Join Our WhatsApp Group

SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH Complete Hausa Novel Document by SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH


SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 48806



SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH

Reading Time: 4 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H)

Author Phone : 080-325-857-34. 070-687-636-00. 080-370-233-43

Book License : Free

Category: Documentation

File Size: 270.9 kb

File Type: txt

Views: 768+

Download: 305+

Last download: 11 hours ago

Description/Story:
SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH!

(Tarihi, Karamomi, Darajoji da Baiwar Jagoran Harka Islamiyyah A Afirka, Shaikh Ibraheem bin Ya'aqub Al-Zakzaky H).

Na:

CIBIYAR WALLAFA DA YAXA JAWABAN SHAIKH ZAKZAKY (H).

(Institute For Completion And Publication of Shaikh Zakzaky's Works).

AUTHENTIFICATION:
Copyright©: Institute For Completion And Publication of Shaikh Zakzaky's Works.
Haqqin Mallaka: Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H).

ISBN: 978-978-959-905-9

TUNTUBA:
+234-80-32-58-57-34. +234-70-68763600. +234-80-37023343.

MASANIYA:
Littafi: Shaikh Zakzaky Ikon Allah!
Rubutawa: Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H).
Jigon Batu: Tarihin Rayuwar Sayyid (H).
Shekara: 1438-Hijira. 2017-Miladi.
Wallafa: 12-Stars Multimedia.
Kanu: Babi 7, Fasali 83.
Kalmomi: Ya Qunshi Kalma 47,650.
Farashi: Daidai da Kasuwa.
Adireshi: Nigeria, WestAfrica.
Tuntuba: 080-325-857-34.

KYAUTARWA:

Muwafaqa a Wannan Littafi, Hadiyya ce ta Musamman Ga Ma'abucin Alfarma Da Daraja, Baqiyyatullahi Fil-Ardh, Sahibul Asr Waz-Zamaan, Imamul Hujjah, Al-Qa'im, Al-Mahdiy Bin Hasan Al-Askary (AF).

IZINI:

Ya halasta a yi amfani da sashen wannan littafi ko dukkansa wajen yada manufa kyakkyawa, kamar yadda ya halasta a sake bugawa don yadawa, amma bai halasta a canza wani abu ko a sake masa fasali ba sai da izinin marubutan.

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

GABATARWA

Da sunan Allah mai Rahama mai Jinqai. Tsira da Aminci su ci gaba da dauwama ga fiyayyen halittu, Annabin Rahama Muhammad xan Abdullahi (S), da Iyalan gidansa tsarkaka ma’abuta daraja, wanda ba sa kuskure ko savo.

Babban dalilin da ya haifar da rubuta wannan xan littafi shi ne, lokacin da gwamnatin Nijeriya qarqashin shugaban qasa Muhammadu Buhari ta abkawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa a birnin Zariya ranar 12 ga watan 12 na shekarar 2015, inda ta kashe almajiransa kusan Dubu xaya, ta raunata xaruruwa, ta kuma tsare xaruruwa, ciki har da yi wa Shaikh Zakzaky da mai xakinsa ruwan harsashi, da raunata su a wurare da dama, da kuma kama shi da tsare shi ba bisa qa’ida ba, wanda hakan ya jawo gangami da Muzaharorin Allah wadai a qasashen duniya da dama.

Hakan ya sa al’umomin duniya a xaixaikunsu da jama’ance suna ta tambayar waye Shaikh Ibraheem Zakzakin nan? Meye tarihinsa? Ya labarinsa yake? Ta yaya za su san wani abu a kansa? Duk xan uwan da ke mu’amala da ‘yan qasashen waje ko da kuwa ta “Social Media” ne, zai iya zama shaida na qishin ruwansu ga neman sanin tarihin Shaikh Zakzaky (H). Wannan ne qashin bayan da ya zaburantar da mu don samar da wani xan abin da zai ba mutane haske game da wannan Jagora mai albarka.

Tarihin Jagoran Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Bin Ya’aqub Al-Zakzaky (H) abu ne mai faxin gaske, da wuya wani marubuci ya iya rubuce tarihin Shaihin Malamin baki xaya saboda faxinsa. To amma Larabawa suna da karin maganar da ke cewa; “Abin da ba za a iya yinsa duka ba, to, bai kamata a qi yinsa kwata-kwata ba”. Wannan ne ya sa muka ga dacewar yin tsokaci game da wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar wannan Jagora a gurguje kuma a taqaice, domin hakan ya zamo manuniya ga masu sha’awar faxaxa sanin tarihinsa ko yin rubuta a kansa, kuma ya bai wa wasu haske game da tarihin wannan babban Malami Jagora a Afirka. Ko kaxan, wannan xan littafin ba zai zamo ya wadatar ga sanin tarihin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba, domin akwai abubuwa da dama da ba a tavo su ba don gudun tsawaitawa, sa’annan waxanda aka tavo xin ma sama-sama aka tava su, an ambaci sashensu ne kawai ba dukkansu ba. Dan haka, mai son sanin faffaxan tarihin shugaban Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sai ya koma zuwa ga wasu littattafan da aka rubuta a kansa, da waxanda za a rubuta nan gaba. Ximbin mutane sun bada gudunmawa mai yawa ta vangarori daban-daban wajan haqqaquwar wannan littafi, ta yadda ba zai yiwu a iya jero ko ambato sunayensu duka ba, amma tattare da haka muna matuqar miqa jinjina da godiyata garesu, Allah ya saka musu da mafificin sakamako. Dukkan yabo da godiya ga Allah suke tuqewa, kuma duk wata dacewa daga Allah take, gare shi muka dogara, kuma gare shi muke neman taimako!

Bissalam.
Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky (H).
080-325-857-34. 070-687-636-00. 080-370-233-43.

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

BABI NA FARKO

TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) A TAQAICE

Salsalar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) :

Tarihi mafi inganci da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da kansa, ya faxi cewa asali iyayensa sun fito ne daga Magrib (Moroko); Daga nan suka zo birnin Shingixi na tsohuwar daular qasar Mali, amma yanzu birnin na Shingixi mai tsohon tarihi yana qasar Mauritaniya ne, daga garin Shingixi kakanninsa suka yo qaura zuwa birnin Mabruk da ke qasar Mali, daga nan kuma suka zauna a birnin Timbuktu, daga birnin Tumbuktu ne kuma suka taho wannan qasa Nijeriya cikin qarni na 12. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 09 zuwa 11).

Nasabarsa :

Salsala ko nasabar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta jero ne kamar haka; Shaikh Ibraheem xan Ya’aqub, xan Aliyu, xan Muhammad Tajuddeen, xan Liman Hussain Batoronke, shi Liman Hussain Bafulatani ne daga qabilar Toronkawa wanda ya zo qasar Hausa daga Mali a zamanin Shehu Usman bin Fodiye, inda ya zama babban limami a garin da yake zaune a yankin Sakkwato. Daga bisani sai xansa Malam Tajuddeen wanda almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne ya biyo tawagar wakilin Xanfodiye na Zazzau, wato Sarkin Zazzau Malam Musa suka taho Zariya tare dan ya riqa karantarwa. Mafi yawan tarihin da ake rubutawa na salsalar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) yana tuqewa ne akan Liman Hussain, wataqil don gudun tsawaitawa, domin jerin nasabar Shaikh (H) tana tuqewa ne ga Imami na biyu cikin limaman shiriya na Ahlul-Bait (AS), wato jikan Manzon Allah (S) Imam Hassan Al-Mujtaba bin Aliy bin Abiy-Talib (AS), xan Sayyida Fatimah Azzahra (SA), wan Imam Hussain shahidin Karbala (AS).

Mahaifinsa :

Sunan mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam Yaqubu Aliyu, ana masa laqabi da Malam Magaji, tarihi bai ambaci takameme shekarar da aka haifi Malam Yaqubu Aliyu ba, amma ana kyautata zaton an haife shi ne a shekarar 1902. Ya taso a gidan malanta da ilimi, dan haka ya taso ne da karatu da riqo da addini, tun tasowarsa mutum ne mai haquri da sanin ya kamata, an shaide shi da kyawawan xabi’u da aiki da abin da ya karanta. Sana’arsa ita ce koyarwa da kuma Noma da Kiwo. Ana kyautata zaton ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 70 daidai (1902 – 1972), ko shekaru 72 a qidayar Hijiriyyah.

Allah ya yi wa mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Malam Yaqubu Aliyu rasuwa ne a watan Fabarairu na shekarar 1972, ya rasu ne a wani kududdufi da ke bayan unguwar Qwarbai cikin birnin Zariya, a lokacin da ya je ceto wata Akuya da ta faxa cikin kududdufin lokacin da ta je shan ruwa, kuma an yi masa jana’iza aka binne shi a maqabartar da ke kusa da kududdufin, yanzu haka qabarinsa yana wurin. Ya rasu ya bar ‘ya’ya 16, maza takwas, mata takwas.

Mahaifiyarsa :

Malama Salaha Muhammad Gixaxo, wacce aka fi sani da Hajiya Hari Jamo ita ce mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Bafulatanar usuli ce daga qabilar Fulani Toronkawa, kakanta Malam Abdulqadir ya taho ne daga qasar Mali ya yaxa zango a Zariya. Laqabinta na “Hari” a harshen Fulatanci yana nufin “Wacce aka haifa a Damina”. An haifi Hajiya Salaha ne a shekarar 1924 a cikin birnin Zariya. Ta haifi ‘ya’ya 12 da mijinta Malam Yaqubu, amma 5 daga ciki sun rasu tun suna qanana, kuma Shaikh Zakzaky (H) shi ne xa na biyar a wurinta.

Mahaifiyar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) Hajiya Salaha (Hari Jamo) malama ce mai ilimin addini, ta kasance tana karantar da mata maqwabta da matan unguwa da kuma qananan yara a cikin gida. An shaideta da yawan ibada, musamman karatun Alqur’ani da yawan addu’a. Ta rasu ranar 17 ga watan Nuwamba na qarshen shekarar 2014 (25-Muharram-1436), sakamakon jinyar da ta yi fama da ita, kuma ta rasu tana da shekaru 90 daidai a qidayar Bature (1924-2014), ko shekaru 93 a qidayar Hijira. Ta bar ‘ya’ya 6 da jikoki masu yawa, qabarinta yana Hubbarenta da ke unguwar Jushi a cikin birnin Zariya.

'Yan Uwansa :

Mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wato Malam Yaqubu Aliyu, ya rasu ya bar ‘ya’ya goma sha shida ne cif a duniya, takwas maza, takwas mata, su Shaikh Zakzaky (H) su bakwai ya bari ta wajan mahaifiyarsu Hajiya Salaha, wato wanda suka haxa uwa xaya uba xaya, maza huxu, mata uku, ga su a bisa jerinsu; Abdulqadir Yaqub, Maryam Yaqub, Fatimah Yaqub (Goggon Qaura), Ibrahim Yaqub (Sheikh Zakzaky), Badamasi Yaqub, Yahya Yaqub, sai ‘yar autarsu Maimunatu Yaqub.

Ta vangaren sauran ‘yan uwan Shaikh Zakzaky guda 9 kuwa, sun haxa mahaifi ne kawai da su, wato mahaifinsu xaya, amma mahaifiyarsu ita ce Hajiya Aminah wacce ake qira (Iya mai Manja), su tara ne, maza huxu, mata biyar, ga su a bisa jerinsu; Muhammad Sani Yaqub, Ramatu Yaqub, Karimatu Yaqub, Usman Yaqub (Sarkin Malaman Fadar Zazzau), Maryam Yaqub, Abubakar Yaqub, Salihu Yaqub, Zaliha Yaqub, sai ‘yar autarsu Hajara Yaqub.

A jumlace, waxannan sune ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) na jini, kuma Shaikh (H) ne xa na shida a wajan mahaifinsu, amma na biyar a wajan mahaifiyarsa, (bisa lissafawa da wansa Zubairu Yaqub, wanda ya rasu yana qarami).

Haihuwarsa :

An haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne gab da hudowar Alfijir na ranar Talata 15 ga watan Sha’aban 1372 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da Talata 5 ga watan Mayu shekara ta 1953 Miladiyya. An haife shi ne a bayan Fada da ke unguwar Kwarbai cikin birnin Zariya jahar Kadunan Nijeriya.

Suna da Laqabinsa :

Sunan jagora shi ne Ibraheem, laqabinsa kuma Al-Zakzaky, wanda fassararsa ke nufin mutumin Zariya, wato mutumin qasar Zazzau, ko Bazazzagi a taqaice. Laqabin Al-Zakzaky ya samo asali ne a lokacin yana makaranta, sai ya zamo su biyu sunansu ya zama iri xaya (Ibrahim Yaqubu), sai aka ce kowa ya qara suna xaya a jikin nasa, sai Shaikh ya qara Zakzaky a jikin sunansa, daga nan ake qiransa Al-Zakzaky.

Wani laqabinsa da ya shahara shi ne laqabin da Shaikh Usman bin Fodiye ya laqaba masa tun sama da shekaru 200 kafin haihuwarsa, wato laqabin Sharafuddeen, wanda fassararsa ke nufin “Mai Xaukaka Addini”. Sai kuma laqabin Ibraheemul-Magriby, wanda ke nufin “Mutumin Yamma” wanda shi ma laqabi ne da ya samo asali daga zantukan waliyai magabata. Sannan akwai laqabin “Khaleel” wanda iyalinsa Malama Zeenatuddeen ce kaxai take kiransa da wannan laqabi. A taqaice Shaikh (H) yana da laqubba guda uku, wato Zakzaky, da Sharafuddeen, da Al-Magriby, sai kuma na khass da iyalinsa ke kiransa da shi, wato Khaleel.

Siffofinsa :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baqin fata ne mutumin Nijeriya a Afirka ta yamma. Matsakaici ne a tsawo amma ya fi kusa da gajarta. Yana da matsakaiciyar qiba. Kyakkyawa ne mai kyan sifa da kyan diri. Yana da manyan idanu matsakaita girma. Yana da faffaxan goshi, da faffaxan qirji, da karan hanci. Yana da hasken fata da madaidaitan kunnuwa. Yana da mayalwacin gemu amma bai da qasumba. Yana da tsaga bibiyu a kwivin idanuwansa biyu, wanda hakan ke alamta cewa shi Bamalle ne a qabilar Fulani. Ta ko ina bai da naqasa a halitta. Yana da cikar kwarjini da Haiba. Yana da izza a cikin tafiya da zamansa. Haziqi ne mai fikira da hangen nesa. Fasihi ne mai fasahar magana. Xan baiwa ne a ilimi, Fikira da sanin fannoni.

Yarintarsa :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taso a gida na addini da tarbiyya, dan haka tun yana yaro qarami ya gudanar da yarinta ce mai tsabta, sam ba a san shi da qin jin magana, ko faxa da yara, ko mugunta da qeta, ko nuna fin qarfi ga wanda ya fi ba. An san shi ne a matsayin yaro mai dattaku, mai tarbiyya, mai girmama na gaba, mai ladabi ga iyaye, mai tausayin qanne, mai taimakon tsofaffi, mai son karatu, kuma mai qwazo da rashin kasala.

Iyaye da ‘yan uwan Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da cewa tun yana qaramin yaro bai tava zuwa neman qarin miya ba, wato in an zuba masa abinci komai qarancin miya ba zai ce a qara ba, kuma in yana cin abinci miya ta qare, to ko bai qoshi ba haka zai haqura, amma ba zai je ya ce a qara masa miya ba. Wannan yana nuna halin dattaku da Makarimul-Akhlaq xin Shaikh (H) ne tun yana qaraminsa.

Wanda suka san tasowa da yarintar Shaikh Zakzaky (H) sun tabbatar da kyawawan halayensa na yarinta. Dattijo kuma xan Sarkin Zazzau Aliyu Xan Sidi, wanda aka fi sani da Alhaji Basiru Aliyu Xan Sidi ya faxi cewa; “A wancan lokaci (na yarinta), sanin da na yi wa Malam Ibraheem Zakzaky yaro ne mai hankali da biyayya ga na gaba da shi, tare da dattako, ban kuma tava jin wani abu na laifi ko kuma aibu akansa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 84).

Shi ma Magayaqin Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya faxi cewa; “Ni dai na san shi (Ibraheem Zakzaky) yaro ne mai kawaici, sannan bai cika maganganu haka barkatai ba… A makarantun da ya yi yana da ladabi da biyayya ga duk na gaba da shi a yawan shekaru, domin mu nan ba mu samu wani abu da za mu soka game da shi ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82).

Wata dattijuwa ‘yar kimanin shekara 100 daga zuriyar gidan su Shaikh Zakzaky (H), wacce ake kira Goggo Fatimah, ta bada kyakkyawar shaida akan yarintar Shaikh xin, ta ce; “Shi dai lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki… tun farko mun ga alamar zai zama wani abu. Yana da biyayya qwarai da gaske. Mutum ne mai zumunci, ya san nasa, duk inda suke zai sa qafa ya bi su da alheri, dama (tun asali) da alherinsa ya taso, ba yanzu ne ya fara ba, tuntuni haka yake… Tun yana yaro bai san faxace-faxacen nan na yara ba, ba ruwansa, shi ya taso kamar Dattijo ne, tun yana yaro kamar dattijo yake, irin sakarcin nan ma na yara shi ba ya yi, sai ma idan yara sun yi abun da bai dace ba, sai ka ga ya tsawatar musu” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 68).

Wani abokin Shaikh da suka taso tare, mai suna Malam Wadan Mai Raqumi yana cewa; “Ibraheem mutum ne wanda tun yana yaro ba ya son wasa ko wulaqanta addini, (sannan) shi ba ya irin mugun wasannin nan da yara kan yi, ko a unguwa ko a makaranta, idan mun zo muna yin (mugun wasa) sai ka ga ya koma gefe guda abinsa” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24).

A taqaice, Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne, tun tasowarsa ya taso ne a matsayin kamili mai halin dattaku, duk wani shexanci na yara bai yi shi ba, da kamala da kyawawan halaye ya taso. Kenan halaye da xabi’un Shaikh Zakzaky (H) rinin Allah ne,...


Read / Download SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

6 months ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album