Join Our WhatsApp Group

YAN UWANA NE Complete Hausa Novel Document by YAN UWANA NE


YAN UWANA NE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 212629



YAN UWANA NE

Reading Time: 17 Hours

Added On: 13, Sep 2023

Author: Billy S Fari ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.22 mb

File Type: txt

Views: 749+

Download: 1155+

Last download: 24 minutes ago

Description/Story: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHIM INA MAI FARINCIKIN SAKE HA'DUWATA DAKU MASOYANA ACIKIN WANNAN SABON LITTAFI NAWA MAI SUNA A SAMA👆 TARE DA ROK'ON UBANGIJINA DAYA BANI IKON KAMMALASA CIKIN K'OSHIN LAFIYA DA AMINCI, WANNAN LITTAFI HAKK'IN MALLAKA TANE BAN YARDA WANI/WATA A SARRAFASHI TA WATA SIGA DABAN BA, YIN HAKAN KUSKURE NE KUMA LAIFINE, LABARIN DAKE CIKI GASKIYANE YAFARU KUMA YAKAN CIGABA DA FARUWA ACIKIN AL'UMMA DON HAKA IDAN YA DACE DA HALINKI SAI KIYI GAGGAWAR CHANZAWA FATANA SHINE DANI DA KE 'YAR UWA MUTARU MUGYARA DON KYAUTATA GOBEN RAYUWARMU A CIKIN ZAMANTAKEWAR AURATAYYA...INA KIKE QAWAR ARZIKI *SAINAH ABUBAKAR (UMMU MINAL)* DUKKANI WANNAN LITTAFIN DON FARINCIKIN KINE, INA ROK'ON ALLAH DAYA HA'DAKI DA ALKHAIRANSA ADUK INDA KIKA SHIGA👏 INA SO KISANI BILLY S FARI NA K'AUNARKI HAR ZUWA LUMFASHINTA NA K'ARSHE, *MOM HAFSAT RANO, YA HAJJA CE, MOM HAFSAT XOXO AND MY LITTLE PRINCESS SALMAH ABALI* INA SO KUSANI DUK WANI ALK'ALAMI NAWA DA ZAN 'DORA WAJEN RUBUTU CIKE YAKE DA ALFAHARI DAKU TARE DA TSANTSAR K'AUNARKU FISABILILLAH!, BURINA ARAYUWA SHINE ALLAH YABAKU FARINCIKI MAI 'DOREWA ACIKIN RAYUWARKU HAR IZUWA AL-JANNAH FIDDAUSI👏


💎Page______1💎


Wata 'yar kyakkawar yarinya ce mai yanayi da k'irar mutanen Japanis, wankan tarwad'a ce da baxa ta wuce 'yar kimanin shekara goma sha hud'u 14 da haihuwa ba. Ita na hango zaune akan matattakalar da zata sadaka da babban falon gidansu dake nan k'asa, ta buga uban tagumi hawaye na zubar mata a idanunta biyu, in ban da tunani da kukan bak'in ciki ba abunda take yi.

"Billy..!Billy..!!...Billy..!!!"

Ta jiyo muryar yayan tah mahmud yana kiranta, kyakkyawan saurayi ne d'an kimanin shekara 27 dake tafe daga abayanta yana kiran sunanta cike da shauk'in dake nuna tsantsar k'auna, shak'uwar dake tsakaninsa da ita, tsananin k'unci da bak'in ciki da suka tarar mata a zuciya yasa ta kasa amsa kiran yayan nata da take matuk'ar k'auna. Mahmud ya kasan ce shine babban d'ah acikin familyn alhaji Bashir mai furniture, yana da k'anne guda biyar uku mata biyu maza Batool, Bilkisu, Basmah, Bilal da kuma Bassam.

A hankali ya k'araso wajen ta tare da dafa shoulder d'inta fuskarsa cike da damuwar yanayin da ya ganeta a ciki yace.

"Sister me yake faruwa dake ne kika zo nan kina kuka, ko wani abun ne aka yi maki? fad'amun don ku 'YAN UWANA NE! bana son abunda zai tab'a mani ku"

Kallonsa Bilkisu tayi tare da kallon gefe gefensu taga babu kowa, turo labenta na k'asa tayi tana neman sake fashe masa da wani sabon kukan, da sauri Mahmud yasa yatsansa akan labbanta,

"Shiiiiii....bana son kukan nan sister, fad'amin waye ya tab'a min ke?" ya Karashe maganar yana mai goge mata hawayen dake neman gurbin zama a fuskarta.

"Yaya don Allah kafad'a mun wane laifi na yiwa small mom da ta tsaneni, ko ince ta tsane mu a rayuwar ta please yaya fad'amun me yasa take yi mana haka..?!"

"Ke Billy!..ba dai d'an na wane kika zaunar kina fad'a masa cewa na tsaneku ba, saboda iya makirci har kina fitar da wasu k'walla tsabar munafurci ko?"

Muryar small mom ce suka jiyo fitowar ta kenan daga bedroom rik'e da hannun bilal ta turo k'eyarsa tare da hankad'a shi har sai da ya fad'i k'asa tana fad'in haka,

Da sauri Mahmud ya k'araso wajen ya d'auke bilal dake k'asa yana kuka ya rungume sa a jikinsa ransa a b'ace yana kallon mahaifiyar tasa kamar zaiyi kuka, Bilkisu na ganin haka ta ruga aguje wajen mahaifiyarta don ta sanar mata,

"Haba mom..! fisabilillahi meye haka kika yi? yanzu d'an wannan yaro me yayi maki da kike neman saukar masa da b'acin rai shima?"

Mahmud ya k'arashe maganar had'e da kallon bilal da yayi lamo (kwance) a jikinsa yana shasshekar kuka, cike da masifa small mom take cewa...

"Banda iskancin yaron nan taya za'a yi yaje har k'uryar d'aki na ya watsarmin da kayan dake kan madubi na, gashi duk sun farfashe don tsabar k'eta da muguntar da aka koya masa shima.."

"Yanzu mom bilal d'in da iya karsa shekara uku yasan wata k'eta da mugunta?" kallon bassam dake gefen small mom yana dariya yayi tare da d'aukesa mari kawau!

"Hey.. stupid boy dariya ma kake yi min don ubanka? wallahi mom yanzu haka wannan shed'anin yaron ne yayi maki b'arnar kika yi zaton Bilal ne"

"Kai Mahmud bana son sharri da yarfe, bassam d'in ne zai fasa mani kaya? In banda kana shashasha taya zaka yiwa d'an uwanka sharri kaso bare kuma kafifita shi akansa?

"A'a mom sumafa 'YAN UWANA NE don me ba zan so suba?, idan har kince sharri na yiwa Bassam dake da shekara biyar ba zai iya yi maki b'arna ba taya zakice Bilal ne yayi mom? don Allah mom kidena yin irin wud'annan abubuwan bana so, Bilkisu da Bilal 'YAN UWANA NE ko kad'an bana farin ciki da abunda zai cutar mani dasu"

Yana rufe baki sai ga Ummi ta fito tare da Bilkisu biye da ita, murmushin k'arfin hali ta yiwa Mahmud ba tare da takalli inda mom d'insa take tsaye ba ta karb'i Bilal, cike da takaicin abunda mom tayi Mahmud yace

"Ummi kiyi hak'u...." Be k'arasa ba Ummi hak'uri ba yaji k'arar Bilkisu dake gefen ta, juyowar da zai yi kenan ya hango Batool rik'e da gashin kanta billy tana ja tama fad'in.

"Munafuka meye na zuwa ki wani kirawo Ummi sai kace kashesa aka yi? wallahi mom yarinyar nan taji bak'in hali, yanzu haka ma ita ta turasa ya fasa maki kwalab'en turare dake kan mirror, nikam ban san ya aka yi wud'annan mutanan suka zamo jinin muba, na tsanesu mom don nikam ba 'YAN UWANA NE ba...!"

A fusace Mahmud yayo kanta "Batool dama ba kida hankali? jinin namu kike cewa haka? to idanke ba 'yan uwanki bane ni 'YAN UWANA NE kuma don ubanki yau sai kin fad'amun ko 'yan uwan waye a gidan nan"

Belt d'insa ya cire tare da yowa kanta, sanin halinsa yasa ta saki Bilkisu ta ruga aguje tana ihu yana binta, ganin da gaske ya keyi yasa ta shiga k'eta ihu tana fad'in,

"Wayyo yaya don Allah karka dukeni da zafi wlh, mom kiceceni, wayyo na bani wlh yaya 'YAN UWANA NE su...!, YAN UWANA NE...!! su yaya, wlh na tuba suma 'YAN UWANA NE....!!!

Mahmud babban yaron Alhaji Bashir Mai funitures mutunen da yayi suna wajen rik'ongaskiya da amana yanada mata biyu da yara shidda ukku maza ukku mata yana matuk'ar kula da iyalansa yanda yakamata babu wani abu da zasu nema surasa indae aduniya ne haka kuma yana kwatanta adalci atsakanin matansa da 'ya'yansa yanda yakamata, Amma kash har yanzu abuguda ke damunsa, shine yanda matarsa kuma amaryarsa bata son a zauna lafiya wanda yayi iya k'ok'arinsa yasan ko meye dalilinta yagagara, lokutta da dama yakan tambayeta meyasa takeyin hakan sai tace masa Bakomai, Hajia Aisha itace uwar gidansa mace mai hakuri, juriya da kuma K'ana'a abu mafi burgewa atare da ita shine gaskiya macece kaifi d'aya Nata son munafurci arayuwarta shiyasa alhaji bashir KE matuk'ar k'aunarta aransa Sunyi aurena da ita bisa zab'in iyaye kuma sae Allah yasa akadace da suna k'aunar junansu sosae, Bayan sunyi aurena da shekara bakwae Hajia Aisha ko b'atan wata bata tab'ayi ba balle asa ran haihuwa mahaifin alhaji bashir ya auro masa 'yar amininsa mai suna hussaina, haka alhaji bashir yayiwa mahaifinsa biyayya yazauna da hussaina bisa amana badon yana Sontaba, Hajia hussaina macece mai son mulkar duk wani wanda take tare dashi kasancewar mahaifinta sarkine yana mulkar wani gari acan cikin birnin kano, ko kad'an tatsani taga fifikon wani akanta tanada matuk'ar izza daji dakai wanda sune suke
taimakonta wajen walak'anta natare da ita harma dana nesa, in kaga tana son mutum to tabbas yana bintane yana yimata yanda take so abunda Hajia Aisha Kenan takasa d'aukar mata shiyasa zamansu yakasa dai daita duk da kuwa mijin nasu na iya k'ok'arinsa.

Wata tara cikin na goma da kawo Hajia hussaina ta haifawa alhaji bashir 'yarsa kyakkyawa sosae Hajia Aisha tanuna farincikinta afili duk da ana kyararta akan yarinyar hakan besa tayi fushi ba takoma gefenta, Kwatsam ranar suna Alhaji bashir ya rad'awa 'yarsa sunan hajia Aisha sbd tausayinta da yakeji na bata haifa ba kuma yayi hakan ne saboda ya faranta mata kamar yanda take k'ok'arin faranta masa acikin dukkanin alamurransa,

Haka kuwa akayi Hajia Aisha tayi farincikinki sosai tare da yiwa mijin nata godiya tana kuka don tsabar jin dad'i,

Lokacin da Hajia hussaina taji sunan 'yarta ba k'aramin bakin ciki tayiba duk da soyayyar da akeyiwa Yarinyar hakan bai hanata fatar inama bata haifeta ba, kwanaki biyu da suna yarinyar ta koma sanadiyar Typoid data yimata mugun kamu, a maimakon Hajia hussaina tadamu sai tanuna ita k'arama da yarinyar takoma duk da ko tanajin radadin rashin 'yar tata azuciya, sosai Aisha tayi kukan rashin takwarar tata tare da fatar Allah yabasu wata mai albarka haka ta fannin alhaji bashir ya damu matuk'a da rashin yarinyar saboda son da yake yimata daga karshe dai duk suka tattara suka barwa Allah ikonsa, Bayan shekara d'aya hussaina tasake haifo yarinya kamarta sak da alhaji bashir amma cikin ikon Allah ko minti goma batayi aduniya ba itama tarasu, wannan karon kam Hajia hussaina tafi kowa shiga tashin hankali tayi kuka sosai rungume da yarinyar bayan tarasu halin d'ah da mahaifi saida akayi dagaske sannan akarabata da gawar yarinyar, bayan wash kwanaki Hajia hussaina ta fara b'ullowa da makircin wai Hajia Aisha ke kashe mata yara don ita bata haihuwa haka tabi dangin alhaji tana cewa ai asirine Hajia Aisha keyimata yaranta namutuwa don ita bata haihuwa, nan take Aisha tafara samun matsaloli da dangin mijinta ciki Kuwa hadda mahaifiyarsa dake matukar sonta, k'aunarsa k'waya d'aya kad'ai takejin sanyinta wato hafsat itama saboda jininsu ya had'u da ita tun kafin akawo Hajia hussaina tariga tasan halinta kuma tasan mezata iyayi da wanda bazata iya ba shiyasa bata shiri da Hajia hussaina ko kad'an,

Alhaji bashir najin suruttan dake yawo acikin danginsa wai Aisha nakashe masa 'ya'ya saboda ita bata haihuwa amma daidae da rana d'aya betab'a bari sukayi tasiri azuciyar saba, wannan abun ya matuk'ar k'onawa hussaina rae don haka tafara kukan wai Hajia Aisha tarigata shanye alhaji baya ganin laifinta dole itama ta tashi tsaye, wannan karon wata goma hussaina tayi bayan haihuwarta tasake haifo santalelen jaririnta kyakkyawa kamar ba ita ta haifeshi ba, kowa farinciki a fuskarsa baya misaltuwa Anata fad'in alhaji yasamu magaji, Aisha kuwa duk yanda taso taga yaron ta d'aukesa aka hanata acewarsu wai umurnin mahaifiyar alhaji ne tace kada abari ta d'auki yaron, ran alhaji ya matuk'ar b'aci akan wannan abun da akayi mata don haka ya riko hannunta suka bar d'akin tunda Aisha take bata tab'a kukan rashin haihuwaba sai yau...kuka maitsanani da ban tausayi tafashe dashi tana cewa

" _Ya rabbhi habli minasswaliheen_"

Cike da tausayawa ya rungumota

"Amin.... Aisha kiyi hakuri komai yanada lokaci insha Allah kema naki nazuwa"

Anan taci gaba da KIMANTA Tana tambayarsa metayi da Hajia tahana tadauki dansa jininsa shidae hakuri kawae yadinga bata tare da kalaman da zasu kwantar masa da zuciya aransa kuma yana jin rad'ad'in zafin kukan da Aisha keyi da kuma abunda akayi mata tun daga ranar yad'au alkawarin ko dukiyarsa zata k'are tun daga nan k'asar har zuwa k'asashen waje sae yakai Aisha an nema mata maganin matsalar data hanata haihuwa itama tahaihu, haka akaci gaba
da hidimar biki Aisha bata tab'a d'aukar jaririnta ba, ga wani irin maseefar son yaron da Allah ya azo mata ana gobe suna saega hafsat kanwar alhaji ta iso wajen buki da yake acan borno tayi aure har da yaranta biyu shiyasa bata samu isowa da wuriba.

Nan yayan nata ya zayyana mata abunda hajiya tace da yake shima bayada abokin kaiwa kukansa ko shawara sai ita kasancewar tanada hankali da tsinkaya gashi itace auta ad'akinsu.

Cikin b'acin rai tace "haba yaya wlh kabani mamaki yanzu don sunce haka Saeka biye masu tanaji tana gani jininka yayi mata wahalar d'auka da gani to wlh tun daga hussaenar har zuwa munafukan dake tare da ita basu isaba" Cike DA isa tabar falon nasa tanufi d'akin hussaina ko kallon wud'anda ke wurin batayi ba ta d'auko jaririn
tafitowarta dashi Tana hucin tab'ani inka isa, Kai tsaye tashiga dashi d'akin Hajia Aisha dake kwance akan gado tunanin duniya duk yabi ya isheta ta kwantar dashi dai dai fuskarta had'e da cewa

"Ga d'anki nan nakawo maki kigani kuma kid'aukesa injini babu wanda zai hana"

Rungumesa Aisha tayi cike da soyayya tana tofa masa addu'o'in kariya fuskarta d'auke da farincikinki tamkar ance yazama nata, man hafsat tayita bata hak'uri da fad'an tacirewa kanta damuwa komai yanada lokaci, sosae Aisha taji dad'i tayi mata godiya, alhajine ya shigo d'akin yana kallon yanda Aisha tayi kyau da jaririn a hannunta yace

"Masha Allah kema Allah ya kawo maki naki rabo mai albarka"

Duk suka amsa da amin

Anan hafsat tacewa yayanta ta rad'awa yaron suna mahmud sae kuma akaci sa'a da sunan mahaifin Aisha kenan shiyasa takarajin son yaron aranta har take kiransa da babana.

Tunda aka haifi mahmud hussaina bata sake haihuwar saida ya shekara goma da wata biyar sannan hussaina ta samu ciki ta hafo 'yarta har lokacin Aisha na shiru bata haihuba sun karad'e duk wasu kwararrin asibitotan dake k'asarnan amma ba'a dace ba, Ranar suna aka rad'awa yarinya Basmah.

Ba'ajimah da haihuwar basmah ba wajen aikinsu Alhaji aka turashi k'asar Egypt yayo couse d'in shekara biyu hakan yasa yafara tafiya da Aisha shima saida akayi daru da hussaina kafin ta amince ai kuwa suna isa Alhaji yamaida hankali sosae wajen kai Aisha asibitota ana duba lafiyarta, duk da haka dae ba'a dace ba har shekarar ta k'are bayan sun dawo kuma saega hussaina tafara laulayi lokacin basmah nada shekara d'aya da wata biyu da haihuwarta don haka tacireta ga nono,

Alhaji yaso barin hussaena gida ya komawarsa shikad'ai tunda cikin nabata wahala ga kuma k'aramar yarinya agabanta abun zai zame masu lalura idan yatafi da ita don haka sai yayi tunanin yabarta gida, Aishace ta nuna masa illar da abun zai haifar k'ara yatafi da ita inyaso itama ya kaita asibiti har tasamu lpy nan yake tambayarta to ya zayayi jinyarta ga basmah da batayi wani wayo ba, Murmushi tayi tace idanka amince itama momynsu ta amince to kubar babanah da basmah awurina insha Allah zankula maka dasu kafin kudawo, koda alhaji yafad'awa hussaina cewar za'abar mahmud da basmah hannun Aisha k'in amincewa tayi saeda yanuna mata idan har bata amince ba toshi ba inda zaije da ita tazauna gida saboda bazae iya kwasar yara...


Read / Download YAN UWANA NE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album