Join Our WhatsApp Group

A TSAKANKANIN SOYAYYA Complete Hausa Novel Document by A TSAKANKANIN SOYAYYA


A TSAKANKANIN SOYAYYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 58282A TSAKANKANIN SOYAYYA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 05, Apr 2023

Author: Aisha Muhammad Maman Shakur ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07012181461

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 332.54 kb

File Type: txt

Views: 7009+

Download: 3725+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: _IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.1️⃣


_How to subscribe littafin ATSAKANKANIN SOYAYYA_
_*zaki turo 300 ta account dina 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting*_
_*zaki iya turo iya turo katin MTN ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_*Free page*
_Laguna Beach, California._
Babban Beach ne mai girman gaske dayaci sunan shi, Beach ne daya sami World recognition wanda har duniya tabashi World Best Beach a shekaran 2018, atsanake fishing vassel (boat) ke tafiya akan blue ruwan, wani dogon farin saurayi ne tsaye ata gaban jirgin yanada dan jiki kadan dan cikakke ne yana thick body irin jikin maza masu sunan maza, yana sanye dawani brown shirt da dan gajeren short na maza wanda da kadan ya wuce bombom dinshi, kafafun shi sanye dawani white bathroom slippers mai kyan gaske dayadan yima kafarshi tsawo, kanshi sanye da wata jan pcap, kunenshi daya makale da dankunne dake walkiya yana tsaye yana kallan blue ruwan da kifaye ke tsalle suna fitowa suna komawa, yakai kusan minti biyu a tsaye ahaka kafin ya fuzar da iska mai dumi ya mika hannunshi yadau fishing rod dake gefenshi jingine da karfen baki bakin jirgin, dauka yayi ahankali ya rike ya warware igiyan kafin yazura fishing rod din cikin ruwan, dan murmushi yasaki for the first time kana gani kasan he loves wat he's doing, jawo fishing rod din yayi waje tunawa da yay mantuwa yasake kallon gefenshi wani dan sachet din ledane da akai zanen kifaye ajiki an rubuta fish food ajikin ledan ya dauka, bude ledan yayi yasa white hand dinshi ciki yaciro abincin kifi guda daya dake kama da cheese balls saidai yafi cheese balls tauri yakama hook din fishing rod din ya makala abincin hook din ya bame abincin bam hakan yasa ya maida fishing rod din cikin ruwan yana jujjuyawa sanin yanzun nan he's about to catch a fish, almost 30sec kafin yay wani irin murmushi cikin wata murya chan kasa mara kara sosai yace "gatchuu" dasauri yay wining spring din igiyan ya shiga dawowa baya, ringing wayarshi dake cikin aljihun short dinshi ya shiga yi dan lumshe ido yayi ya bude daidai lokacin igiyan dake rike da hook din yafito rike da wata katuwar kifi mai rai sai kici kicin kubutar da kanta daga hook din take amma takasa janyo fishing rod din yayi yana murmushi yana kallon kifin ya sauka kasa ya karasa yana tafiya yana kallon fish din yakai gaban wani dan basket mai zurfi all this while wayarshi na ringing amma bai damuba ya jefa fish din cikin basket din sanan ya ijiye fishing rod din akasa yasa hannu ahankali yaciro hadadden wayarshi daga aljihu ya kalli screen din dan yatsine fuska yayi kaman wanda bayason daukan wayar ya danna yakai wayar kunenshi ashgwabe yace "Dadddddd" yawani ja sunan kaman mai shirin kuka, daga tachan bangaren wani muryan wanda yadan manyantane yace "don't Dad me anan, kasan abinda kayi, you know Aliyu, ina bodyguards dinka?" mutumin yafada cike da masifa, yamutse fuska yayi cikin murya chan kasa kaman wanda baison yay magana yace "nasan u already know, why are you asking again?" "kaci gidanku Aliyu, kaniyarka nace, nikake ma magana haka? Ai dama nasan inda suke dasu nafara communicating inji lafiyan d'ana kafin nakiraka, and maza maza ka juya jirgin nan ka koma chan bakin Beach inda ka barsu, idan kanason kai fishing carry them along with you kaje kai fishing dinka since is your hubby, while you are fishing su suna gadin ka, I hired them just to protect you for me, kasan how much nake spending for your security iyye?" sosai shima cikin fushi kaman zai hadiye zuciya yace "ai bance ma inaso ba, I don't need them am old enough to protect my self Dad, and besides Allah is the protector of all mankind, kuma ni stop treating me like a toddler am not that baby you use to feed Cerelac and gaber rice, am 29years 7months am an Adult and ni bansan security ko bodyguards ne whatever their name is, free me Dad please" daga tachan bangaren mutumin yace "sannu Mr Aliyu Adult, yaushe ka girman dududu? Katashi kataho fishing bakasaka sweater ba am sure anjiman nan, anjima kadan zaka fara sneezing up and down, ka juya jirgin nan kawuce katafi wlh kona sassaba maka, zan sassaba maka Gadanga kanajina ko, kawuce katafi kuma next week zaka dawo Nigeria you will be under my watch ko hankalina ya kwanta nima nagaji da kiran security ka every single minute ina tambayan su kai, gwara kadawo gabana ina ganinka kullum hankalina akwance, ka juya jirgin nan katafi and find something to cover yourself am I clear?" shiru yayi yaki magana ya daure fuska sosai batare daya zare wayan daga kunenshi ba cikeda masifa mutumin yace "am I clear Aliyu?" murya chan chan kasa yana turo baki yace "eh" ya katse wayan duk ranshi a dagule ya maida wayar aljihun wandonshi ya kalli fish din daya kamon dahar yamutu yatashi ahankali yay wajen injin din jirgin ya kunna yazo ya tuka jirgin yafara gudu ya juya, yayi gudu na almost 12min sanan yakai bakin beach din idanunshi akan bodyguards dinshi guda biyu dake nan bakin beach din a tsaye inda ya barsu suna sanye da bakaken suit daya yarike babban bargo dayan kuma bai rike komiba, karasawa sukayi bakin ruwan tun kafin yay parking, parking yayi yafito batare daya kallesu ba yafara tafiya, wanda ke rike da bargon ne ya mikamai. "Sir ur Dad asked us to give you blanket to cover yourbody" cikin fushi batare daya kalli bargon ba yace "I don't want it" yay gaba abinshi suka juya da sauri suna binshi agaban wani babban jeep yabude ya shiga baya ya zauna atishawa yayi da sauri guard din daya iso wajen ya mikamai yace "Sir please take it u are catching cold already" wani mugun kallo ya watsamai yace "get in the car and drive me home or I leave the car for you Mr" da sauri duk suka shiga, tada motar yayi sukaja suka fita daga wurin lumshe ido yayi, sosai yaji yanajin sanyi kuma baiso yace sukashe AC motan kaman Dad yay winning kenan ai dayace sanyi zai shigeshi he was so happy earlier but Dad ruin everything ga wanan mayun security dake tare dashi, wani dan wahalallen tsaki yaja ya gyara zama ya rungume hannayenshi, wajen 20min drive sukayi sukai parking agaban wani hadadden gida, da sauri suka fita kafin ma subude mai kofa ya bude da kanshi ya watsa musu harara ya wuce yay cikin gida yabude door yashiga.

Babu kowa a hadadden palor stairs yahau da sauri yana atishawa ya bude wani hadadden daki da komi na ciki yakenan sky blue color, zama yayi kan Royal bed yanajin sanyi har cikin kashin shi hannu shi ya mika zaidau remote din AC dake kan pillow dake kan gadon wayarshi ya shiga ringing daukan remote din yayi ya kashe AC kafin yaciro wayan daga aljihu daure fuska yayi ganin sunan Dad, kaman wanda akace dole yay picking call din ganin wayar na neman katsewa ya kai kunnen shi yay shiru batare dayace komiba cikin kwantar da murya mutumin yace "yanzu fushi kake da Dadyn ka ko Gadanga na?" shiru yayi baice komi ba ahankali mutumin yace "haba Ali Gadanka gusar yaki, yaron baban shi tashi kadau rigan sanyi kasaka kaji Mr Aliyu Adult" dan murmushi yayi dan yasan cikeda tsokana Abban shi yafadi haka. "yauwa tashi to kasaka kaji" "uhm" yafadi yana sauka daga kan gadon yakarasa gaban wani mirror wardrobe dake bangon dakin yana kallon kanshi har hancinshi yay jajir sabida sanyi wani boturi ya danna kofar wardrobe din yabude ya ijiye wayan kan stool din wajen yaciro wata dark sweater mai kyau yasaka tamai mugun kyau yakara fito da hasken fatarshi, daukan wayar yayi yamaida kunenshi Daddy yace "kasaka sweater?" gyadamai kai yayi yace "eh" "yauwa ko kaifa kaga yanzu sanyin zai ragu, stop acting stubborn kaji Aliyu na, I know you sama d kowa, I know how fragile you are bakason iska dayawa, abu kadan mura mura, you need to take care of yourself okay saisa ma nace zakadawo Nigeria kawai ko hankalina ya kwanta" kaman zaiyi kuka yace "Dadddd" "common don't Daddy me my friend" cikin muryanshi mai bala'in dadi da taushi yace "Nigeria weather is super harsh Dad, I don't wanna come back please nika kyaleni" cikin Dan kakkausar murya Dady yace "nakiya, anki a kyaleka din" saikuma yay shiru kafin yadan sassautar da murya yace "haba Gadanga na, eh babana, mai sunan Abba, kafa gama project dinka kagama komi, I've missed you badly, kadawo gida lemme arrange everything idan akwai any available flight gobe kabiyo kadawo gida inda cibiyarka take, kana dawowa kaga saimu nema maka mata kai aure abinka ka ijiye iyali ko Son?" kwanciya yayi akan gadon yaja bargo ya lulluba tareda lumshe ido ya gyara wayan akan kunenshi yace "nikadena min maganan aure, idan shizakamin bazan ma dawoba, women are so lousy I don't think I can ever live with one" da sauri Dad yace "no, no bashi zanma ba, muma bar maganan, please kadawo kaji" ahankali yace "alright but not tomorrow akwai abunda zanyi saidai next tomorrow or rather on Friday kawai" "har Friday, yaufa Tuesday Aliyu, kana nufin nan da kwana uku, please on Thursday kadawo kaji Gadanga na" shiru yadanyi saikuma ya nisa yace "ok Dad" murmushi sosai baban nashi yayi har hakan yasa shima ya murmusa jin mahaifinshi na murna sabida ya yarda zai dawo. "kaci pancake yau kuwa?" yatsine fuska yayi yace "naay" "why? Maiya hanaka cin fav dinka?" kaman zaiyi kuka yace "bakai kabatamin raiba you ruin my day Dad" cikin dan tashin hankali yace "nizaka ma shairi Gadanga?" dan murmushi yayi batare dayace komiba. "karka damu idan kadawo akwai wani pastry shop dat makes d best pancakes, I can testify to that dan ranan danaci pancakes dinsu
saida tastbud din yay rawa zan aika a sayoma harda Valvet cake ma zakaci kaci har sai kaci kature yafi na California ku dadi I promise Nigeria yanzu mun cigaba muma" dan murmushi yayi yana lumshe ido, murya chan kasa agajiye yace "okay Dady" "you are sleepy ko wanan danaji muryanka chan kasa" gyadamai kai yayi yace "yeah" "alright Son, sleep kaji please allow your bodyguards to do their job kaji Son, am paying them just to take care of you, you are too fragile so kadena hanasu kula dakai, now sleep nima am about to enter Chamber, I love you" murya chan ciki yana kara nitsewa cikin gado cikeda gajiya kaman wanda yay dako yace "love you too Dad" katse wayar baban nashi yayi tsabagen gajiyan dayayi yakasa janye wayar daga kunenshi ya juya ya kara narkewa cikin bargo bacci mai shegen dadi yay awon gaba dashi.

_Suleja, Nigeria._

Dan babban falone dake shimfide da ledan daki brown mai gida gida, ga saitin kujeru na daidai rufin asiri masha Allah dakin sai kamshin turaren wuta yake ko ina tsaf tsaf babu ko digon datti, wata matace a tsakar dakin dake kan dadduma tana salla, kana ganinta kasan tadan kwan biyu a duniya tanada jiki sosai, sallame sallan tayi cikeda natsuwa sanan ta daga kai ta kalli agogon bangon dakin tana istigifari, karfe 9:08AM, karfe tara harda minti takwas na safe, tashi tayi daga kan dadduman tadau charbinta tarike tafara tafiya ta doshi kofan fita daga dakin, yaye labule tayi ta leko tsakar gidan da maganganu kasa kasa ketashi wata matace zaune kan tabarma a tsakar gidan babu hijabi a jikinta, kafafun ta da aka zana mata bakin lalle irin na amare dayay mugun kyau ta daura kafafun kan wata yar pillow datai bakin kirin wacce kana ganinta kasan na lalle ne, ta mikar da kafafun anja skirt dinta sama har zuwa wajen gwuiwanta sabida lallen, sai kuma hannu ta na haggu da shima ta mikar dan yasha iska shima ba'a gama da zana mata shiba dan baima soma shirin bushewaba, sai kuma dayan hanunta da ke hannun mai zanen lallen tana zana mata. "Aneesah" da sauri yarinya data dukufa tana zanama matan lalle ta dago kanta da sauri ta waigo, bakar yarinya ce full definition of melanin skin, wani irin glowing dark skin take dashi dake shining bana wasaba, giranta a cike da gashin gira har giran na neman hadewa dan in between space din two giran ma gashine sai dan tawadiyan Allah a tsakiyansu dayay ma fuskarta kyau bana wasaba, tanada dogon hanci sosai kaman karas, kwayan idanunta farare fat kaman madara sabida hasken su, gashin idanunta bakake dogaye wara wara dasu, sai dan lips dinta dakenan pink sosai dayakara haska fuskarta, gefen fuskarta dogayen sajene lub lub a kwance, kanta sanye da bakin hula, kunenta babu dan kunne sai gashin keyanta dakenan a kwance lub lub wasu sunyi coils, kana ganin yarinyar kasan she's so hairy, tana sanye da wata bakar rigan atampa. "Aneesah" Mahaifiyar tata takara kiranta akaro na biyu tana fitowa daga dakin gabaki daya rike da charbin hanunta ta tsaya agaban dakin, da sauri ta ware manyan fararen idanunta ta kalli Maman nata tace "na'am Ammi" "bakigama lallen ba kinsan karfe nawa kuwa tara harda yan kai" zaro ido tayi dan batasan lokaci yaja hakaba adan rude tace "innalillahi Ammi nayi latti, Madam yau zatamin fada, yanzun nan zan gama mata" tai maganan tana gyara xaman lallen a hanunta tacigaba da zanama matar lalle agurguje, ganin yanda take sauri yasa Ammi tace "ki kwantar da hankalinki kimata atsanake kar ayi shirme" gyadama mahaifiyar nata kai tayi tacigaba dayi anatse, komawa daki Ammi tayi dan xigaba da zikirinta.
Ko 5min bata karaba tagama yimata lallen tai murmushi tana kallon hannun tace "ki zauna anan yanzun nan zai bushe, zan jamiki ruwan dazaki wanke dashi inya bushe, ni yanzu wanka zanyi natafi wurin aiki" murmushi matar tayi tana kara kallon lallen nata dayay mata kyau bana wasaba mussamman ma tasan idan Baban Aisha yadawo daga lagos yau saiya yaba lallen shima dan yanason lalle shi arayuwanshi, tashi tayi a gurguje tai wajen rijiya ta kwalama Mamanta kira. "Ammi nagama zanja ruwa nai wanke wanken sainai wanka natafi" Ammi dake kan dadduma tana jan charbi tace "kibar wanke wanken zanyi, ja ruwa kawai kitafi wajen aikin ki kinyi latti dayawa" guga tadauka tazura a rijiyan tace "tom Ammi" a...


Read / Download A TSAKANKANIN SOYAYYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album