Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

YANCIN BAYI Complete Hausa Novel Document by YANCIN BAYI


YANCIN BAYI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19227



YANCIN BAYI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 23, Jun 2024

Author: Surayyerh B Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 112.53 kb

File Type: txt

Views: 2098+

Download: 1237+

Last download: 1 day ago

Description/Story: *Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟*
{Historical fiction}



*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻


*SURAYYERH B.ADUL*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*SANARWA*

*Dafarko littafinnan na siyarwa ne amma saboda murnar shiga sabuwar shekara yasa namaidashi free*


Dz book completely goes to *HASSAN 80k & HUSSAIN 90k*



*Special gift to my besty*

*UMAMATU UMAR ADAM*


*APPIE NEW YEAR 2020*


*PAGE 1*



Bismillahirrahmanirraheem.




Kallo daya zakayiwa gidan ka fahimci cewa talauci yayiwa ahalin gidan katutu sosai a gindinsu,duk da kasancewar gabadaya gine ginen garin na jar kasa ne kuma gajeran gini,amma Wannan gdn daban yake a cknsu don ko arzikin gini da laka ma bai samu ba,ginin langa langa ne itama ta lalace sosai don duk ta bubbule tayi tsatsa,,gajeran ginin bandakin gidan ne kawai na laka amma hatta dakunan ckn gidan na kara ne dama kuma guda 1 ne.


Wata matashiyar budurwa ce wadda batafi 18 year's ba tafito daga gidan ckn sauri kafarta na sanye da wani kodadden silifas wanda aka kulle da leda saboda tsinkewar da yayi,kana kallonshi zaka hango tarin dinkunan da akai masa, tana sanye da bluen yadi dinkin riga da zani single, kallo daya zakayiwa kayan kabashi sunan uniform, batada hijab sai dankwalin da ke daure a kanta wanda bai hana dogon kashin kanta da ke kitse da manyan kitso fitowa ba,dogowa ce siririya chocolate colour,tanada tsananin kyau na fada a ko'ina me ban mamaki,idanuwanta manya wanda idon ka kalleta zakayi tunanin tanajin bacci ne,,hancinta dogo ne me tsananin kyaun fasali,,bakinta girmansa dai² gwargwado abin sha'awa,gaban goshinta wani kwantaccen gashi ne baki sidik wanda yai bala'in kara mata kyau kana kallonta zaka fahimci tanada sanyin hali.

Ckn sauri take kokarin barin kofar gdn nasu tajiyo muryar mahaifiyarta sama² tana kiran *MUWADDAH! MUWADDAH!!*,murmushi tayi tareda girgiza kai tana buga kafa irin na shagwababbun yara,,da gudu takoma ckn gidan tashiga dakin karansu wanda akaiwa labule da wani yamushasshen buhu,mahaifiyarta na xaune da Kofi a gabanta ta zubawa kofa ido da alamun tana jiran shigowar muwaddan.

Tana shiga ta kyabe fuska kamar zatayi kuka, ckn shagwaba tace "Don Allah iyata ki banni nayi tahiyata kada ayi babu niya,,takarasa tana turo baki gaba.


Murmushi mahaifiyartata tayi ckn kulawa tace " muwaddatu na ki rage wanga zumudi kyajiya??,,kizo kisha kunun nan ko kadanne banson ganinki da yunwa koda nikuwa zan dawwama cknta,, takarashe ckn raunin murya.

Shiru muwadda tayi ckn matsanancin tausayin mahaifiyar tata,Abubuwa da dama ne suka shiga dawo mata tamkar ynz suke faruwa,lokaci guda idonta yakawo kwalla alamun zatayi kuka,kallonta takai kan kafafuwan mahaifiyarta da ke kunbure suntum rabinta a rarake an barbada magani amma hakan bai hana hango kashin kafar ba, wani gigitaccen kuka ne ya kwace mata,durkushewa tayi a gurin tanajin zuciyarta tana mata matsananciyar suya, ckn kuka take cewa "Allah yai miki sakayya iyata!!!Allah yaiwa Babana sakayya!!! Wlh natsenesu!!banida makiyan da suka hisu,,Tabbas bantabba ganin mugaye Azzalumai wadanda kansu kawai suka sani ba tamkar *MASARAUTAR ZINARI*,,,natsanesu iyata!!Wlh bana kaunar ganinsu!!!Takarashe dasakin wani gigitaccen kuka.


Cikin dauriyar gaske mahaifiyarta ta janyota jikinta tareda goge mata hawayen fuskarta tana bubbuga mata baya,,tasani tabbas ya cancanta muwadda tayi kuka,amma baxata nunamata hakaba dole ta tausashi zuciyar yar tata saboda shine abinda yafi komai cancanta da tayi ko da kuwa bataso,,cigaba da buga bayan muwaddan tayi har saida tayi shiru sai sheshshekar kuka da takeyi,daukar kofin da ke gefenta tayi tanufi bakin muwadda,,,kauda kai tayi alamun baxata sha ba,Ajiye kofin iya tayi a gefenta tareda kawar da kanta gefe,,dasauri muwadda ta taso tarike hannun mahaifiyarta tareda goge hawayen fuskarta tace " Kiyi hkr kyajiya iyata??To zansha.

Ba musu iya tadauko kofin kunun da baifi rabi ba ta mikawa mata,,karba tayi ta kurba sau uku ta ajiye tareda mikewa tace "iyata ni zantahi,ki tayani da addu'a Allah yasa ina daga ckn bayin da sarki zai y'anta yau,,badon kamai ba don nasamu damar kula da ke.

Ckn kulawa iya tace " Karki damu diyata nayi miki dama,,maxa ki tahi kar ki makara.

Ckn sanyin jiki ta fito daga gidan nasu,,tana tafiya tana sauri tare da sharar hawaye,tayi tafiya mai nisa kafin taxo kofar wani dankamemen gida me tsananin kyawun gaske,,duk iya kulewarka a kallo baxaka hango karshen gidan ba,,gine ne tamkar a kasar turai,bazaka taba tunanin a ckn garin yakeba,,kallo daya zakayiwa gidan ka tabbatar gidan sarauta ne,,A can saman katuwar kofar gidan aka rubuta *MASARAUTAR ZINARI*.

Ckn sauri ta wuce masu gadin gidan ta shige ciki,,bayi ne birjik kowa da abinda yakeyi,,dukansu mazansu da matansu suna sanye da yadi blue irin na jikinta amma maza wando ne,mafi yawansu fuskarsu dauke da annuri suke aiwatar da al-amuransu.


Kai tsaye wata doguwar hanya tabi,batayi tafiya mai nisa sosai ba sai gata a wani bangare me tsananin kyau,,bayi maza guda biyu suna kofar shiga wajen a tsaye sunyi kekam ko cikakken motsi basayi,,yayinda wasu mata bayi suke shawagi a wajen.

Batareda fargabar komaiba tashiga wajen,,hadadden parlour ne mai tsananin kyawun gaske wanda aka kayata da kayan Adon sarauta,,wasu bayi yammata guda 4 suna tsaye a dakin babu wadda takewa yar uwarta mgn,,haka tabi sahunsu ta tsaya a inda suke,,a kalla sunshafe awa 2 tsaye a wajen amma kaf cknsu babu wadda zaka kalla kace tagaji da tsayuwar,don da alama sungama sabawa.


Cikin tsananin takun kasaita da kololuwar ji da kai take tafiya tamkar bata kaunar taka kasa,,bayanta wasu bayi ne a kalla sunkai 8 suke take mata baya,, yayinda daga cknsu ke rike da hadaddiyar Alkyabbarta wadda tagaji da haduwa.

Suna hangota gabadayansu ckn rawar jiki suka zube suna jero mata kirari,,batare da ta kalli ko dayansu ba taxauna akan hadaddiyar kujerar sarauta,,cigaba da jero mata kirarin sukai ba kakkautawa,a kalla saida suka shafe 20mints suna Abu daya kafin daya daga ckn bayin da ke tsaye tace *GIMBIYA JALILA* ta amsa gaisuwarku yayan talakawa.


Sai a sannan suka mike daga tsugunnan da sukayi.

Ckn matukar kyama gami da tsananin wulakanci da kaskanci gimbiya jalila ke binsu da kallo,,saukar da kai kasa muwadda tayi don ko kadan bata kaunar kallon fuskar gimbiya jalila saboda tsananin tsanarta da tayi.

Wulakantaccen kallon da gimbiya jalila ke aikawa muwadda na musamman ne,,batasan me yasaba yarinyar ba abinda tai mata amma tana tsananin tsanarta fiye da kowa,kuma baxata ce ko saboda kyawun muwaddan bane don itama kyakykyawa ce amma tabbas tsanarta me tsanani ce a ranta.


Daga ckn masarautar suke jiyo muryar wani bafade yana sanar da cewa sarki yabada umarnin kowa ya hadu a fada ynz saboda gabatar da yantaccun bayi na Wannan shekarar,,dadi ne yarufe dayawa daga ckn bayin banda muwadda wadda ta tsinci kanta da tsananin bugawar kirji da tsoro dukda cewa tayar darwa zuciyarta tana daga ckn bayin da yakama ace suna sahun farko a wadanda za'a yanta,,ita abinda yasa take kaunar a yantata saboda tasami damar kula da mahaifiyarta yadda yakamata.

Gimbiya jalila batayi mgn ba sai baiwar da tayi mgn dazu ce tabasu umarnin yafiya,,said da suka yi gdy sannan suka fita.


Suna fita ubaida taja hannun muwadda fuskarta dauke da fara'a tace "muwadda nasan kina ckn bayin da zasu sami yanci yau,,na tayaki murna".

Girgiza kai muwadda tayi ckn sanyin jiki tace " Allah yasa ubaidah".

Ameen amma nikam nasan ma hadda ke,,saboda kaf gdnnan babu wanda baisanki wajen aiki ba.

Shiru muwadda tayi har suka karasa katuwar fadar masarautar inda suka tadda bayi dankam wasu suna farin ciki wasu suna fargaba.


Lkc guda wajen yayi tsit tamkar babu wani Abu me rai a wajen sakamakon shigowar *SARKI ALIYU* da ahalinsa.

Zubewa sukayi gabadayansu ckn girmamawa suka kwashi gaisu*Y͟'A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟*
{Historical fiction}


*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻



*SURAYYERH B.ABDUL*




Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k*


*Special gift to my besty*

*UMAMATU UMAR ADAM*

___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


___________________________________






*PAGE 2*



Bismillahirrahmanirraheem.


Sunjima sosai a tsugunne kafin abada umarnin mikewa.


Sarki Aliyu da iyalansa suna zaune akan wasu hadaddun kujeru masu tsananin kyawu gefensu bayi nayi musu fiffita sai kuma wasu a bayansu wasu a zaune a gabansu,waziri ne yamike tsaye tareda yin bayani kamar haka:
"Sanin kanku ne cewa a kowace shekara a masautar nan ana dibar bayi guda 50 a yanta su,,To ynz ma Allah yakawomu lkcn saboda haka ynz ba bata lkc za'a gabatar dasu,ihu mutane sukasa ckn farin ciki tareda jerowa masarautar kirari,,,tunda waziri yafara mgn kirjin muwadda yake bugawa tanajin ance ynz za'a fara kiran sunan wadanda za'a yanta kafafuwanta yayi mugun sanyi kamar zata zube amma ba dama,don babban laifi ne a masarautar sarki yana zaune ka zauna kaima.


Wani bafade ne yamike da zungureriyar takarda a hannunsa yafara kiran sunan wadanda aka yanta,,wajen yayi tsit kowa kirjinsa yana bugu saboda fargaba,,tuni muwadda tagama sarewa ganin an kirawo mutane 46 amma ba sunanta,wasu hawaye ne masu matukar zafin gaske suka shiga tsere a kuncinta,sosai zuciyarta take suya da radadi,bata kara tsinkewa da
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download YANCIN BAYI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album