Join Our WhatsApp Group

SAHLA A PARIS Complete Hausa Novel Document by SAHLA A PARIS


SAHLA A PARIS

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 34764



SAHLA A PARIS

Reading Time: 2 Hours

Added On: 30, Nov 2023

Author: Azizat Hamza ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137311900

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 178.65 kb

File Type: txt

Views: 825+

Download: 444+

Last download: 2 days ago

Description/Story: Wannan littafi mallakar Azizat Hamza ne. Ba a yarda wani ko wata su sarrafa shi ta kowani siga ba, ba'a yarda a karanta shi a youtube channels ba, ba'a yarda a kwafa ko a juya labarin ba tareda hakkin marubuciyar ba.
©AZIZAT HAMZA 2022


Wannnan littafi ƙirƙirarren labari ne. Allah ya yafe min kura-kuren da suke ciki Amin.


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.


001 Ɓarauniyar nama.

Duk ranan Lahadin karshen wata akan yi Family meeting a gidanmu. Wannan family meeting da ake yi ya banbanta da wanda ake yi na gaba ɗaya iyalen marigayi Alhaji Muhammadu Ubandoma wanda ya kasance Kakanmu, Duk wanda ya haɗa jini da familyn Ubandoma walau ta wajen mace ko namiji duk ana haɗuwa ayi meeting ɗin dashi, ana yin meeting ɗinne bayan wata uku-uku, watau sau huɗu kenan a shekara.
Kai akwai wani meeting ma da Hajiya Kaka ke shiryawa tsakanin 'ya'yanta duk sanda ta ga dama, musamman ma idan wani gagarumin abu na alkhairi koma na sharri ya samu 'yayan Hajiya Sadiyya. Matar nan ta kwana biyu da rasuwa amma har yanzu Hajiya Kaka ba ta dena kishi da ita ba.

Yau ma kamar kullum shirye shiryen meeting ake yi kuma Mama ce ke da girki dan haka duk wani kanshi da ke tashi a gidan daga kichen ɗin sashenta yake fitowa.
Karfe goma na safe zuwa shabiyu na rana ake meeting ɗi, dan haka duk wanda ya san yana cikin list na masu tayata aiki to dole ya kasance a kitchen a wannan lokaci.

A gidanmu wajibi ne a kammala abin karyawa kafin karfe bakwai na safe. Wannan jazaman ne dan kuwa in dai mace ta bari yara suka makara zuwa makaranta saboda bata yi abin karyawa da wuri ba tabbas za ta haɗu da fishin Alhaji, in tai haka fiye da sau ɗaya kuwa tabbas za ta bada bayani idan aka zo meeting na wannan wata.

Ina cikin masu aiki a kitchen amma tsabar lalaci sai da aka kusan gamawa na shigo kitchen ɗin. Anty Firdausi ta ce maza na fita na bar musu kitchen tunda iskanci ne ya hana ni fitowa tun ɗazu.
"Anty Firdausi Allah Hajiya Kaka ce ta sakani aiki a ɗakinta" na faɗa ina zumɓura baki.

Mama da ke faman tsame nama a cikin mai ta daka min tsawa "zaki samu abunyi ne ko sai na zo na ɓallaki a wajen"

Na shiga kitchen ɗin da sauri ina faɗin " Mama mi zan yi?"

"Uwarki za ki yi. Shashasha kawai"
Na yi raurau da ido hawaye na shirin zubo mini, ba dan komai ba sai dan bana iya juran a zageni da uwata koda kuwa a zahiri ba wai ita ɗin ake zagi ba, amma in dai za a yi zagi da uwa to kodai na yi kuka ko kuma na fusata na fara masifa. Mama ce tayi zagin dan haka ba halin masifa.

"Maza ki je ɗaki ki fito min da kulolin Alhaji"

Na tura baki ina faɗin 'wai sai ayita cewa mutum uwarshi bayan baiwar Allah ta jima a cikin kasa'

"Mi kike faɗa wai?"

"Mama ban fa ce komai ba"

"Karya nayi kenan"

"Mama to kullum ki dinga ɓoye kulolin Alhaji a ɗaki kaman da gwal aka yi su"

"Sahala zan ci mutuncinki a gidan nan"

"Sahla sunana" na faɗa tareda ficewa da gudu.
Ban kawo mata kulolin ba sai da na tabbatar ta ɗan huce, lokacin dana shigo da su ma masifa take yiwa su Anty Firdausi akan tun ɗazu basu gama haɗa zoɓo da kunun aya ba.

Ni dai ban yi wani aikin wahala ba illa ɗauko wancan miko wannan. Da aka gama komai kuwa aka barni da su Safiyya da Nasiba muna zuzzuba zaɓo a cikin gorunan ruwa na swan water.

*
Idan za ka saci nama sai ka kware a abubuwa guda uku. Kowa ya san abu na farko amma na biyu da na ukun ba kowa ya iya ba. Na sha kama su Yaya Sulayman da su Yaya Abbas dama su Anty Firdausi suna satan nama amma ni dai ban taɓa gwadawa ba, sai dai idan an sata na gani nima a bani kaso na. Ashe dai su ɗin sun kware ne a abubuwan nan guda uku shiyasa Mama ko Ummi basu taɓa kama su ba.
Da farko dai sai ka iya takunka wajen shiga kitchen yadda ba za a ji karan buɗe kofarka ba balle aji na buɗe tukunya musamman idan ka taki sa'a ba a riga an kulle kitchen da key ba. Idan aka kulle kitchen to tabbas sai dai ka hakura ko kuma kayi karya da ɗaukan wani abu idan ka shiga sai ka idda nufinka.
Kowa zai iya buɗe tukunya. Amma ba kowa ke iya rufewa ba. Wato ka rufe ba tareda an ji ka ba, sannan ka rufe ka maida shi daidai yadda ka same shi a da. Da wannan koda wanda ya rufe tukunyar ya shigo ya gani zai ga kamar ba a buɗe tukunya ba balle har ayi tunanin an saci nama sai dai idan anzo rabawa aga nama sun kasa, ayita mamaki ana masifa.
Idan ka kai matakin nan ka kusa tsira kenan, ka kusa zama gwani.
Mataki na uku shine ka san yadda zaka iya naɗe tabarmar kunyarka da hauka idan har aka kama ka hannu dumu-dumu a cikin tukunya. In ba ka iya kare kanka ba tabbas za ka sha dukan tsiya.

Na san dukkan matakan nan amma ban taɓa gwadawa ba, ni dai ku barni da tsame nama a abincin Hajiya Kaka. Ana cewa tsofi basu cika damuwa da ciye-ciye ba amma Hajiya Kaka kam ta fita zakka. Dan in har zamu yi faɗa to baya nasaba da na cinye mata nama ko abinci ne. Kowanni irin abinci aka kawo wa tsohuwar nan sai ta kai baki. Balle yanzu da Anty Rafee'ah ke yin cake da meat pie wallahi duk a nan kuɗinta ke karewa. Koda yake nima har dani a kwaɗayin..

Tunda Mama ke tsame naman kaza a cikin mai nake jin yawuna na tsinkewa. Na san karshe ba abun kirki za a raba mana ba. A gidan nan kaf babu wacce take rabo tsakani da Allah, rabbon gaskiya irinna Anty Rafee'ah. Ita fa duk ranan girkinta ci ake yi a koshi sosai, ga girkinta daɗi.

Da aka gama komai aka ce mu je mu shirya. Mama ta kulle kitchen ta wuce ɗakinta dan ta yi wanka.
Wallahi fiffike ɗaya na yi niyyar ɗauka. Ban je da niyyar ɗaukan nama dayawa ba kamar yadda sauran su ke yi. Amma komai nawa daban yake dama.

Kwaɗon da aka kulle kichen ɗin da shi ya samu matsala, dan haka wani lokaci sai ka gama kullewa sai kaga ashe bai kullu ba, idan baka lura da kyau ba sai ka tafi ka barshi a haka. Ta nan masu satan nama ke samun dama. Nima a yau ɗin na samu dama dan kuwa Mama bata kulle da kyau ba. Na faki ido na yi sauri na buɗe kitchen ɗin na shiga da sauri, na nufi katon roban da aka zuba naman kajin a ciki na buɗe shi. To abunka da ba sabo ba maimakon na ɗauki duk wanda hannuna ya taɓa sai na sa hannuna cikin naman ina kokarin nemo fiffike, ni a tunanina idan na ɗau fiffike babu wanda zai gane an saci nama. Na ɗauko wani fiffike sai naga kaman ya faye girma dayawa za a iya ganewa. Na maida shi ina neman ɗan karami.

"Asirinki ya tonu. Yau dubunki ya cika a gidan nan. SAHALA"

"Mama Allah ba abinda kike tunani bane"

Saukar mari na ji a fuskana. Ta kamo hannuna muka fito daga kitchen ɗin sai masifa ta ke tana kiran mutanen gida kafin kace me Ummi ta shigo falon Mama tana tambayar mi ya ke faruwa.

"Sahala na kama a kitchen tana satan nama"

Ummi ta kama tafa hannu " dama kece ke shiga mana kitchen kina tsame mana nama a tukunya. Shiyasa ko a kasan gado na ɓoye nama bana tsira da shi"

"Wallahi ba haka bane. Su Anty Firdausi, su Abbas su Hanifa ke sace muku nama ba niba"

"Ai Maman yara ki kaita wajen Alhaji kawai dan idan kika bari Hajiya Kaka ta ji zancen nan ma shashashantar da shi za ta yi, gara a kaita gaban Alhaji ya mata hukunci a gaban kowa"

Ni kam dai Sahla bani da sa'a.

*
Karfe goma da minti biyar aka buɗe meeting da addu'a sannan aka shiga karanto jadawalin meeting ɗin. Meeting ɗin dai ya karkata ne kan Anty Firdausi wacce take shirin gama sakandare school bana sai kuma batun su Abban Egypt da za su zo hutun sallah. Da aka gama faɗin mahimman abubuwa sannan Alhaji ya tambaya ko akwai wani mai korafi ko wata matsala ko shawara. Caraf Mama ta ɗaga hannu ta ce Alhaji ina da magana. Alhaji ya bata izini.

Ina zaune a kasan kujera kusa da Hajiya Kaka. Koma mi za ayi dai na san Hajiya ba za ta bari ayi min bulala a gaban kowa ba kamar yadda Alhaji ya saba hukunta yara.

"Alhaji na kama ɓarauniyar nama a gidan nan. Da za a dinga magana ana cewa bama saka isashshen nama a miya yau dai na kama mai satan mana nama"

Kafin Alhaji yai magana Ummi ta fara nata haɗin.
"Alhaji, Sahala ta jima tana mana sata a kitchen. Ba dama ka kauda kai sai ka nemi abu ka rasa. Ranan wallahi abinda ta tsame min a tukunya yafi rabin kaza"

"Allah Karya su ke min. Alhaji Allah ban taɓa satan nama ba. Hajiya Kaka kawai na ke ɗaukewa nama"

"Na kama ki kina sata kice karya muke miki"

"Mama ai ban riga na cire hannuna a roban ba balle kice sacewa zan yi, kika sani ma ko kuda nake son cirewa a ciki. Alhaji Allah su Firdausi da su..."

"Yi mana shiru" Mama ta daka min tsawa.

"Kai Aishatu. Ki bar min jikata. Idanma ta saci naman ke kika siya ne da zaki bi ki ɗagawa mutane hankali. Ke kuma Zainabu yaushe kika dena siyarda kayan abinci da zaki tsalma bakin ki cikin maganan nan"

" Hajiya Kaka zancen nan fa tun ina Amarya ne fa"

"Ya isa!" Alhaji ya daka tsawa

"Zo nan Sahla"

Na mike daga gefen Hajiya Kaka na karisa gaban Alhaji.

"Faɗamin gaskiya kin ji. Na san ba kya karya Uwata"

Na ɗan sunkuyar da kai kasa nace "Alhaji, Allah fiffike ɗaya zan ɗauka shine Mama ta ganni. Da Mama tana bamu nama kamar yadda Anty Amarya ke bamu ai ba zan je na ɗauki fiffike a bayan idonta ba ko?"

"Haka ne" ya faɗa yana gyaɗa kai.

Irin kallon da Alhaji yaiwa Mama yasa ta fara Salati tana faɗin wai sharri na mata.
Alhaji bai min komai ba amma lokacin da Alhaji ya kai Hajiya Kaka ganin likita na daku a hannun Mama.
Ni dai Sahla a komai bani da sa'a.

***

Alhaji Muhammadu Ubandoman Gombe shine kakanmu. Matarsa ta farko 'yaruwarsa ce wato Hajiya Fatima, sun kusan shekara takwas da aure amma bata taɓa haihuwa ba wannan yasa ya auri wata Fatimar wacce a yau kowa ke kiranta da Hajiya Kaka.
Sai da Hajiya Kaka ta haifi 'ya'ya biyar kafin uwargidanta Hajiya Fatima ta haifi Sulaiman sababin haihuwar Allah ya ɗau ranta. Macece kamila sosai, ga hakuri da ilimin addini wannan yasa suka samu zaman lafiya da Hajiya Kaka. Bayan rasuwan Hajiya Fatima Alhaji Muhammadu ya auro Hajiya Sadiyya, har ya bar duniya kuwa babu jituwa sam tsakanin matan nasa, wannan ya ja rarrabuwan kan 'ya'yan.

Hajiya Kaka ce ta raini Sulayman shiyasa ma bata banbance shi da nata 'ya'yan ba.

'Ya'yan Hajiya Kaka sune:

Fatima Bintu
Kabiru
Fatima Zahra'u
AbdulKarim
Umar
Ahmad
Maryam

'Ya'yan Hajiya Sadiyya kuma:

Abubakar
Fatima Batula
Isma'il
Ɗahiru
Shehu

Kabiru shine namiji babba kuma shi ya gaji sarautan mahaifinsu ta Ubandoma. Kowa da Alhaji yake kiransa.

Kafin na cigaba ya kamata ku san wani abu. Lokacin da Kakanmu ke raye yayi kokarin sakawa 'ya'yansa mata suna FATIMA kasancewar sunan mahaifiyarsa kenan sannan sunan matansa biyu. Sai dai duk FATIMAN da aka saka ba ta fin sati biyu ta ke komawa. Kafin Bintu sai da Hajiya Kaka ta rasa FATIMA guda uku a jere. Ta huɗun da aka kirata da Bintu sai ta tsaya. Da ya auri Hajiya Sadiyya ma 'yarta ta farko Fatima aka saka mata ai itama ba ta yi wata ɗaya ba ta koma, sai ta biyun da aka saka mata Batula sai ta tsaya. Wannan yasa Hajiya Kaka ta camfa da cewa in har aka saka sunan FATIMA kuma aka barshi ba a kira yarinyar da wani inkiya ba komawa za ta yi.
Wannan kuma ya zauna daram. Kuma kaman dole sai an saka sunan Fatima a gidan. Ina ji wanda aka raɗawa sunan Fatima a familynmu sun fi ishirin. Daga Fatima kaza sai Fatima kaza. Da ace an bar mana babban sunan da inaga sai dai a dinga cewa Fatima 1, Fatima 2, Fatima 3, har Fatima 30 ko 50.

Ance 'yar Alhaji ta farko ma Fatima aka saka mata kuma ba a ɓoye sunan ba. A kasar turai aka haifeta amma bata yi wata uku ba ta koma. Wannan yasa kowa ya saduda da kiran yaransa da sunan Fatima zalla ba tareda wani inkiya ba. Nima ɗin Fatima Sahla sunana.

Matar Alhaji ta farko Gimbiya Maryam ce 'yar Sarkin Gombe. Dake yana karatu a chan kasar waje dan haka a nan suka fara zama. Yaransu uku a chan kafin auren ya mutu lokacin da ya tada batun kara aure bayan ya gaji sarautar Ubandoma.

Gimbiya Maryam ita ta haifi:

Fatima (ta rasu)
Aliyu Faruq
Fatima Hasina
Fatima Sayyida.

Bayan rabuwarsu ya auri Hajiya Aishatu wacce kowa ke kiranta da Mama, yaran Mama sune:

Fatima Karima
Mustafa
Abdullahi
Yusuf
Amina
Fatima Firdausi
Abbas
Fatima Nasiba

Matarsa ta biyu ita ce Hajiya Zainab wacce muke kira Ummi, yaranta tara amma uku sun rasu.

Sulayman
Asiya
Abbas
Fatima Zuhriyya
Safiyya
Fatima Haniefa

Matarsa ta uku kuma ita ce Hajiya Bilkisu, bazawara ce, yaranta biyu a gidan:

Fatima Fadila
da Fatima Nabila

Matar Alhaji ta Huɗu ita ce Anty Rafee'ah wacce muke kira Anty Amarya. Itama 'yar gidan Sarauta ce, mahaifinta kanine ga Sarkin Gombe. Shekaransu tara da aure amma har yanzu ba ta haihu ba. Ita ɗin likita ce shiyasa ba ta shiga tsurkun cikin gidanmu.

Mai bima Alhaji shine AbdulKarim wanda muke kira da Abba. Shi da matarsa da 'ya'yansa suna zaune a Egypt sai dai su kan zo sau ɗaya duk shekara. Yaransu huɗu ne:

Affan
Fatima Amal
Fatima Amra da
Sulayman (Boy)

Sulayman Muhammad Ubandoma shine mahaifina. Kamar yadda mahaifiyarsa ba ta yi tsawon rai ba haka shima bai yi tsawon rai ba. Kamar ma dai shi da mahaifiyata an halicce sune dan kawai su haifo Sahla sannan su bar duniya. Ance mahaifiyata ko sakani a ido ba ta yi ba har ta rasu. Awa ɗaya bayan ta haifeni ta koma ga mahaliccinta. Babana kuma ina shekara biyu ya rasu a hatsarin mota.

Yanzu Alhaji Kabiru shine mahaifina, Hajiya Kaka kuwa take zaman Kakata kuma Uwa. Amma a wannan gida duk gatana sai da a ka kirani da ɓarauniyar nama. Har yanzu zancen nan yaki mutuwa, in dai ana suyan nama ko a sallah ko a biki sai dai ban shigo ba amma yanzu za a maido zancen....


Read / Download SAHLA A PARIS

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

5 months ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album