Join Our WhatsApp Group

HALIN RAYUWA Book 2 Complete Hausa Novel Document by HALIN RAYUWA Book 2


HALIN RAYUWA Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

DOWNLOAD

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31315



HALIN RAYUWA Book 2

Reading Time: 2 Hours

Added On: 24, Apr 2023

Author: Hafsat Sodangi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07035586299

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 155.06 kb

File Type: txt

Views: 2327+

Download: 627+

Last download: 2 days ago

DOWNLOAD
Description/Story: 
HALIN RAYUWA

1

NA

07035586299

HAJ. HAFSAT C. SODANGI

(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)

1



Hakkin Mallaka [m]
Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne

GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu
ta'ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji.
Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin
Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe
Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da
wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa
ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da
gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace.
Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga
daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje,
Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa
zumuncin da ke tsakaninmu.

Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi
6/7/1434

2


GODIYA

Godiya mai dumbin yawa gare ki.
Rabi'atu Faruk Jauro
(Ministry of Commerce and Industry Yola,
Adamawa State)

Da
Zainab Sunusi Kofar Gabas Danbatta
Zainab Abarshi Yawuri

GAISUWA
Gaisuwar littafin naka ne Muh'd. Kabir Sodangi
(A.T.B.U BAUCH)

3

LITTATTAFAN SODANGI:
Uwar Miji
Naga Ta Kaina
Rabon Kwado...
Cikar AIkawari
Wayyo Duniya
Yi wa Wani...
Abu Naka...
Mata Ma su Duniya
Nufin Allah
Kifi Na Ganinka..
Daga Kin Gaskiya..
Da Kamar Wuya..
Mai Uwa.
Duk Daya..
Mata Da Kicin Dinsu
Wacece Ni?
Wata Fuskar..
Mijin Ta ce
Garin Banza...
Ga ni Gare ka
Biyan Bukatar Rai
Shamaki
Hattara
Mata Masu Duniya
Kyautata
Ayi Dai Mu Gani.
Tabbataccen Al'amari

4

HALIN RAYUWA 2
Washegari da safe gaba daya mutanen gidan
kowa a cikin natsuwarsbi yake, in ban da
Babah Lantana da ke ta faman zirga-zirga
tana fadin maganganu kamar yanda dama al' adarta
take in har wani abu ya 6ata mata rai.
Haka kawai a cizan mun yarinya sannan wani
Rato ya shigo har cikin gida ya dakar min yaro, to
wane irin rashin yanci ne wannan? Ai kayi
hukuncin da za ka yikawai in gani. Lalle ne kuma
kayi hukunci me tsanani don in ba haka ba kam...
Sai tayi kwafa tare da fadin "Hanya ratatata nuna
alamar abinda zai farun ba karamin al'amari ba ne.
Koda Babah Lantana bata furta irin wadannan
kalaman ba zan kasance ne a cikin natsuwata sosai
don na saba jinta tana bada umarnin a rama cizo ko
da kuwa bayan shekara guda ne, to balle ni da nayi
cizo jiya, cizon kuma ya haifar da sakamako mai
tsanani don daga Asabe har SaHau babu wanda bai
samu kanshi cikin wani hali ba matsananci.
Asabe dai tana kwance tana fama da matsanancin
zazzabi, Sallau kuwa bai iya rufa bakinshi ya daina
kurma ihun da yake kurmawa ba, sai da aka kira
Mallam Bahago yazo ya gyara mishi targaden da aka
yi mishia kafada.
Don haka sanin a nayi Babana yana cikin gidan
nan dai shi ne abinda ya zaunar dani a cikinsh da

5

kuma ganin Asabe a kwance tana fama da kanta
nasan a haka ba za ta ce zata rarume ni don ta rama
cizon da nayi matan ba, amma duk da haka ina ganin
Babana ya dauki kwandon tumatirinshi da nufin fita.
Nima zan yunkura in bar musu gidan don ba zai
viFu in 2auna tare da su ba tunda nasan zama da su
din ba zai haifar min da da mai ido ba.
Ina cikin wannai tunanin ne na bango Babana
tsaye a tsakar gida rike da kwandon tumatirinshi a
hannu alamar zai fita kenan nayi maza na jawo
gyalena kusa da ni, don yana fita in bi bayanshi sai
kawai naji ya ce ing Yaacuwuna take?
Nayi maza na ce Gani nan Baba, na fadi daidai
lokacin da na tsuguna a gebanshi, karki sake li fita
daga gidan nan. Gabana yayi mummunan faduwa,
"Kin ji na gaya miki ko ba kiji ba?" cikin sanyin jiki
na ce mishi naji Baba.
Na mike tsaye jikina a sanyaye na koma dakin na
Zuna na jawo littafina ns karatu ina dubawa sai dai
gaba daya hankalina ba a kan shi ya ke ba.
"Kai Sallau!" Sallau ya yunkura ya fito gani
Baba, shirya ka bar min gida ka koma inda dama ka
ke, tunda ka zo kana yi min fada a gida shima
wancan din na aika a gayawa Babanshi ya gaya
mishi kar ya sake shigo min cikin gidana."
gama fadin hakan yasa kai ya wuce zai tafi.
6

Babah Lantana ta bishi da kallo irin na takaici
tare da fadin "A hau, ahau wannan shi ne hukuncin
naka? Taja wani mummunan tsaki ta juya taga
Sallau da ke tafiya da kyar yana rike da ledar
kayanshi a hannu zai bar gidan don cika umarnin da
maigidan ya ba shi.
Sai kawai naji ta daka mishi tsawa "Ina za ka da
wannan jikin naka? Maza maida ledar nan kayi
kwanciyarka ka huta, ai ko za ka bar gidan nan sai
bayan kun rama abinda a ka yi muku tukuna.
Cikina ya badasautin kulululuu! Don nasan me
maganar tata ta ke nufi
Sallau ya koma daki yayi kwanciyarshi yayinda
lia ma ta koma kan hidimominta da maganganun da
take ta yi.
Ana cikin haka ne naji wata irin murya tayi
sallama a bakin kofar shigowa tsakar gidanmu.
Muryar ta mata amma abin mamakın shi ne da sunan
maza naji Babah Lantana ta kira bakuwar.
"Nalami ne kuma har cikin gida ba za ka tsaya
daga waje ka ce ayi maka iso ba? yayi 'yar shewa
tare da 'yar dariya kafin ya ce "In ba kiyi min haka
ba ai ba ai ba ki cika 'yar halak ba, ai ba zan ce kin
amsa sunanki na Butulu' ba ko ba sunan da dama
yan gidanku suke kiranki ke nan ba? Butulu ai
dama kazo ne har gidan mijina ka ci mutuncina?
7

Yayi maza ya ce "A'a ko kadan ai darajar aure
ya shige haka komai iya shegenka in har ka samu ka
shiga karkashin inuwarshi to ka zama mai mutunci
sai a mutuntaka saboda darajar shi, don haka ba zan
ci mutuncinki a gidan mijinki ba.
To tunda ka fadi haka da bakinka muje daga
waje, ya ce a'a nan kuma daya a nan din nan zaan
zauna bau ce zan shiga dakinki ba balle kiyi tunanin
zan hau kan gadonki in kina tsoron kar mijinki ya
shigo ya ganin ne babu komai yana shigowa sai in
gyara zama in maida kaina kanin Babanki in kuma
ki ka ce za kiyi min iya shege to kema kin san ni
babanki ne a nan ma.
Ina iya zuwa har wurin 7aman nasu in yi koma1,
ai ta can na biyo an nuna min shi,don haka dauko
tabarma kawai ki shimfida min."
Ta kawo tabarmar tana shimiidawa yayinda ni
kuma zuciyata ke ta faman kai-kawo a tambayata
wane irin mutum ne wannan? Na yunkura na matsa
na kebe ta matsin kyauren dakin namu mutum har
mutum yasha babbar riga har da hula zanna sai dai
kalamanshi.
"Ashe har mazaunai ne da ke haka? yayi
tambayar daidai ya kaiwa mazaunan nata duka
gabana ya sake faduwa, tayi maza ta kars daure
fuska kafin Nalami ba ka da mutunci ya gyad zama

8
kan tabarmar ya ce, Eh komai ma kina iya gaya min
ni na zo. Ta ce to ka tafi mana ko ni na kira ka?
Ya kalleta a'a ba ke ba ce ai kin samu wurin
zama sai cin mutuncin Jama'a ki ke yi ja' ira kawai
mara tuna baya, kai bebi baki da tuna alheri.
"Dakata ka ji Nalami, na daina amsa wannan
sunan duk wani abu makaman cin wannan da ka sani
na daina shi, mijina mai mutunci ne. "
Yayi maza ya ce "Gaskiya kam gaskiya kam ai
na ganshi ruan Malamai ne da shi inda tambayar
take dai na yanda aka yi ya iya zama da ke ne."
Ta zuba mishi ido cikin takaici ai ba za ka bari
muyi magana ta gaskiya ba ke nan? Ya tsura mata
nashi idanuwan da suka fi kama da gauta saboda
kaduwarsu kafin ya ce ai ba ki da ita ne, gaskiyar
balle ayi maganarta da ke. Ta gyada kai tare da
fadin to shi ke nan naji me ya kawo ka?
A haka zan fara magana ina zuba tun ban ci
komai ba? Ai sai ki kawo min da na shar kajin da a
ka bani labarin kullum a ka zo' gidanki sai an ci.
Yana cin naman da ta kawo mishi yana magana
zuwa nayi in dangwali arzikinki tunda kin shigo
cikin inuwarshi don kuwa nima babu irin taimakon
da ban yi miki ba, sanda su sarka suke wulakantaki,
ko sanda ki ka haifiyaran nan..."
Tayi maza ta katse shi "Ba fa tarihi ka zo karanta
min ba, arziki ka ce ka zo ci." Yayi maza ya ce, "Eh

9
haka na ce, to kai duk abinda ka ke da shi bai ishe ka
ba sai ka zo wurina ni da nake zaune a dakina ko
sana' a bana yi?
To ai ku ne masu rufin asirin amma na wajen
nan menene ne a cikin abin? Kin san fa shari'ar nan
da a ke ta kafawa ta karya darajar al'amuran namu
kana
gaba daya ke dai ayi shiru kawai tunda kana
Musulmi ba zai yiwu ka buda baki ka ce ba ka ji
dadin abin ba.
Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta mika mishi to
ungo rike wannan ko sigari ka sha, lokacin ne na
tuna farkon zuwan Babah Lantana na gidanmu har
sigari sha take ji amma yanzu kam ta daina don na
ma manta in ban da yanzu da naji ta ambata da
bakinta.
Maimakon ya karba yayi godiya kamar yanda
al'adar wanda a ka yi wa kyauta take sai kawai naga
ya harari abinda ta ba shin ya ce kyautar matsiyata
za ki yi min? ko da na ce miki ba ni da harka ai kin
san nafi Rarfin irin wannan kyautar don kin san kont
waye?
To in tsaya daga waje mana in yi bara ki bai wa
yara su kawo min sadaka, ai a sauwake abinda za ki
bani in bar gidannan bakina alaikum jaka guda ne.
Da sauri ta ce mishi a'a buhu guda ba jaka guda
ba gaka guda lafiya ce da za ka ce in baka ita ina na
ganta? Kai barawo ne? A'a to sai in gyara zama ai

10
sai kin samu, to sai in gyara zama ai sai kin samu to
ma me za ki kira ni kuma oho ni dai kin san ba Delu
ba ce da ta taimake ki ta rinka yi mii zirga-zirgar
gidajen Malamai da 'yantsubbu bayan irin wahalar
da tai tayi miki da 'ya'yanki
Sai da ki ka samu kan miji ki ka mallake shi taf
ya zama bai da katabus sai naki sannan ki ka yi mata
irin tukuicin da ki ka saba yi wa wadanda suka saba
taimakonki wanda yayi dalilin da suka rada miki
sunanki na ainihi 'Butulu' ki ka koreta ki ka ce kar
ta sake zuwa miki gidą don ba ki yarda da, ita ba."
"Ita taje ta turo ka ke nan? " kan ya bata amsa sai
naji yaro yana magana a tsakar gida wai Maryan
ana kiranta a waje."
Da sauri Nalami ya kalli Babah Lantana cikin
yanayin rage murya dama ba mu biyu ba ne a gidan
shi ne ba ki gaya min mun yi maganar a hankali ba?
Ba ki kyaufa ba Lantäna, ai wata kusar tafi wata.
Ai in da ná sani ba zan yi îrin wadannan kalaman
wani ya ji ba, na fito zan wuce in je'kiran da a ke yi
min ban sani ba ko zaman Nalamin ne ya hanata
tuna min da dokar da Babana ya. kafa mini ko kuma
don taga ita ma bata bi dokar ba ne oho, tunda nasan
tafi kowa jin an ce ana kirana a waje.
Ina fitowa muka hada ido da Nalami barin komai
yayi ya shiga bina da kallo, wani irin kallo da yafi

11
kama da na kidima, uh' uh uhhh, wacece wannan
Lantana?
Tambayar da naji shi yana yi mata kenan yayin
da ni kuma na shige cikin zaure na bar su a nan ban
jiwo amsar da ta ba shi ba' lna daga cikin zaure na
hango Mubarak a tsaye daga waje yayi kwalliya
sosai.
Karo na farko da ya taka yazo kofar gidanmu
tunda ya dawo daga Ibadan, sai ko jiya wannan
kuwa naji an ce wai Babah Sumaye ce da taji ihun
da nake yi ta aiki Almajirinta da gudu yaje ya gaya
mishi abinda ke faruwa.
Daga cikin zauren naja na tsaya ban ce mishi
komai ba, shi ya matso bakin kofar zauren ya tsaya
kina da wata matsala ne? yayi tambayar yana
kallona, na girgiza kai a hankali nuna alamar babu.
Ya miko min ledar da ke hannunshi cikin zauren
na mika nawa bhannun na karba ya juya ya tafi ba
tare da na ce mishi komai ba.
Na koma baya ta cikin lungun zauren saboda jin
ledar da nauyi ga kuma sai da na nemi wuri mai dan
kyau sannan na zauna na fito da abinda ke ciki,
gasasshiyar kaza ce katuwa tayi matukar gasuwa
gashin injin ga yaji a wata takardar ga kuma ruwan
lemo na kwali mai sanyi.
Lokacin ne na kara tuna har a wannan lokacin da
agogo ya kai kan sha biyu da rabi ban sa komai a

12

bakina ba, da bai zo ya kawo min wannan kazar ba
kuma to da ban san lokacin da zan samu abinda zan
ci ba, ko a haka kuma Babana yake ganin zan iya
tsare dokar da ya kafa min ta kar in tafi ko'ina? Oho!
Ci nayi sai da naga na koshi sannan na dora
ruwan lemon nan a kai sannan na mike na dauki
saura na nade na adana shi a cikin gyalena, na shiga
cikin gida har lokacin Babah Lantana magana take yi
da bakon nata, sai dai a yanzu maganar tasu ta dan
sauya da alamar sun dan samu daidaituwa.
Yana ganina ya saki wani lallausan murmushi
har hakoran Makkanshi suka fito guda biyu, kuma
jajaye yana ganin mun hada ido da shi yayi maża ya
sakar min signal da idanuwanshi. Nima nayi maza
na galla mishi wata irin matsiyaciyar harara na wuce
na shiga dakina.
Wasu sabbin kwanukan abincin na gani wurin
Asabe da alamun fitan da nayi ya kara bada damar
da aka sake kawo mata wani abin.
"Yanzu dai kin gani Hajiýa bani kawai abinda ki
ka ga za ki ba ni tunda ga bayanin da ki ka yi min na
halin da kike ciki in an kwana biyu ai zan dawo."
Da sauri ta ce, "A'a-a'a ni kar ka dawo min gida
in ba so ka ke ka kara min wata matsalar ba."
"A aha, ai ke halinki ke nan ki ka sani ko zuwan
nawa na alheri ne? To ta ina zuwanka zai zame
min alheri ni kuwa?" ya yi murmushi "Uhum, Babah

13

Lantana kenan, ai na daina kiran sunan naki gatsau
sai na sakaya miki shi da Baba ko kuma Hajiya. Ai
kin san shi sunan Hajiya ma mai niyya yake nufi."
"Kai dai karbi amma ni kar ka dawo min gida."
Ya karba yana kirgawa, ai tunda na ce zan dawo zan
dawo din ne kiyi fatan kawai dawowan nawa ya
zame miki alheri." Ya tashi ya tafi.
Ina zaune a gida Babana dokarshi a kaina ni
kadai take aiki, Babah Lantana da 'ya'yanta babu
abinda ya shafe su da ya dawo yazo ya samu Sallau
a gidan ma bai ce mishi kala ba, sannan da zai kafa
min dokar daina fita daga gidan sai ya manta bai
sanya ta bani abinda zan ci dole ba.
Duk da haka na bi umarnin da ya banin na in
daina fita saboda magnar da Yaya Dijah take yawan
gaya min in bi duk wani abinda zai sanya ni komai
wuyarshi, kar in ki yi mishi yayya a kai kar kuma in
lura da cewar wasa ba su yi mishi ba ni ce ya zama
wajibi a kaina in bishi ba su ba.
Ina zaune a haka cikin wani irin matsanancin hali
in ba Mubarak ne ya kawo min abinda zan ci ba
babu mai bani a hakan kuma ga barazana gami da
wulakanci da neman tsokana
Kowane lokaci a cikin maganar ake haka kawai
sai ka ci Babah Lantana ta ce ah cizo? Ai sai kin
rama a natse za ki rama kara warkewa dai kawai
karfinki ya kara dawowa jikinki."

14

Ina kallo Asabe take fitowa daga wanka ta shafa
maina tayi kwalliya da kayan kwalliyata in ta gama
ta jawo akwatin kayana ta zabi wanda yayi mata ta
daura, bana cewa komai saboda ina tsoron kar
maganar da zan yin ya...


Read / Download HALIN RAYUWA Book 2

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

DOWNLOAD
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album