Join Our WhatsApp Group

KARAGAR AJALI Complete Hausa Novel Document by KARAGAR AJALI


KARAGAR AJALI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 84584



KARAGAR AJALI

Reading Time: 7 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Habibullah Muhammad Kabara ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 473.29 kb

File Type: txt

Views: 690+

Download: 768+

Last download: 1 day ago

Description/Story: KARAGAR AJALI

1 PART A

LBR

HABIBULLAH KBR

A wani zamani can baya mai tsawo daya shude alokacin da duniya suka haukace gurin neman daukaka da tarin dukiya
Ba iya sarakuna kadaiba hatta hatta attajirai, matsafa da kuma duk wani mai takama da karfin damtse
Su kansu talakawa a wannan lokaci sunfi daukar dukiyoyi da mahaimmanci fiye da rayukansu
Talaka da duk wani jarumi a wannan lokaci bashi da burin dayafi yaga ya zama attajiri a rana guda
Haka suma attajirai da kuma bokaye
Sarakuna kuwa babban burinsu a wannan zamani shine suga sun mallake duniya gaba dayanta sun dawo da ita karkashin masarautarsu
Domin su sami damar hawa kan wata karaga wacce akewa lakabi da KARAGAR AJALI
Ita dai karagar ajali wata karagace ta musamman wacce fiye da shekaru dubu uku da doriya ba'a taba samun mahalukin daya taba zama akanta
Face mutum guda daya wanda ake kira da sadauki farhan
Shi kadai ne ya taba zama akan wannan karaga wacce take can bangon duniya acikin yankin birnin sin
Cikin wani katafaren gidan sarauta mai dumbin tarihi ana kiransa da darul maut
Wanda tun bayan rasuwar shi sadauki farhan aka rasa mahalukin da zai iya shiga cikin wannan masarauta kuma ya fito a raye saboda tsagwaron. Bala'in da yake ciki
Tun bayan shudewarsa a doron kasa mutane suketa kokarin ganin sun shiga cikin wannan masarauta don su mallaki duniya kamar yadda yayi a zamaninsa
Har zuwa wannan zamanin
Wannan daliline yasa mafi yawan mutane a wannan zamani jarumaine mazansu da matansu
Domin su tsira da rayuwarsu daga farmakin ýan fashi
Acikin wannan zamanin ne akayi wata babbar masarauta mai dumbin tarihi
Wacce ta kunshi kabilu daban daban a wannan lokaci kaf fadin duniya babu masarautar data kai wannan masarauta girma, arziki da tarin dukiya
Ana kiranta da suna ikaril uzbar
Sarkin birnin ya kasance kasurgumin sarki mai matukar karfin damtse gami da sihiri kuma mai tarwatsa maza afilin daga
Ana kiransa da suna gulbas
Arayuwar sarki gulbas babu abindaya tsana face cin amana
Wannan daliline yasa duk duniya babu wanda ya yarda dashi
Hatta 'yarsa ta cikinsa kuwa duk da cewa yana matukar kaunarta kuma sun shaku da juna

Amma duk da haka agabaki daya 'yan majalisarsa da dakarunsa gabaki dayansu babu namiji ko guda daya
Amma ko wacce daya daga cikinsu jarumace kuma mai dakawa maza gumba a hannu saboda tsananin horon yakin da aka basu

Kuma suna daga cikin wadanda suka taimakawa sarki gulbas wajen tara dukiyoyi masu yawa
Saboda su yake turawa da daidai da dai dai kuma asirrance
Zuwa wasu manyan biranen da zarar sun shiga cikinsa. Sun taru sai su farwa dakarun birnin harsai sun tarwatsasu
Sannan su budewa 'yan uwansu kofar birnin da karfin tsiya su yaki mutanen garin
Hatta sarakunan da wadannan 'yan matan dakaru suka hillata ba zasu kirguba
Atakaikace dai wadannan dakaru sun bashi gagarumar gudunmawa acikin mulkinsa
Wannan dalilinne yasa ake kiransu da suna guguwar annoba
Kai bama dakarun birnin ba kadai ba atakaice dai kaf birnin babu namiji ko guda daya face shi kansa sarki gulbas din
Domin kashe mazajen garin ya dinga sawa anayi zaluncinsa bai tsaya iya kan matasa ba hadda yara da tsofaffi
bisa dole suka dinga hijira suna guduwa daga garin
Idan kaga namiji a wannan kasa to ba dan asalin garin bane saidai bafatake
Shidin ma baya wuce kwana uku agarin yake hada komatsansa ya kara gaba
Gaba daya sarakunan dake wannan zamanin babu wanda baya shakkarsa
Kamar yadda sarki gulbas yake da burin mallakar duniya kuma yahau kan karagar ajali
Sai ya zamana cewa bashi kadai bane yake da wannan burin ba
Domin akwai wani gagarumin boka ana kiransa da suna surkais bin bardas
Wanda yake shima takadirin gaskene, haka bayan wannan bokan akwai wani matashin saurayi wanda shima ya kasance sadaukin gaske kuma gagarabadau ana kiransa da jarumi rukyan bin haiwan
shima jarumi rukyan ba kanwar lasa bane a fannin karfin sihiri ba
Domin sau dari ba daya suna haduwa dasu sarki gulbas su fafata kazamin yaki atsakaninsu tsawon kwanaki ba tare da daya daga cikinsu ya sami nasara akan daya ba
Saidai suyiwa junansu jini da majina bisa dole suke hakura su koma kasashensu
Daga karshene tsafinsu ya nuna musu cewa muddin sukayi haduwa cikon ta darin to daya daga cikinsu ba zai tsira da rayuwarsa ba
Sadauki rukyan tun da yake arayuwarsa bai taba tunanin ya yaki wasu sarakunan
Don ya kwace buranensu ba domin gani yake wannan wahala ce matukar ba mulkin duniyar ya karba ba
Dalilin haka ne yasa babu birnin da baya shiga acikin duniya banda birnin da sarki gulbas yake mulki
Kuma dukkan sarakunan biranen sunayi masa biyayyar dole kuma suna girmamashi
Ba komaine ya sanya suke wannan yakinba atsakaninsu face
Sun san cewa duk wanda ya sami nasara akan dan uwansa
Ya kasheshi kuma ya mallaki sihirin tsafinsa to shine zai mallaki duniya gaba dayanta sannan ya dare kan karagar ajali
Kuma ya zama gagarabadau agabaki daya duniya
Tun da sukayi karo na casa'in da tara basu kara fafatawa ba kuma basu sake haduwa da junansu ba don gudun kada bacin rai ya kaisu gayin gaduwa ta darin
A cikin binciken da sukayi ne suka gano cewa matukar suna son ganin bayan juna dolene gaba dayansu
Dole ne su hakura zuwa wani dan takaitaccen lokaci da wani sihirtaccen makami zai bayyana
Duk wanda ya mallaki wannan makami babu makawa sai ya mallaki duniya gaba dayanta
Ba komai bane wannan makami ba face takobin saiful laihan
Wacce a yanzu haka babu wata halitta mutum ko aljan wacce tasan inda aka boye wannan sihirtacciyar takobi
Ita dai wannan takobi alamu sun nuna cewa tun farkon kafuwar duniya
Wasu manyan matsafa ne wadanda suka samar da duk wani sihirin tsafi na duniya
Wato wadannan bokayen wadannan suka kebe kansu acikin tsohuwar rijiya
Har suka sana'anta gunki larazub to sune suka kirkireta suka ajiyeta a wani kebantaccen guri
Cikin gagarumin tsaro na sihirtattun aljanu da dodanni
Tun daga wannan lokaci ba'a taba samun mahalukin daya taba mallakar wannan takobi ba face wani sadauki guda daya ana kiransa da suna farhan da agurin wani mashahurin attajiri mai suna jawwas na birnin taiwan
Farhan bin jawwas shine kadai ya taba mallakar wannan takobi
Har ya iya zuwa ya zauna akan karagar ajali lafiya

Domin tun farkon kafuwar duniya har zuwa yanzu ba'a taba samun jarumi mai sadaukantakarsa, juriya, zafin nama da kuma karfin sihirinsa ba
Lokacinda ajali zai riskeshi ne ya dauki wannan takobin da kansa ya kaita can wani kebantaccen guri mai matukar tsaro ya ajiyeta acan
Yayiwa kansa alkawarin cewa duk duniya babu mai mallakar wannan takobi face ya kasance
Gagarumin sadauki, matsafi kuma mai matukar sa'a da juriyar wahala kamar yadda shi ya kasance a zamaninsa
Kuma saiya karbi horon yaki na musamman a gurin wasu takadiran aljanu
Sunfi guda dubu wadanda ya wakiltasu akan baiwa duk mai burin mallakar wannan takobi horon yaki wanda kuma shine zai zama jarrabawarka
Kuma ta hanyar wannan horone zaka san inda ita wannan takobi take
Kowanne daya daga cikin aljanun da suke bayarda wannan horon jarrabawar kalar nau'in jarrabawarsa daban
Wannan shine dalilin dayasa babu wanda yasan inda wadannan makamai suke
Kuma dole sai ka mallaketa sannan zaka iya shiga cikin masarautar da karagar ajali take ka zauna akanta har ka fito a raye
Tun daga sanda ya mutu har kawo yanzu kowa burinsa shine ya gano inda wannan takobi take domin yaje ya daukota amma an rasa
Manyan sarakuna, bokaye da kuma jarumai marasa adadi sun rasa rayukansu ne agarin neman wannan takobi
Ba tareda daya daga cikinsu ya sami biyan bukatarsa ba
Ita dai wannan takobi wata shu'umar makami ce wacce take kunshe da duk wani irin launin sihiri dake fadin duniya
Masana da masu bada tarihin wannan takobi sun tabbatar da cewa
Duk wanda ya mallaki wannan takobi duk wata nau'in halitta da yake cikin duniya
Sai ya dawo karkashinka kuma zai dinga yi maka biyayyar dole ne
Kamar bawa da ubangijinsa
Da ka mallaketa daga wannan lokaci zaka dinga sarrafa duniya kamar faifai agabanka
Idan dukiya ko daukaka kake nema da zarar ka shafi jikin wannan takobi take zakaga nau'in zinare da lu'u lu'u agabanka iya adadin yawan da kakeso
Koda kuwa yakai girma da zurfin duka tekunan dake cikin duniya
Idan har ka mallaki wannan makami da zarar kayi niyyar sauya kamarka take anan kamarka zata juya zuwa duk siffar da kake bukatar komawa
Idan har wannan takobin tana hannunka zaka iya yakar duniya baki dayanta
Da duk abindake cikinta cikin abinda bai wuce dakika dari da ashirin ba
kuma inda ace zaka shekara kana yaki ba zaka taba gajiya ba
Haka wuta ko makami ba zasu taba amfani ajikinka ba face ita wannan takobin da kanta
Sannan babu wani sihiri ko tsafi da zai yi tasiri ajikinka
Dukkanin abinda aka doka da wannan takobi kuwa take yake dagargajewa kamar gari komai girmansa da kuma kwarinsa koda kuwa ya kasance dutse ne ko kuma karfe
Atakaice dai wannan takobi tana amfani a gurin mamallakinta fiye da kala dubu wadanda su kansu wadanda suka kirkiretan basu gama saninsu ba
Face shi mamallakin ta wato sadauki farhan
Tun daga lokacin dasu sarki gulbas suka gano cewa dolene su mallaki wannan takobi domin su sami damar hawa kan karagar ajali
Sai suka takurawa kansu wajen binciken hanyar da zasu bi domin mallakar ita wannan takobi
Saidaya zamana sarki gulbas ya kauracewa matarsa guda daya tilo wato gimbiya ramsiya
Da kuma 'yarsa gimbiya suhaila tsawon watanni shida ba taredaya gansu ba
Kullum dare da rana babu abinda yake face bincike akan hanyar da zaibi domin mallakar ita wannan takobi acikin dakin tsafinsa
Akwai ranar da gimbiya suhaila ta taba yunkurin shiga cikin dakin halwar tsafin nasa don taga mai yake faruwa aciki
Koda shigar cikin dakin saita iske sarki gulbas azaune ya tankwashe kafafuwansa babu abinda yake yi face bincike acikin hallarar tsafinsa
Har gimbiya suhaila ta karasa inda yake bai juyo ya kalleta ba
Saidata karasa inda yake kawai saita daga hannunta da nufin ta dafa kafadarsa
Koda hannunta ya dauka akan kafafunsa sai taji wani irin mahaukacin zafi kamar ta dorashi akan garwashin wuta
Take ta janye hannun nata daga jikinsa ta ja da baya kadan daga inda yake
Kawai saitaga sarki gulbas ya bude idanuwansa fuskarsa amurtuke kamar wanda aka aiki masa da sakon mutuwa
Ya dubeta cikin daka mata tsawa akaron farko na rayuwarsa alokwcin da idanunwansa suka kada sukayi jajur kamar an gasa dan buda a wuta
Harya daga hannunsa da nufin ya zabga mata mari sai kawai hannun nasa ya tsaya cak akan iska ba tareda ya sauka akan fuskarta ba
Sannan wata kwalla ta zubo daga cikin idanunsa
Ya dubeta yace yake 'yata ki sani cewa shigowa cikin wannan dakin halwar tawa da kikayi a wannan lokaci ba komai kika janyo agareni ba face a sara
Duk tsawon wadannan kwanakin da kukaga nayi acikin wannan halwar badon komai nakeyinsu ba
Face don ganin na cika burina ta yadda ko bayan mutuwata tarihin duniya bazai taba mantawa dani ba
Wannan buri kuwa ba komai bane face hawa kan karagar ajali
Kuma itama wannan karaga bazan iya hawanta ba face na mallaki takobin saiful laihan
Wacce ke kanki kinsan babu wanda yasan inda take a duniya
Ki sani acikin wannan halwar ba komai nakeba face binciken hanyar da zanbi domin na karbi horon yaki daga hannun daya daga cikin hadiman sadauki farhan
Wanda kuma dolene sai na karbi wannan horon amatsayin jarrabawata sannan zansan hanyar da zanbi don mallakar takobin saiful laihan
Abinciken da nayi na gano cewa nanda mako guda zan sami damar fara karbar wannan horon
Kamar yadda suma abokan adawata zasu fara karbar nasu horon
Amma acikin binciken na gano hanya mafai sauki da zan fara karbar nswa horon a wannan ranar
Saidai kuma shigowar nan da kikayi cikin wannan dakin ya ruguza mini duk shirina
Dolene nima sai na jira nan da mako guda don fara karbar nawa horon
Da zarar mungama karbar wannan horo to a sannan ne zamu san inda ita wannan takobi ta saiful laihan take
Sannan muje mu daukota
Koda jin haka sai take nadama tazowa gimbiya suhaila kawai saita fado kan kafadunsa tana mai cewa
Kayi hakuri yakai abbana bansan cewa shigowa ta cikin wannan turakar taka zai zama silar rushewar burikanka ba
Amma zanso idan ka gama karbar wannan horon yakin
Na rakaka zuwa can inda wannan takobi take domin nima na ganewa idona irin matakan. Tsaron da suke kan hanyar zuwa inda take sannan mu dunguma gaba daya mu tafi can darul maut domin hawa ita kanta wannan karagar mulkin data gagara hawa
Dajin wannan bukata ta gimbiya suhaila sai sarki gulbas yayi shiru
Yana nazarin bukatarta acikin zuciyarsa tsawon lokaci mai tsawo daga can sai yace
Yake 'yata wannan bukatar taki ba wacce zanyi saurin. Yankewa hukunci bace
Ki jira fitowata daga cikin wannan dakin tukunna bayan na gama karbar horon yakin idan har na fito a raye zan bayyana miki hukuncin dana yanke
Gimbiya suhaila tayi murmushi tace
Shikenan ni kuma zan zamo mai jiran fitowarka har zuwa lokacin da zaka fito
Tana gama fadin haka sai ta juya ta fice daga cikin dakin
Fitarta keda wuya sai kofar turakar ta maida kanta ta rufe
Sannan sarki gulbas ya koma ya zauna akan buzunsa na tsafi ya cigaba da tsatsube tsatsuben da yakeyi don neman hanyar karbar horon sadauki farhan
Ita kuwa gimbiya suhaila koda ta fice daga cikin dakin sai ta wuce kai tsaye izuwa hanyar da zata kaita can bargar dawakai
Don ta dauki ingarman dokinta ta shiga gari yin rangadi don ta manta da abinda ya faru tsakaninta da mahaifinta
Duk da kasancewar sarki gulbas azzalumin mutum ne kuma mai takurawa talakawansa
Sai ya zamana cewa ita gimbiya suhaila sai halayyarta ta banbanta data mahaifinta
Don ita mace ce mai son talakawa da kuma burin kyautata musu
Wannan dalilinne yasa talakawa suke matukar kaunarta kuma ashirye suke dasu sadaukar da rayukansu adalilinta
A kowacce rana idan suhaila zata bar gidan sarauta dana diban dukiya mai tarin yawa
Kuma bata daukar badakariya ko guda daya domin tsaron lafiyarta
Saboda ita kanta basadaukiya ce kuma wacce take takama da tsagwaron karfin damtse da kuma na sihiri
Domin ita kadai tana iya shiga cikin dubunnan dakaru da karfin tsiya ta tarwatsasu kuma ta kama na kamawa
Idan ta fito tana rabawa talakawa masu bukatar taimako duk wannan dukiyar data debo daga cikin baitil mali
Haka idan tazo guri taga ana aikata zalunci saita tsaya ta hana wannan zaluncin sannan tasa wanda aka zalunta din ya rama daidai da abinda akayi masa
Bisa wannan dalilinne yasa aduk ranar data fita rangadi sai kaga mutane suna walwala da nishadi
Wannan halayya ta gimbiya suhaila ba karamin batawa sarki gulbas rai take ba
Domin shi yaso ace irin halayyar sa ta gado ta yadda zasuyita cin karensu babu babbaka
Lokacin da gimbiya suhaila ta fita daga cikin gidan sarauta ta kutsa kai cikin gari
A wannan lokaci gaba daya ta manta da maganar dukiyar data saba rabawa talakawa
Sai tayita kutsawa cikin gari kamar yadda ta saba amma a wannan lokaci kana kallon fuskarta zaka fuskanci cewa akwai damuwa karara akanta
Wannan daliline yasa gaba daya mutanen da suke daga mata hannu gami dayi mata jinjina bata lura dasu ba
Tana cikin tafiyane kawai sai zo giftawa ta bakin wata katuwar kwata wacce ta kasance magudanar ruwa ce
Har ta gifta ta bakin kwatar kawai saita hango wani dattijo aciki ya fada ruwa yana kokarin tafiya dashi
Koda ganin wannan abu saita daka tsalle daga kan dokinta ta fada cikin kwatar
Ta dauko wannan dattijon koda ta dauko shi saita lura cewa makaho ne domin bashida idanu...


Read / Download KARAGAR AJALI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album