Join Our WhatsApp Group

MAHABEER Complete Hausa Novel Document by MAHABEER


MAHABEER

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 131584



MAHABEER

Reading Time: 10 Hours

Added On: 15, Apr 2024

Author: Xayyneb ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Fasaha online writers f. o. w.

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 733.7 kb

File Type: txt

Views: 282+

Download: 461+

Last download: 38 minutes ago

Description/Story: ο»ΏCompiled By Umar Dalha Funtua.

Copied By Xernerb

🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

*QARAURAWAR SO* d'in dana karkad'a shiyasa nan da nan *ROUKEY PINKEEY* da kuma dai ita d'in taku wato
*DOCTOR DEEJART* suka garzayo a lokacin ba sanya, wanda hakan yasa ba zato ba tsammani sukayi *GAM* *DA KATAR* da *MAHABEER* ya iso nasa wajen shima...............

Uhmm...gaisheku nake yi masoyana a duk inda kuke,
ina fatan alherin Allah ya isar muku.
Fatan anyi *ibada* da *sallah* lpia an kuma gama lpian.

*Bismillaherrah manerraheem✍.*

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ1⃣
🌊🌊🌊
"A garin kaduna a kuma cikin G.R.A.
ta 'Yan majalissu, Anguwa ce wacce ta tara manya manyan masu hannu da shuni zaune a cikin ta,
'yan siyasa da masu hali kenan, sannan kuma a koda yaushe cikin unguwar zaka jita tsit babu hayaniya bisaga sauran anguwanni.
Gidan alhaji mu'aazam saraki shine gida mafi d'aukan hankalin mai kallon sa a layin,
Gida ne tsararre na gani a fad'a, duk da gidajen Suma fitattune a tsari da kuma kyau to amman kuma nasa ya d'ara nasu.
In ka shiga cikin Harabar gidan kuwa ba q'aramin girma ne da ita ba,
Daga can gefe kuma tampal tampal ne shaq'e da motoci na yayi sama da nawa a ciki, dan sunfi q'arfin a tsaya q'ilgasu komin sa idon mutum kuwa,
gudan gefen kuma injinan motsa jiki ne kawai sai lambu daga can side d'in Wanda babu kayan marmarin da babu a cikinsa, sannan kuma ga swimming Wanda ke cike da q'ananun kifaye sunata shawagi a cikinsa da fararen ruwa a cikinsu,
Sai d'ayan swimming d'in na wanka shima wani q'aton gaske ne cike da blue d'in ruwa a cikinsa,
daga gefensa ga Wasu kujeru da kuma fararen matakalu na shiga da fitowa a swimming pool d'in, sannan an ajiye wani d'an q'aramin gado da tebur na ajiye kayan buq'atu na Wanda in ka fito wankan zaka iya kwantawa dan hutawa,
ga kuma bukkar dake kewaye da gadon gwanin sha'awa dai abun,
Sam wurin inwa ce zalla babu rana haka wajen yake rayuwar sa.
Hakama q'aton falon gidan inka shigesa komi yayi, Wanda Keda d'akuna Sama da 7 a cikin sa, kowane d'akin babu abinda babu cikinsa najin dad'in rayuwa.
A hnkali ta ke saukowa daga saman benen kaida ganinta kuma zakasan lallai ita d'in matar mnya ce, fara ce tas da ita a q'alla shekarunta bazasu Gaza 37 ba, dayake bafulata na ce ita sosai.
(Hj umaima knn) hannayenta d'auke da wani dogon file ta q'araso ta zauna inda mai gidan nata yake wato Alhj mua'azzam saraki, zaune yk yana aikin duba wasu files files d'in dake gabansa na ofice d'inshi a nutse.
Zama tayi bisa 6arin jikinsa idanunta sunyi rau rau sun cika taf da q'walla, nan danan kuma ta sakar masa kuka mai cin zuciyar mai sauraro.
da sauri mu'azzam saraki ya maido hankalin sa gareta gaba d'aya bayan ya ture aikin da yake yi a lokaci d'aya.
Hannayenta ya ruq'o ya sanya cikin fuskarsa yayi shiru yakasa furta komi bayan duba file d'in hannunta d'in da yayi shima, hankalinsa ba q'aramin tashi yayi ba ganin irin baya nan da file d'in ya q'unsa a cikinsa.
Cikin muryan kuka tace "nuree kaga alamu sun nuna bazan ta6a haihuwa ba a rayuwa ko?!''
Tun da likitoci sunce wai ita d'in mahaifana bazata iya d'aukan cikin kaba nuree?,
Nuree mike faruwa ne damu haka?
Allah yayi mana Arziq'in dukiya Amman bai bamu yara ba yau shekara 17 knn da aurenmu nuree Amman na Gaza haifa maka d'a?
wayyo ni Allah na"!
Nan da nan ta sake fashewa da wani matsanancin kuka mai girgiza jiki d'in nan.
Kamota yayi yana shafa bayanta alamun rarrashi shima kukan zucin yk wnda yafi na sarari ciwo.
Ya zasuyi da ikon Allah ne to?
inda dai Allah bai basu ba sai suyi haq'uri, wataq'il ma d'an ba alheri bane a garesu yanzun shiyasa Allan bai basuba sai dai ya azurtasu da arziq'in Wanda har kullum suke temakon bayin Allah dashi.
Sauke ajiyar zuciya yayi ya rufe idanuwa sannan ya sake bud'esu jin tayi shiru da kukan alamun tayi tayi har ta gaji sai sauke ajiyar zuciya da takeyi,
minti wajen 11 suna a haka sannan ya duba yaga har tayi barci mai tattare da wata irin sabuwar shessheqar ajiyar zuciya sbd wahalar kukan nata data sha.
Girgiza kai yayi na tsananin tausayinta sannan ya gyara mata kwanciya anan wajen sannan ya sumbaci gefen ha6arta ya miq'e kai tsaye ya shiga part d'in mahaifiyarsa wato *Annah*,
farar bafillatanar dattijiwa mai Addini da sanin yakamata.
Ganin ta zaune kan carpet sanye da farin hijab tas dashi tana lazumi Wanda hakan ya tabbatar masa da sallar walha ta gama tana lazumi,
Agogon hannunsa ya kalla yaga 11 saura a lokacin, waje yasamu ya zauna kan d'aya daga maka maka grass carpet d'in dake falon Annah d'in, dan jiyayi Sam bazai iya hawan kujeran ba Dan har yanzu zuciyar sa bata samu sukuni ba, bakomi a cikin ta sai tsananin tausayin umaimah dan gane da rashin haihuwar da batayi ba,
Tagumi ya rafka tareda rufe idanunsa zuciyarsa na wani irin d'as d'as,,,,
Jin an janye hannunsa daga tagumin ne yasa yayi saurin kallo wajen,
Annah ce ta zauna gefensa har lokacin hijab d'in na jikinta da cazbahar ta tana ja, dan ita abin ma ya zame mata jiki kullum cikin lazumi take, kokuma taita karanta addu'oe cikin hadith hadith nata.
A hnkali mu'azzam saraki ya sunkuya tareda furta "ina kwana Annah?
An tashi lpia?"
"Alhamdulilla yarona, Amman dai kasan tagumi ba abu ne mai kyau ba ko?
Baice komi ba sai Murmushin da ya d'an kalato da q'yar sannan ya miq'a mata file d'in hannunta yace
"Annah wannan shine sakamakon da wannan baturen Dr nayz yayi a bincikensa na zuwan da umaimah tayi jia Egypt dan duba lpiar mahaifar nata"!
amsar file d'in tayi sannan ta janyo medical glass d'inta ta sanya mai q'ara q'arfin ido,
sannan ta bud'a file d'in ta fara dubawa itama,
Takusan minti 5 tana q'ara maimaita karanto file d'in itama sannan ta d'ago kai cikin yankewar zuciya ta dubi mua'azzam tace
"yarona?"
D'agowa yayi ya dubeta ya sake maida kansa q'asa yace
"na'am Annah"
Annah taci gaba da cewa "Kuyi haq'uri, insha Allah komi yayi farko zaiyi qarshe, Allah kad'ai yasan nufinsa akan hakan shiyasa bai Baku haihuwan ba, bakomi Allah yasa hakan shi yafi zama mana alheri gaba d'aya".
nan ta dunga tausar sa da rarrashinsa tana mai q'ara fad'i masa yawan ladan da wad'anda Allah bai basu haihuwa ba suke samu sakamakon haq'urinsu da juriya kan jarabawar da ubangiji ya saukar musu a Kansu.
Cikin lokaci q'anqani kuwa yaji ya rage damuwar sosai Annah tace
"tashi to katafi office Allah shi taimaka,
kuma zan shiga wajen ita umaimah d'in itama zan tausheta abinda haq'uri bai bayar ba ai kuma dai banga dalilin da tsiya zata kawo sa ba,
Mubar komi ga Allah zai kawo mana mafita insha Allah"
"Hakane Annah nagode q'warai,,,, madalla da uwa ta gari "!
Haka mua'azzam
saraki yaje ya shirya direbensa yaja su suka fita zuciyarsa a d'an sauqaqe sosai.
Saida dare ne suna kan carpet d'insu na nan falon inda suka saba cin abinci,
da yake ita Annah Sam bata iya hawan dining table d'in suyi dinner shiyasa suke zama q'asa indai tana nan gidan nasu bata koma can mahaifar su ba wato (katsina).
suna cin abincin ne bayan sun gama anan ita Annah d'in ta dingi tausar zuciyar umaimah itama kamar yanda taiwa mu'azzam saraki shima d'azun gameda result d'in doctor,
har ta q'ara da cewa "kuma ay bnda abinki d'iyata miye ma na damuwar to? ay result d'in doctor bana Allah bane, kawai dai mu d'auka cewar Allah bai kawo haihuwar bane shiyasa.
Dayake Annah ta iya tafiyar da lafazinta a tsanake cikin *Fasaha* shiyasa komi na jikin umaimah yayi sanyi ta shiga furta Astagfurullah cikin zuciyar ta na ganin kamar tayi bore wa Allah ne akan abinda bai basu ba a lokacin da suka so su kuma.
Haka koda zasu kwanta saida sukayi nafilolin su suka roq'i ubangiji Allah ya kawo musu mafita....

Asalinsu...
Mu'azzam saraki shine cikakken sunan sa,
babban ma'ikacin government ne Wanda a q'alla Albasshinsa duk wata zai tasamma 5 million, sannan gefe guda ga manyan kasuwancin sa da yake yi na shigo da gold, diamond. motoci, yana saidawa 'yan kasuwa, sannan kuma ga gidajen mansa Suma Sama da guda 15,
shiyasa kaf fad'in nijeria babu inda zakaji an ambaci sunan *Alhj "mu'azzam saraki*" ba'a san shi ba,
Yana yawan zuwa kai temako a gidajen marayu, isslamiyyu, data Almajirai, haka nan inya samu change yakansa direbensa ya jasa ya kai sa anguwannin dayasan akwai talakawa sosai mabuq'ata ya dinga yi musu kyautar ban girma Harda masu muhalli duk yana basu wa marasshi, irin wadanda ruwa ya zubdawa gidaje,
Shiyasa har murna suke marassa q'arfi ace yau ga Alhj mu'azzam saraki yazo sunsan ranar take salla a wajen su, dan zai basu abinda zasu yi shekara 3 dashi suna juyawa dan kasuwanci,/ noma, ammanfa ga masu burin cikinsu,
Shiyasa addu'a kullum Shanta mu'azzam saraki yakeyi a maban bantan bakunan Al'umma.
Asalinsa d'an katsina ne, mahaifinsa Alhj muntari saraki ya rasu tun yana Q'arami, a hannun mamansa hajara ya taso wacce yake kira da Annah, Ta haihawa kafinsa Amman duk Allah yayi musu rasuwa yaran tun suna q'ananu,
mu'azzam ne yayi tsawon rai cikin rayawa ta ubangiji Allah.
Cikin dangi suke luntsum shiyasa mua'azzam Sam bai san maraici ba, Allah yabasa dangin baba da mama masu zuciyar yi.
Q'anen mamansa shine ya tsaya kan karatunsa har ya girma ya had'asa aure da babbar d'iyarsa umaimah dashi mu'azzam d'in ya nuna yana sonta Wanda dama itama umaimah hakan yake a cikin zuciyar ta.
Lokacin har ya fara Aikin gwamnati harma ya gina gidan sa plate house mai kyau, anan suka fara zama kusan tsawon shekaru 12, sannan akai masa q'arin girma Wanda hakan ya kaisa aiki garin Kaduna shekara 5 kenan da komawar tasu kd, Wanda tun tsawon shekarunn nan Allah bai basu haihuwa ba, lokacin arziq'in sa kuma sai q'ara bunq'asa yake,
Duk bayan lokaci sukanje katsina su d'auko Annah tai musu kwanaki a gidan takoma can katsina,
Bacin sunyi sunyi da ita kan ta dawo gidan da zama taq'i fur, sai dai a zuwan tazo musu Hutu ta koma can.

Wanda yau kwananta 11 kknn da zuwa gidan d'an nata Hutu,
dan su kansu 'yan uwansa ba q'aramin cin arziq'in Alhaji mu'azzam sarakin suke yiba,
Wannan kenan.

***
Washe garin ranar ta Asabar dukkan su 2n mua'azzam saraki da matarsa umaimah suka dinga jinsu cikin farin ciki haka nan, bayan sun gama break fast ne nan umaimah ta shige jikin Annah tanawa mu'azzam gwalon tarigasa d'alewa jikin Annahn tasu.
Lokaci d'aya kuma ta tashi tace "yawwa Annah daman nai niyar bazan fad'i wannan mafarkin nawa a gabnsa shi d'aya sai anan gabnki, dan wataq'il abinda Nike so yai mun kmr ynda nasa rai zaiq'i amin cewa ammn in agabnkine zakisa yayi mun"
ta q'arshe maganar kanta a langwa6e.
dukkan su daga mu'azzam saraki har ita Annah sun zubawa umaimah ido da tunanin mita mafarkato??
Annah tace
"to shiknn 'yata fad'a muji muna sauraronki,
Cikin sunne kai qasa umaimah tace
"Annah jiya ne nayi wani mafarki,
Wato bayan munyi nafilar dare mun kwanta barci,
Nayi mafarki ne wai gani da wani yaro ga hannuna Wanda bai wuce shekara 3 ba, wlh Annah yaron kyakkyawan gaske ne kuma,
nazo wucewa nagansa zaune cikin wasu yara da yawa suna wasa, yana ganina yazo da gudu ya rungumeni kamar ya sanni yana fad'in "Mammy na !" "Mammy na !"
zan zauna dake,
ki kai ni gidan ki wajen babana....!!!
"Annah wlh nan muka zauna da yaron cikin yaran munata wasan tare Amman yaron nan yana manne jikina nima naji banson rabuwa dashi,
Dan a lokaci d'aya naji q'aunar yaron a raina, to muna nan zaune zuwa bayan wani lokaci saiga wata mata tazo ta kwashi yaran har dashi yaron Wanda da q'yar ta samu yabar jikina suna tafiya naga yanata waiwayena tareda mun bye bye,
nima bnsn snda na d'aga hannuna ina masa bye bye ba, har naga sun shiga wani babban gida Wanda naga an rubuta a saman gidan saman wani q'aton symbol, *GIDAN MARAYU*,
to kuma a dai dai nan na farka hankalina a tashe ,,
D'an dakatawa tayi sannan ta miq'e zaune tayi durq'uso a gabnsu tareda had'a hannayenta biyu muryarta na rawa taci gaba da cewa "Annah? nuree? dan Allah Ku yarda Ku amince muje gidan marayu mu samo yaro Wanda zai yayemun damuwar rashin q'waina a duniya, wataq'ilama ta sanadiyyar kulawa da marayan Allah ya jiq'anmu ya bamu namu rabon, Dan wnda ya temaki mabuq'aci tabbas Allah bazai q'i saka masa da mafi alherin sa ba,
Annah nasan kunsan haka kuma, dan Allah Ku amshi q'oqon barana da nazo muku dashi" magana takeyi wasu siraran hawaye na sauko mata a fuska.,
dukkan su sunyi tsit Sai Annah ta dubi mu'azzam saraki shima ya dubeta kuma,
Duban umaimah Annah tayi tare da girgiza kanta tace....



XayynebπŸ’€πŸ’€ .
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ2⃣.
🌊🌊🌊
"Duban umaimah Annah tayi tareda girgiza kanta tace "anya kuwa 'yata hakan mai yiyuwane?"
Shiru umaimah tayi kanta na a q'asa idanunta na zubda hawaye.
Kan Annah ta q'ara cewa wani Abu mu'azzam saraki yayi saurin cewa
"To jeki in mun d'auko shi yaron ma mun riq'eshi inya girma kinsan da sanin dai cewa zai tambayemu inda haq'iq'anin iyayensa suke dai ko?
Sai muce masa mi to a lokacin to knn?
Cikin rawar muryar kuka ta d'ago tace
"kayi haq'uri nuree,
in muka d'auko shi zamu nuna masa mune iyayensa ay har girmansa kaji nuree dan Allah ku taimaki rayuwa ta ku amince wlh jinake kamar zan mutu in zuciyata bata samu abinda take so ba.
Ajiyar zuciya Annah ta sauke tace "to in muka nuna masa hakan mu mune iyayensa mutanen duniya fa ai sun sani,
Cikin sauri da kyarmar murya na wacce ta gaji da kuka umaimah tace "A'a Annah ba zasu sani ba indai mukabi tsarin da nike tunanin zan fad'a muku shi yanzun.
Annah tace to fad'i tsarin naki sai muji ai,
"Annah zaki buga musu waya can family namu na gida katsina kice ashe jimawar da kikayi kina rashin lpia har na tsawon wata 8 baki zo ba to ashe inada ciki Wanda mukaso muyi shiru har sai na haihu dn inkunji labari kuyi mamaki, to zuwanki shine kikaga cikin a jikina wnda harma ya isa haihuwa to shine kuma kika bugo danki fad'a musu sutayamu murna da addua,
faq'at Annah hknma in kikace musu ya wadatar dan nasan zasu yarda ne duka,
To kinji wannan shine shawarana nasan kuma Kun aminta da ita.
ganin sunyi shiru babu wnda yace komi tsakanin mu'azzam saraki da ita Annah yasa taji zuciyar ta ta sake karewa tasan ma q'ilan bazasu amince ba, nan ta fara rusa musu wani sabon kukan tana binsu da rarrafe tana kama q'afafunsu tana zubar da hawaye.
Cikinsu Babu wnda zuciyarsa bata kare ba ya tausaya mata ganin ynda ta q'wallafa ranta akan son ta ganta tana renon d'a.
A zuciyar...


Read / Download MAHABEER

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album