Join Our WhatsApp Group

ZURFIN CIKI 1 to 4 Complete Hausa Novel Document by ZURFIN CIKI 1 to 4


ZURFIN CIKI 1 to 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 106905



ZURFIN CIKI 1 to 4

Reading Time: 8 Hours

Added On: 28, Jul 2023

Author: Jamila Umar Tanko ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 540.72 kb

File Type: txt

Views: 2451+

Download: 2458+

Last download: 9 days ago

Description/Story:
Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 1 part 1
ZURFIN CIKI book 1 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 02:16
UUmmi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu
hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata
tafiya a hankali.daga can gefe ta hango wata
yarinya wadda bazata wuce sa'arta ba.
tace,"yauwa,ga firdausin data tsokane ni" ta nufi
wurinta ,tasha gabanta ta rike kugu. "fiddausi wa
kike tsokana? fiddausi tace "ban tsokane ki ba
fa".cikin tsoro tayi maganar .ummi ta shako mata
wuya. ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga.ban
ce ba inji fiddausi .ummi ta hankada ta tare da
cewa "Allah yaso ki." nikan garin da fiddausin tayi
ya tarwatse a kasa tace "kin gani ko? wallahi sai
kin biyani"ta soma kuka,ummi ta sheka da
gudu,sai gida. tana ajiye man gyadan data siyo ta
nufi ba daki don fitsari ya matse ta .umma dake
zaune tana fadin. "da mutum!da mutum!!" saida
ummi ta bude . Ganin yaya Abba tayi,da gudu ta
juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi
bol da dakakken yajin da umma ta daka zata
soya mai don cin abincin rana. sai kuma ta tuna
cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai binciko ta.ta
fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa. tsohuwar tana
sallar azahar.ummi ta tsallake ta ta kutsa kasan
gado.nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson
sha da zarar ta idar da sallah. Alhaji babba tasa
ya aiko mata da furar daga kasuwa.don tasha da
rana. Abba ya fito wanka ranshi a bace.dakin
umma ya nufa yana fadin "ummi ke ummi zonan"
Ya samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta
zubar, tana fada. Ya ce, "Umma ban san irin
dukan da zan wa Ummi ba yau. Ta ce,"Abba ka
mata dukan mutuwa, na gaji da halin Ummi.
Yarinya sai ka ce 'yar fata? Ka dubata ta tafi
dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a dake ta."
Ya ce,"Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta,
amma ba zan barta ba. Ya juya zai tafi, suka ji
muryar Tsohuwa tana fadin. Ba zan yi fada ba, ka
kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka
barta da rai. Ta dubi Umma" ke kuma Suwaiba
dama kin san ba za ki daraja sunana ba ki ka sa
a ka sa miki don kiji dadin ci min fuska?" Umma
ta ce," Ba haka ba ne Tsohuwa, Ummi ba ta yo
halinki ba. Ita fa rashin hankali ne da ita. Yayanta
fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta
zubar min da barkono. Abba ya ce, "Umma don
Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta
6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta
hana a yi mata fada. Uhm duk fadanki yau sai na
dake ta, ba sunan ki ba in ma kece,"Tsohuwa
tasa kuka gami da salati. "Yanzu mai sunan
Malam ni ka ke fadawa haka?" ya ce, "An fada
miki." Umma ta ce, "kai Abba zan sa6a maka
jeka." Ta juyo wurin Tsohuwa, Don Allah kiyi
hakuri............... Maman Fiddausi ce tayi sallama
tare da Fiddausin suka shigo. Ran Maman
Fiddausin a 6ace, ta tsaya rike da gari a
hannunta ta dubi Umma. Ta ce, Umman Abba
dubi abn da Umminki tayi min don Allah, yarinyar
nan tayo nika da kyar," tun safe sai yanzu na
samu, amma ta zubar min." Abba ya ce, Kinga
halinta ko?" Tsohuwa ta ce, "Wannan ba matar
Bala ba ce?" Maman Fiddausi ta ce, "Ni ce." Ta
ce," To kije kije ki nemi wanda ya zubar da
garinki, Ummi ko fita ba tayi ba. Umma ta ce, "
Ta fita Tsohuwa, na aike ta siyan mai." Tsohuwa
ta ce," Tsokanarta a ka yi to. Umma ta amshe
abin garin ta zuba musu, sannan ta ce, "Don
Allah Tine kiyi hkr." Abba ya nufi daki. Sai da ya
shirya tsaf, sannan ya dauki belt ya nufi cikin
gida, dakin Tsohuwa ya shiga kai-tsaye kasan
gado ya nufa. Ya jawo ta, ta soma kurma ihu.
Daya ya lafta mata amma ta dane shi tare da
cukwikuye belt din tana ihu. Tsohuwa ta iso tana
dukanshi a baya, fadi take "Za ka kasheta ne?
Jama"a kuyo dauki. Haushin hakan yasa shi
damko kanta ya shiga zuba mata kola, ya
sirmiyota ya shiga lafta da takalminshi, tunda ta
hana belt din. Sai da ya mata tas, sannan ya fita
ya bar su, Tsohuwa na kuka Ummi na kuka. , Sai
da komai ya natsa ta leka ta jawo furarta don
tasha, sai ta ganta a zube. Ta ce, A" a ke ki ka
zubar min da fura?" Ummi ta ce, To ba shi ne
janyo ni ba Yaa Abban. Tsohuwa ta ce, "Ai ko sai
ya siyo min furata. Ta mike ta wuce Umma tana
rabon abinci, ta nufi soro in da dakin Abba yake
(Zaure) Ya fito yana rufe kofa, ta ce "Au za ka
fita ba? To ka sawo min furata da ka zubar. Ko
kallonta bai yi ba ya rufe kofarshi ya wuce. Ta ce
mishi "Aikin bana, in ba siyo min ba ubanka ai ya
dawo ko min dare ya sito min. Abba ya ce, Ku ku
ka sani. Ra ce, kaima ka sani, dan jakar uba. Ta
dawo ciki tana mitar ya cika bakin rai. Umma ta
ce, "Ina Abban? Tsohuwa ta ce, "Ya tafi, in bai
sai min furata ba ranshi zai 6aci yau a gidannan.
Umma ta ce "Ni bai ma ci abinci ba ya fita, ke
Ummi zo ki kira min shi, yunwa fa yake ji.
Tsohuwa ta ce, "Ba za ta kira shi ba, ya dake ta
sannan ta kira shi? Tunda bai barta taci da dadin
rai ba, shi ma ba ya ci ba.,, Umma tayi shiry,sai
haushin Ummi da take ji kamar ta shake ta ta
mutu. Ummi tayi wanka ta zura kayan Mkrnt,
tana saka sandal Umma ta ce, "Ina Ummi? Zo
nan." Ummi ta tafi tana cewa a ranta. "ALLAH
YASA DAKIN YAYA ABBA ZA TA AIKE NI, SAI NA
RAMA DUKAN DA YA YI MIN JIYA, DON YANZUN
DUK ME YA MIN SAI NA RAMA.........." Umma ta
katse mata tunani da cewa,"dauki shayin Abba ki
kai masa kada yayi latti,kai shayin ki dawo ki
dauki dankalin,yau shi kadai ma nayiwa dankalin."
Tace,"nifa?"umma tace "ke kina cin dumame
Abba ko ba ya ci,dan haka dan wanda ya rage
shi nayi wa." Ummi ta figi kayan tea din ta nufi
dakin Abba tana tura baki.tare da sallama bata
jira amsa ba,ta daga labule ta fada. Dabi'ar da
yake mata fada akai kullum,ya gama saka
singiletinshi kenan yana kokarin saka riga. Yace,
"wai ke wace irin majanuniya ce?ban ce miki in
kinyi sallama sallama sai na amsa za ki shigo
ba? sai kawai ta saki tiren,ruwan zafin ya zube
masa a kafa,dankalin ya watse kan rigar da zai
saka. tayo waje da gudu,sai dakin tsohuwa.ya
fito da sauri yana cewa,"umma ta kona ni! ta
kona ni!!" da sauri umma ta fito daga dakin Alhaji
babba,shima Alhajin na biye da ita yana fadin
"wacece ta kona ka?" Yace "ummi ce! ummi
ce!!."nan take Alhaji babba ya rike kafar yana tofa
mishi addu'a. Umma ta debo kullun kamu ta zuba
mishi,amma duk da haka sai da yan yatsun
kafarsa suka kumbura. tsohuwa ta fito daga daki
tana fadin,"kai ummi bata ji? wai ni meyasa aka
sa mata sunana?" Abba ya kalli tsohuwa cikin
takaici yace,"duk ba ke kike daure mata gindi ba?"
Umma ta shiga dakin tsohuwa ta janye kayan da
tsohuwa ta jera don kada aga ummi,ta janyota
tun daga dakin take kwallo da ummi har waje.
Alhaji ma yau har dashi aka zane ummi,tsohuwa
dai sai yan mitoci take yi,wai yanxu haka ma
bata sani bane. Abba dai ranar dai bai je
makaranta ba,haka nan da yamma sai da ya saka
ummi a dakinshi ya bata gwale-gwale sannan ya
zane ta. misalin hudu da rabi na yamma,Ahmad
abokin Abba yayi sallama a kofar gidan,Abba ya
amsa ya fito. Suna zaune kan dakalin kofar gidan
suna hira,sai ga ummi ta yanko da gudu tana
waiwayen baya. Ya ce,"zo nan."tazo yace,"kinyo
tsokanar fada ko?" tace,"a'a.yace in har tsokana
ki kayo zaki sani shegiya mummuna kazama. Ta
murguda baki,yasa takalmi ya jefeta,ta shige gida
sai ko ga wani yaro jiki duk kwata yayyanshi na
biye dashi. ya tambayesu,suka ce "ummi ce ta
jefa shi kwata"ya taso yaron har cikin gida ya
kamota dakin tsohuwa ya tsareta ta wanke ma
yaron jiki,ta kuma wanke kayan. sannan ya
zuzzuba mata kola a kai.tsohuwa tana ta yiwa
yaran fada,wai ita ma su daina tsokanarta Umma
ko lekowa bata yi ba,ya fito ya samu Ahmad yana
cewa "kayi hakuri na barka kai kadai." Ahmad
yace,"ba komai" sai Abba ya zauna sannan
Ahmad ya dube shi. Abba wannan kanwar taka
kuwa bata da Aljanu? Abba yace,"ba kowa
akanta,sai iskanci." Ahmad yace."a'a,kai dai ku
kaita ayi mata rukiyya." Abba yayi dariya,sannan
yace kasan Allah ba kowa akan ummi,saboda
Alhaji karami ya taba yin wannan tunanin. ya
dauke ta yakai ta rukiya bata da komai."Ahmad
yace tabdi!,gaskiya in ta isa aure duk wanda ya
aureta akwai aiki babba a tare dashi. Abba ya
ce,"wane mahaukaci ne ma zaya dibar ma kansa
ummi?"Ahmad ya ce,"sai ai muku hadin ggida..."
ya kaima Ahmad naushi a gefen ciki,Ahmad ya
kauce yana masa dariya. Abba ya ce,"ka cuce
ni,ace in auri ummi ai sai na hada kayana na bar
garin nan. nan. Ahmad ya s heke da dariya har
da rike ciki.sannan ya ce,"don me? Abba ya
ce,"to wannan yarinyar ba sai ta hada maka
gobara gida ba?gata kazama ga muni." Ahmad ya
ce,"kama dai kuke yi." Abba ya bata rai,"Ahmad
bana so.in har da gaske ina kamada ummi ba sai
na koma ciki an sake haifana ba. Don Allah ni
tashi ma ka tafi,don wallahi da don kai bane kake
fada min haka da sai munyi rigima,na tsani
ummi,bana sonta sam! Zaune suke a kofar gidan
Alhaji babba kan katuwar tabarma,sun jere abinci
suna ci. kullum Alhaji babba da Alhaji karami nan
suke zama tamkar tagwaye,suna matukar kama.
mafi yawancin lokuta ma kaya iri daya suke
sakawa,domin Alhaji babba duk kayan daya saya
tare yake sai musu. haka nan hula ko
takalmi,haka nan matansu baya
bambantawa.shima Alhaji karami duk da bai kai
samun babba ba yana koyi dashi. Alhaji babba ya
kalli karami yace,"Aminu ya zancen makarantar
bashir?" Alhaji karami ya dubi wansa ya ce,"Alhaji
bashi fa ya fadi jarabawa,jiya na tsare shi da
maganar sakamakon jarabawarshi yace bai duba
ba,saida yaji nace zan hada shi da Abba suje
sannan yace min yaje wai duk ya fadi. Alhaji
babba yace,"Ash sha! sai ya maimata shekara
kenan?"Alhaji karami ya ce,"to in ma ba zai
maimaita ba Alhaji shi ya sani,ba sahura ta bata
su ba? shi Abba ai ba haka yayi ba,ka dubi fa
yadda yaki aikin kanikancin nan,uwarshi ta zuga
shi wai yayi karatu kadai yayi aikin gwamnati.
kullum haka sahura take kitsa ma yaran."Alhaji
babba yayi yar dariyar takaici,sannan yace"in
banda abin sahura yadda kasan nan tamu ta
zama waye zaici alwashin aikin gwamnati? ina ce
masu digree ne ke yawo ba aiki?" "har masu
masters." inji Alhaji karami.ya tashi zaune daga
kishingidar da yayi,yace dubi misalin dan
abokinnan naka Alhaji buhari." Alhaji babba ya
ce,"kwarai kuwa,mas'ud ba.yanxu ma fa kasuwa
yake zuwa,sai yanxun yake koyon kasuwancin."
Alhaji karami ya ce,"to daya dora shi a kasuwar
fa tun farko?shi yasa na fada ma sahura ta bar
yara su hada da sana'ar hannu. Donni dai yaro
kamar bashir yanxun ba zan dauki kudina in ba
shi ba."Alhaji babba yace,"shi yasa kulum nake
kara son Abba,yaron nan da kanshi yace min in
kai shi shagon dinki. Har naki suwaiba ta
ce,"Alhaji ka kai shi in ya iya sana'ar hannu ko
bai samu aikin gwamnati ba zai rike kanshi da
sana'ar nan." Alhaji karami ya ce,"to ai kasan ita
suwaiba tasan abinda take yi.amma sahura sai
addu'a." Sallamar Abba ce ta katse su,ya zauna
can gefe sannan ya gaishe su,duk suka amsa tare
da tara hankulasu gurinshi. Ya mika ma Alhaji
babba kullin takarda tare da cewa "Alhaji gashi
maganin (ulser)ne" Alhaji babba ya amsa ya
ce,"Abba sarkin amsa magani, a gurin wa ka
samo wannan kuma?" ya ce,"Ahmad abokina na
raka ya amso ma babanshi,shine nace bari in
amso muku" yace to Allah ya saka da
alkairi."Alhajikarami yace"dame ake sha?" Abba
ya ce,"da madara peak." suka ce"to" daya mike
zai shiga gida Alhaji babba yace ya shige da
kwanikan abincin. yau kam Abba bacci yake ji da
wuri,don haka ya baro shagon dinkinsu wanda ya
kan kai goman dare a ciki ya nufo gida. Ya bude
dakinshi ya shiga ya cire riga sai singileti da
gajeren wando na jeans.ya nufi ciki don ya kama
ruwa ya kuma yi wa ummanshi sallama. tsakar
gida ya sameta zaune ta zabga tagumi,inda
abinda Abba ya tsana shine,yaga ummanshi cikin
damuwa. da sauri ya isa wurinta,"umma
lafiya?"ta dube shi "ina fa lafiya,ummi ce tunda
tayi sallar isha'i ta fice kusan awa guda zance
jiya ka mata dukan fita wasan dare?" Abba yace
"to wai me za'a yi wa ummi ne ta zama irin
sauran yara?" umma tace,"addu'a ce Abba,kuma
muna yi kullum." ya juya cikin bacin rai,layin su
Amina kawarta ya nufa,don bata wuce can.duk da
cewa Amina bata kaita rashin ji ba. can din kuwa
ya sameta,ta tara zugan yayan layi sai tsokanar
fada suke yi,ita ce shugaba. wata falwaya Abba
ya samu ya jingina yana kallonsu,don yana iya
tunkararta su diba da gudu. shi kam ba za ya iya
guje-gujen nan ba,duk wanda yazo wucewa sai
sun tsokane shi,wani su jefe shi,wani kasa zasu
watsa masa su gudu wani kuma rigarsa zasu ja.
c can wani shida budurwarsa sun zo wucewa ta
fizge ledar hannunsu ta watsar,sannan suka ruga
da gudu. tayo gurin da Abba ke tsaye bata zaci
da mutum a gurin ba,sai dai taji anyi caraf da
ita.sai da Abba ya zabga mata koso a tsakiyar
kai har tayi fitsarin wuya,sannan ya tasata har
gurin mutumin data yaga ma ledar. suna
tsugunne suna tsintar lemunsu da ayaba ya
ce,"malam ga wadda ta yaga muku leda." da
zafin nama mutumin ya mike,Abba ya
ce,"gata"mutumin ya shakota yace yau sai naga
ubanki." Abba ya ce,"ko kara ka kai gidansu nine
zan hukuntata,don haka gata na kawo maka
kanwata ce kuma naga lokacin data tsokaneka."
jikin mutumin yayi sanyi ya ce,"na gode bawan
Allah,taje taci albarkacinka." Abba yace "daka
nade ta." mutumin yace,"ba komai,ke kuma ki
canza hali ke mace ce." Abba yace nagode"
sannan ya tasa ta zuwa gida. Bokiti ya cika da
ruwa ya dora mata,,umma rasa bakin magana
tayi daya sanar da ita tsokanar daya tarar da
ummi suna yi. Daga karshe ta ce,"Allah ya
shiryaki,abind ya sameki kada ya sami sauran
dangi. Alhaji kuwa daya sameta dauke da bokitin
tana kuka tana fadin "yaya Abba na tuba,bazan
sake ba." ya ce,"uwata bakya ji ne fatan Allah
yashirye ki."ya nufi dakinshi.tsohuwa takaicin
Abba ne ya hanata fitowa tayi magana. nata
ganin,ummi bata wuce fita tayi wasa da
kawayenta ba,a cewarta ba laifi ba ne. amma an
bi an tsangwami yarinya,an hanata walawa.sai da
Abba ya gaji dan kanshi sannan ya sauke mata
ruwan. Sannan ya mammaka mata
takalmi,sannan ta shige dakin
tsohuwa.tsohuwana daga kwance ta dubeta.
"yaga dama ya kyaleki?kai mai sunan malam
akwai mugunta.zo ki kwanta." cikin kuka ummi
tace,"kayana sun jike,bokitin ruwa fa ya dora
min."tsohuwa tace,"barshi da halinsa,ace mutum
ba zai sake ba?" ummi tace,"ai sai na rama,shima
din sai yayi kuka."tsohuwa ta ce,"a'a,kada ki
soma zancen ramakon nan.kin san ko kin rama
ke ce zaki kwan ciki." ummi ta ce,nifa sai na
rama."tsohuwa ta ce,"baki gaji da shan wahala
ba kema da shegiyar gaddama,ga zanina nan
kikin raki ciro ki daura kizo ki kwanta." ummi tayi
lamo bayan tsohuwa tana tunanin dame zata
rama abinda Abba yayi mata jiya.har bacci yayi
gaba da ita waiwaye............. SULAIMAN shine
asalin sunan Alhaji babba,Aminu kuma shine
Alhaji karami. tsohuwa itace mahaifiyar su,kuma
su kadai ne yayan data haifa.Asalinsu yan
zamfara ne a kauyen daji a karamar hukumar
kauran-namoda. malam Idris mahaifinsu shine ke
zuwa yawon fatauci,har Allah ya zaunar dashi a
garin kano,da matarshi Habiba. sunzo da
yayansu guda biyu,sulaiman da Aminu.sun yi
karatun muhammadiyya mai zurfi,amma basuyi
karatun boko ba. sannan ya dora sukan harkar
kasuwanci,Allahya albarkaci kasuwancin Sulaiman
inda harkoki suka bude mishi cikin kankanin
lokaci. matsalar shi daya rashin boko,malam
idrisu mahaifinsu yana daya daga cikin wadanda
basu amshi boko ba lokacin da tazo. Don haka
sam bai saka yayansa ba.Sulaiman ya auri
Suwaiba wadda suka dauki watanni suna
soyayya,ita yar...


Read / Download ZURFIN CIKI 1 to 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album