai ta zauna da jininsa Buba,




Bayan aure masifa kala-kala da tashin hankalin ba wanda Mallam bai gani ba a gidan sa tun yana magana har ta sa sakata a bakinsa, ko kashi tayi a 'kasa tace ya taka ko ya kwashe cikin da 'barin jiki zai aikata hakan samun sararin ta yayi yawa har ta kaita ta da'uko Yaranta daga can Adamawa state a can 'karamar hukumar Ganuwa cikin wane Ƙauye, haka ta kwaso su suka zauna a cikin gidan Baffa suke zuba mulki , abinda taga dama shi takeyi uffan ba ya ce mata takan sayar da shanu ta gabata Yaranta mazan kaff suyi ta busha sha cikin 'kauyen Bauchi basa zuwa kiwo ko d'iban ruwa kai har takai aikin gidan ma baffa kiyin sa, ya d'ibo musu ruwa yayi shafa yayi girki shi da Buba ,, ita kuma tayi da Yaranta ta bashi kwanan ka sanan yayi wankin , idan wanke gidan ya taro tsaff zai zauna ya wanke musu kuma ya cigaba da rainon Buba cikin wannan wahalar gaba-ɗaya sun mai dashi sha'awa baisan ciwon kansa ba ta kwace komai da farko taso ta gudu ta barshi amman ta yanke shawar ta zauna don ganin cewa bata da riba idan auren ya mutu, yanzu ma idon ƴan ƙauye na jiran mutuwar auren
bawan Allah Baffa baruwansa shida Buba kawai yasani har ga Allah da yasan inda zai nemo dangin su da suka watse a daji suna kiwo ba'abunda zai hana ya gudu to amman yanzu ko tunanin gudu ya bar Inna Mairo 'kazamiya ya daina sai abinda tace akeyi a gidan ,,iro shine babban Yaronta wanda a'kalla zaikai shekaru ashirin a rayuwar sa, sai Jalo mai binsa da shekaru sha takwas, sai Bala dake da sha shidda sai bukkar dake da sha hud'u sai autan ta mai shekaru goma sha biyu yana karawa da Buba ..
yanzu Hakan baffa na can wani yankin daji dake jahar Bauchi yana rayuwa a cikin ba'kin ciki da takaici rayuwa gaba ɗaya yanzu bashi da muhimmanci da dukiya a rayuwar sa kaf shanun da yake kiwo Inna ta saida wasu kuma makiyaya sun gudu dashi ganin ya zama shugaban matsorata wace mace ke juya sa a'kalla mutum gidajsn kara da zana yakai kimanin goma sha biyar dake rayuwa a wannan tsibirin daji, Shanaye tara ke hannun Baffa, wanda Buba ke kiwatasu suma sune 'karfin Inna ta cinyi ne da tagama dasu….


WANANN SHINE LABARIN GIDAN BAFFA DA INNA 'KAZAMIYA ,
********************************
Ball Iro yayi da butar dake gindin tsarkar gidan yayi "wai Inna wannan kukan jinjirin daga gidan ubanwa yake, domin kunnuwana ina barci ko hala haihuwa kikayi da wannan tsohon kwanjalin?", "heeeeee lallai Iro baka da kunya na haihu nakai Yaron gidan ubanwa da wannan matsiyacin jefa na aure shine domin dukiyar sa da naji labari ashe ma duk 'karyace gata ta ƙare, bata tsinanamin komai ba sai tsuman da ke gungumina kukan jinjiri kuma daga gidan uban Buba yake fitowa can ta matse musu ya gama yawon barikin karuwarsa ta bashi digirin girmamawa na Yaron da ta haifa shine yake rainon sa" cewar Inna tana d'aura zani,,
"haba INNA ya zaki bar su su kwana mana a gida inji da kukan wannan Yaron ne wallahi na gaji", da gidan nan cewar Jalo yana jan wandon sa dake zamewa a kwankwaso sa yana fidda sigari "to Jalolo na ya zanyi da uwar miji banda ido" daukar ashana yayi ya kunna ya fara janta hararrarsa Iro yayi ya ce "amman kaifa wawa ne Jalo don wandon ubanka ina tsaye anan zaka kunna haya'ki", "to d'an jar uba ai gwanda wandon ubanka da naka uban dake yawo gari-gari yana tallar dadddawa" shewa Iro yayi ya cakumu Jalo suka fara dambartuwa da junan su "ohhh ne Ƴar dangin tangad'i yanzu Yaran nan da safiyar nan kuƙi dambe kuci kanku kusha ruwa Ƴan Iskan Yara",, Buba ne yayi sallama da tulu bisa kansa na ruwa,







tunda ya ce wannan uban ashar na tashi yasan halin Ƴan uwa nasu ne yasa ko sallamar sa ba wanda ya amsa. cikin sanɗa ya juye ruwansa yayi zummar fita zauren gidan "to kai don uban ka zo nan baka iya gaisuwa bane ko ba'a koya ma gaida manyan kaba" cewar Iro dake nishi sama-sama bayan sun rabu da Jalo, zuwa yayi ya durƙusa ya gaida su dukka su biyu Jalo ya ce "idan ka gama d'iban wannan ruwan ka fito mun da kayana da nasa jiya da ta jiyan can ka wanke min dan tsohon ka", amsawa yayi kana ya fita cikin ba'kin ciki halin Ƴan uwa nasa.






Baffa dake goye da Kamal a bayan sa yanajin duk abunda ke faruwa amman ko leƙowa ya kasa rarrashin kamal yakeyi har ya samu ya koma barci sannan ya fito bayan ya kwantar dashi ya fitta domin girgirin abinda zasuce da Buba kafin ya tatso nonon Saniya ya baiwa Kamal yasha , Buba kuma ya tafi kiwon sa .








wanan kenan daga garin Bauchi sai muce Allah ya kyauta ya shirye su , ya 'kubutar da su daga sharrin Inna da Yaranta ….












🥰🤰DUHU CIKIN HASKE ♥️🤰


AL'KALAMIN ƘANWAR SOJA ✍️








🌗DUHU CIKIN HASKE🌗
Dark in light
60% true life
story
by
'kanwar soja ✍️💞
The writter of Mijin Mage , and now 🌗DUHU CIKIN HASKE 🌗





paid book 200 only
wattsppt number
08101235739










_page _


👇👇👇👇

1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣


HANYAR GOMBE






Haka Jauro ya rik'e amanar Ruk'ayya har cikin garin Gombe acan wani local government Bajoga ya samu masauki a gidan wani Abokin sa tunna Yarinta bai 'boye mai komai ba dangane da wannan Yarinyar, cikin ikon Allah ya samu wani gidan

Please Login or Register in order to submit comment